Tuzuru Hausa Novel Wattpad
TUZURU
*Littafin kuɗi ne ki biya ki karanta hankali kwance,masu fitar min da book,da uwanda suke karantawa ba tare da sun biya ba,da uwanda suke sharing ɗin shi,da uwanda ke cewa saboda book an gaya masu magana to dukan ku kuji zafi ku bar karanta haƙin da ba na ku ba mana mai buƙata ta yi min magana ta WhatsApp +22795045822*
*PAID PAGE* 55-56
“Niger en deuil”shine kawai kake gani a statut mutane yayinda wasun su ma ke ƙarawa da videos na sojoji sai su saka emoji ta kuka.
Kamar daga sama Faruk ya shigo gidan cike da tashin hankali,Mami wacce tun jiya gabanta ke faɗuwa ta yi saurin tashi ba tare da ta amsa gaisuwar da Faruk ɗin ke yi mata ba tace “wajensu ne aka kai harin(attaque,farmaki)ko?har da Waleed ɗina ko?ya mutu shi ma ?”ta na maganar ne cikin kuka.
Nabeela wacce ta rama cikin wuni ɗaya ta ƙurawa yayanta ido ta na jiran amsar shi,kai Faruk ya sunne yace “Mami sai haƙuri duk musulmi doli ya ɗauki ƙaddara mai kyau ko akasinta, wannan attaque ta rutsa da su Waleed ne sakamakon…”kafin ya ida maganar Nabeela ta saki wani ihu wanda yayi daidai da murɗawar cikinta nan take cikin jikinta ɗan kimanin wata biyu ya ɓare tun kafin su kai asibiti.
Kurkukun Kaddara Hausa Novel Complete
Dakyar aka samu nasarar tsayar da jinin aka yi mata wankin mara,drip ɗin hannunta ta kalla ta na zubar hawaye.Kanta Mami ta shafa tace “ki kwantar da hankalin ki Waleed na nan a raye kawai ya samu rauni ne wanda ya kasance babba ƙaddara”murya na rawa tace “dagaske Mami Tarhanine bai mutu ba?”kai Mami ta jinjina mata tare da sakin murmushin ƙarfin hali tace “eh shine abinda Faruk ke son faɗa mana”Nabeela ta goge hawaye tace “amman Mami wayar shi ba ta shiga tun jiya da abun ya faru kuma bai kira ni ba”cikin son kwantar mata da hankali Mami tace “zai kira in shaa Allah har ya samu nutsuwa”ba dan Nabeela ta yarda ba ta rumtse idonta ta na son barci ya ɗauke ta ko ta samu sukuni amman yace yi ni inda kika ganni, moments ɗin da suka kasance a tare suka yi ta dawo mata a kai tun daga ranar da ta fara ganinsa,first night ɗin su,wayar da suka yi ta shaida masa ta na da ciki yanayin yadda ya nuna murnar shi da son ɗan cikinta kawai sai hawaye suka shiga ɓulɓulo mata.
A can compagnie kuwa duk sojawa ne sun yi cirko-cirko sun saka ƙatuwar tv a gaba suna kallon mutanen da suka rasa rayukansu, hotunan su da kuma sunayen su wasu kuma babu hoto sai suna kawai.
Faruk sai sake maidowa ya ke baya dan sake tabbatarwa kansa babu sunan Waleed cikin matattu,tabbas babu shi ɗin sai dai ya na cikin cas d’urgence uwanda har yanzu ba su san halin da suke ciki ba ko rai ko mutuwa.
Radiyo aka kuma yi(kira dan samu ko kuma bayar da wani labari)aka sanar masu wasu sun farfaɗo wasu kuma sun mutu cikin cas d’urgence ɗin.
Zuciyar Faruk ce ta fara dakan tamanin-tamanin lokacin da aka turo liste ɗin sunayen sojojin,tun daga farko ya fara dubawa har ƙasa nan ya sauke wata ajiyar zuciya kafin ya fito ya nufi office ɗin shugaban su.
Cike da alhini Chef Nuhu ya kallesa yace “Faruk zuwan ka ba zai hana komi ba dan haka gwara ka zauna “cikin aro jarumta Faruk yace”a’a Chef ba zan iya ba,wlh doli na isa Mali na gane ma idona halin da abokina ya ke”cikin tsawa Chef yace “to ba za ka je ɗin ba,ban kuma ba ka izinin zuwa ba”Faruk yace “in kuma fah na ajiye maku kakin ku?”da sauri Chef ya ɗago ya kalle sa yace “Faruk kayi hauka ne?aikin na ka za ka ajiye?”cikin jin haushi yace “Toh tare aka haife mu ne?”Chef ya sauke ajiyar zuciya yace “ba wai na hana ka zuwa ba ne dan wani abu a’a tafiyar ka zai ɗagawa ahalin shi hankali su yi tunanin ciwon na shi gaba ya ke yi alhalin yanzu ya fara samun sauƙi”cike da tuhuma Faruk ke dubansa yace “amman ya aka yi ban ga hakan cikin rahoto ba?”Chef ya miƙe tsaye yace “Faruk ni na sa a ɓoye halin da Waleed ke ciki saboda shine Chef de compagnons sannan a yaƙin nan ba ƙaramar ɓarna ya yiwa ƴan ta’addar nan ba,na sani sarai su na haƙon sa kuma burin su shine su ji ya mutu in kuma ba haka ba za su sake kawo farmaki ne dan ɗazu ma shugaban su ya saki wata video ya na cewa sai ya raba kan Waleed da gangar jikinsa”Chef na kawowa nan ya furzar da huci ya cigaba da cewa”yadda kuke bin rahota daki-daki suma haka,jira kawai su ke su ji situation ɗin Waleed shiyasa ko ku ban sanar da ku ba wannan babbar ƙaddara da aka ce ta faru da shi”jiki a sanyaye Faruk yace “minene ya same shi Chef?dan Allah ka sanar da ni”cikin jimami Chef yace “Waleed ya rasa ƙafar sa guda sakamakon tattakewar ƙashinta,tuni kuma an ƙundileta”ɗabar Faruk ya zauna a ƙasa hawaye na masa zuba kamar wata mace.
“Sai haƙuri duk wata rai za ta rinƙa fuskantar ƙalubale da jarabe-jaraben rayuwa masu yawa da manyan ƙaddarori har izuwa ranar da za ta koma ga mallicin ta,haƙiƙa L’armée tayi rashin jarumin soja kuma gwarzo na san da sauran ƙura a gaba dan ba lalle ne Waleed ya yarda da rashin aikin sa na cikakken soja ba”kasa cewa komi Faruk yayi,Chef ya danna ordinateur ɗin gabansa kafin yace “zo ka gani”ƙarar na’ura”tiii!tiii!” Da Faruk yaji ne yasa shi miƙewa jiki ba ƙwari ya leƙa fuskar system ɗin.
Kwance ya ke cikin blue ɗin yadi wanda ake saka ma maras lafiya,fuskar shi tayi fyau sai ƴar zurmawa da tayi.Hancinsa laƙe da oxygene na ƙarin sheɗa,yayinda ƙafarsa ta hangun wacce aka guntsule ta ke naɗe da farin bandeji.Barci ya ke wanda kallo ɗaya za ka yi masa ka gane ba na jin daɗi ba ne, system ɗin Faruk ya shafa wasu sabbin hawayen na silalowa.
Kashe system ɗin Chef yayi ya na sauke ajiyar zuciya, Faruk yace “sai yaushe za’a kawo sa Niger?”Chef yace “sai ya dawo hayyacin sa dan har yanzu bai farka ba”Faruk ya jinjina kai ya na duba kiran Amal da ke shigowa wayar sa.
After 5days
Jikin Nabeela yayi sauƙi haka ma na Waleed,zuwa wannan lokacin kuma su Mami sun san abinda ya faru da shi kuka kuwa dukan su sun sha shi dama-dama Daddy.
Anty Nafissa sai da ta kwaso ta zo haka ma anty Jamila,su Amal amare ma anzo ita da A’ishah.Sosai ganin su ya ɗan kwantar da hankalin iyayen,Nabeela kuwa banda hoton Waleed ba ta da wani aiki in ta kalli gudululun ƙafarsa sai taji wani irin tausayin shi ya kama ta.
Sai da Waleed ya kwashe wata guda cur sannan aka fara barin mutane na shiga ganin sa,su kan yi appel video da mutan gida a ƙoƙarin na kwantar mashi da hankali sai su ɗaga mashi shi dan yawan jajen sai ya ke fama masa ciwon rashin ƙafarsa.
Ido ya lumshe ya na kallonta yadda ta ke turo baki da yadda ta ke shagwaɓa duk sai ya saukar masa da kasala,”Tarhanine…”ba tare da ya buɗe ido ba yace “uhum Tarhani”baki ta kuma turowa tace “yaushe za ka dawo?”ya ware idonsa yace “a’a na ƙi na dawo yanzu sai na warke ta yadda tun ranar da na dirar maradi na kaiwa yarona ziyara”gabanta ne ya faɗi ita sam ta manta da cikin jikinta ya zube,a sanyaye tace “a’a ni dai ka dawo yanzu ai a hakan ma za ka iya ziyartar shi “sai da ya ɗaga gira ya kashe ido ɗaya yace “kai haba?kice za ki yi min aikin?”ido ta rufe ta girgiza kai,ya kwaɓe fuska yace “dan Allah Tarhani,kin san kuwa nayi kewar ki sosai dubi yadda joué ɗin ki ta ta tashi”😹
Ya yi maganar ya na kai wayar ga mazantakar shi wacce ta tona asirin sa ta bisa drap ɗin da ya rufa,dariya yayi yace “ko na buɗe maki ki gan ta a zahiri?”cikin gatse yayi maganar Nabeela ta ɗaga kai babu zato ba tsammani ta ga ya yaye drap ya fiddo mata ita,da sauri ta kashe kiran zuciyarta na dakan uku-uku sai zarar ido ta ke.
Bawan wasu watanni sosai hankalin ahalin ya kwanta yayinda kuma aka shiga yin shirye-shiryen tarben Waleed wanda kuma aka tsara za’a sake yin bikin auren su🙄 da na tarewar Nabeela a sabon danƙareren gidan da état ta gina masa.
Ɓarin madarar turare aka yiwa Nabeela yayinda aka tsantsara mata kwalliya irin ta amare,robe ta saka ta amare sannan aka yafa mata wani mayafi mai kamar sange.
Da misalin ƙarfe shidda na marice sojoji ne ringis sun yi shiga cikin kakin sojoji kala ɗaya,komin su iri ɗaya wasanni suka fara yayinda dangi da abokan arziki uwanda suka zo tarbe da taya Waleed murna suka shiga taɓawa haɗi da shewa.
Kanta na sunne aka buɗe mota ta shiga,sai da suka fara tafiya taji tatausan hannun shi cikin nata da sauri ta ɗago kai ta kalle sa ido cikin ido.
Ƙafafun sa ta kalla ta gan su biyu ras sai kawai jikinta ya fara kyarma,lura da hakan yasa ya jawota ya bata ƙyaƙyawar sumba a gefen wuya ya na mai raɗa mata “Tarhani…?”
Duk wacce ta karanta min book ba tare da ta biya ba Allah ya isa wuta balbal
Add Comment