Mawahib Hot Love Hausa Novel
MAWAHIB
(Hot luv)
Writing By Amnah El Yaqoub
1&2
‘Yanmata ne guda biyu suke tafiya cikin nutsuwa,kana ganinsu kasan bazasu wuce shekaru goma sha takwas ba,d’ayar tana Sanye cikin uniform na islamiya,tanada duhun fata kad’an,a hankali ta juya ta Kalli qawar tata, wadda take Sanye cikin kayan gida,babu uniform din ajikinta saide dogon hijab irinna d’ayar,wanda yazo mata har qasa,kalar hijabin ruwan toka yayi mutuqar qawata farar fatarta,Wanda kana gani kasan cewa hutu dakuma Jin dadi ya ratsa fatar tata.
Jiddah tace”MAWAHIB,kiraba mana musu dan Allah”
Ahankali tajuyo dara daran idanunta wanda yayi kama Dana mejin bacci, ta Kalli qawar tata, sannan tace”musun me Jiddah?”
Wadda aka Kira da Jiddah tace”wallahi musu muke dasu Hassan da Hussainin gidanmu,nace duk unguwar Nan sukadai ne ‘Yanbiyu matasa, shine sukace min wai Yaya ASHRAF din gidanku Shima ‘Yanbiyu,nikuma nace ba ‘Yanbiyu bane, Yaya Ashraf ne kadai yayanku,saboda nide tunda nake dake,Kuma duk yanda nake qawance dake,baki taba cemin kunada ‘yanbiyu a gidanku ba”
Saida ta yatsina kyakykywar fuskarta mai cikeda gashin gira alamun batason maganar, sannan ta motsa dan qaramin bakinta Mai launin pink,tace” ‘yanbiyu ne,d’ayan baya zuwa sosai shiyasa baki sanshi ba,ai kinsan Yaya Ashraf dinko?,toshima d’ayan kamar kinsan shi,yanda kikaga Yaya Ashraf Shima haka yake,yana Nan kullum yana fama da uniform,basuda banbancin kamanni, komai nasu iri dayane,nikaina idan suka hadu su biyun bana Iya banbance su,saboda komai iri daya suke sakawa,kawai de hali ne kowa da irin nasa”
Cikin mamaki Jiddah tace”ashe Ana Samun ‘yanbiyu maza manya kamar Yaya Ashraf,? Amma Mawahib baki taba bani labarinsa ba”
Cikin sauri Mawahib tace”menene hadina dashi dazan baki labarinsa? wannan marar imanin inani inashi?, halinsa daya da mahaifiyarsu,duk yanda kike tunaninsa yawuce Nan,miskilancinsa yayi yawa,baida fara’ah,kenifa bari Kiji Infada miki na tsaneshi, tun saudaya dana ta6a yimasa laifi ya Sumar dani, daga ranar naji nasake tsanarsa”
Cikin sauri Jiddah ta zaro ido(😳)
Tace”nashiga uku Suma fa kikace?”
Cikin tabbatar wa Mawahib tace”suma kuwa,Ina zaune Yaya Ashraf yazo yacemin naje nagyara masa dakin su,Wai ashe shine zaizo daga Abuja,nikuma bansan ranar zai dawo ba,dana gama gyaran saina dan kishingida akan gadon su,nadan dora kaina a wani fillo Mai laushi,Bansan lokacin da bacci ya daukeni ba,daya dawo yaganni a’inda yake kwanciya,kuma nadora kaina akan fillonsa, shine ransa ya6aci,daya damqi gashin kaina bansan lokacin dana saki ihu ba,shine yasaka kaina a cikin sink din toilet dinsu yabude ruwan,nide nasan yasakani a ruwa,amma daga Nan bansake sanin inda kaina yakeba,Sai farkawa nayi naganni a kwance a gadon dakina”
Cikin tashin hankali Jiddah tace”innalillahi….amma Abbanki baice komai ba?”
“Jiddah mezaice tunda sun dauki power sun bashi?,haka itama NABIHA yata6a jimata targade ahannu,shiyasa nida ita bamaso yazo gida, musanman ma ni,na tsaneshi Jiddah”
Jiddah tayi ajiyar zuciya tace”A a Mawahib,kidena fadar haka,koba komai ai dan’uwan ki ne, gidanku daya,sannan kobabu wannan dangantakar,shidin dan’uwan ki ne musulmi, Kuma babu dadi ka dinga cewa ka tsani mutum,Amma Kuma nayi mamakin yanda naji labarinsa a wajanki,saboda su Hassan din gidanmu har cemin sukai idan yazo har kudi yake rabawa mutane abakin get dinku, wani lokacin ma harda kayan abinci,toke menene ma yakaiki kwanciya a gadonsa?”
Cikin sauri tace”Gadonsa ne shi kadai?gadon su ne shida Yaya Ashraf”
Jiddah tace”duk da haka nide Ina kokonto akan wannan halaiyar tasa dakika fadamin,mutumin dazai dinga yin Alkhairi da kudinsa na aljihunsa shine za’a yi masa wannan shedar?”
Cikin taqaici Mawahib tace”to Jiddah aikuma Sai kiyi,ya Ina fada miki mutum bashida Imani kina min maganar wani kudi,kudinsa na banza da wofi…? ni Kinga tafiya ta”
Tana gama wannan maganar tayi gaba tabar Jiddah a tsaye a wajan cikeda mamaki,Jiddah tasaki ajiyar zuciya tabi Bayan Mawahib da kallo, meyake damun qawarta ne?aiko wani taji yana aibata dan’uwan nata kamata yayi ace Sai inda qarfin ta Yaqare,amma suna gida daya,ana Samun wannan matsalar?(🤔)
******
Tana shiga gida, cikin fara’ah megadinsu dayake zaune a kofar get din gidan yace”yanmatan Mamy har andawo daga islamiyar?”
Cikin ladabi tace”Baba Musa nadawo, sannu da aiki”
Al’adar Mu Hausa Novels Complete
Bata jira amsar saba taci gaba da tafiya tana qarewa manyan motocin gidan kallo Wanda suke sheqi da daukar ido tundaga ma’adanar su, taqaraso get na biyu, tabude tashiga,anan zahirin gidan yake, gidane hadadde wanda ya amsa sunansa gida,saide bashida fadi sosai,duk da hakan an qawatashi da adon furanni Masu kyawun launi,anan compound din gidan taci karo da mutanan gidan a zaune,manyan mata ne guda biyu, saikuma wata yarinya wacce bazata wuce sa’arta ba, cikin sakin fuska tayi sallama, Nabiha da hankalin ta kekan wayar dake hannun ta, tadago kanta da sauri Jin muryar yar’uwar tata,qawa, Kuma aminiyar ta.
tace”Mawahib Kin dawo? Ya Sayyadi yayi dorin karatu?”
Cikin tsokana tasaki wani irin murmushi,murmushin yayi mutuqar yimata kyau har hakan yasa dimple dinta guda biyu suka futo sannan tace”anyi dori,Kuma anbada number,tunda yau da niyya kikaqi zuwa”
Hajiya KILISHI datake zaune gefe kan kujerar roba,lokaci daya tabi Mawahib dawata irin harara kamar idonta zai fado qasa,cikin izza da gadara,tareda tsantsar iko tace” ‘ya’yan ma’aikata andawo Kenan,INA GANIN IKON ALLAH NI KILISHI,anfita angama yawon gantali andawo,nikam naga mijin wannan yarinya,Kuma fa ahakan ake neman miji nagari…”
Lokaci daya jikin Mawahib yayi wani irin sanyi,Nabiha ta sunkuyar da kanta qasa,alamun bataji dadin furucin hajiya Kilishi Akan Mawahib dinba,cikin sanyin jiki Mawahib tadubi Hajiya Kilishi,babbar mace ce Mai kimanin shekaru Hamsin da biyar,fara ce tas,batada digon baqi a jikinta, hutu dakuma Jin dadi ya boye shekarun ta, bazaka ce takai adadin wannan shekarun ba,tana kyau sosai,saide fuskar ta cike take da qunci da rashin walwala, cikin ladabi ta russuna tace”sannu da hutawa Momy”
Hajiya Kilishi ta kawarda fuskarta gefe batareda ta amsa gaisuwar ba
Mawahib tasaki murmushi Mai ciwo, sannan ta dubi d’ayar matar datake zaune kusa da Nabiha, wadda a shekaru bazatafi Mamyn taba, tace”Mama sannu da hutawa”
Cikin sakin sakin fuska wadda aka Kira da mama tace”sannu Mawahib”
Cikin sanyin jiki tashige kitchen,kasancewar tasan yau girkin mamyn tane, Kuma Bata dawo da wuri daga wajan aiki ba, tasan har yanzu tana kitchen bata gama wasu ayyukan ba,tana shiga kitchen din kuwa taganta a tsaye tana duba farfesun ganda Wanda qamshinsa yagama cika kitchen din,kallo daya zaka mata ka tabbatar da cewa mace ce Mai aji dakuma tsari,uwa uba yar boko maiji da gayu, komai nata tana yinsa a nutse,manya manyan zobuna ne a hannunta na gold sunkai guda uku,Riga da zanine ajikinta na leshi kanta yana daure da dan kwali Amma duk da haka jelar kitsonta ya sauko harkan gadon bayanta, black beauty ce, kokadan bata kama da Mawahib, launin fatarsu daban, saide sanyin hali dakuma dabi’arsu da tazo daya, a hankali tace”Mamy sannu da aiki”
Batare data kalletaba tace”sannu da zuwa ya makaranta?”
Cikin rashin walwala tace”Lafiya kalau Mamy,bari inje in cire kayana inzo natayaki”
Kallonta tayi a Karon farko ta karanci akwai damuwa a fuskar ‘yartata, amma Bata nuna mata komai ba,cikin hikima tace”A a,aina gama komai,dauki wannan salat din kawai kije ki yanka min,Abbanki yace ayi masa kwadon salat kafin yadawo”
Ahankali tasaki ajiyar zuciya,sannan tacire hijabin dake jikinta,doguwar rigar gown din dake jikinta ta atamfa ta baiyana,rigar ta kama jikinta sosai har hakan yasa shape dinta futowa fili,hips dinta yacika rigar dam,saida ta bubbude girkin da mamy din tayi tagani bayan farfesun ganda,harda fried rice,da Alalan dankali, da fried cabbage with meat,a hankali tadauki salat din ta futo daga kitchen din tanufi hanyar part dinsu, Hajiya Kilishi tabi bayanta da kallo,ta Kalli yanda uban Hips dinta suke juyawa acikin rigar kamar da niyya take kad’asu, ta watsa mata wata irin harara tace”ina ganin ikon Allah ni Kilishi”(😂)
Tajuya ta Kalli matar datake gefenta tace”Sadiya,dole zanyi wa ALQALI magana yaje yasamu shugaban makarantar islamiyar yaran nan ayi masa magana,ai bazai iyu abar yara suna zuwa makaranta babu uniform ba,suci wannan uwar kwalliya suna juyawa malamai kwankwaso,Kuma ahakan ake neman miji nagari….,bazan Iya cigaba da zama anan ba Sadiya,baqin cikin wannan yarinyar zai Iya illata ni,idan Kinga zaki Iya cigaba da Zaman jiran abincin, to bismillah Nina tafi,wannan horon yunwa har Ina? ai sai asa ulser ta tatashi”.
tana wannan sababin ,tajuya cikeda iko da izza irinta yayan mulki ta wuce part dinta.
Mama Sadiya tayi murmushin qarfin hali a hankali tace”Allah yarufa asiri”
Sannan tadubi yarinyar ta Nabiha dake gefenta tana daddanna waya, tajuya taga tabbas Hajiya kilishi tashige part dinta, sannan tace”Nabiha yi maza kije kitchen idan akwai aiki a wajan Mamyn Mawahib ki taimaka mata”
Nabiha ta amsa cikin ladabi, sannan tashige kitchen din, Mama Sadiya saida tasake kallon part din Kilishi ta tabbatar de Hajiya Kilishin bataga lokacin da Nabiha tashiga kitchen dinba,sannan tasaki ajiyar zuciya ta wuce nata part din,tun dazu taso tatura mata Nabiha,domin ta taimaka mata da aiki tunda Mawahib din taje islamiya,to amma tsoro dakuma shakkar Hajiya Kilishi yahanata.
Tana shiga falonsu ta ajiye salat din ta wuce dakin ta tayi sauri ta watsa ruwa,ta futo Sanye da riga da wando,ta zauna adaya daga cikin rantsatstsun kujerun falon Masu launin ruwan toka,Sai qananun fillo dasuke Kai,ta dauki remote din esi ta kunna, sannan tafara yanka salat din cikin qwarewa,batafi minti ashirin da zama ba mamy ta shigo falon, tun daga bakin qofa ta qarewa ‘yar tata kallo,tana ganin irin dirin da Allah yabata,Riga da wando ne a jikinta baqaqe, wandon gaba dayansa Iya gwiwarta yatsaya,rigar Kuma batada banbanci da vest saboda ko hannu Bata dashi,sai farar hula shara-shara Wanda kana Iya hango tulun gashin da Allah yabata, Wanda ta gajeshi a wajan mamy, a hankali tasaki ajiyar zuciya tace”kin kunna esi kinzo kin saka wannan kayan, banason shirme tashi kije ki sauya kaya,idan sanyi ya kamaki fa”
Cikin shagwaba tace”Mamy Ana Kiran sallah zancire fa”
Cikin tsare gida tayi mata kallo daya,babu musu ta ajiye wuqar hannun ta ta wuce dakin ta domin sauya kaya.
Lokacin sallah nayi kowa yashige dakinsa domin gabatar da sallar magrib,tana idar da sallar ta dauko Alqur’ani tabude tafara karanta inda aka biya mata dazu a islamiya,Bata dade da fara karatun ba mamy taturo qofar dakin ta shigo hannun ta daukeda counter tana dannawa,ta dubi Mawahib tace”kije kikaiwa su Yaya Abinci”
Badan tasoba tarufe Alqur’anin,tafice daga part din nasu zuwa babban kitchen din gidan,ta dauki abincin mama Sadiya tashiga part din tareda sallama,falon nasu yatsaru Iya tsaruwa da kujeru nasu launin dark green,babu tarkace sosai Bayan kayan kallo dayake falon, Kai tsaye ta wuce dinning dinsu ta ajiye abincin, sannan tashige dakin Nabiha,tana zuwa tazube akan gadon ta tace”sarkin danna waya,kina Nan kina sana’ar taki”
Nabiha tayi murmushi tace”to saina zauna shiru dan Allah? aigara indinga danna wayata”
Mawahib tace”hakane Kam,Nima yanzu tunda mungama exam ai yanzu zan maidata qawata”
Nabiha tace”Mawahib yaushe Yaya Ashraf zai dawo?”
Saida ta juya idanunta Mai kamadana Masu Jin bacci sannan tace”wallahi bansaniba Nabiha,jiyama bayan munfuto daga last paper nayi masa flashing, amma bai kirani ba,kikirashi mana idan magana zakuyi”
Ajiyar zuciya Nabiha tayi,cikin ranta tana jinjina maganar Mawahib datace ta kirashi,tayaya ne zata samu qwarin gwiwar kiransa bayan bataga fuskar hakan awajansa ba?
Cikin basarwa tace”to shikkenan,babu damuwa”
Cikin sauri Mawahib tatashi tace”bari inje inkaiwa Momy kilishi abincinta karnayi laifi”
Nabiha tace”wallahi kuwa,bare keda dama kamar qiris take jira”
Sallama tayi mata ta futo daga part din, takoma kitchen dinsu ta dauki abincin hajiya Kilishi sannan tawuce part dinta,gabanta yana tsinkewa.
Da’ita taci karo tana Bude kofar falon,qiris yarage subugi juna, cikin sauri Mawahib taja baya
Cikin 6acin rai Hajiya kilishi tace”Ina ganin ikon Allah ni kilishi, ai saiki dinga nocking kafin kishigo, idan anbaki iznin shigowa saiki shigo tunda bakida iko da part din bare kidinga shigowa Kai tsaye haka”
Ahankali ta sunkuyar da kanta qasa cikin ladabi tace”kiyi haquri momy, dama abinci ne nakawo”
Batareda ta kar6i abincin ba tace”bude nagani”
Cikin nutsuwa ta sauke kwandon dake hannunta, sannan ta bubbude mata abincin,Nan da Nan qamshin girkin yacika wajan,abincin ya tsaru kana gani, kasan girki ne nazamani.
Yatsina fuska tayi tace”wanne irin gantalallen abinci ne haka zaki debo jiki kikawo min,?da alama kema haka zakije kinayi a gidan naki mijin….,kinga koma dashi kawai”
Babu musu Mawahib tarufe abincin sannan tadauko tanufi part dinsu dashi, tanajin yanda Hajiya kilishi take rufo qofar part din nata da qarfi.
Tana zuwa part dinsu dayake babu Nisa a tsakani, anan taci karo da Mamy tana zaune tana kallo,cikin mamaki mamy ta kalleta tace”yanaga kindawo da abincin?”
“Mamy nakai mata tace in dawo dashi”
Cikin yanayi na rashin damuwa Mamy tace”to Bari inkai mata dakaina”
Mamaki yacika Mawahib, babu musu tabata kwandon abincin, mamy ta karba tafice daga nasu part din tanufi part Hajiya Kilishi.
Tana zuwa tatura kofar falon tashiga bakinta dauke da sallama,falo ne har falo,yaji kayan qawata gida da lafiyaiyun kujeru milk color,tareda kafet Mai mutuqar laushi dawani daddadan qamshi dayake tashi gamida sanyin esi,can gefe inda dinning yake, anan ta hangi Hajiya Kilishi tana qoqarin hada tea, Kai tsaye ta nufi wajanta tace”yaya ga abincin angama, Mawahib tacemin kince adawo dashi, kiyi haquri Yaya yau dinne munsamu marasa lafiya a asbiti dayawa,Ina shirin tahowa aka kawo wata mata tana naquda,nice natsaya nakula da’ita harta haihu,sannan nataho gida shiyasa na Makara bandawo da wuri nayi abincin ba, amma kiyi haquri Yaya”
Hajiya Kilishi tace”ina ganin ikon Allah ni Kilishi,nace kinyi wani laifi ne Maryam?kawai abincin naki ne yau bazanci ba,kinyi wata shinkafa haka a tsatstsaye bata dahuba,kiyi mana abincin da muka saba Namu na gargajiya kinqi, saina ki na Yan zamani, kega ma’aikaciya,wannan naman gandar daga ganinsa ko silala baiyi ba bare ayi batun dahuba”
Cikin ladabi tace”kiyi haquri Yaya, me kikeso nadafa miki yanzu?”
Hajiya Kilishi ba tace komai ba, tajuya tabar mamy a tsaye a wajan tashiga dakinta,mamy tasaki ajiyar zuciya ta wuce takai abincin dinning, sannan ta futo daga part din.
Tana komawa part dinsu taga Mawahib a zaune tanashan farfesun data gama a hankali cikin yanga kamar batason ci,Wanda a zahiri ba yanga takeba,haka cin abincin yake, hankalinta yana kan TV, tana ganin shigowar mamy, ta ajiye plate din dake hannun ta takoma kusa da ita ta zauna, ta dora hannayen ta akan cinyar mamy, sannan ta kalleta cikin damuwa tace”Mamy, Wai dan Allah meyasa Momy Kilishi bata sona?menayi mata Mamy?”
Cikin kwantar da hankali mamy taqarewa ‘yartata kallo tana ganin tsantsar yanda take kama da mahaifinta, a hankali tace”tana sonki mana,itace tace miki bata sonki?”
“Mamy bata sona,dazu har cewa tayi wai itakam taga irin mijinda zan aura…,Mamy ahaka zamuci gaba da zama ne komai akai kinayin shiru?har cemin fa tayi wai nima ahaka zan qare danawa mijin idan nayi aure”
Cikin sauri mamy tace”insha Allahu ba’ahaka zaki qareba,mijinda zaki aura lafiya kalau zaki zauna, ba zakiyi irin wannan rayuwar ba”
Ahankali Mawahib tasaki ajiyar zuciya Jin furucin mahaifiyar tata,sannan tace”to Mamy meyasa ke bata sonki?”
“Wai waye yace miki bata sona? Kawai halintane haka, banason tambaya Mawahib,kitashi kije ki kwanta”
fan’s ya kwana biyu?🤔
Amnah is back💃🏼
Mawahib littafin kudi ne,zaki biya naira 500 kacal,ki karanta abinki cikin kwanciyar hankali,sayan nagari maida kudi gida 💃🏼
Zaki turo 500 ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034
Idan kina buqatar a tallata miki hajarki a Facebook page dinmu,da whtspp,da status,farkon shafi ko tsakiya,ko qarshan shafi, duka akan farashi me sauqi,ki tuntu6eni ta wannan number 08033300034
Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/9, 9:20 AM] AMINA KABIR CAPS: 💗MAWAHIB💗(Hot luv)
Writing By Amnah El Yaqoub
3&4
Please🙏🏻kuyi Subscribe YouTube Channel dina,domin samun Audio Novel’s👇🏻
https://youtube.com/@Amnahelyaqoubnovels
____
Ba dabi’arta ce yin musu da mahaifiyar tata ba,danhaka babu musu tatashi ta dauke sauran farfesun datake ci takai d’an qaramin kitchen dinsu dake cikin falonsu,sannan ta futo tazo dining tazuba wata uwar madara a cup, tazuba ruwan zafi kad’an, tad’auki cornflakes d’in dake gefe tazuba acikin madarar, sannan ta wuce dakinta.
Mamy tana ganin shigarta daki tasaki ajiyar zuciya,yanzu har Mawahib yarinya ‘yar shekara sha takwas tagane tsanar da Hajiya kilishi tayi mata harta fara sata agaba tana tambayarta dalili? Itakam meta tsarewa matar nan ne? aikin gomnatin datake ne yazama matsala? kokuma wannan ne sakayyar dazata mata bayan rainon yaranta datayi mata Abaya?
Labarinsu:
GIDAN ALQALI….,sunan da ake Kiran gidan dashi Kenan.
Duk unguwar inde kace gidan Alqali to kowa yasan cewa gidansu Mawahib ake nufi,Alqali mutun ne shi mai ra’ayi d’aya, baya magana biyu,yanada dattako,kowa nasa ne, yanada faram-faram da mutane,kowa shedar kirki yake masa,amma duk da wannan sakin fuskar tasa hakan bai hana yakasa gudanar da gidansa yanda yakeso ba,shine yake kafa doka agidan,duk abinda yabada umarni shi akebi,kasancewar shine babba a gidan,sai qannansa guda biyu Alhaji khaleed dakuma qaramin su Alhaji Isah.
Alqali fari ne tas,zaka Iya cewama ba bahaushe bane, amma bahaushe ne cikakke mutumin garin kano, yanada sauqin kai, kuma baya goyon bayan rashin adalci,tun yana qaramin ma’aikaci yake kokarin yin aikinsa da gaskiya da amanah,har Allah yabashi matsayin Alqali,wanda yazama abun koyi a wajan sauran Alqalai,babu ruwansa da kar6ar cin hanci, aiki kawai….🤗
su uku ne rak a wajan iyayensu wanda suka mutu suka bari,Alqali Ibrahim shine babba,da matarsa daya tun auren saurayi da budurwa wato HAJIYA KILISHI,lokacin da akayi auren sunsha surutun mutane ganinta fara tas kamar ba yar hausawa ba, shima kuma fari, wannan yace anhada kyau da kyau za’a ga irin yaran dazasu haifa,ire iren wannan surutun tun yana damunsu harya dawo yazame musu jiki, suna zaune lafiya tsawon wasu shekaru,Hajiya kilishi itace take kula da duka gidan zatayi girki Alhaji khaleed da Alhaji Isah zasuzo suci abincin su sutafi harkar gabansu.
Tsawon lokaci shiru shiru babu haihuwa, tun ‘yan gulma suna saka ran ganin abinda zasu haifa har suka haqura, saida aka dauki wasu shekaru kafin ubangiji ya azurtasu da samun haihuwa, karon farko Hajiya kilishi ta haifi yaranta ‘yanbiyu dukansu maza,lokacin da akayi haihuwar kai tsaye Alqali yace a dinga 6oye yaran,saboda Allah yayi musu kyau kamar ‘ya’yan larabawa,Kuma bakin mutane wani bazai furta Alkhairi ba, sun dauki kyan uwa dakuma na uba sun hada waje daya, sunada mutuqar shiga rai babu wanda zai gansu baiji aransa yana qaunar yaran ba, ranar suna aka sakawa babban sunan mahaifinsu Alqali wanda yarasu,sai suke kiransa da ASHRAF,sai qaramin wanda aka sanya masa sunan mahaifin Hajiya Kilishi, suna kiransa da ARYAN….
Tun lokacin da kilishi ta haihu,take nan-nan da yaranta,kwata kwata batason abinda zai ta6a mata lafiyar ‘yanbiyun ta, tanaji dasu kamar ranta,musanman ARYAN, wanda yaci sunan mahaifinta,ta dauki duk wani hope d’inta, ta dorashi akan ARYAN,idan har ta yiwa Alqali laifi to ta hanyar yaran yake hukuntata, saboda yariga yagano cewa yaran nata sune weakness dinta,tun suna zama Hajiya kilishi take gane-gane, yau taga maciji gobe kunama,idan d’aya yana kuka tad’aukeshi tana lallashinsa shima dayan saiya fara kuka,tarasa yanda zatayi ta lallashe su duka su biyun saboda haka saita ajiye d’aya idan d’ayan yayi shiru saita lallashi d’ayan,to duk ranar datayi hakan abincin gidan baya ciyuwa,haka zata dinga sakawa abinci wuta qarshe saide ayi asarar sa,data gane saitake had’asu duka su biyun take lallashin su,d’aya abaya,daya a hannu, daga lokacin bata sake ganin kunama ba,sai lokacin dasuke rarrafe idan sukai ta’adi tad’an dakasu alamun abinda sukai ba daidai bane,tana barin wajan taga wata baqar kunama,sai wata aminiyarta tabata shawara akar6o musu abincin maqota azuba musu akan murfin tukunya bazata sake ganin komai ba,haka akayi kuwa taje maqota takar6o abinci, tadauko murfin tukunya zata zuba musu Alqali yace karta fara, wannan duk canfi ne na mutane, Allah ne kawai yake kawo kunama amma ba yayansa ba,duk surutun mutane ne.
a hankali rayuwa taci gaba da tafiya ‘yanbiyu suka fara tafiya har suna fita kofar gida wasa,ba’a Isa adakesu ba yanzu Hajiya kilishi zata sa6a mayafi koda sanin Alqali ko babu saninsa,zataje har gidan yaron daya dukar mata ‘yanbiyu tarama musu, sannan takamo ‘ya’yanta sudawo gida, wannan halaiyar kwata kwata Alqali bayajin dadinta.
Amma hajiya kilishi inde akan yaran nan ne, to zaka Iya Jin kanta dakowa, kasancewarta yar sarauta idan aka taba su Ashraf,mantawa take ita yar sarauta ce taje ayi wacce za’a yi,kokadan batason abinda zai ta6a mata lafiyar su,lokacin da aka haifeta, a lokacin a kayiwa mahaifinta sarauta, shiyasa mahaifinta ya Sanya mata suna KILISHI.
tashin datayi a gidan sarauta yasa take wa kowa kallon raini da Kuma nuna Isa da taqama da izza,kana ganin yanda take gudanar da al’amuranta zakasan cewa jinin sarauta yana yawo a jikinta,ahakan ma saboda Alqali a tsaye yake agidansa, shiyasa take rissinawa.
Bayan Alqali Ibrahim Sai qaninsa na biyu Alhaji KHALEED,adede wannan lokacin yayi aure, yaso yazauna agidansa shi kadai amma Alqali yace babu inda zaije, ya zauna a gidan duk suyi zamansu tare babu wanda zaibar cikin gida, Alhaji KHALEED ya auri Mama Sadiya mace mai kawaici da kawar dakai akan komai, kasancewarta mace mai tsoron fitina yasa zamanta da kilishi ya d’ore,bata Isa tayi komai ba saida iznin Kilishi, komai zatayi saita tambayeta,hakan yasa kilishi take qarajinta asama,kanta yana sake kumbura tana jinta eh lalle ita d’innan fa yar sarauta ce.
Alhaji Khaleed baifi wata shida da aure ba, Alhaji ISAH shima yataso da batun nasa auren,wato d’an qaramin su, babu abinda yayi na aure komai Alqali da Alhaji Khaleed ne sukai masa kasancewar sa shine qarami a cikinsu,kuma sunaji dashi tun bayan rasuwar iyayensu,to duk abinda Isah yace yana so suma shi suke so, tun yana yaro suka shagwa6a shi abinda yakeso shi suke masa,alokacin Maryam, wato Mamy tagama degree dinta nafarko fannin Nursing,yar asalin garin maiduguri, ganin wahalar datasha a karatun ta yasa ta fad’awa Alhaji Isah cewa itafa bayan auren nan zatayi aiki, bazata bar karatun ta yatafi ahakaba,tanaso tabawa yan’uwanta mata gudunmawa ta fannin karatun ta,Alhaji Isah yasamu yayunsa su Alqali yafada musu qudurin Maryam, Nan take Alqali yace ai babu komai,aikin nata ai 6angaren lafiya ne,inde har tana son d’an’uwan nasu to babu matsala tazo tayi aikinta.
Wannan mataki da Alqali ya dauka yayi bala’in qonawa kilishi rai, tayaya suna zaune agida,za’a bar yarinya tazo cikinsu tana aikin gwamnati? me suka rasa agidan daza’a zo musu da wani fi’ili na aikin gwamnati? hukuncin Alqali baiyi mata dadi ba, daga nan ne matsalar tafara faruwa tsakanin Mamy da Hajiya Kilishi.
Bayan Maryam, wato Mamy tayi sati buyu a gidan Alqali, a lokacin Alqali ya tarasu duka su ukun yayi musu maganar girki, tunda harkarsuce tacikin gida Yaya suke ganin zasu tsara girkin?
Nan take Mamy tace tunda tana aiki, tana ganin kawai kowa yayi nasa girkin,ba zai iyu ace saita dawo daga wajan aiki sannan zata dafa musu abinci ba, lokaci daya Alqali yace hakan bazai iyu ba, shida qannansa qwaya biyu rak a duniya bazai iyu su raba girki ba,hakan yana nufin kenan dan autan su Alhaji Isah haka zata dinga barinsa da yunwa harsai ta dawo aiki ne zata dinga dafa masa abinci, a lokacin Mamy saita nuna masa cewa inde cikinsu ne daga ita Sai mijin ta Alhaji Isah,bazata bar mijin ta da yunwa ba, amma Alqali yace Bai yarda da wannan batu nataba,dole zasu hade girkin su, sai Mamy tace to tunda ita tana fita aiki, tana neman Alfarmar su Hajiya kilishi da Mama sadiya abar mata Iya weekend su sai suyi sauran ranakun, nan take Hajiya kilishi ta watsawa Mamy harara tace bazai iyu ba, a dinga yi kwana bibbiyu, babu wani weekend daza’a barmata,Alqali baiji dadin furucin kilishi ba, amatsayinta na babba a cikinsu kamata yayi ace taja matan qannan nasa a jikinta, su zama qawayenta kuma qannanta, koba komai matar autan nasu alfarma tanema akan su bar mata weekend din,kuma babu wanda yawuce yanemi alfarma, to har zai dauki mataki saiya fasa ganin harkar suce ta mata, daga haka taron ya tashi.
Ko wata uku ba’a yi ba,Hajiya kilishi taga Mamy bata musu girki akan lokaci, saita dawo daga wajan aikinta sannan ne zata fara shirin dora musu abinci, sauqinsu daya idan aikin yamma takeyi, to shine kafin tatafi take musu girkin,kuma Mamy Bata girkin gargajiya,saboda tana aiki da kudin ta take kashewa tayi girki mai rai da lafiya,wanda duk wanda yaci, saiya so ranar girkin ta yasake zagayo wa, to daga nan ne Kilishi tayiwa Alqali magana yakamata asake zama akan batun girkin nan, Maryam bata musu abinci akan lokaci idan aikin safe ne da’ita saita taso wajan karfe uku na aana sannan za’a fara shirin dora musu abinci,tosu yanzu sun yafe gara ta dinga yi da weekend din kawai,(😂)
Alqali yayi murmushi bai tanka ba,tun farko abinda yahango musu kenan, shiyasa yaso subata weekend din, tunda Alfarma ta nema,sannan itace qarama a cikinsu kuma matar dan autansu, kamata yayi su ja yarinyar a jikinsu musanman ma ita Hajiya kilishi tunda itace babba, amma mugunta ta rufe mata ido, takasa gane hakan tun farko.
Haka Alqali yayi mursisi yaqi saka baki akan maganar girkin.
Mamy tanada masifar haquri,zaiyi wahala kaga 6acin ranta,tana zaune da kowa lafiya a cikinsu Kuma da zuciya daya, tanajin dadin yanda Mama Sadiya take janta ajiki,nan da nan sai suka saba, suka zama kamar qawaye,duk lokacin da Hajiya kilishi ta 6atawa mamy rai, Mama sadiya ce take bata haquri, kuma Mamy bata ta6a fadawa mijinta ba, saide tabar abun aranta.
Tunda tazo gidan ta lura kwata kwata Hajiya kilishi bataso su Ashraf suzo wajanta,koda wasa taga sunyi hanyar part din Mamy toda gudu zataje ta janye su, abun baya yiwa Mamy dadi, tana bala’in qaunar yaran, amma babu damar daukar su saide tadinga leqensu daga nesa.
Hajiya kilishi ganin Alqali yaqi kula maganar ta dangane da girki, hakan yasa wata rana Mamy tana girki Hajiya kilishi taje ta sameta a kitchen din tayi mata tatas,Mamy ko uffan batace mataba, ganin Mamy taqi tanka mata yasa tafara zaginta, tayi mata zagi nacin mutunci,hartana fada mata yar gidan talakawa wadda take aiki saboda talaucin iyayenta, juya….wacce bata haihuwa tunda tazo gidan ko 6ari bata ta6a yiba(😥)
Mamy bata ramaba saide kuka da takeyi duk da hakan tana bata haquri,ashe duk abinda ake Alqali yana ganinsu yazo wucewa,cikin 6acin rai yayiwa kilishi magana cikin tsawa,itama 6acin rai ya rufe mata ido tarama,nan take babu 6ata lokaci Alqali yabawa Hajiya kilishi jan Kati, yayi mata saki daya(🙆🏻♀️)
Sannan agabanta yaje yadauko Ashraf da Aryan yace yabawa Mamy su halak malak(😳)
A wannan lokaci kilishi hauka ne kawai batayi ba,taji tsanar Mamy tasake nunkuwa aranta,tanaji tana gani haka tabar ‘yanbiyunta a hannun matar data tsana tafice tabar gidan Alqali.
A lokacin Mamy tajasu ajiki sosai kamar ‘ya’yanta,musanman yanda takeson haihuwa amma gashi Allah bai bataba, idan taje asbiti taga mata sun haihu tadinga kula da yaran kenan bata kyamatarsu, hakan ne yaja mata farin jini a wajan aikinta,dama hajiya kilishi ce tayi mata iyaka da ‘yanbiyun, amma tana sonsu sosai, Alqali yana danqa mata su kuwa tabude bakin aljihu tadinga yimusu siyaiya, shikuma yaro inde za’a bashi, musanman kayan chocolate to yanzu zaka siyeshi, tun basa sakin jiki da’ita har suka dawo suka saba da’ita,sune suka fara kiranta da MAMY, tun suna yara Mamy ta lura Aryan baya son surutu,yafison ya zauna yanata game da wayarta,koda tajashi da zance irin dan surutun nan na yara saide taga yace mata eh kokuma a a,saide in yanason abu zaice Ma-my inason sweet, kokuma Ma-my ruwa, kai tsaye de yace Mamy,ba zakaji yafadi hakaba, wannan saide Ashraf, amma shide Aryan a rarrabe yake kiran Sunanta.
Tayi amfani da hikima sosai wajan shawo kan yaran,haka kawai tana dawowa daga wajan aiki zata cire uniform dinta tasa qananun kaya tadinga goyasu sunata wasa saide Alqali yajiyo su sunata qyalqyala dariya,da yamma haka zata musu wanka ta shirya su tsaf suyi kyau, sufuta wajan wasan yara takai su suyi wasa son ransu, sannan su dawo gida,harta kai takawo idan zata fita aiki ma dasu take tafiya, kowa yasan su a wajan aikinta,qawayenta na wajan aiki har chocolate suke kawo musu, wasu Kuma kayan wasa suke kawo musu,mutane dayawa suna tunanin ma yaranta ne, saide su din farare ne sosai kuma identical twins kwata kwata baka banbance su,amma ita kam sarai tana ganesu, kai tsaye zata nuna Ashraf tace wannan ne babba, shikuma Aryan rashin surutun sanema yakesa nan da nan aganeshi, amma kuma idan shida Ashraf ne har mamakin yanda yake surutu take,inde dagashi sai dan’uwan ne yanzu zakaji yanata masa magana, daga qarshe a kaure da fad’a, saide fadan nasu baya zuwa ko’ina zakaga sun shirya, Mamy tasan halin kowa a cikinsu, Ashraf gaba daya halin Alqali yad’auko, babu ruwansa, inde yazo waje sai kasan yazo,haka idan tahada musu tea dasafe, gashi de tea din bawani zafin kirki gareshi ba,haka Ashraf zai dauka yasha abunsa, yayinda Aryan yadebo halin Hajiya Kilishi gaba d’aya,tun yana qarami Mamy ta fahimci yanada son girma, baya son raini, gashi de shine qarami amma Ashraf bai Isa yace ya girmeshi ba,kuma kokadan bayason zafi,shide kawai sanyi, idan tahada ruwan dumi zata musu wanka nan da nan zai fara kuka shi bazata masa da ruwan dumi ba saide na sanyi, ita kuma tana tsoron kar ruwan sanyin yayi masa illah, haka zata riqeshi yana kuka yana cewa ruwan da zafi, ahaka suke wankan kullum, idan Ashraf yaga Aryan din yana kukan ruwan zafin saiya saka hannunsa acikin ruwan, ya kalli Aryan din yace kaji ruwanfa babu zafi(😂)
Darana kuwa taci karo dawata baqar kunama a qofar dakinta,cikin tsoro tajuyo aguje,suma suka bita da gudu suna dariya,mamaki ya kamata,tadauko abu zata kashe Ashraf yace shine zai kashe,yasaka hannu ya dauki kunamar shima Aryan yace saiya bashi,shikuma Ashraf yahana,lokaci daya kunama tahada su fada, ganin ana qoqarin fada akan kunama kuma gatanan tana ganinta qiri qiri a hannun Ashraf lokaci daya Mamy ta suma a tsaye, batasan lokacin data saki qaraba,tariga tabayar kunamar zata cutar dasu.
ganin tana kuka yasa suka dawo wajanta suma suna kuka,saida tagama kukan tafara lallashin su anan taga babu kunamar a hannun su babu dalilin ta,haka tayi shiru da bakinta bata tambayesu Ina take ba.
Haka Mamy tadinga kula dasu, yanda take kaffa-kaffa dasu yasa su kayi mugun sabo da Mamy, yanda suke liqe mata saika rantse itace ta haife su,ko dare yayi bazasu kwanta ba saide a jikinta, haka zata tofesu da Addu’ah har suyi bacci, saide cikin dare ta lallaba ta gudu wajan Alhaji Isah,suyi abinda zasuyi (🙈)
kafin ace sun farka sun fahimci bata wajan su zata dawo cikinsu suci gaba da baccin, kuma hakan kokadan baya damun Alhaji Isah saboda qarancin kulawar dayake samu a wajanta, saima dadi da yakeji yanda take riqe ‘ya’yan dan’uwansa kamar itace ta haife su.
Sun kwashi watanni a wajan Mamy,yau suyi fad’a tadinga rabiya, gobe azauna kalau ahaka har sukayi mugun sabo da’ita, komai Mamy,bakajin komai a bakin su sai maganar Mamy, ta rainesu yanda ya kamata, raino wanda zaiyi wahala yaro ya manta da uwar rainon sa.
Ganin Alqali yayi mursisi baije bikon Hajiya kilishi ba, hakan yasa tadinga yiwa yan gidansu magana har sukuma suka yiwa Alhaji Khaleed da Alhaji Isah magana, suka basu haquri akan laifin kilishi suka roqesu Alfarmar suyiwa yayansu Alqali magana akan dawowar kilishi dakinta,domin sude bazasu Iya tunkarar sa da maganar ba, domin kuwa Alqali akwai kwarjini,hakan akayi kuwa, Alhaji Isa da Alhaji Khaleed sune suka shige gaba, aka maida auren Hajiya kilishi da Alqali Ibrahim,suka sake bawa yayan nasu haquri akan katsalandan din dasuka masa, badan Alqali yaso ba, haka yayi haquri kilishi ta dawo dakinta, bayan alqawari data dauka masa cewa hakan bazata sake faruwa ba.
Mamy kuwa tayi tunanin ganin hajiya Kilishi tadawo zaisa su Ashraf su koma wajanta, saitaga yara sunyi mursisi sunqi komawa wajan Hajiya kilishi,irin murnar nan ma taganin uwa sude ba suyi ba, saida Alhaji Isah yasata tahada musu kayansu sannan yace tarakasu wajan mahaifiyar su, a lokacin data gama hada musu kayan harda kukanta, a lokacin yarinta tasa basu fahimci kukan me takeba,Ashraf ne yafara matsowa yana goge mata hawayen,amma shikam Aryan da bai Iya lallashi ba shima saiya kwanta a cinyarta yafara kuka (😂)
Haka tarakasu wajan Hajiya kilishi, tayi mata sannu da zuwa ta amsa mata da qyar, itade Mamy ahaka ta futo tabarsu tareda mahaifiyar su.
Tunda Hajiya kilishi tadawo taji suna kiran Maryam da Mamy,babu 6ata lokaci tahanasu fadar sunan, saide suce Anty, sukuma basu saba da Anty ba, da Mamy suka saba, dan dolansu babu yanda suka Iya shine suke kiranta da Anty Mamy,maimakon suce Anty kadai,sai suka hada mata duka biyun suke kiranta da Anty Mamy
Bayan wasu shekaru suna kammala primary school dinsu Mama Sadiya ta haifi yarta mace, aka sanya mata sunan Mahaifiyar su Alqali, suna kiranta da NABIHA, adede lokacin Alqali yafitar dasu qasar waje karatu,saida karatun su yayi nisa sosai sannan Allah yabawa Mamy ciki,ta haifi yarta mace mai tsananin kyau kamar balarabiya,mahaifinta ya sanya mata suna RUQAYYA,Mamy kuma take kiranta da MAWAHIB.
ma’anah (MAI YAWAN KYAUTA).
Mawahib tun tana qaramarta Allah yayi mata diri,tanada jiki mai daukan hankalin samari, tanada sanyin hali kamar Mamy, kwata kwata batada hayaniya,Allah yayi mata baiwar hips kamar ita ta sakawa kanta,saide batada cikar qirji, boobs dinta ba manya bane kuma ba qananu bane, ‘yan madedetane hakan ne yasa suke a tsaye qyam….
Mamy da Abbanta sunaji da’ita,sosai Mamy take siyo mata qananun kaya daga nashan is’ka harna bacci, haka zata saka kayan ta tayi uzurinta Iya part dinsu babu wanda yake mata magana, haka 6angaren kayan kwalliya ma ba’a barta abaya ba,idan Mawahib ta dauki kwalliya babu musu zakace mata yarinyar Momy da Daddy ce,saide bahaka bane,kawai Mamyntace ta tsaya mata take shigar ta yanda taga dama, tunda samarin gidan bawani zama suke ba.
Aqasar waje su Ashraf sukai secondary school dinsu,suka dora da jami’ah,bayan sungama jami’ah suka nunawa Alqali cewa suna so suzo gida, yace su dakata suyi masters tukunnah,duk tsawon wannan shekarun Mamy tana nan a ransu, tun basa fahimtar mahaifiyar su Hajiya kilishi bata son Mamy, har suka dawo suka gane,idan suka tambaye ta awaya Ina Mamy nan da nan Hajiya kilishi zatayi kicin kicin darai ta nuna musu batason mu’amularsu da wannan matar.
Haka sukai haquri basuzo gidaba saida suka kammala karatun su kamar yanda Alqali yakeso, sannan suka dawo gida, anan sukaga an sauya tsarin gidan, ansake masa fasali, anyi masa get biyu,gida yakoma gidan zamani ankashe masa dukiya, a wannan lokacin Alqali yayi ritaya,yana zaune agida yana hutawa,duk wani nauyin kula da gidan yakoma kan Alhaji Khaleed mahaifin Nabiha, saikuma Alhaji Isah mijin Mamy, gida de ya sauya, saide halin Yan gidan dabai canja ba(😂),tunda suka dawo Ashraf yaga Nabiha da Mawahib shikkenan yake jansu a jikinsa, musanman Mawahib din Mamy, yana bawa Mawahib kulawa yanda ya kamata, jinta yake aransa kamar me,duk abinda takeso nan da nan zakaga yaje yasiyo mata,amma kwata kwata baya bawa Nabiha wannan damar, tsakanin sa da’ita saide gaisuwa amma fuska asake yake amsawa, shikuwa gogan ko a jikinsa, daga Mawahib din,har Nabihan, gaba dayansu baya shiga sabgarsu, kwata kwata baya son raini, suma su Mawahib da sukasan halinsa koda wasa basa shiga harkar sa.
Bayan sunyi bautar qasa Ashraf yasamu aiki a NNPC dake Rivers state,shikuma Aryan dama burinsa yasamu aikin soja,kuma yasamu, har yakai matakin CAPTAIN,shiyasa su Mawahib suke kiransa da YAYA CAPTAIN, yana aikinsa a Abuja,bai cika zuwa gida sosai ba, Ashraf ya fishi zuwa gida.
Kamarsu daya da Ashraf sak,zaiyi wahala ka banbance su idan suka saka komai iri daya,suna fad’a ajunansu,saide fad’an nasu babu inda yake zuwa nan da nan zasu shirya, idan Ashraf yayi budurwa shima Aryan yana ganinta zaiji yana sonta, daga dawowar su daga qasar waje zuwa yanzu dasuke aiki Ashraf yayi ‘yanmata dayawa, amma wai irin ya nunawa dan’uwansa sabuwar budurwar da yayi, sai shima Aryan din yace wallahi sonta yake (😲)
Babu yanda Ashraf zaiyi saide ya haqura da yarinyar tunda bazai iyu su auri mace daya ba, sunyi haka yakai sau biyar,kuma shima Ashraf din dan masifa kamar anyi masa dole muddin yasamu budurwa saiya nunawa Aryan ita,shikuma yana ganinta kai tsaye zai fada masa wallahi Shima yana sonta,haka Ashraf din zaiyi haquri yabar masa yarinyar kokuma su barta duka su biyun,shikuma captain Aryan baya kula yanmata bare ayi tunanin zai samo wata, yana zaune saide in dan’uwan yasamu, yace shifa duk duniya shima wannan yarinya yakeso,haka zasu haqura da yarinyar gaba dayansu.
Ashraf yanason ruwan zafi,halinsa sak irinna Alqali, shiyasa koda yaushe yake ta’ammali da tea,kuma babu ruwansa da zafin tea dinnan haka zaisha abunsa, amma captain Aryan bahaka bane, kokadan baya hada hanya da ruwan zafi, yafison ruwan sanyi, duk sanyin da ake agari bazaiyi wanka da ruwan zafi ba, dana sanyi zaiyi, wannan dabi’arsu ce tun suna Yara.
Har zuwa wannan lokacin Hajiya kilishi bataso su ra6i Mamy,amma har yanzu suna sonta,kuma suna mu’amula da’ita dan dole Hajiya kilishi ta haqura tabarsu.
Fatan Alqali da Hajiya kilishi shine su samu mata suyi aure, Hajiya kilishi ta dauki buri ta dorawa yanbiyunta kawai so take su samo mata yanmata nagani nafada na kece raini suyi aure irin auren ‘ya’yan Masu dashi dakuma ‘ya’yan masu mulki, amma har yanzu basu kawo kowacce yarinya gida ba,har gara Ashraf yana dan kula Mawahib,yana Jin dadi idan yaganta, yana sakata aiki kamar gyaran dakin su,girki marar wahala,yana wasa da dariya da’ita, amma baya kula Nabiha sosai, amma ita kullum tana tasa,bata da aiki sai tambayar Mawahib yaushe Yaya Ashraf zai dawo,? Sunyi waya da Yaya Ashraf?
Cigaban labari:
Dasafe Mamy tagama shirinta tsaf domin tafiya wajan aiki, tashiga dakin Mawahib taganta a kwance a gadon ta tayi d’aid’ai tana bacci,dogon gashin kanta duk ya barbaje akan katifar,tana sanye cikin wata yar 6ingilar rigar bacci gaba daya rigar iyakarta rabin cinyarta,hakanne yasa fararen cinyoyinta suka futo muraran,babu bra ajikinta amma yan madaidaitan boobs dinta suna nan a tsaye cak har kana Iya hango tsinin nipples dinta.
Mamy bata damu da kayan dayake jikin Mawahib ba, asalima itace take siyo mata su,tana duba agogon dake daure a hannun ta,mai mutuqar tsada, sannan tasaki dan qaramin tsaki tace”Mawahib tashi daga baccin nan haka, kina sana’ar taki ta bacci ko gidan baki gyaraba”
Cikin shagwaba tace”Mamy ramuwar baccin exam nake fa…”
“kitashi haka kiyi break fast kar yunwa ta kamaki,akwai kudi agefen gadona Abban ki yace ki dauka kije gyaran jiki,karki yarda kidawomin gida da wannan gashin naki babu gyara”
Idonta a lumshe tace”to Mamy saikin dawo”
Bayan Mamy tafita a hankali tazuro qafafunta qasa, tashafa shafaffan cikinta,sannan ta wuce toilet tayi brush, ta futo ta gyara musu part din nasu, ta kunna turaren wuta, ko’ina yadauki qamshi, sannan takoma daki tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga Abaya,wadda ta bude daga qasa, daga sama kuma ta fitar da shape din qirjin rigar, abincin tazuba tafara ci a hankali kamar bataso, adede lokacin Alhaji Isah Yafuto cikin shirin fita aiki,cikin sauri ta gaida shi, cikin mamaki yace”a a,karfe nawa yanzu baki tashi kinci abinciba sai yanzu kike break fast? meyake damunki ne Ruqayya? ”
Saitayi wani sororo kamar bada ita yake magana ba,saboda ita kanta mantawa take Sunanta Ruqayya, saboda Mawahib din da’ake fada mata ya6oye Ruqayyan.
Cikin shagwaba tace”Abba bacci nakeji sosai shiyasa”
Kansa ya girgiza yace”kiyi sauri kifuto Ina jiranki saina saukeki kafin in wuce”
Bai jira amsar taba yawuce, cikin sauri tahada tea tasha, sannan tadauko hand bag dinta yar qarama mai kyau, tazuba kudin da Abban yabata, sannan ta futo, key tasa tarufe part din nasu, sannan ta wuce part din Hajiya Kilishi kamar yanda Mamy takafa mata doka kullum taje part din kowa ta gaishe su, tun kafin ta qarasa part din taji wani qamshi mai dadi ya bugi hancinta,a hankali ta lumshe Idonta, sannan ta bude, qamshin yayi mata dadi, cikin nutsuwa tatura kofar falon tashiga, dashi tafara yin tozali da alama saukar dare yayi, shiyasa batasan da zuwan sa ba,kyakykywan saurayi ne mai kyau da aji kana ganinsa kasan zaikai shekara 37,sumar kansa sai wani sheqi take,ga wani saje daya sake qawata farar fuskar sa,yanada dan qaramin lips launin ja.
tun kafin tagama qarasowa cikin falon Hajiya kilishi tafara watsa mata wani irin mummunan kallo,duk da tana shakkar Hajiya Kilishi, hakan baisa ta 6oye murmushin ganin Yaya Ashraf ba, cikin ladabi ta tsugunna tace”Momy Ina kwana?”
Daqyar Hajiya kilishi ta amsa,murya can ciki tace”lafiya…”
ta amsa tana qarewa surar jikinta kallo, shikuwa Ashraf kamar wanda tatafi da imanin sa tana shigowa haka yabita dawani irin mayen kallo,shi kansa baisan lokacin dayabita da wannan kallon ba,da alama yama manta da’inda yake zaune(😲)
Tun kafin Mawahib ta gaida Ashraf,Hajiya kilishi tace”Ina ganin ikon Allah ni kilishi…..ke Kuma irin tarbiyar da uwar taki take baki kenan? bazaki Iya jira akaiki gidan miji ba tun a titi zaki fara nunawa duniya jikinki? Kuma ahakan kuke neman miji nagari ko? banga sallaman man dazai kwasa ba….”(😢)
Cikin sauri Ashraf ya runtse idonsa,bayason wannan furucin datake yiwa Mawahib,bayajin dadinsa ko kadan.
domin ya katse zancen, ya Kalli Mawahib wadda ta sunkuyar da kanta qasa tana wasa da dogayen yatsun hannunta, qiris yarage tafashe da kuka, yace”Mawahib zaki fita ne?”
Cikin sanyin jiki tadaga masa kai batareda tace uffan ba,domin kuwa bazata Iya magana ba, inde tace zatayi magana to kuka ne zai biyo baya,a hankali tatashi ta futo daga falon.
Tana fita Hajiya kilishi ta kalleshi Cikin fada tace”Ashraf kafita daga harkar yarinyar nan,banason Jin wata magana daga baya,koda wasa banason ganin wani abu yashiga tsakanin ku,naci buri akanku sosai,sonake kuyi aure nagani nafada auren kece raini,shiyasa ARYAN yake birgeni, saboda baya shiga sabgar wannan yarinyar”
Ashraf yayi murmushi tareda shafa sumar kansa yace” kiyi haquri Momy”
Tana barin part din Hajiya kilishi qunci da damuwa yasa ko kallon part dinsu Nabiha batayi ba bare tashiga, wani irin kuka ne ya taho mata,to amma data tuna Abban ta yana jiranta a waje, zai gane tayi kuka, Sai tayi sauri tadaga fuskarta sama, tana kokarin maida hawayen,tarasa me matar nan take nufi da’ita, nafarko ita batace tana son ‘ya’yantaba, tarasa meyasa tasata agaba,kuma Mamy taqi fada mata Dalili…..