Littafan Hausa Novels

Badriya Hausa Novel Complete

Badriya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BADRIYA

A lady with concealed gender (MX)

 

~Storie and written by~

*~Unknown Author

 

*Da sunan allah mai rahama mai jin kai ina wa allah godiya daya bani ikon kawo muku wanan littafin na BERDRIYA fatan zaku Bini sannu a hankali dan jin mai labarin yake tafe dashi ina fatan yadda allah yasa na fara lafiya allah ya bani ikon gamawa lafiya

 

 

*~PAID BOOK 300~*

 

 

~Little note!!!~

*Ban yadda wani ko wata ya juyamun labari ta kowacce irin hanya ba littafin BADRIYA mallaki nane sanan ka kaggen labari ne bata yadda zaiyi kama da tarihin ki ko labarin ki domun ban yishi dan cin zarafin wani ko wata ba do mun bada shawarwari ko wani korafi kofa abude take fatan za’a kiyaye nagode๐Ÿ™๐Ÿป*

 

*FREE PAGE* 1

*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

 

Kamar yadda mukai da kai tin a farko Alhaj buba kudin daka fada bai kai na dau ya guda na baka ba,saboda abu na farko banma sanka ba bansan mazaunin kaba in akai duba da ribar da kace shima bai kai dalilin da zaisa na dau yarinya na baka ba dan mutun ake magana ba kaya ba dan haka ka dai kara wani abu sai na duba nagani.

 

Mawahib Hot Love Hausa Novel

Kayi hakuri malan sule amma ni iya abunda zan’iya badawa kenan miliyan hudu da dubu dari tara kai kanka kasan tafiyata mai nisace sannan in na tashi komawa bani kadai zan koma ba dan dole na cire kudin cinta shanta da kudin motar ta har allah ya kaimu inda zan mika ta

kasan ma dan anriga da ansan yarinyar da aka turoni dauka ne da wallhi yata ta kaina zan bada kodan na amshe wadannan makudan kudaden da kuma sauran kudade masu zuwa dan iya masu aikin gidan ma kadai a wata na farko da fara aekinsu indai kayi yadda ya dace to tabbas duwani makusancin ka wahala ta dauko karewa masa,bare kai yadda aka zabo sunan yarka tin acan kasar ai kasan abunda yafi aikatau zatai,

dan haka du yadda kaga ya dace kayi nidai daga haka bazan kara komai ba dan ribar gaba taka ce bata kowa.

ya kare maganar cike da gajiya ganin kusan awa na hudu kenan suna abu daya shifa har mamakin malan sule yake dan tin kan suzo nan saida sukai bincike akansa alamu na nuna baya daya daga cikin mutane masu san zuciya ko son abun duniya shiyasa sukai zatan zasu sha wahala wajan fahimtar dashi da kudi hakan yasa suka kaiyade yawan kudin amma yadda malan sule ke nuna zalama akan kudin kamar ba malan sulen da aka basu labari ba.

 

 

Dan muskutawa wanda aka kira da malan sule yay yana sosa gemunsa hadi da yin mici mici da ido yana kara lissafa ribarsa a abunda yake shirin aikatawa mai kama da san zuciya. Saida ya gama yan tinane tinanensa kan ya dago yakara kure alhaji buba da ido kamar maisan sanin asalin gaskiyar batun ta idonsa.

kau da kai malan sule yay sannan ya dora da fadin nagane toh amma indai hakane dole ni ina da yan wasu sharidai wanda karbar kudinku bazai hanani gindaya muku suba in kun amince zance ya kare in kuma baku amince ba saidai nace ku kara gaba

Shuru dakin ya dauka alhaji buba baiyi magana ba yana ta tinanin shawarar yanke wa

 

Yayin da malan sule shima azuciyar shi yake cewa tinda naji kace wadan da suka aiko ka sun riga da sun santa nasan cewa tafiya da ita ta zama dole toh dan haka bazaku tafi da ita haka kawai ba koba komai dai wai hausawa suka ce amfanin zunubi rom__gyaran muryar alhaji buba shiya kaste masa zancen zucinsa.

Nisawa alhaji buba yay kan yace

 

 

ina sauraran ka malan sule minene sharudan naka bayan naji zanje nai magana da wanda ya turoni sai muji ko zamu iya cika su.

 

 

 

Hakan yayi sharadi na farko bamai wahala Bane aguna bansan agun kuba sharadin ko shine kan tafiya da yarinyar nan dole sai da igiyar wani akanta dan bazan ci amanar siyar da ita ba kuma naci amanar mutuncin taba sannan ta haka ne kawai mahaifiyar ta zata kuma yarda da tafiyar ta cikin sauki

abu na biyu shine komai na auran za’ayi shine ba tare da wani boyeboye ba musanman dai daurin auran inaso ayishi agaban mu bawai sai anje can ba kaga ba wanda zai yada jitajitan da ba ita bace sanna koda zuwa gaba wani abu mara kyau ya biyo baya kamar ta dawo ita daya da yara ba mai sheganta min jika ko kuma batawa yata suna wanda bana fatan hakan ma,

sharadi na karshe shine ina san sanin inda zaka tafi da yar mu,gunda zata zauna, da kuma mazaunin ka kasan koba komai itadin jininace wataran inna samu dama zan iya kawo mata ziyara ko ni ko yan uwanta,

wadan nan sune sharudan๐Ÿ’… ni kuma nace wanan shine karshen page 1 lol๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜

 

**_________*Tata huf huf ya to ya kukaji?! nace ya kukaji*

*Hi๐Ÿ™‹๐Ÿปโ€โ™€๏ธall my peoples how was the first episode* ๐Ÿ˜ *hope u guys like and also love it*

*what is ur expectations about it huh* ๐Ÿ‘‚ *i need a good good comments it’s just first page your read more for tomorrow goes besed on ur today’s comments so ina jiran ruwan comment Ku dauka Mu hadu gobe domin jin yadda zata kayak*

 

_*shin alhaji haba zai yadda da sharudun malan sule*_

 

_Karku manta kuyi sharing a group’s group’s dinku na WhatsApp nagode da kasancewar ku tare dani taku har kullun_

 

*The unknown author

BADRIYA

A lady with concealed gender (MX)

 

~Storie and written by~

*~Unknown Author

 

*Da sunan allah mai rahama mai jin kai ina wa allah godiya daya bani ikon kawo muku wanan littafin na BERDRIYA fatan zaku Bini sannu a hankali dan jin mai labarin yake tafe dashi ina fatan yadda allah yasa na fara lafiya allah ya bani ikon gamawa lafiya*

 

 

*~PAID BOOK 300~*

 

 

~Little note!!!~

*Ban yadda wani ko wata ya juyamun labari ta kowacce irin hanya ba littafin BADRIYA mallaki nane sanan ka kaggen labari ne bata yadda zaiyi kama da tarihin ki ko labarin ki domun ban yishi dan cin zarafin wani ko wata ba do mun bada shawarwari ko wani korafi kofa abude take fatan za’a kiyaye nagode๐Ÿ™๐Ÿป*

 

*FREE PAGE* 2

 

*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

tin fara jawabin malan sule alhaji buba ya nemi nutsuwar sa ya rasa daurewa kawai yake amma Lallai tsohon nan dagaske yake cewar alhaj buba azuciyar sa

 

afili kuma karfin halin cewa yay gaskiya sharudan ka masu tsauri ne a garemu duk da dai muma abunda muke nema agunka bamai sauki bane sannan tafiya da ita kamar dole ne a garemu zan zanta da mai gidana zakaji bayani daga baya insha allah nagode sosai akaha sukai sallama batare da alhaji buba ya ci komai ba daga abunda aka kawo masa ba duk da irin rokonsa da malan sule yake dan shi bai lura da yanayin na alhaj buba ba

 

Allah Allah kawai alhaji buba yake ya bar dakin malan da chikin gidan baki daya kai harda kasar ma so yake ya bari, gaba daya ya birkice baza kace shine yazo gun da safe ba lokaci daya idanunsa suka koma ciki kamar wanda ya kwana yana gudawa ga wani shahararriyar faduwar gaba da yake ji

Yana fitowa sukai musabaha da malan tare da cewa sai ya gansa sannan ya nufi wata farar benze wace take kellin sabunta yana karasawa driver na bude masa kofa bayan ya shiga ya zauna driver din ya maida murfin ya rufe suka dibi hanya

 

Hotel din ko airport cewar driver’s

 

Shuru yaji ba amsa kallan fuskar Alhaj buba yay ta mudubin gaba da alamu ya fada duniyar tinani baima san yana yiba

 

sar!? sar?

 

Firgigit alhaj buba ya dawo hayyacin sa idanunsa da suka sauya cikin kankanin lokaci ya sauke kan direban murya a dishashe yace kayi magana ne

 

Eh sar nace hotel ko airport din zamu nufa

 

a’a sharada zamu tukunna daga chan kuma airport din

 

Ok sar

 

waya alhaji buba yazaro ya kara a kunne sanan yace ka sameni a sharada 1 daidai layin mai yola

 

Bayan sunzo sharadan dadai wanin dan lungu yace direban yay parking ya bude kofar da kansa yafito saida ya gama waige waigen sa baiga kowa ba sannan ya zaro wayarsa ya kira wata number kamar minti biyar saiga wani dattijo ya karaso gun yana kama da alhaji buba kamar original da photo copy saidai yanayin jikin sune ba daya ba

 

 

bayan ya karaso wajan nesa sosai sukai da mutane kan alhaji buba ya fara magana a hankali yace abu na farko shine koma mai zai faru kar kowa yasan ni naje gidan su yarin yarnan da fuskar ka komai da komai na yadda mukai da uban yarinyar yana cikin wayar nan,daka gama ji sai ka ajiyeta inda ba wanda zai taba iya ganin inda take sai kai daya,in shugaba ya yarda da sharudan suma ka karbi evidence karkayi komai ba hujja akan lamarin nan saboda gaba,

bazan iya zuwa kaiwa shugaba da kaina bane saboda hukuncin sa gareni zaiyi tsauri dan haka ka tabbatar da ka bawa shugaba bayanan komai da komai kuma kamar yadda shugaba yace dole muyi badda kama sabod bamusan suwaye suka biyo muba amma abinda na sani shine kar sakon ya wuce yau dinnan (saboda komai a kasuwa yake gidan su yarinyar ma a kone yake ) *wanan wani yaren sune da sukan yi in basa so wani ya gane abunda suke nufi* abunda yake nufi shine kar sakon ya wuce yau ba a gama komai ba saboda basu kadai bane suke san daukar yarinyar sannan koma waye uban zai’iya bawa matukar yafi saurin zuwa sannan kuma ya yarda da sharudan sa,sannan abubakar sai kayi ahankali domin sharudan bamasu dadi bane a wajan shugaba damu mu baki daya dan sharudan rashin nasarar mu kadai yake nunawa ba komai ba sai ka kula(idan ayanya bata samu damar zuwa ba nanda kwana 2 sannan aya ta koka sai akaiwa su aya sakon uzurinta wajan shugaba zai sanya hannu a takaddar hakan salama ce ga ayanya )ma’ana idan har allaj buban bai samu damar ganawa da shugaba nan da kwana biyu ba sannan ahalinsa suka koka toh shi abubakar ya sanar da shugaba game da iyalansa yasan zai kula dasu alkawarin shugaban ne

 

 

Ba abunda zai faru dakai alhaj buba insha allah dakai komai zai daidai ta kowa kuma zai samu abunda yake nema insha allah sai yanzu dattijon da aka kira da abubakar yay magana ton fara maganar sa da alhaji buba

 

 

Hannu alhaji buba ya kai wajan fuskarsa ya cire fuskar sa da take kama da ta abubakar take asalin fuskar alhaj buba ta baiyana wanda ba iri daya take da ta abubakar ba.,

bayan alhaji buba yaba abubakar sakon sukai sukai sallama cike da alhini da kewa ya juwa zuwa gun motar sa inda direban sa ke jiran sa baya bude gidan baya ya shiga tare da rufe kofar direban ya tashi motar suka dau hanyar airport direct gaba daya hankalin alhaji buba baya jikinsa dan ma bashi yake tuki ba ,

 

direban sai zuga gudu yake bisa umarnin alhaji buba da yake ganin kamar ba tafiya motar take ba,

 

Kusan za’a ce tsakiyar ranane lokacin kuma iya motar suce kawai a baban titin kandahar din haka yawancin lokuta titin yake kasan cewa saboda nisan sa,

babbar mota ce tayo kan motar su alhja buba kara ware ido direban yay yana salati duda da nisa kadan tsakanin su amma kana gani kasan saitin su tayo kuma titi hannu dayane ba biyu ba bare ace sai tayi kusa dasu sanna zata kauce musu da wani kalan ihu a burkice alhaji buba yace wa direban yay ribos su juya ya, da sauri drivan ya taka motar yaci uwar ribos ya juya baya sadai kan ya ankara wata babbar motar irin dayar dake bayan su itama ta yo kansu ta buge bayan motar su.

 

wanda saida motar tai katantan wa sau uku sanan ta tsaya gu daya a kife tana hayaki babbar motar da zo ta wuce dayar babar da gudu itama dayar saida ta kara ingiza motar zuwa gefan titi ta gangara chikin ciyayin gun sannan mai tuka baban motar ya karsa kusa motar dake kokarin kamawa da wuta saboda hayakin da ke tashi a jikin ta ba tare da ya fitoba matu kin ya kunna laita sanan ya wurgo chikin motar sannan ya taka motarsa ta glass din hanunnun motar ya hango wutar da ta maka da motar.,

 

bakin mutumin dake gaban motar ya zaro waya yana murmushi yace yace alhaji an gama da wanan shafin saura gidan su yarinyar zanyi magana da su ojo zasu satota zuwa gobe da dare tana hannun mu daga haka ya katse kiran yana taka motar tasa da uban gudu ,

 

a chikin motar kuwa gaba daya su alhaji na kokarin fitowa jiki du jini amma kofar taki buduwa har wutar ta karaso kansu suna ihun naiman tai mako babu matemaki haka suna ji suna gani suka kone kurmus wan nan kenan.

 

 

Alhaji abubakar da har lokacin yana staye inda alhaji buba ya barsa ya saka hagu ya saka dama haka kawai yake jin fargaba ga tinanin alhaj buba daya adda besa da kalaman sa ahankali kamar mara laka ya nufi gunda suma sukai parking din mototinsu guda uku gaba daya motocin bana wasa kana gani kasan maisu duniya na damawa dashi bayan karasawa daya daga cikin excord din dake wajan ya bude masa kofa ya shiga sai da yay conecting wayar da alhaji buba ya bashi da btooth din sa ya rage volum ta yadda ba mai ji sannan ya kunna yana jin gaba daya tattaina war da alhaji buba yay da malan sule shikan shi jin sharudan saida suka sashi rudu lokaci daya nustuwa tai masa kaura Aminu kano airline ya iya cewa da direban kawai ,

ta CC btooth drivan ya sanar da sauran excord din inada suka nufa take.

 

 

Malan sule kuwa bayan tafiyar malan buba komawa cikin dakinsa yay jakar kudin ya adana akasan gadon sa kan ya rufo kofar dakin gaba daya ya nufi massalci jin ana kiraye kirayan sallan ahzahar yana tafe yana sakawa da warwarewa shi daya sai kada kai yake kamar kadan gare bayan fitowa daga masallacin kasuwar dake kusa da su ya wuce kayan cefanan rana ya siya sannan yay gida ta ianahin kofar shiga gidan ya shiga wadda ke kusa da dakin sa daya fito dazu matsakai cin gidane mai dauke da dakuna hudu chiki harda na malan wanda yake da kofa ta chiki da ta waje sai dan karamin kichin da ban daki ba kowa a tsakar gidan da rana ta kwllewa sannan sti kamar ba mai rai a gidan daga kofar kicin din kuwa shinkafa ce a babban faranti danya a yashe sai tukunya akan gawayi wanda keta hayaki shi kadai direct chan malan ya nufa yana aje ledar hanunsa sannan ya fara kwada kiran

 

ummusalma ? ummusalma ?

 

“Ehemm”” akace a daya daga chikin dakunan dake jere a tsakar gidan karasawa yay dakin ya dage labulen dakin ya shiga bawani tar kace achikin dakin gado ne babba kan gadon ne dai ba dadin kalla saboda kayane zube ta ko ina sai sifdin kayan sawa wadda take duka kofofin suke a bude suma kayan ciki du a hargitse suke wasu kar kasa suka zulalo sai madubi wanda iya durowar madubin ne kawai ba fuskar shima kacha kasa yake da su kofi ledar buredi da sauran tarkace na mata dakin dai gaba daya a kargiste yake akan wata 2seater dake dakin ya hango matar tasa wato ummusalma itama dai sai ka ganta dai da ita da dakin babanban cin kadan ne ๐Ÿ˜‚dattujuwa ko mata zamu cemata oho a

zaune take hannunta rike da waya keypad tana danna wa bakin ta kuma chike da goruba irin wadda ake fashetan nan ga ledar a gefen ta kasan dakin kuma ledace gaba daya ta gama yayyagewa wani wajan akwai leda wani wajan sumunti ne daga ta wajan kafarta kayane a kulle kamar dai wanki aka hada gabansa kuwa kofunane kusan guda shida a wajan kudaje kuwa sai bi suke da alamu na karin safe ne daba’a dauke ba ga kanakun buredi nan du a waste dakin dai ya chika ya chike akira shi da mazaunin kazan ta uba uban wani kalan kamshi da yake fitarwa mara dadin ji

 

 

Saida ya gama kare ma mai dakin da dakin kallo yana yasti na sannan yace.,

 

ummusalma ashe bama sallah kike ba kike cemun ehem

 

Wadda aka kira da sunan ummusalma ta dago tai masa wani kallo kan ta dauke kai kuma har lokacin batace komai ba

 

Shima dauke kai yay kan yace anjima kizo daki ki sameni sanan tin yaushe na kawo kawo shinkafar nan da baki girkafa kitashi kiji kiyi yanzun nan yana kaiwa nan ya juya zai wuce batare da ya jira ji daga gare ta ba

 

 

wuff kamar wadda aka tsikara haka ta tashi har dan kwalin kanta na fadu tasha gaban sa tan masa wani kallo cike kuma da jaraba ta fara fadin kadai san ba kayan wanki kazo ka ajiye ba ko da zaka wani kawo zallar shinkafa ba mahadi wani ne zai baka mahadin sannan ka wani zo kana mun maganar na bika daki in je inyi mi da rana tsaka baka aje komai ba sai tara yaya da jaraba ko ciyar da su ka kasa toh dasake wlhi malan ta fada tana wani jijjiga jiki hadi da rike kugu ๐Ÿง๐Ÿ™„

 

Lalai ummu dade warki agidan nan harta baki lasisin fadan magnar banza akan yayana ke kike ciyar mun dasu dana saka ciyar dasu din sannan kun taba wayar gari baku ciba ko kun taba kwana baku ciba sanan kin duba kicin din baki ga mahadin bane zaki zizo kina mun iya shege marasa godiyar allah kawai zanyi maganin kine dani kike wlhi

 

 

Wowowo ka daiji kunya wlhi malan dama kai burunka kenan kaiwa mutane gorin jimawa da aure toh kaji ka kara sani malan wannan auran nawa dakai ba mai mutuwa bane,

ka saki ko nawa zaka saka ka kuma auri ko nawa ne da muwarka ce ni dai dince nan gani nan bari dashen allah ce ba yadda zaia dani atoh tana kai wa nan ta angije malan tafice a dakin

 

 

Salma tijara malan yace cike da jimantawa kansa a hankali ya sako kai yana leka tsakar gidan ganin ba kowa wajan yasa shi sauke ajiyar zuciya kana ya fito daga dakin yana fadin zanyi maganin ku ne daya bayan daya a sannu

 

Dakin dake kusa da inda ya fito ya nufa ya daga labulan daga waje ya tsaya yana jan tsaki afili ya furta anata baccin asarar kenan kafa yasa ya bugu kyauri dakin da karfi

 

wanda hakan ya sanya wadda ke sheme akan gadon zabura baki du yawun bacci zani a jefe sai iya under siket dinta tana fadin isuhu kune kun dawo ne ku,…. wanda ta gani a kofar ne ya sata washe baki yalayen hakoranta suka baiyana dakin gaba daga kari yake daga zarnin futsarin yara sai warin dauda har wank karni karni dakin yake kai har gwara dakin ummusalma da wannan san wanan ko minti biyar chikkek mai kyau baza kai a ciki ba ko ledar dakin ita babu

 

 

ah malan har ka dawo sannu da dawo wa yanzu fa na kwanta ashe baccine ya kwashe ni tafada tana hamma dani da sosa gashin kanta wanda kiston ya gama tsufa ko tsagar baka gani,

 

wata uwar harara malan ya watsamata yan kara jan staki sanan ya nunata da yasta rai bace yake fadin dan allah kalleki kalleki maman isuhu allah nagode maka da wadan nan kalolin kazaman matan da ka jarabceni da su yan z……

 

Ah kadai jarabci kanka da mu ko malan gyara maganar ka wata ta kaste masa maganar sa daga waje.

 

Ba ummusalma bace watace daban tai maganar da alamu itace cikon ta ukun matan nasa dan itama dai gata ga kalan su

ita shigowarta gidan kenan riga da zanine ajikinta da suka gama kodewa sai wani uban sharbeben stoho silifas dan madini daya gama sudewa sai go to a bayan ta amm goyon irin gowan wulakancin nanne akaiwa yaran du ya zazzago hancinsa da fuskar ba kyan gani ga wata uwar jar poss dake makale a hammatar matar wadda itama ta gajida life ๐Ÿ’…๐Ÿป

 

Jama’a wani abu sai matan malan ๐Ÿ˜‚

 

*shin suwaye suka kashe malan buba minene kuma dalilin su na yin haka?* *sanan ahugaban su abubakar zai amince da sharudan malan sule kuma duda jin cewa sharudan faduwace gare su?* *shin su ojo zasu sace yarinyar kamar yadda wanan driver din ya ma alhajinsa alkawari*? Ya abun yake ne jama’a

 

*Naga comment sosai jiya kuma naji dadi na gode sosai da sosai allah bar zumunci masu tambayar sunanna ku zan fada muku karku samu damuwa*๐Ÿซ ๐Ÿ˜

 

 

*Hi๐Ÿ™‹๐Ÿปโ€โ™€๏ธall my peoples how was todays episode* ๐Ÿ˜ *hope u guys like and also love it*

*what is ur expectations about it huh* ๐Ÿ‘‚ *i need a good good comments it’s just first page your read more for tomorrow goes besed on ur today’s comments so ina jiran ruwan comment __Ku dauka Mu hadu gobe domin jin yadda zata kayak_*

 

_Karku manta kuyi sharing a group’s group’s dinku na WhatsApp nagode da kasancewar ku tare dani taku har kullun_

 

*The unknown author

Add Comment

Click here to post a comment