Jikar Iya Hausa Novel Complete

Jikar Iya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Jikar Iya Hausa Novel Complete

Mallakin

Teemerh Cool

08161316781

 

 

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

 

 

“`Wannan littafin gajeren labari ne,kuma ƙagagge, wanda yaga labarin ya yi daidai da rayuwarsa ya yi hakuri arashi ne, ina yiwa masoya fatan alkhairi ina matuƙar alfahari daku da nuna ƙaunarku gareni“`.

 

 

*Wannan littafin na sadauƙar dashi ma duk wanda ya rasa mahaifiyarsa, Allah jiƙanta ya gafarta mata da duk al’ummar musulmi*

 

 

Page 1️⃣🆒2️⃣

 

 

“Hello Mummy how are you?”

 

“am fine my son how about you”tayi maganar cikin sakin fuska, shima murmushi ya mata ya buɗe baki zaiyi magana sai ya dubi bayansa, ganin yadda tashigo masa cikin video call nasa, taɓe baki ya yi gami da fadin”Mummy ” cikin sauri take tambayarsa wacece tagani a zaune a bayansa.

 

“Au na manta Mummy ban fada miki ba, matata ce watan  mu uku yanzu dayin aure” ya yi maganar yana mata wasa da kafa dan akanta yanzu kansa yake.

 

“What! kasan abun da kake faɗa kuwa? so kake kace mun kayi aure? sannan ma da goyon bayan waye kayi???” tayi maganar cikin tsawa.

 

“At least Mummy ki tsaya namiki bayani ko, ni a wannan abun lefina daya ne, da na manta ban faɗa miki ba amma batun wai da izinin wa nayi aure ai kinsan bai taso ba,to banda abunki banda izininki da izinin wa kuma kikeso nayi, ko kina nufin wancan photocopy ɗib”

ya yi maganar ciki jin takaicin abun da ta faɗa.

 

 

 

“Waye photocopy?, kana nufin shi Daddy dinku ne photocopy?, are you out of your sense” tayi maganar tana jin zafin abun da ya fada.

 

“Mummy kinsan dai kawai aiki daya Daddy yake iya yi cikin hankalinsa shine aikin office bayan nan duk kece kike juyasa, kece kike basa umarni, to mai zance inba photocopy ba?” ya yi maganar yana kallon ƙafar wacce tinda yake wayar take kallonsa, kashe mata ido ya yi gami da fadin”sweet ikfa dan allah kiyiwa mummy gwalo” dukansu suka sa dariya, Mummy kuwa daskarewa tayi da waya a hannu, bata ankara ba se ganin an kashe wayan tayi.

 

 

Tsayawa tayi tana mamaki, ita tama rasa me za ta ce masa, tashi tayi ta fara zagaye a ɗakin, kamar wacce tayiwa Sarki karya, jin anyi knocking ne ya dawo da ita hayyacinta, ganin wacce ta shigo yasa ta fadin “Yauwa daman yanzu nake son kiranki dan ina neman ki, akwai magana mai mahimmanci da zamuyi”.

 

Taunar cingam takeyi tana latsa wayarta, zama tayi akan wani kujera dake ɗakin tare da cewa”Allah yasa ba daɗewa zakiyi kina maganar ba, dan yanzu Areef ya kirani yanason mu fita”.

 

“Ke magana ne mai mahimmanci” ta fada cikin bacin rai.

 

Kallonta tayi, cikin yatsina fuska tace “wani kalan magana ne haka, da har yafi Areef a muhimmanci, bayan kuma kisan matsayinsa a wajena, ko kin manta ne shidin Saurayina ne, amma inajin ki faɗa min abun da zaki fada”taci gaba da latsa wayar tana taunar cingam.

 

“Wai Zohaib ne ya yi aure, batare da munsani ba “tayi maganar cikin tsigar mamaki.

 

“Okay ai wannan ba matsala bane, ballanta ma shi namiji ne, kuma ai ba wani abu yake nema a wajenku ba shiyasa kikaga bai fada muku ba, dan Allah Ummi kyakkyawace? fadamun ya take?, ya sunan Matar tasa, Allah yasa dai wayayya ce, dan mu bamason akawo mana bagidajiya family, ko da yake ma tinda a london take karatu wayayya ce, dan Allah inkunyi waya kice ya turamun photonta danni inna tambaya bazai turamun ba” ta karashe magana tare da tashi cikin taunar cingam nata.

 

Har zata fita sai ta juyo ta ce”au Ummi zamu fita nida Areef, dan in Dad ya tambayeki karkice baki sani ba, au koda yake ma ba zai yi miki komai ba ko ban dawo ba tinda kece mai gudanar da gidan” tayi maganar tana dariya ta fita da nunawa mahaifiyarta kamar tana zolayarta.

 

Hajiya Kamala kam daskarewa tayi a wajen, duk da ba baƙon al’amari bane a wajenta, amma ai wannan din yakamata su duba sugani, ya za’ayi ya yi aure batare da kowa yasani ba a familyn su.

 

 

LONDON

 

“Ni kasan mata basa gabana inba Amrish ba, kasan ni ba na kallon mata itama Amrish gani take kamar ba sonta nake bane, hakanne yasa muka nemi waliyai a school aka daura mana aure” tinda yake maganar yake binsa da kallo.

 

“Lalle Zohaib kai ko kunya maganar ma bakayi, wai kake bani labarin yadda akayi kukayi aure, kaima kanka dan kasan lkcn na tafi Nigeria ne, amma wlh da bazan bari ka auri Amrish ba,Yarinya batada mutumci ga rena na gaba da ita, batasan kimar mutane ba, kana ganin yadda take taka kowa a school fa, sannan duk mace da tayi aure batare da sanin iyayenta ba mai sunanta, au ashe har namijin ma” ya yi maganar cikin ɓacin rai.

 

“Ka gama Daddy?, nace ka gama Daddy ko da sauran magana ne, in akwai kawai ka karasa” fadan Zohaib ya yi maganar cikin tsiwa.

 

“Ni ba Daddy bane ni abokinka ne, kuma yazama dole na fada maka gaskiya a matsayina na abokinka” ya yi maganar yana mikewa tsaye.

 

“Wai kai meye damuwarka ne da wannan auren?, ni har ina murnan zuwanka ina cewa yau zamuyi lunch tare, ashe kai bazama zakayi ba” ya yi maganar yana dariya.

 

“Is okey Zohaib bana bukatar komai daga wannan gidan, sannan kuma indai bazaka canza hali ba bazamu daidaita ba,” daidai lokacin Amrish ta shugo ɗakin.

 

“Wayene yazo gidan sai haushi nakeji tin dazu, shiyasa nace bari nazo na duba,”t ayi maganar tana duban Sa’ed dake tsaye.

 

Yake ya mata wanda hausawa sukace yafi kuka ciwo ya ce “Amarya kenan wannan karen da yazo yanzu zai fita dan ya zo ne badan zama ba, sannan kuma ina mai faɗa miki indai muddin baki daina jefawa mutane magana ba to kina tare da wahala,” ya yi maganar yana nunata da yatsa, duban Zohaib ya yi wanda yake fama da laptop ya ce “na barku lpy Rosha “ya fita cikin gudu-gudu.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

____”Wlh yau koni ko Malam Barde, zamu yi ta a garin nan,ya rasa wacce zai taɓa sai Marainiyar Allah, aikuwa alamu ne na ɗan wuta, tinda ya taba Marainiya” tayi maganar tana zarar mayafi daga kan igiya.

 

Sai sauri take zubawa tana ta faman jan silifas, wanda yafi karfin ta,kowa ya ganta acikin unguwar sai ya kara kallon ta, saboda yadda take tafiyar.

 

Rike yake da Yarinya wacce bazata wuce Yar shekara goma ba,sai harara take zuba masa, duk da dukan da ya yi mata.

 

Fincikarta tayi tana kokarin faduwa, tsabar fisga da tayi mata.

 

“Ashe kai ba mutumin kirki bane, tinda har ka iya dukan marainiyar Allah, wannan shine yake nuna alamar kai dinnan bazaka gama da duniya lfy ba, mugu azzalumi da wani kai kamar rodi” tayi maganar tana tsince takalman Yarinya dake watse a wajen,shi rasa mai zai ce mata ma ya yi, sai kallo da ya bita dashi.

 

“Kinga Muje Indo dan zan iya faɗa da Uban kowa a wannan garin, indai suka taba marainiyar Allah” tayi maganar tana jan hannun Indo suna kokarin barin wajen.

wani dutse Indo ta dauka ta jefa masa tare da da fadin “Allah ya isa mugu, kuma wlh sai dai Tasi’u ya daina fitowa mu zuba nida kai”tayi maganar cikin tsiwa.

 

“Ƙyalesa Allah zai hadasa da jifar sheɗan basai kin jefesa ba” tayi maganar suna barin wajen.

 

Suna tafiya tana tayiwa Iya surutu akan abun da Malam Barde ya yi mata, sikuwa yasha zagi da tsinuwa a wajen Iya,da haka har suka karaso gida.

 

Jifa tayi da mayafinta, sannan taje ta sheme akan taburmar da take shimfiɗe a tsakar gidan, “wayyo Iya bayana ciwo yake yi, dan Allah ki taimakeni da man zafi, ki shafa min dan wannan mugun ya wahalar dani, kuma wlh bazan kyale Tasi’u ba”tayi maganar cikin tsiwa.

 

Man ta ɗauko tana kokarin shafa mata,tana cewa “karki ragamasa tinda shima ubansa bai ragamiki ba, ke Marainiyar Allah ya miki haka sai shine za’a fasa yima masa, inda damama ki karya ƙafar yaron” ta faɗa ya yin da take rufe maganin da ta gama shafa mata.

 

“Kyaleni dashi Iya zaisan ya taɓa Indo ta Iya ” tayi maganar tana kai lomar abincin da tagani a rufe a gefenta.

 

Cikin kan katifar ta take birgima abunta, buɗe idonta tayi ta ware, ganin garin ya waye yasa ta mike ko addu’ar tashi daga bacci batayi ba, mikiwa tayi tsaye tana mika tare da sakin hamma,ta ce”Allah abun gdy tinda mun tashi da ranmu bamu mutu ba,to yau ranar ɗaukar fansa ce” tayi maganar tana kara sake hamma.

 

Fitowa tayi taga Iya tana ta fama da wuta da ta hura,washe baki tayi tana cewa

” Iya yau mai zaki dafa mana?”

“Indo kin tashi kenan,ai sai abun da kika ce shi za’a dafa”

 

“Iya zauna yau ba girki zamuyi ba, zan kawo mana abun da aka kawo mun a mafarki,”

 

Binta tayi da kallo tare da rike baki ta ce

“au Indo kice har a mafarki ake baki abinci?!, Allah sarki marainiyar Allah, in ba Maraya ba waye Allah ya bashi wannan baiwar?” jinkirtawa ta yi kafin ta ci gaba da cewa ” sai kin dawo dan yau zamu karya da abun da akabawa marainiya cikin mafarki” ta karashe maganar tana washe baki tare da kashe wutar.

 

Tana fita kamar walkiya ta bace, dan haka take in abun da suka dibeta bazakasan ta inda tayi ba.

 

Sai gata ta karyo kwana tare da sanda a hannunta, tafiya take tana wake-wakenta har sai da ta karaso wani wajen mai shayi, zama kallon ko ina tayi kafin ta karasa, cikin sa’a ta samesa yana ta ciki da alama taliyar yara yake dafawa, babu kowa a wajen shi ɗaya ne, buɗe kwallar shayin tayi tare da faɗin “Dauda Mai Shayi” dagowa ya yi ya kalleta sai da gabansa ya faɗi, rufewa tayi ta karaso inda yake.

 

“To Malam Dauda yaufa sako aka bani na baka, kuma sakon kala biyu ne,” binta yayi da kallo aransa yana sakawa cewa “indai kaga Yarinyar nan ba Alkhairi bane”.

 

“Acikin mafarkina yau ance kaciyar dani ko kuma ka mutu a yau dinnan” tayi maganar tana yamutse baki.

 

“Ke yau ko da sheɗanu kike tafe karyarki, sai ki tayiwa mutane iskanci a gari, kuma yau tanan kika ɓullo, maraici hauka ne? takanki aka fara maraicine?”ya yi maganar yana nunata da yatsa. murmushi tayi tare da daukar bread guda ɗaya tayi gaba tana tafiya a hankali, aikuwa biyota ya yi aguje,kin guwa tayi tana cewa “Malam Dauda da ka barni da wannan kadai amma inka hanani to zaka iya rasa abubuwa da dama,”

 

“Ke kwal ubanki, kaf garin nan kinsan ni bana jure irin wannan abun, danni daka ki zanyi, bani abuna” fizgewa ya yi a hannunta, ya yi shagonsa aikuwa yana zuwa yaga babu bread dinsa har leda biyar, sannan kuma babu taliyar yaran da yake dafawa, leƙawa ya yi baiga kowa ba, sai Indo da yake hangota ita kadai tana tafiya hannu rabbana babu alamar akwai abu a hannunta.

 

“Banda rashin hankali irin nawa nida muke tare da Indo ma bata shigo nan ciki ba, sannan kuma babu alamar mutum ma a layin ” haka yaita magana shi kadai kamar mahaukaci,bakaramin surewa ya yi ba da wannan al’amarin.

 

“Ashe gaskiya Indo take fadamun ance na ciyar da ita a mafarki,i nkuma naki zanyi asara kuma gashi hakan ya faru, nima kaina sai nayi wata kafin naci taliyar yara gashi yanzu nayi asaransa harda rabin jarin bread”zama ya yi yana kuka kamar wanda aka masa mutuwa.

 

 

Tana shan kwana ta haɗu da Musa, dariya sukeyi harda zubewa kasa, sannan tace “zo mu kara gaba tukun na kar wani ya hango mu dan area nan akwai munafukai ” tayi maganar tana karbar taliyar yaran dake cikin leda da zafin ta, tafiya sukayi Musa yana bata labarin yadda akayi bayan Dauda yaga ba abubunsa ya dinga kuka, niko ina ta lekasa,dariya suke har suka karasa wani babban bushiya sannan suka dakata.

 

Washe baki tayi tana cewa “yanzu abun da za’ayi shine kai ka dauki guda biyu kaje dashi ,na barmaka ni bari nayi gida dan yinwa nakeji ,”tayi maganar tana karɓan biredi leda uku daga wajen sa.

 

Tana shiga gida ta shiga washe baki tana cewa “Iya kina ina?ki fito na dawo ”

“au har kin dawo “shimfiɗa taburma tayi tare da cewa “na ganki da ledodi bari na kawo mana ruwa tukun na…..

 

 

 

By Teemerh Cool🖊️

 

*Wannan littafin na kuɗi ne, ki biya kuɗinki ki karanta shine mutuncinki, ban yadda a fitar mun da littafi ba dan kin siya, duk wata mace mai aji bazata karanta littafin sata ba, ki mallaki naki akan naira 300 kacal post kwana biyar a sati, special 500 post kullum , 9048703453 Fatima Muhammad Aliyu opay bank or Khadija Musa Ibrahim ja’iz bank ….sai ki turo shedar biyan kuɗinki ta wannan number 08161316781, in kuma kati ne MTN, AIRTEL,9MOBILE, duk ina using dashi, sai a turo hoton Katin, na gode sosai.

 

TEEMERH COOL

Post a Comment

Previous Post Next Post