Sarauniyar Zuciya Hausa Novel Complete
SARAUNIYAR ZUCIYA
(Queen of the heart)
written by
M. Jaruma Luxury
Free page 1
Tana ‘karasowa harabar gidan ta taka birki da ‘karfi, kashe motar ta yi ta fito…..Samha ‘yar shekara ashirin da biyu a duniya fara ce doguwa, amma ba doguwa sosai ba, bata da ‘kiba kuma Ba za a ce da ita ramamma ba, yanayin halittan fuskarta na matukar daukar hankali, hakama yanayin dirin halittar jikinta, sanye take da English blouse golden color daya bi jikinta ya yi matukar karbarta, ta yi packing gashinta a tsakiya da wani kibiya (Chinese style) fuskarta na dauke da makeup na musamman daya ‘kara fito da kyawunta,….tafiya take yi takalminta na bayar da sauti ‘kwas ‘kwas har ta iso main falo na gidan, Inda Baba Surajo da Haj Binta zaune suna tattaunawa….yanayin data shigo ta tsaya tana kallonsu tana huci yasa suma suka kafe ta da ido…Lokaci daya kuma ta marairaice ta yi yanayin tausayi tana kallon Baba Suraj ta shiga fadin “Daddy, ya zaka yi min haka, daga wurin birthday din ‘kawata Zarah nake, sai kirari ake min ‘yar Sanator, zan yi amfani da kudin account dina na yi manni yaki fita, mutane a wurin sai dariya suke min, wasu har nuna ni suke yi suna fadin yarinyar stinging Sanator, shine na kira bank na yi musu complain, shine suka ce Wai ai kai ka yi umarnin da a yi min frozen account, why Daddy? Please Daddy zaka iya min kowani hukunci amma don Allah a bude min account dina
Akwai Irinsu na Oum Hairan Complete Novel
Wani kallon sama da ‘kasa Haj Binta ta bita dashi sannan ta ce Samha why are you so arrogant? Your Dad is just a common Sanator not a president, ya kamata ki sakko da kanki ‘kasa
Cuno baki Samha ta yi cikin shagwaba ta ce mummy kenan kina sane Daddy ya yi min haka?
Mikewa Baba Surajo ya yi yana fadin “Akwai offern daya shigo hannuna na Mortage bank, Idan kina bukata let me know, sai ki je ki yi interview, Idan kin yi nasara zaki fara yin aiki dasu”
Cikin tsananin mamaki Samha ta ce what! Daddy don Allah kada ka yi min haka……bai saurareta ba ya bar falon, komawa ta yi kan Haj Binta “Mummy don Allah kisa baki Daddy ya bude min account dina” wani harara ta watsa mata “is better ki ‘bace min da gani kona miki rashin mutunci wallahi” cikin kuka Samha tabar falon
Dakinta ta shigo ta fada kan gado ta cigaba da kuka, sai da ta yi kuka mai isanta sannan ta tashi zaune ta shiga tunanin wani hanya zata bi domin Baba Sarajo ya bude mata account dinta, don ita a gaskiya ba za ta iya aiki a mortage bank ba, nawane zasu dinga biyanta? tasan da allowance da salary da komai ba zai wuce dubu dari uku zuwa dubu dari hudu ba, me zasu mata? Ita da a sati take kashe kudi kusan dubu dari da hamsin zuwa dubu dari biyu…..
****
Haidar shi kadai a cikin harabar gidan yana kaiwa da komowa (Jogging) Baba Lamido ne ya fito cikin harabar gidan, ganin Haidar na jogging yasa ya yi smile sannan ya ‘karasa wurinsa yana fadin “Is too late ka je ka kwanta”
Dakatawa Haidar ya yi yana kallon Baba Lamido sannan ya ce okay Dad
Jerawa suka yi zuwa ciki, Baba Lamido na fadin “kwana nawa ya rage maka ka koma England?”
“Kwana uku ya rage?”
Baba Lamido ya ce that is great, gobe Insha Allah zamu yi sallama da kai, zaka tafi Abuja wurin Babanka Surajo, daga can zaka yi booking flight zuwa England
Zaro ido Haidar ya yi ya ce Daddy gobe kuma? Zuwa Abuja gidansu Baba Surajo baya cikin tsarina a yanzu
Tsayawa Baba Lamido ya yi yana fuskantar Haidar sannan ya ce yau muka yi waya dashi yake nuna min rashin jin dadinsa akan shekaru hudu baka ‘kasar nan, yanzu daka shigo ka shafe kusan 3weeks ko kiransa baka yi ka gaidashi ba, kuma gaskiyarsa ne, bani da wanda ya fishi, yadda nake babanka, shima babanka ne, dani dashi uwarmu daya ubanmu daya
Wani ajiyar zuciya Haidar ya yi ya ce okay Daddy zan tafi amma zuwa jibi
“No, na riga dana fada mishi gobe zaka zo, ba zan zama ‘karamin mutum ba wurin yin magana biyu, akwai ‘yan uwanka a can, Ina son ku ‘kara ‘kulla zumunci sosai, ku tattauna akan rayuwar duniya
Rike ‘kugu Haidar yai, ya yi shuru na wani lokaci sannan ya ce Tom shikenan, Allah ya kaimu goben
“Ameen Ameen my son” Haka suka cigaba da tattaunawa a tsakaninsu kamin daga ‘karshe Baba Lamido ya wuce ‘bangarensa, shima Haidar ya wuce dakinsa
Washegari wuraren sha biyu Haidar ya kammala shirinsa na tafiya, mahaifiyarsa Haj Aysha ta ‘kasa daurewa sai da ‘kwallan daya cika a idanunta ya sakko kan kumatunta, rike hannunsa ta yi tana fadin “my son ka kula min da kanka don Allah, addu’arta zata cigaba da bibiyarka a duk inda kake, inshaAllah burinmu zai cika
Kai hannunsa ya yi ya share mata hawaye “mummy Idan har zan cigaba da ganin hawayenki babu inda zan tafi”
Nasreem goge hawayenta ta yi ta ce Hanma Haidar Allah ya tsare, zamu yi missing dinka
Baba Lamido ya ce kai Haidar mu tafi na aje ka airport, Idan ka biye ta nasu babu abinda zaka tabika…..Haj Aysha da Nasreem na tsaye suna kuka, Haidar da Baba Lamido suka shiga mota suka wuce
Kai tsaye airport suka wuce, Baba Lamido bai bar airport ba har sai da jirgin su Haidar ya tashi, jiki a sanyaye ya je ya shiga motarsa ya ja ya wuce
****
Cikin ‘kankanin lokaci jirgi ya sauka a Abuja, inda babu ‘bata lokaci Direban da yazo daukarsa ya daukesa zuwa katafaren gidan Baba Suraj
Gida ya dau farin ciki sosai da ganin isowar Haidar, kadama a ce Baba Suraj, ji ya yi kamar ya hadiye shi tsabar soyayya
Haj Binta smile ta yi tana kallon Haidar ta ce tabarakallah, ka ‘kara kyau sosai, dakyar na iya ganeka
Ya Mansur ya ce gaskiya ‘kanin nawa masha Allah
Smile Haidar ya yi sannan ya ce ban ga sauran ‘yan uwan nawa ba, Hamma Mansur kadai na gani
Baba Surajo ya ce dan uwanka Adamu na Malaysia yana matakin ‘karshe a jami’a, ‘yar uwarka Samha tun jiya take ‘kunshe a dakinta wai fushi take yi, sai Saleem shi kuma yana wurin abokanshi, zai dawo anjima
“Amma meyasa ‘yar uwa Samha take fushi?” Haidar ya yi maganar yana kallon Baba Surajo
Ya Mansur ya ce manta da wannan ‘kanwar taka, matsalolinta nada yawa
Smile Haidar ya yi ya ce Haba Hamma Mansur, bai kamata ‘kanwata ta kasance cikin fushi ba, yakamata ta yi farin ciki, Ina take yanzu?
Haj Binta ta ce bata jin magana, kawai ka fita sha’aninta, Idan ta ga babu wanda ya tankata dole zata dawo dai dai
Baba Surajo yana kallon Haj Binta ya ce a’a ki ‘kyaleshi ya je ya rarrashi ‘kanwarsa……ya mayar da kallonsa kan Haidar ya ce jeka sameta
Haj Binta ta ce yakamata ya fara huce gajiya, ya ci abinci ya yi wanka, sai komai ya biyo baya
Mikewa Haidar ya yi yana fadin “i have to pamper my sister first, Ina dakinta yake?”
Baba Surajo ya ce ka haura matakalan bene na ‘bangaren dama, daki na farko shine nata, tana ciki
Haidar ya ce okay sannan ya yi hanyar direction din da Baba Surajo ya bashi
****
Samha zaune kan Sofan dakinta tana waya da ‘kawarta Zarah, cikin tsananin damuwa take fadin “Zarah ki bani shawara, menene zanyi? Daddyna dagaske yake yi, babu wanda ya damu dani, kowa ya yi banza dani” hankalinta komawa ya yi kan turo ‘kofar dakin da aka yi, Haidar ne ya shigo cikin sallama, bata amsa sallamarsa ba, sai dai ta kafe shi da manyan idanunta masu daukar hankali, yanayin kallon da take binshi dashi ya tabbatar da bata ganeshi ba…cire waya ta yi daga kunnanta tana fadin “Zarah mu yi waya anjima” tsinke wayar ta yi tana ‘kara kallon Haidar da shima kallonta yake yi, ya ‘kasa cewa komai sai binta yake yi da kallo, ta sauya ba yadda ya santa a baya ba, ta ‘kara girma, hasken fatanta ya ‘karu, yanayin shigarta ya nuna yanzu ita babban yarinya ce…hakika ya ji wani bakon yanayi a tattare dashi
“Excuse me” Samha ta fada tana kallon Haidar
Smile ya yi batare da ya ce komai ba, ‘karasawa ya yi ya zauna kan table din dake fuskantar ta, yanzu idanunsa na cikin nata, ‘kwarjininsa ya daki zuciyarta….sai yanzu ta iya gane shi, bude baki ta yi da ‘kyar ta ce Hamma Haidar
Tsiririn smile ya yi ya ce na yi tunanin ba za ki gane ni ba ai
Shuru Samha ta yi bata ‘kara cewa komai ba, saukar da idanunta ta yi ‘kasa
“‘Yar uwa Samha kina da kyau sosai, ba wai Ina fada miki bane a iya fatar baki, zuciyata ce take magana da kanta, sai dai kash kina ‘bata kyawunki da fushi, baki san idan kin yi murmushi ba kin fi kyau” Jin kalamansa ta yi sun bigi zuciyarta, dago idanunta ta yi ta kalli nashi idanun sannan ta ‘kara sauke su ‘kasa batare da annuri ya baiyana a fuskarta ba
“Ki dago idanunki Samha ki kalleni, Ina son na tantance kyawunki da sarauniyar England, a gaskiya kin fita kyau” duk yadda Samha taso daurewa ta ‘kasa sai da wani smile ya baiyana a gefen fuskarta
ya ce wow! What a beautiful smile, tunda nake ban taba ganin murmushi irin wannan ba, don Allah ki sake yi min na gani, ki sake yi min nagani kin ji ‘yar uwata
Smile yaki barin fuskar Samha, har sai da hakoranta suka baiyana a fili
“Yauwa ko kefa, amma taya zaki zo ki ‘kunshe kanki a daki Wai kina fushi, yanzu ki tashi muje mu ci abinci, daga nan Sai ki dauke ni yawo ki nuna min garin Abuja” kai ‘karshen maganar ya yi yana tashi daga zaune
Langwabe kai ta yi ta shiga magana cikin sanyin murya da shagwaba da yasa ya ‘kara jinshi cikin wani yanayi na daban “nifa babu ruwana da Daddy da mummy” ya ‘kasa cewa komai sai aikin bin ‘karamin bakinta da kallo, ‘kokartawa ya yi ya danne zuciyarsa sannan ya ce ba dole sai nasan meyasa kike fushi dasu ba amma ai kinje islamiyya, Kinsan dai fushi da iyaye babu kyau, trust me kafin na wuce zan daidaita komai, ki kwantar da hankalinki ‘yar ‘kanwata, tashi muje ki ci abinci
Samha ta dan jima a zaune Kamin ta tashi, ‘kare mata kallo Haidar ya ‘kara yi, “Masha Allah” ya fadi a zuciyarsa, gaba ta yi yana biye da ita a bayanshi…da sauri ya dauke kanshi daga kallon mazaunanta, ji ya yi tsigar jikinsa na tashi, zuciyarsa na harbawa
Comment, like and share fisabilillahi
Let meet in page 2
Jarumarku ce
SARAUNIYAR ZUCIYA
(Queen of the heart)
written by
M. Jaruma Luxury
Free page 2
Haidar ya yi iya ‘kokarinsa a kan Samha wajen dawo da murmushi fuskarta, duk yadda taso ta shiga damuwa sai yasa ta murmushi….duka family sun hadu a dining domin yin lunch, ana wasa da dariya da raha abin dai gwanin ban sha’awa, Samha kamar ba ita ce take fushi ba, duk ta sake sai hira ake yi ana dariya……bayan kammala yin lunch, Samha hanyar dakinta ta yi zata wuce, dakatawa ta yi sanadiyyan kiran sunanta da Haidar ya yi, juyowa ta yi ta sauke idanunta a cikin sexy eyes dinshi, ‘karasawa ya yi gab da ita ya tsaya sannan ya ce ki shirya zuwa yamma, Ina son ki nuna min garin Abuja
Smile ta yi ta ce Tom Hamma, Allah ya kaimu
“Ameen” ya fada….bata jira ta ji me zai ‘kara fada ba, ta juya ta yi tafiyarta, binta ya yi da kallo har sai data ‘bace daga idanunsa, har yanzu ya ‘kasa yarda da abinda zuciyarsa take raya masa, tunda Allah ya halichche shi bai taba jin wata mace a zuciyarsa ba, a kullum ikirarinsa ‘kwallan ‘kafa shine abar ‘kaunarsa, bai taba mafarkin akwai ranar da zai ji sauyin yanayi a cikin rayuwarsa ba
Masaukinsa ya wuce, bayi ya shiga ya watsa ruwa, ya yi alwala sannan ya fito ya sanya jallabiyarsa ya yi ‘kasaru, bayan ya idar ya fada kan gado amma ya ‘kasa rintsawa, koya ya rufe ido Samha kadai yake gani, har yanzu ya ‘kasa gasgata zuciyarsa a kan ‘kaunarta yake yi, haka ya kasance cikin wannan yanayin
****
5:00PM
Haidar shiryawa ya yi cikin ‘kananun kaya da suka yi matukar amsar jikinsa, feshe jikinsa ya yi da turaruka sannan ya dauki wayayinsa ya fice…..kai tsaye dakin Samha ya wuce, daga ‘kofar dakin ya tsaya ya shiga knocking a hankali
Ta ‘bangaren Samha kwance take kan gado rike da wayarta tana chatting da ‘kawayenta, hankalinta ya kai kan knocking dake shigaowa dakin, ta jima tana kallon ‘kofar kafin ta sauka daga kan gadon ta ‘karasa ta bude ‘kofar, ganin Haidar tsaye yasa ta saki wani lallausar smile sannan ta ce Hamma Haidar
A kowani dakika ‘kara jinta yake a cikin zuciyarsa, “na ga baki shirya ba, kin manta na fada miki zaki fita dani ki nuna min gari” dafa kai tayi tana fadin “oh! Wallahi na manta, to bari na shirya yanzu na fito mu wuce”
“To shikenan, zan jiraki a main palour” ciki ta koma, shi kuma ya dawo main palour ya zauna yana jiranta….ya kai kusan minti talatin yana jiranta kamin kunnuwansa suka fara jiyo ‘karar takun takalmin “kwas kwas kwas” Da sauri ya kai kallonsa direction din da yake jiyo sautin
Ta yi matukar kyau cikin bakar Abaya, babu kwalliya a fuskarta, mayafin abayan ta yafa a kanta, sai sanyayyar ‘kamshin turarenta mai dadada zuciya
Mikewa ya yi a dai dai lokacin data ‘karaso wurinshi tana fadin “Hamma Haidar Na gama shiryawa, sai mu tafi”
“Kin fadawa Mummy zamu fita? Jeki fada mata sai ki dawo mu tafi”
Yatsine fuska ta yi ta ce nifa har yanzu ban gama fushi dasu ba
“Ai na fada miki ba’a fushi da iyaye, ki je ki fada mata tukun, Ina jiranki” babu yadda Samha ta iya, yana tsaye yana jiranta tabar main palour, bada dadewa sai gata ta dawo
Yana kallonta ya ce kin fada mata?
“Eh, ta ce sai mun dawo”
“Tom ya yi kyau muje”
Jerawa suka yi suka fita, harabar aje motoci suka ‘karasa, Samha ta bude motarta ‘bangaren Direba ta shiga ta zauna, Haidar ya shiga dayan bangaren, Samha ta ja motar suka fice
Hadadden wurin hutawa Samha ta kawo su, wurin na musamman ne, babu mutane da yawa, kowa harkan gabansa yake yi, shukokin furenni ta ko’ina masu daukar hankali, daga gefe kuma wani ‘kayataccen pool ne….Haidar da Samha ‘karasawa suka yi suka tsaya a bakin pool din suna hira
“Kin iya ruwa kuwa?” Haidar ya yi tambayar yana kallon Samha
Girgiza kai ta yi tana fadin “No, I don’t know how to swim, amma kai ka iya?”
“Yes, na iya sosai, ni da abokaina muna zuwa yin swimming duk sunday”
“I thought kai da Auntynmu kake zuwa” Samha yin maganar ta yi tana smile, wani kallo ya kai mata yana fadin “ji bakinta Sai ka ce da Auntynmu kake zuwa” ‘karamin dariya ta shiga yi ‘kafarta ya yi baya, bata ankara ba ta ji ta fada cikin pool, far far ta fara yi tana neman agaji….Zaro ido Haidar ya yi, bai tsaya ‘bata lokaci ba yabi bayanta
Kamota ya yi, ya cincibota cikin hannusa sannan suka fito, sai kuka take yi tana ajiyar zuciya da ‘kyar, ta langwabe a jikinsa, taki yarda ta tsaya a kan ‘kafufuwanta….wani yarrr yake ji na ratsa ilahirin jikinsa gabadaya, ya ‘kasa dauke idanunsa daka kallon ‘karamin bakinta, yanayin sautin kukan da take yi na ‘kara tayar masa da hankali, wasu hawaye na fita daga sexy eyes dinta yana bin gefen idanunta….a hankali take furta “Hamma Haidar mubar nan wurin don Allah”
Haidar ya ce sorry ‘yar uwa Samha, bai kamata mu koma gida haka ba, sanyi zai kamaki, bari na kama daki, na ga boutique a waje, zan samo miki wasu kayan sai ki sauya
Bata ce komai ba sai ‘kara langwabe masa take yi a jiki cikin tsananin shagwaba, yanzun ji ya yi breasts dinta a ‘kirjinsa, kai kallonsa ya yi ‘kirjinta, kayanta duk sun manne a jikinta, shatin manyan breast dinta duk sun fito waje, ya ‘kasa dauke idanunsa, wani abu ya shiga ji tun daga tafin ‘kafarsa har tsakiyar kanshi….Cikin dashashshiyar murya ya shiga fadin “muje ki sauya kaya, mu wuce gida” cuno baki ta yi tana fadin “I can’t walk with my legs, ba zan iya tafiya da ‘kafafuna ba Hamma”
“To ya kike so na yi? Ki daure ki taka, sanyi na kamaki”
“Ni ba zan iya tafiya da kai na ba” tsayawa ya yi yana kallonta na wani lokaci kamin yasa hannu ya cincibeta kamar jinjira, bude idanunta ta yi suka hada ido, mayar da idanunta ta yi ta rufe
A haka Haidar ya ‘karasa reception yana rike da Samha, babu ‘bata lokaci ya kama daki….yana Isa dakin daya kama ya dire Samha a kan Sofan dake dakin yana fadin “bari na je na sama miki kayan da zaki sauya” bai jira ya ji me zata ce ba ya yi ficewarsa, bayan fitarsa ta tashi zaune tana Smile, zuciyarta sai wani ‘karsashi take yi, a hankali take ‘kara tuno yadda Haidar ya tsamota daga cikin pool, da yadda ya cincibota kamar jinjira ya shigo da ita daki, jawo filon sofa ta yi ta rungume a ‘kirjinta tana smile….ta kai tsawon lokaci a haka kamin ta tashi, bayi ta shiga ta tube kayan jikinta gabadaya, daukar farin tawul ta yi ta daura, tsawon tawul din iya rabin cinyarta ya tsaya, cire ringbom din data cifke gashinta ta yi, ta saki gashin ya kwanta a gadon baya….fitowa ta yi rike da wani ‘karamin tawul a hannunta ta je ta zauna a kujeran dake gaban mirrow ta shiga goge gashin kanta
Haidar budo ‘kofa ya yi ya shigo cikin sallama rike da ledar boutique a hannunsa, juyowan da zai yi ya kafe idanunsa a kan Samha, ta cikin madubi ta ganshi ya yi tsaye yana kallonta, murmushi ta yi sannan ta mike, juyowa ta yi tana kallonshi gami da cuno baki tana magana cikin shagawa “Gashina yaki bushewa”
Bai iya ce mata komai ba, wani kallo ya shiga binta dashi tun daga ‘kafafunta, ya zo kan manyan fararen cinyoyinta masu matukar daukar hankali, ji yake kamar yaje ya rungumesu, ya ‘karasa da kallonsa kan ‘kirjinta, nonuwanta sunyi cirko cirko a cikin tawul din da take daure dashi, a take idanunsa suka sauya kamanni, hankalinsa na ‘kokarin dishewa…..Cikin shagwaba ta ‘karaso gabanshi ta tsaya, ‘dai ‘dai ta yi da ido tana fadin “Hamma Haidar baka ji abinda na ce ba, gashina yaki ya bushe, hannuna ya gaji, gashi ka goge min” kai ‘karshen maganar ta yi tana mika masa tawul…..hannunsa na rawa ya amsa
“Tom Hamma mu je ka goge min” kamar wawa ya bi bayanta, kai tsaye zuwa ta yi ta zauna bakin gado tana kallonsa, shima kallonta yake yi, babu abinda zuciyarsa bata fada masa…yana daga tsaye ya shiga goge mata gashin, bude baki ya yi da ‘kyar yana fadin “baya bushewa da wuri”
“Eh, da akwai hand dryer da yanzu ya bushe ai”
“To ba sai aje a siyo hand dryern ba”
“A’a ba sai an sayo ba, Ina dasu a gida” aje tawul Haidar ya yi kan gado yana fadin “je ki saka kaya mu tafi gida, sai ki busar da gashin a can” langwabe kai ta yi cikin shagwaba ta ce A’a ba yanzu ba, ni bacci ma nake ji…kai ‘karshen maganar ta yi tana kwanciya
Kawar da kai ya yi da sauri daga kallonta yana fadin “please ki tashi muje, can is more comfortable” gyara kwanciyarta ta yi tana fadin “please Hamma ka barni na yi bacci kona awa daya ne, please don Allah
Shuru ya yi bai ‘kara cewa komai ba, ledar boutique din daya shigo dashi ya dauka, fito da sabon kayan daya siyawa kanshi ya yi, ya shiga bayi, ya cire na jikinsa ya saka sabo sannan ya fito
Kai kallonsa ya yi kan Samha data rufe ido tana bacci, zuciyarsa na raya masa ya ‘karasa wurinta, cinyoyinta masu daukar hankali sai ‘kara jan hankalinsa suke…..
Comments, likes and shares fisabilillahi
Mu hadu a free page 3
Jarumarku ce….