Littafan Hausa Novels

Al’adar Mu Hausa Novels Complete

Al’adar Mu Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

AL’ADAR MU

 

By _Qamshi_

 

✍️ _FIRST_ _CLASS_ _WRITER’S_ _ASSOCIATION_ 💖✨.

 

 

 

✨ *Bismilahir* *Rahmanir* *Rahim* ✨

 

 

1…..

 

A ka ce dukiya maganar me ita take ji, hak’ik’a na k’ara gasgastawa a lokacin da idanuwana suka yi tozali da wannan katafaren d’akin, wanda ya k’awatu da kayan alatun rayuwa, kama daga furnitures d’in ciki, dama duk wani abu da ya k’unsa, yanayin d’akin kad’ai ya isa ya bayyana ma awane irin gida kake ciki, ba tare da an fad’a maka ba, wato gida ne na masu hannu da shuni, wad’anda ba su san babu ba ballantana rashi, sai dai matsolin rayuwa, wad’anda kud’i ko mulki basa maganin su,. Kuka take tamkar wacce uwarta ta mutu, kuma deep inside her fatan ta bai wuce ganin mutuwarta a wannan lokacin ba,

 

 

dan tana ganin mutuwar ce kad’ai maganin matsolin ta in sha Allah, Sosai hajiya Aysha ke kallon ta, abubuwa dadama nayi mata yawo akai, amma takasa ce mata komai, saboda sanin datayi mata na mace me matuk’ar hak’uri, ta tabbata yau hak’urin yayar tata ya gaza, dan abu ne me matuk’ar wuya ka ganta cikin damuwa, no matter how hard the situation it’s, amma ga shi a ‘yan kwanakin nan har da kuka, kuka kuma irin me cin ran dukkan ma’abocin sauraro, kuka wanda yake nuni da tsantsar rauni irin na ‘ya mace, gaba daya ta fige ta rame ta kuma yi bak’i, hatta da lips d’inta sun bayyana k’ararar damuwar da take ciki, in a just 2wks ta koma tamkar wacce bata tab’a sanin wani abu da’ake kira farin ciki a rayuwa ba, Sai da ta share hawayen kan fuskarta, sannan taruk’o hannunta, cikin sanyin murya ta fara magana,..”Pls Aunty kiyi hak’uri”.

 

Gyad’a mata kai hajiya Marwah tayi, saboda ita kanta ta gaji da kukan, sannan tana matuk’ar tausayin k’anwar tata, saboda yanda ta d’aura wa kanta damuwa, itama har ‘yar rama tayi, saboda damuwar yayar tata, “Kici abinci kisha magani Aunty”. Hajia Aysha tace, saboda lura da rashin son rarrashin da hajia Marwahn keyi, dan ma mik’ewa tayi ta nufi mirror, hankerchief din dake saman mirrorn ta d’auka, ta share hawaye, sannan tace “ni ban da yunwa Aysha, zan shiga in watsa ruwa, Cikin yanayi na damuwa hajia Aysha dake k’ok’arin fita ta dawo, tace “Na ji kamar kin yi magana”?, “I, nace ba ni da yunwa”, to me kika ci?, “ki ji ni da Aisha, to nasha tea, kai aunty wane irin tea, abinda kika sha shi tund’azun, kinji kide shiga ki watsa ruwan, ni bara na samo maki wani abu med’an saukin nauyi ki sama ciki, murmushi kawai Hajia Marwah tayi, daga haka ta shige bathroom, ita kuma hajia Aisha ta nufi kitchen, stew din da ta gani a fridge ta d’auka tayi warming, sannan ta dafa couscous, within few minutes ta gama, saboda dukka abubuwan ba masu wuya ba ne, d’aura warmers d’in awani silver tray ta yi, sannan ta nufi d’aki, Koda ta koma d’akin bata iske yayar tata ba, saboda data shiga wankan zama tayi tasha kukan ta, sannan ta mik’e ta watsa ruwan, tana fitowa taga hajia Aysha abakin gado tayi tagumi, kallo d’aya ta mata ta d’auke kai, saboda sanin ma’anar tagumin nata ko da ko ba’a fad’a mata ba, “Lafiya ko Aisha”?, murmushi tayi, dan batayi nisa acikin tunanin nata ba, kafin tace “Bakomai Aunty”, Kawai dai ina mamakin k’ok’arin Faridah ne, “Hmm ke dai bari Aisha, ni wallahi har yau na ka sa yarda Faridah ta gudu ne dan kanta, kullum gani nike kamar wani zezo yace man shine ya tursasata”,

Rayuwata Hausa Novel Complete

Tursasawa kuma Aunty?, to waze tursasatan?, kede kawai ki kalli dan yau, kamar kuma yanda kike cewa ne ba’a shaidar shi, wallahi banyi mamakin hakan ba, saboda k’arancin kwab’on da suke dashi, bama kamar su Meerah, narasa meke damun mahaifansu sam, gade nasabar amma sunk’i maintaning d’inta, kuma dan Allah Aunty karki kuma tunanin furta kalmar tursasa Faridah akayi, dan da kinyi kuskuren fad’a a gaban wani za’ace dama can da goyon bayan ki”. Ringing’s d’in da wayar hajiya Marwah tafara yine yasa su yin shiru, sunan daya bayyana akan screening d’in wayar ne yasata hanzarin picking, ba tare da sallama ko wani dogon zance ba, wacce takiratan tafara magana cikin muryan fad’a, “An ga Faridah kuwa”?, rasa ansar bata ya sata yin shiru, tambayar ki fa nake Marwah kika yi man shiru, a’ah ba’aganta ba, hajia Marwah taba yayar tasu ansa dashi a tak’aice,. ‘”Oh ni Maimunatu”!! wai yanzun Marwah kina son kice mini ba’aga Faridah ba kike zaune gida hankalinki kwance, ‘yar ki mace fa, ‘yarki mace ta gudu tabar gida akan abunda ki ke da damar yi mata, kikasa sannan ki zauna d’aki kinashan AC?, anya Marwah kina da hankali kuwa?, kinsan me kikeyi kuwa?, da’an magana ki fara kuka kina cewa har yanzun an kasa fahimtar su waye dangin mijinki, su dangin mijin naki ba suda nagaba ne?, ko idan basuda nagaba ba hukuma ne?, ni wallahi da Ina kusa da sai nasaka an d’aureman wasu daga cikin su, dan banga anfanin bad’i ba rai ba, ace wai sunaji suna gani yarinya tab’ata har na tsawon sati biyu amma har yanzun ba wata k’wak’wk’warar magana Fisabilillah”‘. yanzun haka zaki zura masu ido, kina ganin idan cikin ‘ya ‘yan so ne zasuyi haka Marwah?, afa wannan zamanin da muke ciki baka jira a temake ka, mik’ewa kake da kanka ka tai maki kanka, kuma ni anawa tunanin yanzun ko d’anki namiji ya gudu yabar gida ai bakya zauna ki zira ido ba, ballantana kuma ‘ya mace, ‘ya mace budurwa, budurwa mai ji da gata, wayewa da kuma wadatattun kud’i a account, “Yakike ganin wannan lamarin Marwah?” Yakike gani idan akace yanda yaran mu suka saba da almubazzaranci zatayi kina ganin kwana nawa kud’in account d’in nata za suyi mata?, Sannan bayan wannan kiyi tunanin halin da za ta shiga a lokacin da suka k’are, ashe ba zakiyi yun k’uri akan guduwan yarinyar nan ba tun kafin lokaci ya k’ure maki Marwah?, ki duba fa kiga wannan lamarin, cikin sheshshekar kukan daya dawo wa hajia Marwah sabo tafara bama yayar tata baki akan maganganunta, “Ana nan anata bincike Maman Sudais”, Kuma Abbanta yace yana sa ran soon za’a ganta in sha Allah”. “Taya Marwah?, hajiya Maimunah ta katse ta da fad’ar hakan, yace an samu information akanta, toh Allah dai yasa, hajiyan tace, dan har cikin ranta taji bata gamsu da maganar k’anwar tata ba, saboda sanin halinta na sanya da kawaici, ta naji tana gani rayuwar ‘yarta zata wulak’anta, amma taja baki tayi shiru, sai anjima, tafad’a daganan ta katse wayar, “Kina jina da Aunty ko Aysha”?, Hajia Marwah tafad’a tana murmushi. Sallamar da akayi abakin k’ofar d’akin ne tasa hajiya Aysha dakatawa da maganar datake shirin yi, “Wa alaikumus salam”, Hajiya Marwah ta ansa dashi, Ummah granny na kira, wata ‘yar matashiyar yarinya ce tafad’i hakan bayan shigowarta, cousin sis d’insu Faridah ce, “Tana part d’in wanene”?, hajiya Marwah ta tambayeta a tak’aice, Umman su Malik, ta bata ansa dashi sannan ta juya tafita, “Ya kukayi da Auntyn”?, Hajiya Aysha ta tambayeta?, bari in dawo hajiya Marwah tace tana zira hijab ba tare da tasa kaya ba, wannan gaggawar fa ta me cece Aunty?, so nike naje naji ko lafiya Aysha, kin san ance da zafi zafi akan daki k’arfe, “Eh hakane”. To amma dai da kinsa kayan, tunda ba guduwa zasuyi ba, kuma a yanayin wad’annan dangin mijin naki ai da sunji shiru ma zaki gansu, ke kuma ganin nasu kike son yi koh?, saboda Allah be sa kina k’aunar zaman lafiya ba, to in sha Allahu ba zaki gansu ba”. Tafad’a tana cire hijabin da tasa, murmushi hajia Aysha ta farayi kafin tace. “Subhanalillahy”, Aunty yau nice kuma mara k’aunar zaman lafiyan?, tabd’i, kawai dai nafad’i abinda nasani a game da sune”, “To ai kin kyauta”. Tafad’a sannan tabar d’akin, dan tuni ta zira doguwar rigar data ciro, Part d’insu Umman Malik ta nufa, kamar yanda Naanah tafad’a mata, da sallamarta ta shiga, amma ba wanda ya ansa mata, duk da ko muhimmanci irin na sallama, Hajiya Bilki, Barr d’inta da kuma mahaifiyar su ta gani zaune a d’akin, kowa se huci yake kamar wad’anda sukayi gudun fanfalak’i, “Innalillahy wa’inna ilaihir raji’un”, Tafad’a a k’asan ranta, sannan ta samu wuri daga d’an nesa da Yabi wato maman mijinta, tace “Ina yini mama”, a’aah Marwah daban yini ba ai bazaki ganni anan ba, kokin tab’a ganin matacce na gudanar da rayuwar shine?, dan made bak’in cikin ki dana yaran ki nata rugurguzan d’an sauran farin cikin da ya saura man, ai dama nafi hakan, “Wane ita”?, ai sai dai tayi wanda zata iya, hajiya Bilki tace tana jijjiga K’afa, “Dan Allah Hajiya mubar wannan zancen muyi abunda ya kawo mu”, Barr yafad’a cikin muryar damuwa, “Um kinga inda ‘ya da uwa suka samu d’aurin gindi nan, to inba anan ba a ina?, na ga dai dukkan mu a tsaye muke, to duk tsayuwar mu in mijinta be nuna mata hakan ba ai ta bazan ce, a de juri zuwa rafi Marwah, wallahi wata rana da kanki zaki gane wannan bokan naki k’arya yake fad’a, shikam ai Barr yana jin hakan yayi shiru, saboda sanin halin yayar tashi da hawa kuma ta tsaya, “Ke yanzun Marwah kina ganin shawarar da kika ba ‘yarki me billewa ce?, Yabi ta fad’i hakan cikin murya mai tafe da wani irin amo dake nuni da tsantsar damuwar da take ciki, “Hai, hai mama”. Kekam kinada son d’aurawa kanki rigima, ga abunda muka zauna tattauna akai amma kin kamo wani zance daban, ina ruwan ki da batun b’atan Faridah, tunda uwarta taga hakan shine ze bille masu?, “a’ah, Bilkisu barni in magantu akan Faridah, kar da uwarta taje gaba tana cewa saboda tsanar da nayi mata ko damuwa ma banyi da b’atan ba, “Hmm mama kenan” To aisu dangin miji basa gwaninta, ko da ko fad’uwa k’asa za kiyi kina mirgina saboda b’atan Faridah, uwarta ba gani zatayi ba, saboda haka kawai mu yi abunda ya taramu, kamar yacce me gidan ta yace, to ai shikenn” Yabi tace tana jinjina kai, dan sosai b’atan Faridan ke yi mata ciwo, saboda akan shi tafara samun k’alubale da sauran jama’ar su,. “Zagin ta tas hajia Bilki ta yima Hajia Marwah, ita dai ko d’ago kai ba tayi ba, balle susa ran zata tankasu, sai da suka gama sannan sukace zata iya tafia, A sanyaye ta mik’e ta nufi bakin k’ofa,.”Aff kinga namanta”, Uwar masu ‘yancin da yafi na sauran ‘ya’ya, hajiya Bilki tace tana murmushin gefen baki, ko kad’an hajiya Marwah ba tayi alamar juyowa ba, duk da jikinta ya bata cewa da ita take, amma sai ta d’auke kai ta cigaba da tafiya, dake fa nike Marwah, hajiya Bilki tafad’a cikin muryan gatsali, Na’am tace sannan ta juya, nace ba “Ki sallami wannan bak’uwar taki hakanan, tana gama fad’ar hakan ta mik’e tafita ta back door, ba tare da ta jira ji daga bakin hajiya Marwah ko wani daga cikin d’akin ba, Sororo hajiya Marwah tayi, saboda mamaki da al’ajabin da ya cikata, yau kuma Ayshan ce bak’uwa, “Ahhh lallai Aunty Bilki”, Tafad’a a k’asan ranta, sannan ta kama hanyar nata part din, ba tare da ta bari Koda kuskure sun had’a ido da gwanin da ayanzun take nadamar auren shi ba, duk da ko yanda ya kafeta da ido, koda ta isa part d’inta, ta iske hajiya Aysha zaune a parlor tana tsakurar abinci, kallo daya zaka mata ka hango damuwar da take tattare da ita, K’arfin halin d’agowa ta yi tace “Harkin dawo”?, Eh na dawo, Toh dama ina nan inata jiranki, lafiya dai koh? hajiya Marwah ta tambaya a d’an dame, “Uhmm dama Abban Nurain ne ya kirani wai gashinan ya dawo gida zazzab’in da nace maki ya kwana dashi jiya yadawo”. Boyayyiyar ajiyar zuciya hajiya Marwah ta sauke, dan dama tana ta tunanin ta inda zata fara yima k’anwartata bayanin cewa ta tafi gidan, saboda sanin halinta na kafiya da rashin tsoro, ta san sarai zata iya zuwa ta sami Aunty ta tambayeta dalili, musamman idan ta d’ago cewa itace ta fad’i hakan, sannan kuma tasan itama Auntyn zata iya zuwa ta duba tunda ita rashin mutucin gaba ta bashi ba baya ba, shiyasa duk ta shiga damuwa, amma jin abinda k’anwar ta ta tace ya saka ta samun wani irin relief har cikin ranta, duk d
a ba taso wannan d’in ya zama dalilin tafiyarta ta ba, sannan kuma taso suyi magana akan abinda Auntyn tace mata, amma ai ba komai tunda zasu kuma haduwa, “Subhanalillahy”!! Allah ubangiji ya bashi lafiya, yanzun zaki tafin kenan?, “Eh” Tace bayan ta mik’e, to da mota kikazo ko na kira driver ne?, a’ah na kira driver, kuma na san in sha Allahu yana hanya, ok toh hakan ma is ok,. Bedroom d’in hajia Marwah suka nufa ta saka mayafi, tad’auki handbag d’inta, da nufin cewa za taje parlor ta jira kiran drivern, ai koma suna isa parlorn Kiran shi ya shigo wayarta, nan tad’aga da fad’ar “Har ka k’araso”, Eh hajiya kawai yace mata ta katse kiran, ba tare da ta cemai komai ba, hanyar fita suka nufa inda sukaci karo da hajiya Bilki, “Oh ashe kin samu da sallamar tan”?, I thought ba zaki iya bane shiyasa nazo da kaina, kin san ance zuwa dakai yafi d’an sak’o, juyawa hajiya Aysha tayi tana kallon yayarta, dan ita tana bayane, k’arin bayani take nema, amma ba taga fuska ba, dan sosai hajiya Marwah ta d’aure fuska, muje kawai tace mata, da ga hakan suka tafi suka bar hajia Bilki tana murmushi, A compound suka iske drivern yana jiranta, yana ganin ta ya bud’e mata motar tun kafin ta k’arasa, “Sai munyi waya” Hajia Aysha ta cema yayar tata bayan tashiga mota, “Okay a gaida me jikin”, Zaiji in sha Allah, daga haka driver yaja sukabar compound d’in, ita kuma ta koma cikin gida, zuciyarta cikeda rashin k’arfin guiwa da kuzari, gaba d’aya zaman gidan ya isheta, ta rasa me mutanen nan ke nufi da ita, “Shikenan ita ba ta da ikon yin motsi acikin gidanta, ko wani d’an abu ya faru sai akawo ido a zira mata daga ita ko har ‘ya ‘yanta, haka rayuwa zata cigaba da tafiya, ba wani say ko katab’us acikin gidan ta, da ma acan baya Faridah ne ke shiga lamarin da kuma k’arfafa mata guiwar zaman gidan, to gashi yanzun tayi mata nisa, nisan da kusan 90% ta zama sila, dan tun kafin Faridah ta isa aure ta kance ma mahaifiyar ta itafa bazata yarda da auren had’i ba, a lokacin in tafad’i hakan seta kama fad’a, tare da k’arawa da kada Allah yasa taso, tunda tafi sauran ‘yan uwanta ‘yanci ne, ko tafi su galihu da suka hak’ura, ko kuma taga sun mutu, A sanyaye ta shiga bedroom d’inta, sai da tacire hijab sannan ta jawo wayarta, dialling numbern Faridahn ta k’arayi akaro na ba adadi, amma har iwarnan lokacin ba sauyi daga call ended sai switch up, ganin ba zata sameta bane yasata mik’ewa da nufin shiga d’akin Faridahn, tana shiga ta fara dud duba side drower’s d’inta, da tunanin ko za taga wani abun, amma har ta gama ba taga komai ba, cikin tsananin damuwa ta nufi hanyar fita amma sai zuciyar tabata shawaran duba wasu wuraren, tunda ba’anan kad’ai take ijjiye ijjiyenta ba, a hankali ta koma cikin d’akin, wurin handbags d’inta dake sagale a saman hanger ta fara nufa, daya daga cikinsu ta d’auka ta fara dubawa, k’aramar wayarta ta gani aciki, saboda haka sai ta koma saman gado, dan taji ba ita kad’ai bace aciki, ilai ko sega babbar wayarta a wani side din, kunna ta tayi, dan tasan password d’inta, direct wurin message’s ta nufa, all time fav” taga anyi saving numbern da message d’inta yake unread dashi, a hankali ta bud’e message din, abinda tagani ne yayi nasarar tarwatsa duk wata natsuwa data saura mata, take taji kanta ya na sara mata, “Tayama zata yarda da abinda idanuwanta suka gane mata in har ace wanine ya fad’a mata?, taya zata yarda da cewa Faridahn tace ta jefa kanta a irin wannan rayuwar? “Garin wane sakacin da rashin sa idon?, ta jefawa kanta tambayoyin a lokacin da taji kan na k’ara sara mata sosan gaske, Rashin samun ansar ko guda daga cikin su ne ya sata tafiya kai tsaye whatsapp, kamar tasan zata kuma gano wani abun da ze gigita mata lissafi, “Innalillahy wa’inna ilaihir raji’un!! Innalillahy wa’inna ilaihir raji’un!!, tayi ta maimaitawa a fili, duk da abunda ta gani da farko yafi muni amma na whatsapp yafi mata zafi, dan she neva expect that from them, dama gaskiya ne kenan da ‘yan uwanta ke fad’ar ita d’in sakaryar uwa ce?, da gaske kawaici da alkunyar tane za suyi silar d’aidaita mata ahali?, da gaske ne duk abubuwan da suke fad’a amma ta kasa fahimta, ta rink’a ganin kamar sun sa mata ido?, Hasbunallahu wani’imal wakil, “Allah natuba”, Shine abunda hajiya Marwah tafad’a a lokacin da taji gaba d’aya tsanar kanta da tausayin yaran nata na ka mata, tabbas ta tausaya masu da ta kasance uwa a garesu, ta tausaya masu da tazama wani jigo na rayuwar su, dan dole ne ka tausaya wa duk wanda yayi rashin ja jirtacciyar uwa, Jarumtar maida mata tarkacen ta tayi sannan ta d’auki dukka wayoyin, a hankali ta mik’e ta nufi hanyar da zata sadata da nata d’akin, yanda take tafiya kad’ai ya isa ya bayyana ma tsananin k’arfin halin da takeyi.

*08152163536*✍🏻.

[24/10, 10:27 am] +218 92-2035171: AL’ADAR MU

 

 

By _Qamshi_ ✍️

 

2…

 

Baki d’auke da sallama ta shiga bedroom d’inta, edge d’in gado ta nufa ta zauna, wayoyin Faridah data kashe ta saka acikin handbag d’inta dake saman gado, sannan ta mik’e ta nufi d’akin su Jiddah, kwance ta sameta akan gado, kallo d’aya zaka mata ka hango tsananin damuwar da take ciki, d’auke kai hajiya Marwah tayi da ga kallon da takeyi wa ‘yar ta ta wacce ba tasan da shigowar ta ba, saboda nisa da tayi acikin dogon tunanin da takeyi, dafatan da tayi ne ya sakata yin firgigi, tare da sakin murmushin da yafi kuka ciwo da k’ona zuciya, “Ummah”, Jiddahn tafad’a tana k’ara fad’ad’a fara’ar kan fuskanta, dan sosai takeson b’oye damuwar da take ciki. “Meke da munki?, hajiya Marwah ta tambayeta bayan ta samu wuri ta zauna, kaina ke yiman ciwo, tabata ansa dashi, tana d’an yatsina fuska, alamun tanajin ciwon sosai, murmushi Ummahn nata tayi, dan ta fahimci tanayi ne kawai saboda ta kawar mata da tunanin kilan damuwa take ciki, “Bayan kai sai kuma me Jiddah”?, Babu komai Ummah, kin tabbata?, Ummahn ta tambaya tana murmushi, itama murmushin tayi duk da murmushin mahaifiyar tan ya d’an bata tsoro, sannan tace “Eh”, Ok toh ki tashi ki shirya muje asibiti, zaro ido ta fara yi, kafin tace Ummah wanene kuma ba lafiya?, kene bakida lafiya, tafad’i hakan kai tsaye, a’ah Ummah nifa ciwon kai kawai nace maki inaji kuma fa nasha magani, do what i said, Ummahn tace, sannan tabar d’akin tana fad’ar in kinga ma ki sameni a daki, “Oh Allah” what’s wrong with Ummah?, tafad’a tana dafe b’arayin da takejin yana sara mata, veil and shoe’s d’in da ta shiga dasu school d’azun ta saka, sannan tabar d’akin, ba tare da tayi tunanin duba fuskar ta ba, a parlor ta iske hajiya Marwah ta nata safa da marwa, motsin Jiddahn ne ya sata saurin goge hawayen da suka fara wanke mata fuska, sannan ta juyo tace “Kin shirya”?, “Eh, ta bata ansa dashi a tak’aice, muje kawai tace mata, daga haka suka kama hanyar fita, “Ummah zanyi driving d’in” Jiddahn tace a lokacin da suka isa compound d’in gidan, kallonta hajiya Marwah ta farayi daga farko kamar me tunanin wani abu, sai kuma ta ce “Zakiyi driving”?, Eh Ummah, a ta yaya?, ke da bakida lafiya, “Kai Ummah headache ne fa kawai kuma nace maki nasha drug’s”, Jiddah tafad’a tana turo baki, “Ooh haka”, to jeki anshi key wurin Manniru, key’s d’in motar ta anso tazo taja suka bar compound d’in, Hanyar family hospital d’insu ta nufa, saboda dai tasan dole can d’in zasu, amma ga mamakin ta da taji Ummahn tace gidan su Aysha Kabeer za muje, waigowa tayi tana kallon mahaifiyar ta ta, kafin tace “Wacece kuma Aisha Kabeer Ummah”?, kawar Faridah, tabata ansa dashi a tak’aice, shiru tayi Jiddah tayi na wasu lokuta k’alilan, saboda tunanin abunda ze kai Ummahn nasu gidan su Aunty Ayshan, kafin tace “To”, Duk da tasan cewa Ayshan bata gari, amma tana ganin bai kamata tafad’a ma mahaifiyartan ba, dan tasan tana iya cewa ya akayi ta sani, kuma ita abunda yasa ta sani, shine sunyi chatting a daren jiya, tasan kuma Ummahn na iya cewa daga sch taje, shiyasa tafad’a mata hakan, dakatawa da reverse d’in da take ta k’ok’arin yi tayi saboda maganan Ummahn nata da taji ta tamkar saukan aradu, kinyi shiru baki ansa ni ba, ko bakijini bane na maimaita?, hajiya Marwah tafad’a tana share hawayen da ta keta k’ok’arin b’oyewa tund’azun, amma k’unar dake cin zuciyarta ya hana hakan kasantuwa, kasa cewa komai Jiddah tayi, saboda nauyin da tambayar tayi mata, “Nace da gaskene ban cancanci zama uwa ba Jiddah?, ta maimaita akaro na biyu, cikin rawar jiki da murya, dan har k’asan ranta takejin maganar, itama Jiddahn kukan ta fashe dashi, saboda yanda taga mahaifiyar tata na kuka, murya na rawa tace “Ummah dan Allah ki daina fad’ar hakan, na rok’eki”, Taya Jiddah?, hajiya Marwah ta tambayeta, bata kuma jira jin ta bakinta ba ta cigaba da magana, cikin sheshshekar kukan da yagama cinyeta, “Bayan hakan ba k’arya bane”, Bayan hakan shine gaskiyar magana, ba kuma abakin mutun d’aya na jita ba, sai dai a yanzun na k’ara gasgastawa, da naji mutanen dake yi mini kallon uwa sun fad’i hakan da bakin su, kuka Jiddah ta rink’ayi tamkar wacce uwarta ta mutu, tarasa abunda zata ce mata, wai itakam ta ina zata fara ne?, ya zatayi da wad’annan tambayoyin na mahaifiyar ta?, ba tagama tunani akan maganar Ummahn ba taji ta kuma jeho mata wata tambayar, murya cikeda tashin hankali, wani sabon tashin hankali da tunanin yanda akayi Ummahn tasan wannan zancen ne ya dirar mata, “Dan Allah Ummah kibar maganar nan”, Dan Allah, d’an murmushi hajiya Marwah tayi, saboda dai ta fahimci a yanzun ba zata samu ansarta ba, duba da yanda taga Jiddahn ta fita a hayyacinta cikin lokaci k’alilan, “Muje Jiddah”, Hajia Marwah tace, saboda son kawar da wannan tashin hankalin da taga tana neman jawo masu akan titi, sai da Jiddah ta share hawayen kan fuskarta, sannan tace “Gidan su Aunty Ayshan”?, A’ah gida zamu koma, tada motan tayi suka wuce, Cikin rashin kuzari take driving d’in, duk kuma bayan some seconds takan saci kallon mahaifiyarta, dan taga awane irin yanayi take ciki, a haka har suka isa gida, hon tayi abakin makeken gate din nasu, da gudu gate man yazo ya bud’e, koda suka shiga ciki rasa inda ya kamata ta dosa tayi, dan tana da tabbacin inhar ta zauna parlorn da take tunanin nan Ummahn zata zauna to fa question’s se wanda ta manta, idan kuma ta tafi d’akin su baza ta samu natsuwa ba, saboda haka sai tayi k’ok’arin kawar da damuwa da wasi wasin da take ciki tare da cema hajiya Marwah, “Ummah zan kwanta”, Kin tabbatar dai kin sha magani koh?, hajiya Marwah tafad’a a lokacin da take ta k’ok’arin kunna Tv, dan sosai take son tayi yak’i da damuwar da ta d’aurawa kanta akan yaran da basu d’auketa a matsayin uwa ta azo agani ba, yaran da suke gulmarta a tsakanin k’awayen su, sannan suka gummaci fad’a ma kawayen su sirrikansu akanta, duk da yanda take jansu a jiki, kuma duk hakan ne dalili,. Ko kad’an batayi tunanin hakan daga garesu ba, dan a tunanin ta idan a ka ce abada shaida akan uwa wacce ta iya kula da tarbiyyar yara to zata kasan ce ta d’aya a wurin yaranta, amma ina a she tunanin ta k’arya yake fad’amata, duk da ta san bazata iya yin abunda take kudurtawan ba, amma dai tana son ta k’ok’ar ta ko yayane, saboda ta nuna masu wacece uwa, ko min ko lalacewar ta, kuma tana da tabbacin koda batayima Jiddah komai ba, koda kuma bata canza mata fuska ba, zata sha jinin jikinta, saboda tambayar da tayi mata, tunda tana da tabbacin cewa ba tasan Faridah tabar wayoyinta ba, “Eh nasha”, Tabata ansa dashi cikin raunanniyar murya, “Zaki iya tafiya, kawai hajiyan tace mata, cikin rashin kuzari ta shige d’akin su, tamkar wacce kwai ya fashewa, fad’awa tayi saman gado tana sakin kuka cikin wata irin murya, wacce bata tab’a sanin cewa ta na da ita ba, “Why Aunty Ridorh”?, Why did u do dis to us, shi take fad’a acikin ranta, muryan Anwar taji yana jijjigata kuma yana fad’ar “Dan Allah Aunt kibar kukan hakanan, Ummah tace soon za kiji sauk’i, kinji ki dena kukan, ciwon zai tafi in sha Allahu, a hankali ta mik’e tana k’arewa d’an k’aramin k’anin nasu kallo, idanun shi duk sunyi ja, alamun ya muryazasu, irin yanda yara keyi, share hawayen kan fuskar ta tayi, kafin ta sakar mai murmushi tare da cewa “Yaushe Ummahn ta fad’a ma banda lafiya”?, d’azun ne, kuma Yaya ma ya fad’aman hakan da zamu je school, yatsina fuska ta farayi kafin tace ni bazan warke ba sai kabani chocolate d’inka nasha, “shiii!! yace yana d’aura yatsa a baki, tamkar wani babban mutun, kafin yace is ok, let me go and look for it, kin san Ummah ta b’oye since day before yesterday wai na cika shan zak’i”, Murmushi tayi tare da cewa “Yi sauri, before i die”, da gudu yafita,.Maida duban ta ga Ikhram tayi, saboda yanda taga tana k’are mata kallo, kamar wacce ke neman tuhumar ta, kamar zata ce mata kallon fa?, sai kuma ta fiske ta koma ta kwanta, a zuciyar ta kuma ta ce koma menene idan kika gaji zakiyi magana, “Aunty wai da gaske ba kida lafiya”?, Ikhram d’in tace hakan tana zauna wa kusa da ita, Bangane da gaske banda lafiya ba Ikhram, what did u mean by asking me dis kind of question?, yatsina fuska tayi kafin tace i don’t mean anything, it’s just a question, to karya na keyi lafiya na k’alau, sai kuma mene?”, Sai bakomai, Ikhram tafad’i hakan sannan ta mik’e t
a nufi akwatin ta, da kallon mamaki Jiddah tabi ta, dan gaba d’aya taji kanta na sara mata, ta rasa me Ikhram take nufi da wannan banzar tambayar tata, “Aunty ga chocolate d’in da Anwar yace ne ya yadawo da ita daga tunanin takaicin da takeyi agame da Ikhram, ansa tayi tana fad’ar “Thank you”, Saida ya murmusa sannan yace “Nasha wuya Aunty, saboda da k’yar nasamu Ummah tabani”, Eyya sorry dear tafad’a tana rungumo shi”, Tare suka sha chocolate d’in, daganan ya fara yi mata zubar abinda ya faru a makaranta…”Ummah dan Allah kice wani abu”, d’ago jajayen idanuwant a tayi tana kallon shi, kafin tace “Ince mene Khalipha”?, shiru yayi kawai saboda be da abun ce mata, “Kasan komai Khalipha, ka san yanda bahaushe ke tafiyar da rayuwar shi da iyalan shi, musamman yaran shi maza, amma ni gaba d’aya na jaku a jikina, na nuna ma ku soyayya irin wacce ba ko wace uwar bahaushe bace ke yin hakan, kasan duk menene dalilin yin hakan Khalipha”?, hajiya Marwah tafad’i hakan tana d’an yima yaron nata murmushi, girgiza kai yayi, zuciyar shi cike da rauni, fad’i mana Khalipha, kasan meyasa?, “A’ah”, Yafad’a cikin sanyin murya, murmushi ta kuma yi kafin tace, wai dan duk na had’a kawu nan mu, dan duk mu zama d’aya dani daku, dan duk mu zama abokan shawaran juna, dan duk muzama abokan share kukan juna, dan,. Kukan da yaci k’arfin ta ne ya hanata kai k’arshen zancen, shima Khaliphan cikin muryan kuka yake fad’ar “Dan Allah Ummah kibar kukan nan haka”, Ta jima ta nayi, shima kuma yayi ta rarrashinta kafin tad’ago tace “Amma duk ban samu wannan albarkar awurin ku ba Khalipha, banci wannan arzik’in ba, sai ma shafaman k’asa a ido da kuka yi, kuka tabbatar wa da ‘yan uwan ubanku cewa ni d’in kaskantacciya ce acikin su kamar yanda suke fad’a, niba kowa bace ba kuma zan tab’a zamo wa kowa ba, koda ko a wurin yarana ne, me nayi maku Khalipha?, meyasa na cancanci hakan daga gare ku?, Sosai jikin Khalipha yayi sanyi, duk da har yanzun be fahimci zancen mahaifiyar tashi ba, sai dai kukan da takeyi ne yakesa shi jin wani iri, da farko yayi tunanin maganar Faridah za tayimai, amma yanzun yaga ne cewa wani abun ne ya faru, to menene wannan din?, ya tambayi kanshi, sanin da yayi baze samu ansa bane yasa shi d’ago kai tare da cewa “Ummah kiyi hakuri”, Ko me mu kayi munyi shine bisa kuskure, sannan on my behalf am pleading u to forgive sis Faridah, pls don’t sa,.. dakatar dashi tayi ta hanyar cewa “Mubar zancen nan”, Kasa cewa komai yayi, saboda sabon yanayin daya hango a cikin k’wayar ta, menene ya faru da Ummah?, tabbas yasan da ciwo ka wayi gari kaga ba d’anka, kuma ace wannan d’an naka ba b’ata yayi ba guduwa ne, sannan kuma guduwan akan dalilin da be taka Kara ya karya ba, akan dalilin da yasan zai iya haddasa ma mahaifanshi matsala, to amma shi anashi ganin ba kuka ya kamata ayi tayi ba, ka mata yayi suyi ta addu’ah, wata k’ila Allah ya tan k’wari zuciyar Faridah ta dawo gida, “Shikenn narasa abokin shawara Khalipha”, yanzun ba nida wanda zan iya tarba da sunan bango abun dafawa, ba nida abokin kuka Khalipha, ba nida wani abokin fira Khalipha, shikenan yanzun idan naji damuwa sai dai nabarwa cikina, tana fad’ar hakan ta mik’e tayi hanyar bedroom d’inta, da sauri Khalipha ya rungumo ta, aiko kamar jira take ta saki wani irin kuka, shima kukan ya saki, saboda tsananin tausayin shi ga mahaifiyar tashi, tabbas yana tausayinta, saboda ita d’in guda ce tamkar da dubu, jaruma kuma abun koyin duk wani mutun nagari, walau mace ko namiji, mace me hakuri, juriya, tawakkali, mijinta nada kud’i, amma ‘yan uwan shi dama sukan su ‘yan uwanta sun maishe ta sakarya, saboda kawaicin ta da kuma yanda mijin ya d’auke ta, tabbas Ummahn shi mace ce abar a tausaya, so dayawa takan shiga damuwa amma bata tab’a nuna masu ko kad’an, sai idan ta k’ure mata sosai, kuma dagashi sai Faridah take fad’awa, su d’in ma takan ce ba ta fad’a masu bane dan suyiwa kowa rashin kunya, ta fad’a masu ne dan taji sanyi, sometimes idan tace hakan har kuka su kanyi, bama kamar shi da yake da k’awa zuci akan mahaifiyar shi, ko yanzun ma yana da tabbacin damuwa ce tayi mata yawa, “Kiyi hak’uri Ummah”, Ya fad’a bayan ya bata lokaci tayi kukan ta ma’ishi, a hankali ta jaye jikin ta daga nashi, fuskanta kuma d’auke da fara’ar da ba sai an fad’i ta mecece ba, “Bara nashiga ciki Khalipha, kaga ana kiran sallah, kai ma ya kamata kaje kayi”, Tsayawa yayi yana kallonta, duk da ita ta riga ta wuce, wucewan daya san daze lek’a da sai yaji tamkar ya fasa zuwa sallahn, saboda damuwar da zai gano, A hankali shima ya tafi zuwa toilet, alwallah yayi sannan ya tafi masallacin dayake cikin estate d’in nasu, ana idar da sallahn ya d’auki mota yabar gidan, direct gidan Aunty Aysha ya tafi, duk da yasan ba lallai Ummahn nashi taso hakan, sai dai yana ganin bashi da wani zab’i da ya wuce yin hakan, zaune ya sameta akan cushing ta tasa Tv gaba, ita ba kallo ba itaba tunani ba, gade tanan, sallamar da yayi ne ta sata waigowa, fuska ba yabo ba fallasa, ganin shine ya sata sanya fara’ah akan fuskar ta, “Aunty ina yini”, ya fad’a tun kafin ya zauna, harara ta watsamai daganan ta d’auke idonta daga kallon shi, murmushi yayi, saboda yasan ma’anar hararar ta ta, “Aunty ina yini”, ya maimaita akaro na biyu, bayan ya samu wuri ya zauna, “I thought sauri kake shiyasa ka gaisheni a tsaye”, Murmushi yayi dan dama dai yasan dalilin kenan, sannan yace a’ah ba sauri nike ba, ohwoo to y gidan ko anga Faridahn ne?, wani murmushin ya k’ak’alo kafin yace “A’ah Aunty, dama dai nazo muyi magana dake ne, Gyara zama ta farayi kafin tace “Magana”?, To akan mene, ko ince ta mene?, Aunty akan Ummah ne, b’oyayyar ajiyar zuciya ta sauke, saboda ita ta rasa gane wani irin hali ‘yar uwarta ta ke dashi, daidai gwargwado tana da tawali’u amma kuma ta cika rauni, 2wks kenan da guduwan Faridah, amma yanda ta koma bazaka tab’a tunanin hakan ba, duk tabi ta d’aurawa kan ta damuwa,. “Ina jinka Khalipha” Tafad’a bayan ta tattara gaba d’aya natsuwart a gareshi, “Aunty pls ina son ki fadaman ko Ummah tafad’a maki wani abu da mu kayi mata”, saboda gaba d’aya ta canza a yau d’innan, sai wasu irin maganganu ta keyi wanda ni gaba d’aya na kasa gane inda ta dosa, nasan cewa Ummah nada rauni, to amma maganganun da takeyi ayau ba sa da alaka da raunin ta, pls Aunt ki fad’aman, saboda in san ta yanda zanfara rarrashin ta, “Wa anne irin maganganu ne wad’annan”?, Ta katse shi ta hanyar yi mai tambayar, fad’a mata duk yanda sukayi da Ummahn yayi, girgiza kai kawai hajiya Aysha tayi, saboda dai acikin maganganun yayarta ta bata hango komai ba face tsantsar damuwar da tayi mata yawa, kuma bata nufin komai face fitar da damuwar ta cikin siga mai matuk’ar rud’arwa ga me k’aramin tunani, “Khalipha” Takira sunan shi a hankali, shima a hankali ya d’ago kafin yace “Na’am”, cikin sanyin murya, ka san menene? a’ah ya fad’a, babu wani abu da kuka yima Ummahn ku, damuwace kawai tayi mata yawa, wanda a yanzun ni bani da abun cema daya wuce kaje ka kula da’ita”, Kasan yanda zakayi ka d’e be mata duk wata kewa da Faridah ke d’e be mata a matsayinta na mace, inma bazaka iya ba to ka umurci Jiddah dayin hakan, sannan kasan yanda zaka kauda damuwar mahaifinka data ‘yan uwanshi a zuciyar ta tun kafin wani ciwon ya sark’a feta, kasan yanda zaka sanya farin ciki acikin rayuwar ta ta zahiri data bad’ini, ma’ana afili da kuma b’oye, kana jina?, “Eh Aunty”. kuma insha Allah zan k’ok’ar ta, sosai ta bashi shawarwari akan matsalar Ummahn ta shi, daga haka ya mik’e yana me cewa nizan tafi, zaro ido ta farayi kafin tace “Ka tafi ina bayan ko ruwa baka shaba”?, ahh Aunt ni kam a k’oshe nike sai dai next time, to ai shikenan, saura kuma kaima ka d’aurawa kanka damuwa, kaga shikenan mada din ta samu natsuwa sai ta k’ara rud’ewa, tunda kasan inhar ka shiga damuwa to sai ta k’ara ninka damuwar da take ciki, insha Allah ba zanyi hakan ba Aunty, ni na tafi, to agaishe ta tace, shi d’in ma to yace sannan ya fita. Ko da ya shiga mota waya ya ciro yayi dialling numbern Jiddah, ringing’s 3 tayi picking, “Big bro”, tafad’a a can b’arayin ta, na’am jiddoh kina menene yanzun?, bakomai ta bashi ansa dashi a tak’aice, ok zan shigo gida yanzun, pls mu had’u a garden, sai da tayi jim kad’an, a zuciyarta kuma tana kissima dalilin k
eb’ewar su a garden d’in, sannan kuma tace “Ok toh sai ka shigo, Within 15mnts ya k’ara so, kai tsaye garden d’in ya nufa bayan yayi parking, zaune yasa meta itada Anwar yana ta yi mata zuba, da fara’ar sa ya k’arasa, saboda ganin nasu, wanda ya keji tamkar tsoka d’aya a miya, ita batama lura dashi ba, sai da Anwar yace “Aunty, Yaya, a hankali ta waiga ta ganshi, ita ma sanya ma fuskan ta fara’an da tagani akan tashi fuskar tayi, kafin tace boos, harara ya watsa mata kafin yace, “Zanci gidan ku Jiddoh”, ‘Yar dariya tayi wacce take jinta har k’asan ranta, dan sosai take alfahari da yayan nata, kamar yacce Ummahn su tace ne, duk tana yin abubuwa ne dan kansu ya had’u, to aikam hakan takasan ce, dan dai ko ita tasan hakan, kawai dai matsalar da’aka samu ita ce rashin powern ta awurin miji, dan ginshi da kuma ‘yan uwanta, wannan matsala ita ke dagula masu dukkan lissafi, ita ke saka Faridah da Jiddah zama suyi maganar mahaifiyarsu, sometimes ma idan ta basu haushi su kanyi kamar su zageta, saboda kwata kwata ba sa da kwab’o, duk da ita tana k’ok’ari wurin ganin ta kwab’a masu, amma dai duk da hakan sai a hankali, “Jiddoh how far”?, Ya fad’a yana d’aura Anwar akan cinyar shi, sai da ta d’an yatsina fuska sannan tace “Wallahi norms, Good ya fad’a sannan ya zurawa k’asa ido na kusan 15 seconds, shi d’in ma saboda tace “Big bro lafiya ne”?, Yasa shi d’agowa tare da cewa lafiya, me kika gani ne?, It seems like something is wrong, zaro ida ya farayi kafin yace with who?, with u, tafad’a ba tare da tayi wani dogon tunani ba, a’ah babu, “ok, to lafiya kace mu had’u a garden?, Sai a sannan ya kalleta da kyau, yace magana zamuyi akan Ummah, waige waige ta farayi kamar wacce ke gudun ajita, ganin bataga kowa bane ya sa ta dawo da duban ta gareshi, amma ba tace mai komai ba, murmushi ya farayi kafin yace “Lafiya dai koh”?, Lafiya lau, kawai dai ina searching ne to see ko zanga wani, so that idan naji Ummah tayi magana me kaman ceceni da wacce mu kayi ingane wanda ya fad’a mata, “I don’t get u”, Ya fad’a yana ka feta da ido, bashi labarin yanda su kayi da Ummah tayi sannan ta karkare zancen da cewa kuma fa a waya mukayi chart da Aunty Faridah lokacin da taje excursion, amma sai gashi d’azun tana fad’aman komai, kuma da alama yyi mata zafi sosai.

 

 

*08152163536* .

Add Comment

Click here to post a comment