Kayar Ruwa Hausa Novel Complete

Kayar Ruwa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Kayar Ruwa Hausa Novel Complete

*_BISMILLAHIR-RAHMANIR RAHIM. dukkan yabo ya tabbata ga Allah (S.W.T), ina gode masa, ina neman agajinsa da gudunmawarsa da taimakonsa. Salati da sallama da ɗaukaka da daraja, su tabbata a bisa manzonmu Annabi Muhammadu (S.A.W), cikamakin Annabawa shugaban mazanni, wanda Allah ya aiko domin ya zama rahma ga al’umma. Ina roƙon ya Maliku da ya ba ni ikon rubuta abin da zai amfanar da alumma, ya hane ni rubuta abin da zai ruguza al’umma, Ya Hayyu Ya Qayyum yanda na fara lafiya kasa in gama lafiya._*

Huriyya by Khadija Candy Hausa Novel

*_Gaba ɗaya littafin sadaukarwa ne ga Hajiya Binta Garba Saleh Daudawa, Alkhairin Allah ya isar miki, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana, ya biya miki dukkan buƙatunki, yasa ayi kyakykyawan ƙarshe._*

__________________________________

*_Littafin Tukwici ga Fatima Sulaiman Mum Aysar, tabbas ke ɗin ta dabance, ina matuƙar godiya ga ubangijina da ya haɗani da ke a rayuwa, ina kuma roƙonsa da ya lulluɓe rayuwarki da rahamarsa, ya bani ikon kyatata miki da faranta miki, ya baku zuri’a ɗayyiba masu jin ƙan ku, yanda kika sanya farinciki a fuskata ubangiji ya bani ikon sanyaki sama da haka, Allah ya ja da ran mahaifa yasa ayi kyakykyawan ƙarshe._*

______________________________

*GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI GA:-*

*•Anty Habiba Abubakar Imam*

*•Sadiq Abubakar(C.E.O Lafazi Writers)*

*•Jamila Umar Janafty*

*•Safiyya Huguma*

*•Mamugee*

*_Allah ya shiga lamuranku._*

______________________________

*JINJINA ZUWA GA:-*

*•Muhammad Kareem*

*•Jibrin Adamu Rano*

*•Abu Hisham*

*•MD Asnanic*

*•Zaharadden Hazazi*

*•Kabir Yusuf Anka*

*•Rabi’u Lallan*

*•Fatima Musa Anty Nice*

*•Ramlat Mai Dambu*

*•Da dukkan ƴan cikin group na FITATTU BIYAR LIBRARY*

______________________________

*YABO NA MUSAMMAN ZUWA GA:-*

*•Ya Aisha(Mum Sayyeed & Noor)*

*•Anty Bilkisu Rabi’u Ado*

*•Anty Bilqees*

*•Ya Nusaiba*

*•Jamila M Ladan*

*•Ummu Abdallah*

*•Anty Halima Mabo*

*•Aisha Aliyu(Maman Baffa)*

_______________________________

*_Sannan ga masoyana kuma makaranta littafaina, ba ni da bakin godiya gare ku, ba zan gajiya da yi muku adu’a da godiya ba bisa goyan bayan da ku ke ba ni, Allah ya faranta muku ya yafe muku zunubanku, yasa ku gama da duniya lafiya, masu fuskantar ƙalubale a dalilin jinkirin aure ubangiji yasa hakan ya zama alkhairi babba a gareku, haka masu fuskantar ƙalubale a zamantakewar aure Allah ya gyara lamura…A wannan karon dai tafiyar ta dabance, kusa kuɗi ku siya, ba zaku yi nadamar siya da karantawa ba, a nuna min son so…har kullum ƙofa a buɗe take domin karɓar saƙonninku._*

_______________________________

*_All rights reserved. No part of this book may be reproduced or transmitted in any form without seeking permission from the writter. This novel is a work of fiction, Names, characters, business, places, events, and incidents, are either the products of the author’s imagination or used in a fictitious manner. Any resemblance to actual persons, living or dead, or actual events is purely coincidental. A person who commits an act of piracy, is liable on conviction to life imprisonment and a fine of not more than N50,000,000…So becareful of copying any part of this story._*

*©️Copyright2023 Halimahz.*

_________________________________

*SHIMFIƊA.*

_A wasu lokutan da bamu tsammaci rikicewar al’amura ba, sai ya zamana al’amuran sun runcaɓe mana babu zato babu tsammani. rayuwa kan canja tayi juyayi da mutum, wasu ta juya da su duniyar rikicewa, firgicewa da tashin hankali har mutum kanji tamkar shi kaɗai aka tsana, yayin da a gefen wasu juyin rayuwa kansa su mance da baƙin ciki, haushi, da damuwa, su dulmiya a jin daɗin rayuwa. babu abin da bai da farko, babu abin da bai da asali, haka babu abin da bai da tushe, kazalika babu abin da bai da ƙarshe, sai dai yarda da Allah kan tafiyar da komai cikin daidaito._

_kamar dai yanda darasi ya ke a matsayin koyarwa da miƙa saƙo, hakan yasa a yau zan rubuta labarin rayuwarmu, sunana Sa’ida Salman, kuma wannan shi ne labarin *ƘAYAR RUWA*…_

________________________________

*(1)*

Kwance na ke akan makeken italian royal bed a cikin tamfatsetsen ɗakin barcina. Wayata ƙirar S22 na gefena ina sauraren karatun alqur’ani mai girma cikin ƙira’ar Muhmood Hosary, idanuwana a lumshe suke tamkar mai bacci, sanyin acn da ke busawa na bin dukkan ƙofofin gashin jikina, yayin da gefe guda hancina yake shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren wutar da na kunna a burner wanda ba ya ko ƙaurin kamawa saboda irin salon yanda nake bi wajen sanya shi.

 

Sanye na ke cikin doguwar rigar material mara nauyi, rigar na ɗaya daga cikin sutturun da nake so sosai a kayana duk da material ɗin ba wai mai tsada ba ne, fuskata fayau babu kwalliya ko ɗiso, sai hakan ya ƙara fito da ramar fuskata.

 

Gaba ɗaya yau jina nake yi kamar mara lafiya kuma kaman an yi min mutuwa, sai dai babu ko ɗaya a ciki, tun safe da na tashi bakina babu ɗanɗanon komai ga tsananin faɗuwar gaba na damuna, hakan yasa tun lokacin nake ta adu’oi da tasbihi, kuma karatun ƙur’anin da na kunna ina saurare ina bi shi yake d’ebe min kewa, to amma dai duk da hakan ina ji a jikina cewar akwai wani babban al’amari da zai girgiza duniyata nan kusa, ina jin kamar nan kusan zata zamar min ƙarshen komai na rayuwata ne.

 

Ajiyar zuciya na sauke mai nauyi, na juya kwanciyar da nayi inda a yanzu na ke fuskantar bakin ƙofar shigowa, cikin zuciyata ina roƙon ubangiji da yasa komai zai faru ya zama alkhairi, ya kuma ba ni ikon cinye kowacce kalar jarabawa da iya ɗaukan ƙaddara.

zoben azurfar da ke hannuna na ke ta kallo ina jin wani abu mai girman gaske na tsarga min, yayin da tunanin wasu shekaru yasa fuskata ƙwacewa da murmushi mai faɗi, murmushin da za’a kira shi da na yaƙe.

 

Wayata na ɗauka don duba lokaci, ƙarfe biyar da mintina na yamma ya nuna min, zaune na miƙe da mamakin gudun lokacin a cikin raina na furta “har biyar?, Lallai duniya na gudu, Allah kasa mu cika da imani”.

 

Da azama na zuro ƙafafuna ƙasa ina gyara ɗaurin ɗan kwalina, ji nake kamar zan faɗi saboda rashin ƙwarin jiki, kaman wadda ta sha zawo ya zabgar da ita a yini ɗaya. Tsayuwa nayi gaban tafkeken madubin ɗakin na tsaya ina ɗaukar tissue in shiga goge kwantsar ciki saboda ciwon idon da nake fama da shi daga shekaran jiya zuwa yau.

 

Kallon kaina na tsaya yi a cikin madubin, lallai in har akwai rayuwa da shekaru to tabbas akwai sauyi, gaba ɗayana kamar ba ni ba, kallo ɗaya da zaka min ba sai ka ƙara na biyu ba zaka ga zallar ƙuruciyar da ke kan fuskata, wanda zai bayyana maka cewar shekaruna ba su da yawa. Sai dai kuma in har kayi min farin sani a baya, to a yanzu zaka ce na sauya, ba wai sauyi na ɗabi’a da halayya ba, a’a sauyi na halittar jiki. A baya ni ɗin ƴar duma duma ce mai kyawun dirin jiki tubarakallah, ina da irin jikin nan da babu kalar damuwa balle yunwa, saɓanin yanzu da ko’ina a jikina ƙashi da jijiyoyi ne suke magana, ido kuwa ramar da ta fito da shi waje yanda kasan na mujiya, gefen kumatuna duk ya zurma ciki, shi kansa uban hasken da nayi ba na komai ba ne sai na shegiyar ramar da nayi, albarkatun ƙirjina kuwa duk sun kwanta shalaf kamar wacce ta shayar da ƴaƴa ɗari, duk na zama wata babu kyan gani kai baka ce me tashen ƙuruciya ba shekaru ashirin da huɗu a duniya.

 

Lokaci guda idona ya cika da tarin ruwan hawaye, sai dai basu sami nasarar zubowa ba, cikin yanayi na bala’in tausayin kaina na sunkuyar da kaina ƙasa ina jin wani dunƙulallan abu na tsaya min a maƙogoro yaƙi wucewa, hakan sai ya zama famin ciwo a gare ni, wanda da zan samu in korashi da yawun bakina ko kuma ya wuce da kansa wataƙila da na sami sassauci. Cikin ƙarfin halin da na saba na ɗago kaina ina mayar da tarin ƙwallar da ta cika min ido, ɗakin kawai nake bi da kallo, ko a iyaka shi aka bar bawa rayuwa ya ishe shi jin daɗi da more rayuwa, damuwarsa ta gushe, ballantana kuma ace rayuwa kake yi a cikin tamfatsesen gidan nan da yake sai kace a ƙasashen turawa, lumtsum nake a cikin daula, duk wanda yazo gidana ba ya son tafiya, iya dukiya dai an narkata wajen ginin gidan, zaka rantse da Allah ba duniyar da talakawa ke rayuwa ba ne, idan ba Allah ya soka da rahma ba sheɗan sai ya shagaltar da kai da yin ibada.

 

Sau tari ƙawayena da ƴan uwana kan ce min ke kam Sa’ida kin more, ba ki da saurin baƙin ciki da takaicin duniya domin Allah ya kashe ya ba ki, arziƙi ta ko’ina, kalli gidan da kike ciki kamar ba za’a mutu ba, irin motocin da ake fita da ke a cikinsu zamansu kaɗai yasa kiyi ƙiba ki fresh, abinci kullum da nama, ke kam ba ki da sauran damuwa, ba su san da cewa ba anan take ba wai abin da yawa mutuwa taje kasuwa, sai da kwanciyar hankali ake jin daɗin.

 

Madubin da ke gabana na kalla da kyau, na sauke babbar ajiyar zuciya tare da yin murmushi mai ciwo, ina mamakin masu faɗa min irin wannan zantukan, ban sani ba ko iyaka daular da Allah ya ajiye ni a ciki kawai suke kallo shiyasa ba su taɓa lura da cewar akwai ƙalubale mai wahala a gefe, bana jin daɗin gidan, bana farin ciki sam, su ka kasa ganin irin lalacewar da nai, su ka kasa fahimtar gwara ma rayuwata ta baya akan ta yanzu, su ka kasa fahimtar ina da buƙatar taimakonsu. Su na ganin cewa zan iya yi musu komai tun da su na kiran wannan ƙaton gidan da gidan Sa’ida, ba su san cewar babu abin da zan iya, domin ba ni da komai, tun da komai ɗin da su ke kallo ba mallakina ba ne ba taƙamata ba ne.

 

Ƙwarai kuɗi da rai da lafiya rahma ne, kuɗi komai ne bayan lafiya, babu abin da yafi ace yau kafi ƙarfin komai, ace yau kai ne kake ɗauka ka bayar ba wai a ɗauka a baka ba, kaci mai kyau kasha mai kyau ka kwanta a mai kyau kasa sutturu masu kyau da tsada, ka hau jirgi ka keta hazo zuwa in da kake so, ka ɗiba ka kashe babu mai ƙayyade maka, kayi mu’amala da mutanen da su ka fika. To amma me?, duk da irin tarin dukiyar da kake da ita, da irin daular da kake rayuwa a ciki, muddin babu kwanciyar hankali to babu farin ciki da jin daɗi. Ni a wurina gwara in rayu cikin talauci akan ace ga tarin dukiyar amma babu zaman lafiya babu kwanciyar hankali balle na sami natsuwar zuciya.

 

Na sake sauke ajiyar zuciya mai nauyi a karo na uku, murmushin da yafi kuka ciwo nayi ina girgiza kaina wanda ni ɗaya na san ma’anar hakan. Abu ɗaya na barwa kaina sani shi ne kowanne matakin nasara ba’a hawansa sai da ƙalubale, kuma komai na duniya fararre ne ƙararre, kuma dogaro ga Allah jari, babu kuma mai yi sai Allah, muddin akwai yau, gobe da jibi to komai zai shuɗe ya zama tarihi. Na gyara ɗaurin ɗankwalin da ke kaina, turare na ɗauka oil na shafa, sannan cikin sanyin jiki da mutuwarsa na fita a ɗakin ina jin ƙafafuna tamkar a ƙanƙara.

 

cikin sauri da rashin jin daɗi a raina da ban ankarewa tafiyar lokaci ba na fita, na san duk inda Hubbi yake yanzu yana kan hanyar dawowarsa gida, wataƙila ma ya dawo ban sa ni ba, tun da ƴan kwanakin nan bana sanin dawowarsa in ba zaman parlo nayi ba, kamar yanda ba zan san fitarsa ba, ga shi ko abinci ban ɗora ba sakacin da ban taɓa yi ba, abincin da idan nayi ma ba’a masa cin kirki ko kuma a barni da kayana, amma duk hakan ba zai sa in daina ba, zan ta ƙoƙarin sauke hakkin da ke kaina na dafawa tun da an siyo an a jiye. Ina fitowa daga bedroom ko ƙasa ban sauka ba don gani nake zan ƙara ɓata lokaci ne.

 

kitchen ɗin sama na wuce kai tsaye, babu ɓata lokaci na buɗe fridge na ɗauko gwangwanin bama da nake zuba dafaffen kayan miya a ciki, ni kam ba ruwana da wahalar jajjage ko markaɗe kullum, da ya jido uban kayan miya na ke markaɗe su in dafa in juye a kwalabe. Ina aiki ina ta muraja’a, A ƙanƙanin lokaci na kammala dafa taliya jallof sai tashin ƙamshin busassan kifi take yi da ƙamshin kayan lambu, na juyeta cikin tsadadden kular abincin da Hubbi yazo da su last week daga dubai, wanda naji Hamida na kuɗinsu ya kai dubu ɗari biyu, bayan nan na ɗauko bilenda na haɗa lemun abarba na juye shi cikin jug.

 

Da kammalawata na kwashi komai na kai parlon Hubbi da ke nan sama na jera akan table, na gyara ɗakin ko’ina ya ɗauki ƙamshi sannan na fito na kulle. da na leƙa parking lot ta window banga motar da ya fita da ita ba na san bai dawo ba, hakan yasa nayi komai a nutse sai dai kuma cike na ke da mamakin rashin dawowar tasa da wuri yau, tun da shi duk inda biyar da rabi take ya dawo gida, da yaci abinci zai kwanta sai an kira magrib zai fita masallaci ba zai dawo ba sai bayan isha’i, in da nake jin daɗi kenan Allah bai bani miji mai son zaman majlisa ba, yafi ganewa zaman gidansa, duk da yanzu na kanyi fargabar dawowarsa duba da bama wanyewa lafiya da shi, ga shi na rasa gane kan dalilin hakan, na rasa silar tashin hankalin, na rasa ta ina aka samu saɓanin.

 

Ɗakina na koma nayi sabon wanka, na fito na shirya cikin riga da skirt na atamfa da ɗinkin yay matuƙar amsar jikina, skirt ɗin ya fito da cikakken ƙuguna, musamman hips ɗina wanda shi ne abu mafi ɗaukar hankali a jikina bayan baiwar madaidatan ƙirji. Na bar ɗakin ina ta baza ƙamshi, duk da halin da na san ina ciki yanzu a rayuwar aurena, hakan ba shi ke hana ni gyara jiki in ci kwalliya in isa ga mijina ba, ba kuma shi zai sa na waje ya shigo in bari ya gane ina cikin matsala ba, na iya sirrinta zaman aurena.

 

In da sabo na fara jure halin ko in kulawar mijina yanzu, hakan yana damuna amma na kan nuna masa bai dameni ba balle hakan ya ƙara ingiza shi, ban taɓa fasa hidimta masa ba, shi kansa ya san ina da mugun haƙuri don idan wata ce tuni anji kansu, a yanzu banda burin da ya wuci mu zauna mu fahimci juna da shi, ya karanta min kuskurena in gyara, domin har ga Allah bana jin daɗin irin zaman da muke yi, auren soyayya muka yi ba auren ƙiyayya ba, kuma tsawon shekara takwas da aurenmu bamu taɓa zaman da za’a ce don mun sami saɓani wai zamu shafe sama da kwanaki babu ruwan wani da wani ba har ta kai ga muna raba makwanci, ga shi yaƙi bani damar magana da shi balle ya karanta min laifina, ni kuma iyakar sanina ban masa wani laifi ba, haka dangisa ma, ban san matsalar da ta gifta a tsakaninmu ba da kowa ke nuna min ƙiyayya ƙuru ƙuru, har shayin shiga cikinsu nake, sun dinga min kallon banza kenan ana jajja baya da ni kamar mai warin jaɓa, sai in shiga taro ma in fita babu wacce zamu yi magana da ita in ka cire gaisuwa da zata haɗa mu, abin da yake matuƙar ɗaure min kai duk wannan matsaltsalun cikin ƴan watanni ne, da can komai lafiya, har gani nake tamkar duk matan duniya babu wacca tayi dacen dangin miji irina, so da ƙaunar da suke nuna min kamar za su cinye ni, miji kuwa ai sai son barka, a ko ina zan bugi ƙirji in ce nafi kowacce mace sa’a, sai dai banda yanzu, yanzu kam ɗaya na ke da wadda aka aurawa mijin da bai sonta.

 

A yanzu haka so nake na samu wani in karanta masa halin da nake ciki ko na ɗan ji sanyi cikin raina, sai dai gaba ɗaya na rasa wa ya kamata nayi maganar da shi, ni dai ban isa na tunkari ƙawa da zancen matsalar zamantakewar aurena ba, ban ma ni da shaƙiƙiyar ƙawa, mahaifiyata kuma bana so na tunkareta da magana makamanciyar wannan, ba don komai ba sai don gudun shigarta damuwa, tun da a ko yaushe burinta taji nace mata lafiya muke babu wata matsala, haka kuma a kullum nasiharta a kaina in ta haƙuri in kuma guji kai ƙorafi domin hakan na ƙara taɓarɓare zamantakewar ma’aurata, kuma bani da Yaya mace ko Ƙanwa balle in shaida musu halin tsananin da na ke ciki, sai Yayyu maza da Allah ya bani har huɗu, su kam bana jin ma zan yi kuskuren musu wannan maganar, kun san ance mai ɗaki shi yasan inda ke masa yoyo, idan zan kira su in kwan dubu ina faɗa musu matsalar da ke faruwa ba zasu taɓa yarda ba, in ace matsalar daga ni ne to nan za suyi saurin cafewa har a iya samun mai zuwa har gidana ya naɗa min na jaki, amma batun wai in faɗa musu laifin Hubbi ne tabbas ruwan ashariya sai na sha na ƙoshi, ba kuma wai don basa sona ba ne, su na mugun sona tun da ni ɗaya ce mace a cikinsu, kuma su na matuƙar tausaya min, amma batun dai su goyi baya ga laifin mijina sai dai ya zama zance, gwarama ranar da Ya Imam ya zo duba ni yaga duk na bushe ya zauna yay min nasihohi masu ratsa jiki akan zaman duniyar gaba ɗayanta ƴar haƙuri ce. Abbana kuwa zafi ne da shi, ina fara faɗa masa zai sa azo a ɗauke ni ko kuma yace in kwaso kayana in taho, duk ranar da mijin ya san darajata yazo ya bada haƙuri in koma ko ya rabar masa da ƴa, ni kuma ko kusa bana son abin da zai ja igiyar aurena ta sami tangarɗa, ina cikin matan da za su iya shanye kowanne kalar baƙin cikin gidan aure akan dai a sake su, wani waje daban ma ban so inji aure ya mutu bare a kaina.

 

Tun barowata sama har na sakko ƙasa kiran lambar Hubbi nake yi bata shiga, zuwa yanzu da akai magriba hankalina ya kai ƙololuwar tashi, ga dai shi ba wai dare ne yayi ba, to amma ban saba ba, tun aurenmu sau ɗaya ya taɓa kaiwa bayan isha’i a waje, shima kuma dalilin hatsarin da ya samu ne, shiyasa ko yanzu nake ta jin kaman da akwai wata matsalar, sai dai ina ta kore mugun saƙe saƙen da zuciya ke min.

Mayafi na yafa na fita, mai gadi na hangoni ya taso da sauri ganin na fito a furgice, gabana ya russina yana tambayar lafiya, da ƙyar na daure na haɗiye kukana nace masa.

 

“Tun da Hubbi ya fita bai dawo ba ne?”.

 

Mamakin tambayar tawa ya bayyana ƙarara a irin kallon da yake min, na san mamakin bai wuci ace ni da za’a tambayi fita da dawowar mijina ba amma wai ni ce ke tambayar.

Cikin girmamawa yace da ni,”Hajiya ai bai jima da fita masallaci ba, amma dai da mota ya fita inaga ba masallacin nan kusa ya tsaya ba”.

 

Wani ƙunci naji ya ziyarci zuciyata, na kawar da ɓacin raina da damuwata nace,”ok”. Abin da na iya faɗa kenan na wuce na bar wajen, don idan nace zanyi doguwar magana tabbas sai ta tsarƙe da kukan da nake dannewa.

 

Ina komawa ciki na shiga bedroom nasa na ƙasa, ya daɗe da dawowa kam daga yanayin yanda ɗakin ya nuna. Abin da ya bani mamaki matuƙa shi ne sabon ƙamshin turaren da ban san da shi ba, turarensa ɗaya na sani a duniya wanda tun kafin muyi aure da na taɓa basa kyautarsa shikenan ya riƙe shi bai taɓa canjawa ba sai a yau, kuma yanzu da nake ganin sabuwar kwalba akan madubi bayan ga waccen kwalbar bata ƙare ba.

 

Ɗakin na bi da kallo, idona ya kai kan warm coolers ɗin da ke ƙasa guda uku, wani abu naji ya soke ni kaman sukar mashi. Ƙafafuna na rawa na isa gabansu da sauri na buɗe, ƙamshin lafiyayyan abincin ciki ya doki hancina, babu tantama abincin wata ƙwararriyar chef ɗin ne. Na bar ganina daga kai ina kallon kan gadon da kayansa ke zube waɗanda ya cire, sai naji kamar ana jana zuwa bakin wadrobe, jikina duk na rawa na buɗe ɓangaren da jallabiyunsa su ke, kaf guda goma sha ukun da yake da su suna nan ciki rataye a hanger babu ɗaya da ya saka ya wuce masallaci kamar yanda ya saba.

 

Lokaci ɗaya naji yawun bakina ya bushe gaba ɗaya, cikin rasa makamar abin yi na rarumi wayata na shiga kiran lambarsa, farko not available su ka ce min, na biyo kuma ringing ɗin bai je ko’ina ba aka danna user busy, na kalli agogo naga lokacin sallar isha’i ya wuce, hakan yasa na ƙara danna kiran, amma har sau huɗu abu guda ake faɗa min user busy ni kuma ƙara kiran nake yi.

 

Zuciya da bata da ƙashi tuni ta fara ƙissima min tunanin wasu lamura, har tana haska min hoton hakan a cikin idanuwana, babu shiri na rumtse ido gam ina girgiza kaina, ban san lokaci da na sami mazauni a gefen gadon ba ina damƙe zanin gado, wani abu ya soki ƙirjina, cikin raina faɗi nake ina ƙara maimaitawa ba yanda za’ai Hubbi yayi min abin da zuciyata ke rayawa, ko da komai ya canja shi ba zai taɓa sauyawa daga mutumin kirki ba, nagartaccen namiji mai wuyar samu, ba ɗan kuka na aura ba, duk tsanani Hubbi ba zai taɓa juya min baya ba, ba zai taɓa cin zarafina ta irin wannan hanyar ba, matsayin da nake da shi a zuciyarsa ya wuci gaban yaci mutuncina ta irin haka, yana tsanin sona na sani, kowa kuma shaida ne.

 

Kaman daga sama na jiyo ana kwaɗa sallama a parlo, na miƙe da sauri ina saita natsuwata na fita da sassarfa, da zumuɗin da na fita inci karo da Hubbi nah a asalin Hubbin da mu kayi aure cike da so da ƙauna gami da kwanciyar hankali a zamanmu na baya.

 

Sai dai me! Ina isa falo gabana ya faɗi ras sakamakon tozalin da nayi, duk sai na daburce ina neman rasa ina zanyi kuma mai ya kamata inyi. Yayar Hubbi ce ta zo Maijidda wadda muke cewa Yaya, daga ƙanne har ƴaƴa da ƴan uwa kowa Yaya yake ce mata, ita ce babbar su wadda ta zamar musu tamkar uwa, kowa na sonta haka kuma kowa na tsoronta, sai abin da tace ayi haka kuma idan ta faɗa ta zauna, ko mahaifiyarsu bata fiya yanke hukunci ba sai dai ta bata wuƙa da nama, haka duk abin da za’a yi sai da shawararta, ba’a taɓa yin abu ba tare da masaniyarta ba, ana girmamata sosai da mata biyayya, kuma itama tana mutunta kowa, ba zan ce bata da kirki ba idan na faɗi haka na zalunceta, macece mai ƙaunar nata, duk abin da ta tattaro na ahalinta ne, burinta taga kowa cikin farin ciki, haka kuma kowa ya tashi kai kukansa ita yake kaiwa, kowa Yaya komai Yaya, sai dai tana da zafi, bata ɗaukar raini, idan ta tashi faɗanta da masifarta shafar kowa yake yi, shisa kowa ke kiyaye abin da zai haɗosa da ita.

 

Kaf cikin matan ƙannenta tafi sona babu ya ni a wurinta, ba wai don su ɗin bata son su ba, a’a nima albarkacin tsananin soyayyar da take ma Hubbi ne yasa na zama ta gaban goshinta, yanda take nan nan da ni kamar ƴarta Shatu wacce mubke sa’anni, amma duk wannan tarin soyayyar tata da kulawarta gareni sun rushe cikin ƴan watanni, halinta da ɗabi’unta sun sauya, ban san laifin me na mata ba haka kawai ta ɗora dukkan fushinta da karan tsanarta a kaina, ko bikin da aka yi watan da ya wuce cewa tayi kowa ya zauna ya huta ni a tattara min duka ayyuka, haka na zama kamar wata ƴar aiki ko baiwa, nayi ta fama da uban wanke wanken kwanukan taron biki, shara kuwa har sai da na ranƙwafa saboda mugun riƙewar da bayana yay, da an tashi rabon abincin zata kira sunana ta yarfo min zagi tace in ɗauka in bi mutane in raba musu, ban da damar zama ko na sakanni, hatta kashin ƴaƴa da wankan yaran baƙin kunya duk ni ce, haka tasa aka wareni a gefe wai banda amfani, ta mayarni kaman wata jaɓa, na sha baƙin ciki da takaici a bikin nan, har sai da na dinƙa jin kaman in gudu gidanmu, sai dai ban isa ba YaShaik tsab zai takeni idan yaji cewar nayi yaji.

 

Su kan su ƴan bikin sai da suka ɗinka tausaya min wasu na cewa ya kamata a barni in huta, in huta tunda surukan gidan gamu nan fal, to amma ban isa ba, zaman hutawata daidai yake da zaman hutu a gidan iyayena tun da har Yaya na fushi da ni. To ni kam yanzu mugun tsoron Yaya nake yi, Wallahi a baya da zarar ta ganni take washe baki ta buɗe min hannaye in tafi jikinta ta rungume ni, amma yanzu har gwara naga hukuma su ce kamani suka zo yi akan ganinta, ganin ma ace a gidana.

_________________________________

_Sabon salo, sabon zubi, sabuwar shimfiɗa kuma sabuwar tafiya, saboda haka ku ɗaura ɗamara domin tafiyar mai zafi ce…tabbas tafiyar doguwa ce me ƙunshe da tarin darussa, tafiyar da ta juya matakin rayuwar wasu mutanen…_

_ku yi ƙoƙarin mallakar abu mai inganci, masu iya magana su ka ce siyan na gari mai da kuɗi gida, saboda haka na ke cewa kar kuji ɗarr ɗin mallakar littafai biyar na *FITATTU BIYAR*, ku yarda fitattun ne da suka yi zarra, kuma basu fito ba sai da suka shirya, ku yarda a fara da ku a ƙarke da ku, kar kuyi saken da za’a barku a baya, alƙalamin haziƙai ba na wasa ba ne, ku garzayo da ƙwarinku mu dama tare da ku a cikin ƙasaitattun labaranmu, masu sanya nishaɗi da ɗebe kewa, labaran da ba’a iya mantawa da su…_

 

*FITATTU BIYAR 2023 paid books:-*

 

1- *ƘAYAR RUWA na Halimahz*

2- *FARGAR JAJI na Aisha Abdullahi Yabo*

3- *WASA DA RAI na Fadeela Yakubu Milhat*

4- *LOKACI NE na Fatima Oum Mumtaz*

5- *KWANTAN ƁAUNA na Nana Haleema*

 

_LITTAFI ƊAYA:- ₦500_

_LITTAFI BIYU:- ₦800_

_LITTAFI UKU:- ₦900_

_LITTAFI HUDU:- ₦1000_

_LITTAFI BIYAR:- ₦1200_

_VIP 2k._

 

Za ku biya kuɗi ta wannan account…

*6314170140*

*FIDELITY BANK*

*SA’ADIYYA ZAKARIYYA HARUNA*

 

sai ku tura da shaidar biya tare da sunan littafin da kuke biɗa a wannan number….*Oum Mumtaz(09061794195)*

 

katin waya zaku tura hoton MTN da sunan littafin ta wannan number…*Milhat(07083818353)*

 

*ƳAN NIGER KU TURA DA KUƊINKU TA Mkoudi 89356025 airtel, SANNAN KU TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBA…Aisha Yabo(08162576936).*

 

_LITTAFI ƊAYA:- 350f_

_LITTAFI BIYU:- 600f_

_LITTAFI UKU:- 650f_

_LITTAFI HUƊU:- 750f_

_LITTAFI BIYAR:- 850f_

 

“`ƳAN KASUWAN DA ZA’A TALLATA MAKU HAJOJINKU DOMIN KASUWANCINKU YA ZAGA IN DA BAKU YI ZATO BA, TALLAN YA KASU KASHI-KASHI:-“`

 

*_TALLA A KOWANNE PAGE NA BOOK 500, 5pages2k, Complete Book 10k._*

*_•TALLA A VEDIO NA YOUTUBE 1500_*

*_•TICTOK 1500_*

*_•INSTGRAM 1500_*

*_•FACEBOOK 1500_*

*_•WHATSAPP STATUS; 24hrs500, 48hrs1k, 72hrs1500, 168hrs3500._*

 

“`ku tura da kuɗin ta account numbern da ke sama sannan ku tura da shaidar biya haɗe da details na abin da kuke so a muku talla akai ta wannan lambar…NanaHaleema(09030398006.)“`

 

*Youtubers da su ke son mallakar littafanmu domin ɗorawa a channel sai kuyi magana a wannan lamba…Halimahz(07018098175).*

 

MUNA MARHABAN DA KOWA CIKIN MUTUNTAWA, A ISO LAFIYA🤩

 

*Godiya tare da adu’an fatan alkhairi ga duk wanda ya siya littafin Fitattu Biyar…son so fisabilillah😍*

_________________________________

“`Ya hayyu ya qayyum, birahmatika astagheeth, aslih lee sha’anee kullah, wala takilnee ila nafsee tarfata AAayn🤲🏼.“`

 

#Halimahz

#Alkhaircharityfoundation

#Gamjiwritersasso

#Ƙayarruwa

#2023

[10/10, 1:14 pm] +234 701 497 9567: *ƘAYAR RUWA*

FitattuBiyar 2023.

 

*©️Halimahz*

*halimahz@arewabooks*

*Halimahz_@Wattpad*

*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

____________________________________

*(2)*

Harar da ta banka min ita tasa na razana na ƙarasa gaban kujera cike da furgicin ganin fuskarta babu annuri. haka na rakuɓe tsugune kamar an jijjiga ɓera a buta, ji nayi gaba ɗaya ta cika falon saboda irin matan nan ne zabga zabga masu ƙiba, duk da idona a ƙasa yake amma ina jin irin banzan kallon da take jifana da shi, tana aikin kyaɓe baki kamar taga amai, ganin na buɗe baki cikin fusata ta katse ni.

 

“Lumɓu-lumɓu wutar ƙaiƙayi, tsiga tsiyau kazar matsiyata, wato saboda ba ki da mutunci, ba ki da tarbiya, ba ki da ɗa’a, ba ki san darajar na gaba da ke ba, ni kike jira in gaishe ki…me kika taka da har kike ganinki daidai da ni?, ko saboda an ɗauko ki daga tsiya an rufa asirinki cikin daula shiyasa kike ganin kinfi kowa?, aikin banza shafa lalle a ɗuwawu uban me ma kika aje a gidan da har za ki gadara. to ko shi me gidan yayi kaɗan in zo gidansa ya wulaƙanta ni wallahi, ke ga ƴar iska kina so ki nuna min dangin mijinki mutanen banza ne a wurinki, shiyasa har kina ji ina kwaɗa sallama ki ka barni a shanye, wato in gaji in bushe in kama gabana, to idan ba ki sani ba ki sani, ni mai sakawa ya sallameki ne kuma kin sallamu wallahi, ko idan danginki ne za ki wulaƙanta su har haka?, wato sai ni Yayar mijinki ƴar banza tazo miki gida ba za ki amsa sallamarta ba ko?”.

 

Jiki na rawa na girgiza mata kai alamar a’a ina faɗin,”duk ba haka ba ne Yaya, don Allah don Annabi kiyi haƙuri, wallahi sam banji sallamar ba ina aiki…”.

 

Daka min tsawa tayi tana katse sauran maganata, cikin faɗa sosai take cewa,”dalla rufe min baki munafuka algunguma makira mara tsoron Allah, aikin uban me kike yi a gidan nan banda kici ki kwanta, to idan ma aikin ne fina yayi da ba za ki iya katse kome ne ba, ballantana babu aikin da kike kina kwance sharaf kaman kayan tsinuwa, rashin mutunci dai irin na matan yau shi ya hanaki fitowa”.

 

Na haɗiye abin da ke tokare a maƙoshina ina karanto hasbunallahu, cikin sadda kai ƙasa nace,”don Allah kiyi haƙuri hakan ba zai ƙara faruwa ba in sha Allahu, ki yafe min Yaya don Allah”.

 

Sai na miƙe tsaye jiki babu ƙwarin kirki na shiga gyara kan kujerar da yake a gyaransa nace,”Bismilla Yaya ki zauna”.

 

Ta maimaita,”in zauna?…Sa’ida saboda raini da cin fuska ni kike kallo kina ce min in zauna saboda ga jarababba ta isheki da hayaniya, Yo Sa’ida har wacece ke a gidan nan da sai kin ban izini akan abu, ko tunaninki umarninki nake jira shiyasa nake tsaye har wa yanzu?, Ehh lallai yarinyar nan kin riƙa, wuyanki ya isa a yanka, raini da cin fuska mai muni har haka?, ina Yayar mijinki za ki wulaƙanta ni?, to uwar me kike gadara da shi a cikin gidan nan?, tun da aka auro ki wacce tsiyar kika aje?, shekara takwas babu ɓatan wata balle ɓari, kin kasa ajiye ko tsinke sai aikin ci da kasayarwa, kuma a hakan kike neman gadara da gida, to ke a wa?”.

 

Sai tayi shiru tana bin ko ina na cikin falon da kallo,”ina Nazifin yake?”.

 

“Ya fita”.

“Ya fita ina?, Ƙarya za ki min, shi dama yana fita ne ya wannan lokacin?”

 

Nace,”ai in ya fita magriba sai anyi isha’i yake dawowa, kuma yauma da mota ya fita ba lallai nan kusa zai dawo ba”.

 

Zagayowa tayi ta zauna kan kujera, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgiza su, tana ta kaɗa kai. Na wuce kitchen na ɗauko ruwa da lemu na kawo mata, a kofi na tsiyaya ina ce mata ga shi, na duƙa gefen ƙafafunta, cikin taushin murya nace da ita.

 

“Yaya don Allah ina neman afuwar laifin da nayi”.

 

Ba ta dai ce min komai ba har wucewar wasu sakanni, kafin ta kalle ni cikin zafin rai tace,”wallahil azim idan ba ki bar min magana ba zan zabga miki maruka a wannan damammiyar fuskar taki da ta zame mana musiba cikin ahali, kuma ki kwashe kayanki tun da ban ce miki a yunwace nake ba”.

 

Ni dai ban ko motsa ba kaina na ƙasa ina ta biya kalmar innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Yayin da ita kuma na ke jinta tana ci gaba da faɗin,”haba wannan wacce kalar annoba ce, yarinya sa’annin aurenku duk sun haihu daga masu ƴaƴa biyu sai uku, amma ke kina zaune sai dai a ciyar da ke ki cikawa mutane masai da kashi, aure shekara takwas babu wani labari, ai wallahi da sake a wannan lamarin, dole a duba”.

 

Furucin nata yasa na ɗago da sauri na kalleta, ta ƙara jefa min wani matsiyacin kallon tace,”ƙarya na miki?, ko sharri na miki?. to ki kira min mijinki duk inda yake ya dawo ina son magana da shi, yazo ayiwa tufkar hanci, ba zai yiwu yayta ɗawainiya da ke yana faman hidimta miki amma kin kasa biyansa da ƙyanƙyasar ƙwai ko guda, gida har gida kamar wannan ace babu ƴaƴa, wa zai gaji uban dukiyar da aka tara?, to idan shi baida hankalin tunani da lura mu ƴan uwansa da muka san ciwonsa zamu nemi mafita. Yazo ya ɗauke ki a daren nan kuje asibiti ayi miki gwajin haihuwa, idan haihuwar ce ba kya yi muji, idan kuma irinku ne masu dogon jinkiri shima muji, ke idan ma da gayya kika hana haihuwar zamu ji ai, don ni nafi tunanin mugunta ce irin ta ɗiyar talakawa, bai wuci zuwa kika yi aka sa miki tsarin iyali ba. Yo me ma ake da ƙarin aure da ba zai yi ba ya ke ta zama da baƙar aniya, ai wallahi muddin ɗaya cikin abin da na lissafa ba za’a shafe wata guda curr ba sai ya ƙara aure tunda ke ba abar mora ba ce, gwara auren wadda ahali za suyi alfahari da ita, waye ba ya so yaga zuri’arsa?, yo wannan ma ai cutarwa ce ace yana zaune da macen da bata haihuwa, me amfanin auren?, Ai ko ma’aiki cewa yay kuyi aure ku hayayyafa domin in alfahari da ku ranar gobe ƙiyama…don haka Maza maza tashi kira min shi a waya, kuskurena ne ma da ban zo da tawa ba, ki kirasa yazo kuje asibiti yanzu yanzu, wallahi ko haihuwa ko ƙarin aure, ba za’a ci gaba da zama a yanda ake ba”.

 

Maganganunta duk sun saka jikina ɓari, cikin kaina babu abin da ke nanatuwa sai kalmar rashin haihuwa da ƙarin aure, wato duk a baya basu san da matsalar rashin haihuwar ba sai a yanzu. Kuma har tana da bakin kirana ƴar talaka, ehh lallai ciki mai manta kyautar jiya, saurin share hawayena nayi ina ƙoƙarin daidaita yanayina, domin kuwa tun da har na gano manufarsu ta tsangwamata to ba zan taɓa bari suga raunina ba, ballatana su ƙara samun damar cin zarafina yanda suke so.

 

“Ba kiji me nace miki ba ne, ki tashi ki kira min shi a waya, ni ba wajenki na zo ba balle ki sani a gaba da kirsa”.

 

Hmmm ɗan Adam kenan mai wuyar gane hali, dama ai shi gwano ba ya jin warin jikinsa, ban da haka mancewa tayi ƴarta ta fari har yanzu bata haihu ba, shekararta goma sha shida da aure shiru babu labari, kuma babu wanda ya tsangwameta ƙarshe ma ɗa aka samu a dangi aka bata, sai ni da ban ko rufe shekara goma ba zata ƙwazzafe ni, ta ɗaga min hankali, ita ba ɗanta nake aure ba, yo ko ɗanta na ke aure irin rayuwar da na yi da shi ai ta shafa min lafiya.

 

Ji nayi ba zan iya yin shiru ba da zage zagen da take ta yarfo min, hakan yasa murya a hankali nace,”Yaya dama wannan shi ne kuskuren nawa wanda yasa duk ku ka juya min baya?, soyayya ta koma ƙiyayya?, akan abin da bani na ɗorawa kaina ba, akan lamarin da yake na ubangiji shi ne ake tsangwamata haka. Yaya haihuwa fa ta Allah ce na san kin sani, haka duk wanda ya haihu ba shi ya bawa kansa ba, kuma duk wanda aka haifa ba shi ya haifi kansa ba. in har ace ina da iko da haihuwa ai da tuni wani labarin ake, domin nima ina so na ganni da zuri’ata, na ga yau na kafa nawa ahalin”.

 

Muryata ce ta raunana a daidai wannan gaɓar, sai dai ban bari ko kusa ta fahimci cewa kuka nake so nayi ba, tabbas ba zan juri wulaƙanci ba matsawar akan wannan matsalar ce, ai bani kaɗai zan haihun ba, dole sai da ɗan uwan nasu, don haka muddin za’a duba lafiyata akan rashin haihuwata to shima sai an duba tasa. Maganarta naji a tsakiyar kaina tana faɗin,”kin gama min wankin babban bargon?, Nace kin gama zagin nawa?”.

 

Na kasa danne abin da nake ji a ƙirjina na ɗago kaina ina kallonta, lokacin ta miƙe tsaye tana gyara yafen mayafinta, na rumtse ido nace.

 

“Ki haƙuri ban faɗa miki komai da rashin kunya ba, iya gaskiyata na faɗa, haihuwa ba ni zan bawa kaina ita ba Allah ne mai bayarwa, kuma mafi aksarin jinkiri alkhairi ne, bamu san mai Allah ya shirya mana ba, da haihuwar yuyuyu gwara haihuwar babu, rayuwar nan ba’a ƙareta ba duk da bamu san gawar fari ba, amma ni ina da yaƙinin ba zamu kai ga kushewa ba sai Allah ya azurtamu da haihuwa, sai Allah ya bamu mai jin ƙanmu da alfaharinmu. Kar ki tafi zan kirasa a waya muje asibitin yanzu a duba ni, amma don darajar Allah kar ku yanke hukuncin ƙarin aure, don Allah kar ku saka ya ƙara aure, ba don bana sonsa naƙi haihuwa ba, Allah ne bai kawo lokacinta ba ki duba min Yaya, nayi ƙaranta ace za’a min kishiya yanzu”.

 

“Mtswwww”. Taja wani dogon tsaki mai muni wanda yay duka har tsakiyar ƙwaƙwalwata. tasa ƙafa tayi fatali da teburin gabanta, lemu da ruwan da suke kai suka zube akan carpet.

 

“Sa’ida kici min mutunci ki tsammaci za ki ci gaba da rayuwa ke ɗaya a wannan tamfatsetsen gidan, kice ke ɗaya za ki mori dukiyar Nazifi?, Bayan kin tauye masa hakki kin hana shi ƴaƴa kice ba zai auro mace mai lafiya ba, ai ƙarya kike wallahi…ni bani hanya na wuce ko in bi ta kanki, banza juya kawai marar amfani”.

 

Juya! Kalmar tayi wani tsallen maimaituwa a ƙoƙon kaina, na ɗaga idanuwana nabi ta da kallo har ta fice ta bar parlon. Juya! Juya! Juya!, kalma mafi ciwo da raɗaɗi a duk cikin kalaman da ta gaggaya min, wannan hanyar da suka ɓullo da ita tabbas zata zama hanyar karayata, bana jin zan jurewa gorin haihuwa, duk haƙurina ba zan ɗauki wannan ɓangaren ba.

Idanuwana naji su na zugi, duk da ban kallesu ba na san sunyi jajur, sai dai ko kusa ko alama hawaye sun kasa zuba daga cikinsu. Plate da kofunan da ta kifar na tattara na kai kitchen, na dawo ɗauke da tsumma na goge lemun da ya zube kan carpet, ac na ƙaro saboda wurin yay saurin bushewa gudun kar yay ɗoyi.

 

Cikin ƙarfafawa kaina gwiwa na wuce ɗakin barcin Hubbi, ina shiga na gyara ɗakin kaman ko da yaushe da na saba. na hau sama na kwaso kayan abincinsa na sakko da su, akan tebir na ajiye, haka kuma ban canjawa warm coolers ɗin da na tarar ba waje. Ayyuka na daban na tsira duk dan in mance da cin zarafin Yaya, ina ji aka fara kirayen sallar isha’i, ban tsaya da aikina ba naci gaba kasancewar ina cikin jinin al’ada, gyara na musamman na yiwa bedroom ɗin nasa a wannan daren, duk wani kai komo da nake maganganun Yaya ba su bar haska min a cikin kaina ba, sai dai ina ta ƙoƙarin kawar da komai ɗin domin bana son hakan ya tsaya min a rai, don ko Hubbi ba zai san da wannan labarin ba, shiru shiru har ƙarfe tara Hubbi bai dawo ba, kuma bai kirani ba bai tura min saƙo ba.

 

Ɗakina na koma na sake wanka don idan ina cikin jini sam bana sakewa, sai in ta jin kaman jikina duk ya ɓaci, haka kuma kaman ina ta ƙarni.

Murmushin takaici nayi da na kalli kaina a madubi, me yasa nayi wannan saken?, ta ya zan bari jikina yay wannan lalacewar?, dududu shekarata nawa?, ni akaran kaina ƙirjina ya daina burgeni balle kuma miji da kansa, ba komai ya lalata ni ba irin saka damuwa a rai, ni da ban taɓa shayarwa ba ai bai kamata ace na bar nonuwana sun zube ba yaraf, bayan na san Hubbi na matuƙar son su, to dole na miƙe tsaye, zan dawo asalina mai cikakkiyar sura ta ko’ina, in kuma fita daga cikin sahun mata masu dugun kai a gidajen aurensu ta ɓangaren shimfiɗa soyayyar aure. Sai da na gama kimtsa jikina tsab tukunna na fito ɗakin na kulle duk ɗakunan sama da kitchen, na sakko ƙasa na kashe fitilun falo tare da kunna karatun ƙur’ani wanda dama da shi muke kwana kullu yaumin. Agogo na kalla naga har ƙarfe goma daidai, tsammanina zuwa lokacin Hubbi ya dawo tun da na jima a ɗakina, sai dai ina shiga ɗakinsa naga babu alamarsa, kenan har yanzu bai dawo ba, take zuciyata tayi zullo na fara jin tsoro, ban san me yake faruwa ba, fatana ɗaya Allah yasa lafiya.

 

Kasa tsaye nayi na kasa zaune, in kai mari in kai gauro saboda kiran lambarsa da nake yi bata ko tafiya. Tunanin in kira office ɗinsa yazo min, sai dai ko da na kira aka tabbatar min da cewa ai tun biyar ya bar office. nan fa hankalina ya tashi, na rasa wa zan kira tun da shi ba wasu abokai gare shi ba, haka yake kamar mace mara son ƙawaye.

laluben lambar ƙaninsa na shiga yi, ko da ya ɗaga bamu wani tsaya gaisawa ba na tambayi ko Hubbi yaje gida, yace ba ya gidan tun da rana da yazo gaida Iyam. muna gama wayar na ƙara gwada kiransa, wani sanyi naji a raina da ta fara ringing, sai da nayi kira har sau goma bai ɗaga ba sai daga ba ya message ɗinsa ya shigo.

 

“Ba na son damu akwai abin da nake yi”.

 

abin da ya rubuto min kenan, kuma ina gama karantawa na aje wayar jiki a sanyaye, ko ba komai naji dama-dama tun da lafiya yake, sai dai naji babu daɗi sosai, domin kamata yay ace in akwai adalci ya ɗaga wayan ya faɗa min uzurinsa, ko kuma ya rubuta min idan babu daman ɗaga wayar, amma saboda rashin sanin hakkina da girmama aure yana can lafiya ya barni anan cikin damuwa da tashin hankalin halin da yake ciki, ko abinci na kasa ci haka cikina yake fayau tun ruwan safe da na sha.

 

gudun tunanin da ka iya rufe ni na miƙe na kwanta akan gadon. Sai dai me? daga kwanciyar tawa na saki marayan kukan da nayi ta dauriyar riƙewa tun tafiyar Yaya, sautin kukan ya cika ɗakin, kuka nake kamar wadda aka yowa aiken mutuwa don kawai in samu in fitar da baƙin cikin da ke raina. na janyo filo na toshe bakina da shi amma duk da haka sautin kukana bai ɓuya ba. Lokaci ɗaya jikina ya ɗauki zafi na kama kyarma dama ni ban iya zazzaɓi ba. A wannan lokacin duk wani mai imani ya ganni sai zuciyarsa ta motsa da tausayina. Haka na ke ta faman zubar da hawaye, ban isa na goge su ba don ina gogewa wasu na sakkowa.

 

Na daɗe ina kuka don har wajen sha ɗaya da rabi, zuwa wannan lokacin kam na fidda ran dawowar Hubbi, banga alamun yau zai kwana a gidan ba. saboda haka na miƙe na shiga banɗaki na wanko fuskata ina hana kaina ci gaba da kukan da baida amfani gare ni, adu’a maganin annoba ita ya kamata in riƙe ba wai damuwa da kuka ba. Ina fitowa na wuce nasa key na kulle ƙofa duk da zuciyata na faɗa min komin dare zai dawo, bai da wani wajen kwana a daren nan sama da nan ɗin dai da yake ƙauracewa, tsakin ƙasan maƙoshi nayi, to ina ruwana da dawowarsa, raina ɓace na fita falo na bi duk ƙofofi shigowa na saka musu maƙulli, zanga ta in da zai shigo, ai sai dai yay kwanan ɗakin mai gadi, ba abar banza ba ce ni, auroni yay don yana so ba cusa masa aka yi ba, kuma a gidan iyayena ya ɗauko ni ba gidan marayu ba. kamar ma in koma ɗakina amma sai na dawo ɗakin nasa, na murza key na kashe fitila me haske na bar mara hasken wacce ke kan durowar gefen gado.

 

Bacci nake ta so nayi amma gaba ɗaya na kasa, sai juyi da nake ta faman yi, zuciyata kuma cike da saƙe saƙe, kaina kuwa ya cika fal da tunani daban daban. Ni dai lafiya ƙalau muke da mijina, sai dai tun bayan dawowarmu nan gidan da wata bai fi biyar ba komai ya canja na daga yanda muka saba rayuwa, ni da shi kamar abokai haka muke, amma yanzu ya zamar min wani horo har tsoronsa nake yi, magana ma shakkar masa na ke, komai nayi ban iya ba, saɓanin a baya duk abin da nayi ko da bai masa ba zai yaba min kuma yace nafi kowacce mace iyawa, yanzu abu kaɗan zan yi ya zama laifi, zama da shi ban isa ba in ba haka ba ya dinƙa ƙunci kenan ni kuma bana son ƙuncinsa, hatta makarantar tahfeez ɗin da nake zuwa yanzu nema yake ya kashe zuwanta, don duk san da zan tafi sai yayi ƙorafi akai, sai yace ai tunda na iya karatun sallah na san wankan tsarki na kuma san zaman aure ya ishe ni, da nayi magana sai yace ai shi ke biyan kuɗin ba wani ba saboda haka yana da ikon ya hana zuwan.

 

Na kau da tunanin matsalata da mijina, na koma tunanin furucin Yaya na za su sa ya ƙara aure, tabbas na sani ƙarin aurensa tozarcin da nake sha sai ya ninku, don sai na ƙwammaci ina ma ban auresa ba, Allah ɗaya ya san irin wulaƙancin da matarsa zata dinga min, balle ta san don manufar da aka aurota, zata goranta min fiye da yanda dangin miji za su min, kuma daga zarar ance ta sami ciki ta haihu shikenan tawa ta ƙare, zaman auren sai ya ishe ni, takaicin da zan sha ba daga wurinta ba kaɗai har da shi uban gayyar. ni kaina na sani Hubbi yayi ƙoƙari, ba kowanne namiji ne za’a kai wannan lokacin ace bai yi ƙorafi ba, kamar yanda Yaya ta faɗa shekara takwas ban taɓa ɓatan wata ba balle azo ga maganar ɓari, kuma ko da wasa Hubbi bai taɓa min magana ba, balle ya nuna min damuwarsa ko ƙorafi, ni ce ɗin ma na ke damuwa, don sau tari har kuka na kan yi, sai yay ta min nasiha yana ƙara faɗa min lokaci da rabo ne, idan na ɓata masa rai akan nuna masa kar a fara cewa bana haihuwa ya dinƙi faɗa kenan, yace min duk wanda ya fasa faɗar hakan ba ya ƙaunar Allah, kai duk wanda ma yay min gorin haihuwa in sanar masa hukuma ce zata raba su, watarana kuwa da nace masa muje asibiti a duba ni bai ci abincina ba. yanzu kuwa yanda muke zaman babu daɗi da shi ai nayi kaɗan in kai masa ƙarar Yaya akan cin mutuncin da tazo ta min, kuma ko da ace shima wannan ne dalilin samun matsalarmu ba zanga laifinsa ba, a yanzu kam yana da buƙatar magajinsa, wanda zai ɗora akan kasuwancinsa ya kuma mallakawa kadarorinsa. sai dai fa ya tuna ana barin halak don kunya, ko mai zai yi min banda wulaƙanci, don ni na sha gaban ya wulaƙanta ni a rayuwa, domin na masa abin da ko ƴan uwansa basu masa ba, ya kuma san hakan, sai dai in ya butulce, kuma shi butulci dama ai ba sabon abu ba ne a wajen ɗan adam musamman wanda ka yiwa rana.

 

Haka dai a wannan dare nayi ta tunane tunane, in raya wancan in saƙa wancan, in lissafa wancan, sai dai na kasa warware komai, haka duk na ƙosa gari ya waye, ni ba sallah ba balle in yi nafilfili, a haka dai har ɓarawon bacci ya ɗauke ni a lokacin da ban san ko ƙarfe nawa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post