Munafukin Miji Hausa Novel Complete

Munafukin Miji Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

MUNAFUKIN MIJI

True life story

 

 

SHIMFIƊA

Free book

 

Wattpad: Nimcyluv

 

Wani irin murɗawa mararta ta yi, kafin ɗan dake cikinta ya samu damar juyawa daga hango zuwa dama, dalilin wani rikitaccen tashin hankali daya tattaro waje guda ya ruftuwa zuciyarta wacce take a ƙudundune tsayin shekaru ta tsaya mata a tsakiya, baƙar fuskarta sai maiƙo take kamar an yi ɓarin baƙin mai a saman kwalta.

“Zaki kashe ni,

da gaske zaki kashe ni Mar…”

Sauran maganganun suka tsaya mata cur a maƙoshi kamar tsayi yiwuwar bushashshen itace. A gigice kuma ta yi wurgi da wayar dake maƙale a hannunta ƙirar Infinix ban da sauke ajjiyar zuciya da jan numfashi babu abinda take yi, mararta ta ɗaure tamau kamar mai jin fitsari. Bata so ko ƙaunar juyawa ta sake ganin mummunan photon dake saman fuskar wayar ƙara gani na nufin wani abu, hakan daidai yake da bugawar zuciyarta wacce zata iya kawo sanadin ƙarshen numfashinta.

Jawaheer Hausa Novels Complete

Hannu Maridiyya ta sanya tare da riƙe kafaɗun Ridayya, da son dawo da ita cikin nutsuwarta ta riga ta fahimci a zauce take haukata kanta take son yi da gaske akan ɗa namiji.

“Kin yi wawta Ridha, lallai kin yi wawta soyayya ta rufe miki ido, kin cilla zuciyarki inda ba a maraba da ita, ba a gani kima da darajarta, inda ba a san muhimmacin ta ba, kin tafka kuskure na tsayin rayuwarki wanda zai ta yin motsi a zuciyarki, kin bada soyayyarki wajan da ba a son ƙimar SO ba, ba a kuma gane bambanci matar aure da budurwa ba, matar halak da wacce take waje sakakkiyya!”

Girgiza kai kawai Ridha ke yi cikin tsanar kalaman Maridiyya wanda suke kamar saukar dalma a zuciyarta.

“Baƙin ciki kike mini Maridiyya? Ni kike ma baƙin da zaman gidan mijina Diyya?” Maridiyya ta girgiza kai cike da tausayin Ridha, wani abu na motsa mata a zuciya, da son sanyata cikin zullumi har take jin tamkar ta rabu da Ridha domin ta riga da ta yi nisa, wanda ba zata iya jin duk kiranyen da za a yi mata ba, haƙurin Ridha daban yake lallai da gaske zata ci ribar hakan.

Maridiyya ta sauke wahalallan numfashi wanda take riƙe da shi tsayin daƙiƙo kafin ta ce

“Ridha ba zaki yarda photon mijinki Zameer ne wannan ba? Baki yarda shi ɗin ne riƙe da hannun mace ba?….,”

 

“Idan shi ne mene ya faru? Kina da matsala da haka ɗin ne?” Ridha ta dakatar da Maridiyya da faɗin hakan, tare da buƙatar jin meye matsalarta da rayuwar aurenta a gidan mijinta? Murmushin takaici Maridiyya ta yi, ta gane Ridha makauniyyar gaske ce, makanta biyu ta haɗe mata, data ido da zuciya!

“Ni kam bani da matsala, ina son taimaka miki wajan fiddoki daga kabarin da kika rufe kan ki ne, Ridha ba damuwata macen dake photo tare da mijinki bane, gigitata bai huce ganin yarinyar da Zameer ya kawo miki cikin gidanki matsayin ƙanwar miji ba, ƙanwar shi; ki duba da kyau Riddahh, duba da idanunki wanda suke aiki ba makafin ba”

 

Ridayya ta ƙurawa photon ido, da gaske abin begenta ne, rayuwarta ne, farin cikinta ne, tsaginta ne, bugun numfashinta ne, mutumin data sadaukar da abubuwa da yawa saboda shi, ZAMEER! mijinta ne a photon. Ta bi fuskarsa dake shimfiɗe da lallausan murmushin da ba ko yaushe take ganinsa da shi ba, gajiyayyun idanun nan nasa masu narkar da raunatacciyar zuciyarta zube akan yarinyar dake gefen shi, yadda idanunsa ke kanta zai fasaltawa mai kallon photon gane wani irin ɓoyayyen sirri dake cikin su, sirrin dako shi kansa Zameer bai sani ba, baya da tabbaci akai,bai kuma san komai dan gane da hakan ba, akwai zalama da muradi a idanun wanda kai tsaye yanayinsu ya bayyana abin da zuciyarsa ke rufewa, yarinyar kusa da shi kuma ta ɗan shagwaɓe fuska tana kallon hannunsu dake sarƙafe da juna.

 

Ridayya ji ta yi kamar fitsarin dake maƙale a mararta na bin cinyoyinta, numfashinta ya fara kai komo a karo na biyu! Ta sake cilli da wayar tana dafe cikinta daya girma, wanda yake gab da shiga watan haihuwa.

“Karki nemi haukata ni Maridiyya, karki saka na haife abin da ke cikina ba tare da cikar wa’adinsa ba, me mijina ya yi muku? Da kuke son tilasta ni naga baƙin shi? Ina son shi, ku fahimta ku barni,ku barni haka nan,ku barni Maridiyya….”

Ridayya ta daddafe kanta dake juyawa ta kasa gane ainahin meke damunta. Bata son ma ta gane ɗin balle ta samu rauni da ji da motsin son Zameer.

“No man succeeds without a good woman behind him. Wife or Mother, if it’s both, he is twice blessed” Maridiyya ta faɗa Idanunta cike da hawaye.

 

RIDAYYA! Kallon Maridiyya kawai take a makake, a yadda ƙirjinta ke ɗagawa yana bada ƙyakkyawan sautin da kai tsaye yake samun masauki a kunnen Diyya, ya tabbatar mata cewa; tunanin Ridha ya yi ƙaura daga ƙwaƙwalwarta, zuciyarta da fankon gangar jikinta ce kawai zaune kamar mutum mutumi.

 

“Ridayya…” Diyya ta kira sunan Ridayya tana matse kafaɗunta da girgizata da ƙarfi, wanda hakan sam bai yi tasiri ba, kallonta take kamar zautacciyya! Bata ganewa bata fahimta. Ruwa mai sanyi Diyya ta ɗakko tana daga tsaye ta sheƙawa Ridha, sanyin ruwan ya sauka har tsakiyar kanta, gargasar jikinta ta mimmiƙe bugun zuciyarta ya ƙaro fiye da bugawar lokaci, a sarƙe numfashin Ridha ke fita kamar mai ciwon lamoniyya ko Asthma.

 

“Na shiga uku Diyya, na shiga uku, nikam na kaɗai” Zantukan ke fitar da kansu ba tare da bin umarnin zuciya ba, balle subar ƙwaƙwalwa ta yi aikinta na da cewar fitar mashin da sukai, gabaɗaya ƙofofin jikinta a buɗe suke idanunta a rufe ruf bata son gasgatawa, bata so, bata so, bata muradi. “Samu nutsuwa Ridayya, karki mace mini,ki saurarawa kan ki haka” Ridayya bata taɓa sanin kuka yin kansa yake ko samun damar fita ba sai yanzu, a wannan jirkitacciyyar ranar data juya ƙyakƙyawan tunaninta akan mijinta zuwa mummuna, ranar data zama silar rusa dukkan wani motsi da ji na soyayyar mijinta, ta yaye mata nauyin dutsen dalar daya danne kanta tare da yi mata murfi, rana mafi muni a sauran ranakun data ruska, ranar data fito daga cikin kabarin data rufe kanta da kanta.

“Ridayya!… Ridayya! Na shiga uku”

A gigice Diyya ke magana tana taro Ridha da numfashinta ke ƙoƙarin tsayawa iya ƙirji ya tukare mata.

“Bar wannan haukan Ridha, tun a waya nake shaida miki ba a yiwa namiji haka, namiji ƙanin aljali, namiji hankaka, gabanshi fari bayanshi baƙi, namiji ba a gane gabanshi sai Allah…,

Namiji rigar ƙaya, idan kika sata sai ta sokeki, Namiji ƙarin ƙunama, idan bai kashe ki ba, to zai saki jinya, namiji ɗan yaudara, ina ka fito yaudara ina zaka yaudara! Ki goye shi a baya, yazo na zagin bayan, ki biya mishi buƙata, kuma ya ce haƙuri dake ya ke yi..,

Namiji ne ke lallaɓa yarinya a gidan ubanta, idan ta zo gidanshi ta zama Baiwa! Namiji baka tausayin ta gida sai ta waje, iyalanka su roƙe ƙa naira goma ka ce babu; a waje ka bada dubu ɗaya ko ba a tambaya ba, namiji ba ɗan goyo bane…!”

Maridiyya ta ce “Wasu fa, a maza akwai ƴan halak na nunawa sa a da yin kwatance da girman suffarsu, wacce ke nuna halayyarsu, ban da irin naki mijin Riddahh babu irin naki, bayan abubuwan da na faɗa miki ke naki mijin ya kasance lamba ɗaya ya zamto MUNAFUKIN MIJI”

 

Zumbur Ridha ta miƙe tsaye duk da nauyin da cikinta ya yi mata, ya tattaro ya sauka ƙasa ya tsaya mata baya ko motsi balle ta gasgata lafiya yake.

“Maridiyya ko?”

“Ban gane ba?” Maridiyya ta buƙaci jin manufar kiran da Ridha ta yi. Wani irin murmushin takaici da kin raina mini hankali Ridha ta yi kafin ta ce.

“Tashi ki fice mini daga gida Maridiyya, ta shi maza tun kafin zuciya ta sani yin abinda ban yi niyya ba” Da mamaki ta ce “Ni kike cewa na fita?”

“Bana maimaita magana kin sani, bana son damuwa juya mini tunani take, na fahimci baƙin ciki kike mini da auren da nake, idan kuma Zameer kike so sai ki shaida mini na sani”

 

“Mijinki? Me zan da mijinki Ridha? Munafukin Mijin? Akan shi…,”

Wani bahagon mari Ridha ta saukewa Maridiyya, ita kanta ko a mafarki aka ce zata mari Maridiyya zata musanta. Diyya ta dafe kunci ta ce

“Da gaske ni kika mara Maridiyya? Akan mijinki?”

Da sauri ta ce

“Ya shige akai, wallahi wallahi akan Zameer Abba da Mami kawai zan ɗagawa ƙafa” Ta sauke numfashi zuciyarta na mata wani irin zugi da raɗaɗi kafin ta ɗora da

“Idan kullum Zameer zai sanya wuƙa ya yanki naman jikina to zama da shi yanzu na fara, na ga ji ina muku kawaici ni nake rayuwa da shi ku barni, idan musgunawa ce bani ya kewa ba? Balle ni kaɗai nasan irin so da ƙaunar da MEER ke yi mini, bana buƙatar sake ganinki a rayuwata bana buƙata fita, idan kuma son shi kike bismillah ki faɗa ina ji”

Miƙewa Maridiyya ta yi tare da ɗaukan jakarta da wayarta, idanunta jajur ta nufi ƙofa har ta je ƙarshe ta ce “Akwai ranar da zaki fahimci na fi mijinki muhimmaci a rayuwarki, na gode ƙwarai” Tana faɗin hakan ta fice daga cikin gidan hakan ya yi daidai da shigowar Meer sanye da wata dakakkiyar shadda hannunsa zube cikin aljihu fuska ɗaure ba walwala ko inuwar Maridiyya bai kalla ba, balle ya san halin da take ciki. Ya shige abinsa.

 

Ƙyakƙyawan namiji ne, tsaye akan duga-dugensa baya da wasa baya ƙaunar raini, gyara zaman shi ya yi a saman katifa, yana yatsuna fuska idanunsa akan wayarsa yana bin photon dake maƙale akai, ƴan mata yake kallo kala-kala daga Instagram zuwa twitter, kana ya dawo Tictiok. Har aka kira magariba bai tuna da ita a gidan ba, balle cikin jikinta, ganin datar shi ta ƙare ya sanya ya miƙe tare da ɗaura alwala ya nufi masallaci, sai bayan Issha ya shigo gidan yana takun ƙasaita zaune ya ganta a parlour ta yi wanka tare da yin kwalliya sai ƙamshin turare take fuskar nan tana da zuba maiƙo, Meer ya kwaɓe fuska yana zama nesa da ita sai kuma ya miƙe ya ƙarasa dab da ita ya zauna, a taushashe ya ce

 

“Mai sona Ridayya”

Shi ne kalaman shi a kullum ta kalle shi da kyau a sanyaye ta ce “Ka jima da shigowa ashe? Ya hanya da aiki?”

Ya ɗaga girar shi duka biyun yana kashe mata ido, wanda shi ne ke ƙara narkar da zuciyarta zuwa gare shi. Ya yi shiru.

“RAYUWATA”

Ridha ta kira shi da sunan data bashi, jin ya yi shiru ta zungure shi ta ce “Zameer!”

“Yes, mai sona” a hankali ta ce “Tun safe ban ci abinci ba, ga cikina ya daina motsi ina jin tsoro”

“Ridha ya kike so na yi? Baki da godiyar ALLAH?”

Ta girgiza kai tace

“Ka yi haƙuri, Mami ta kira ɗazo” Ya ajjiye wayar idanunsa a kanta bai ce komai Ridha ta sunkuyar da kai ta ce “Ta ce na fifitaka akan su, wai cutar dani kake watarana zaka kashe ni” A zuciya Zameer ya ja tsaki a fili kuma ya marairaice fuska tamkar zai kuka ya kama hannun Ridha ya ce “Me ya sa dangin ki babu mai so na? Meyasa suke son rabani da ke Ridayya?” A hankali ta ce

“Duk wanda baya son ka, nima bana son shi Rayuwata” Ya yi shiru can ya ce “Na samu aiki a Company, zan tura takaddu amma ta online”

Farin ciki sosai akan fuskar Ridha kafin ta ce

“Allhamdulillah, Allah ya sanya albarka ka yi maza ka tura to” Baya son surutu a taƙaice ya ce

“Ba data, bana da kuɗi”

Wayarta ta ɗauka ta bashi ta ce “Ɗazo Yaya Bilal ya tura mini kuɗi, daman jira nake ka dawo ka yi mana jefa ne, ka yi transfer na kati ka sanya data sai ka nemo mana abinda zamu ci”

Amsa ya yi ya duba balance yaga dubu goma, murmushi kawai ya yi kai tsaye ya tura dubu takwas account ɗinsa ya bar mata dubu biyu, bata ce komai ba, da ita da kuɗin mallakinsa ne.

Ya rungumeta a jikinsa yana sumbatar kumatunta a hankali ya ce “Thanks Mai sona”

Yana faɗin hakan ya fice, Ridha ta rufe Idanu tana fargaba na rashin motsin cikin, Zameer na fita ya siyi data abinsa ya ci-gaba da kallon ƴan mata, ya je ya siyi lafiyayyen tsire da shayi ya sha abinsa yama manta da batun Ridha.

Cikin bacci wata razananniyar wunya ta farkar da ita, cikinta ya ƙara mata nauyi ga ciwon da mararta ke mata sama sama, daga ita sai kayan bacci ƙafarta sanye da takalmi ta nufi ɗakin Zameer bata sha wahala ba sbd akwai nepa a gari, tana shiga ta tsaya cikin tsautsayi da rashin sanin abinda zata gani ya sanya kai tsaye idanunta ya sauka a wajan, tashin hankali firgici damuwa kaɗuwa da gigita ya sanya wani irin ruwa ɓalle mata ya fara bin cinyoyinta idanunta ya shiga rufewa, komai ya tsaya mata duniyar ta jirkice mata, da ƙyar ta iya lallaɓawa ta rufe ƙofar tare da jan ƙafafuwanta, sautin ƙofar ya dawo da Zameer nutsuwarsa, Ridha tunaninta ya tsaya, bata ma san me take yi a duniyar ba, so take ta jita a kushewa bata son yarda da abubuwan da ake faɗa mata akan mijinta, bata ƙaunar yarda da gasgata abinda idanuwanta suka gane mata a yanzu. Kitchen ta nufa lokacin data tuna tana da fiya-fiya kai tsaye ta ɗauki kwalbar ta nufi ɗaki, tana shiga ta saka key ta rufe ɗakin bata san manufa da illar wanda ya kashe kansa ba, tana tunanin mutuwarta a yanzu shi ne zai tabbatarwa da Zameer irin son da take masa, ta manta da ƴan uwanta, ta manta da Mami, Abba ta manta da dukkan masu so da ƙaunarta idanunta rufe ta buɗe murfin kwalabar tare da kafata a bakinta ta tuttulawa cikinta fiya-fiya ɗin….

 

 

 

Free book ne, kuma labarin gaske yin comment da share shi zai tabbatar da yadda kuka amshi labarin, duk wanda ya a karanta ya yi share shi ne roƙana da jin daɗina🥰👏🏻. SHIMFIƊA ne Wannan gobe zamu fara page 1.

 

 

#Ridha

#Meer

#Mardiyya

#ZamanAure

#RayuwarMace

08119237616

Post a Comment

Previous Post Next Post