Jawaheer Hausa Novels Complete
*JAWAHEERA*
*Littafin haɗaka*
Na
*NUSAIBA ALKAMAWA*
PROFICIENT WRITER’S ASSOCIATION
Tare da
*SAYYADA ✍️ Barrister*
MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION
Part 1
_Bismillah rahmanir rahim_
_Yacce muka fara wannan_ littafin ya Allah _kabamu ikon kammala_ _shi lpy Amen_
Wannan ƙirƙirarran labarine.
_________Zaune nake akan dining,ina juya cokali da yake cikin abinci agabana ina tunani akan maganar da habeeb yayi min,nayi nisa cikin tunanin har ammi tazo bansan tazo wurin ba , jawaheer, jawaheera ?
Amman shuru taɓoni Ammi tayi aikuwa firgigit nadawo daga duniyar tunanin dana shiga na kalli ammy,cikin wata iriyar murya mai haɗe da damuwa nace ammy yaushe kika zo ?ammy tace dama yaushe xakisan nazo nan tunda kinsa kanki cikin damuwa ,waini jawaheer meke damunki kwana biyun nan ne ?? murmushi nayi wanda za a iya kiranshi da yaƙe t
nace la ammie babu komai fa! kawai dai exam din da xamuyi ne nake tunani akanta.
“Badon ammie ta yarda ba tace mata to shikkenan,Allah yabada Sa’a tana faɗan haka ta zauna akan kujera dake kallon ta jawaheera,amen cewar jawaheer .
“Sallamar Imran sukaji amsawa sukayi cikin kasaita ya iso gurin,yaya Barka da shigowa jawaheer ta fada cikin so Da kaunar yayan nata.
Sirri Boyayye Hausa Novel Complete
_______ murmushi yayi mata cikin natsuwarsa yace me kike tunani naji Ammi na miki magana ?”yaya tunanin exam din da xamu fara ne kasan next week xamu fara ,”ashema kun kusa farawa kuma shine kike wani tunani akanta nidai nasan ƴar kanwar tawa Akwai kokari don hakama kidaina wani damun kanki,”to yayana,ammy ce ta katse sa dacewa kinga jawaheer kici abincinki kar ya makarar dake,to, ammy tafada tafara cin abincin cikin nutsuwa,shikuma imran dagowa yayi ya kalli ammy yace ammy nibanga dan autan naki ba ?
“Auta kamanta yatafi makaranta da wai yafara rigima waishi baxaije makarantar ba aidama ammy duk ke kike ɓata abeed dake da Abba kuyita ɓatashi .
“to kodai kishi kake dashine cewan ammy?ah haba dai Allah yasauwake nayi kishi dashi yanxu ai mungirma, ni dai jawaheer ban ce komai ba na gama na mike na nufi dakina, toilet na nufa kaitsaye nayi wanka ina fitowa daure da towel ajikina wanda baifi iya gwiwartaba santala_santalar cinyoyina wanda suke farare tas ,Suka bayyana wajan mirror na nufa na dauko lotion dina mai tsada nashafa ina gama shafawa na dauko doguwar riga ta mai azabar kyau baka wanda taji kwalliyar duwatsu sai kyalli take na saka ajikina ban shafa komai ba a fuska ta ba domin zafin da ake mayafin na dauka nayi rolling din kaina sannan na dauki school bag dina nafito gaskiya jawaheer ni babkaramin kyakkyawa bace kuma kyakkyawace ta ajin farko ina da idanuwa dara_ dara bakina pink dan mitsitsi hancina dan dogo atakaice dai jawaheera ina ɗaya daga cikin kyawawan mata .
*WACECE JAWAHEER*
Jawaheer na kasance ɗiyace ga Alhaji *ABDULLAHI*
Haifaffen garin Bauchi ne a unguwar Magaji kwatas,iyayenshi suna da ɗan rufin asiri daidai gwargwado dan babanshi manomie ne noma kuma ya karbeshi ya auri matarshi mai suna khadija bata taɓa haihuwa ba tun suna sarai harsuka daina sarai,suka barwa Allah lamuransa ana haka kwasam wata rana khadija ta tashi da matsanancin zazzaɓi aikuwa babu shiri alhaji muhd ya kaita asibiti dayake yaje Makka yadawo suna zuwa Asibiti aka tabbatar mai da tana dauke da juna biyu aikuwa murna wajan alhaji muhd ba a magana suna zuwa gida yafara sanar da ƴan uwa da abokai arziki aikuwa tana samun kula ta bangaran kowa da kowa .
_____Ciki na shiga wata tara ta santalo yaronta mai kyau ranar suna yaro yaci suna Abdullahi, Abdullahi yataso cikin gata da kulawa wajan ilmi kuwa ba a magana dan Abdullahi akwai kokari ta bangaren bokoma haka yana iya bakin kokarin sa tunda yagama secondry dinsa yace shifa yafisan kasuwanci shine fa babanshi ya nemi wani amininsa maisuna alhaji Ibrahim Muhd yake sanar dashi abinda yakeso aikuwa Alhaji Ibrahim bakaramin dadi yaji ba saboda daman yana san Abdallah nan danan aka fara masa shirye-shiryen zuwa Kano .
Alhmdllh amfara kasuwanci a Sa’a suna Saida atamfofi da shadaddodi da sauransu kuma kudi yana xuwar wa alhaji Ibrahim yanajin dadin yin kasuwanci dashi SBD amanar sa da gaskiyar sa
“Wata rana Abdallah yaje gidan Alhaji Ibrahim donsu tattauna akan kayan daxa a kawo musu sai yashiga gidan yayi sallama a parlour wata kyakkyawar matashiyar budurwa yagani akan kujera shekarunta baxa suwuce ashirin ba.
Amsa masa sallama tayi tare da gaidashi,ya amsa babu yabo ba fallasa yace Abba yana nan ?bayanan sai yace mata ummi fa ?ta nanan ta haura sama tashiga dakin ummi tace mata tayi bako ,wanene?nima bansanshiba Ohk to kice masa gani nan zuwa to ummi saukowa tayi tace masa tana zuwa ok , kawai yace mata yaci gaba da danna wayarsa azuciyar sa cewa yayi kodai Wannan ita ce ƴar abban da yake cewa yana da ƴa .Muryar ummi ce ta katse masa tunani da cewa ah daman kaine bakon da hafsat tace nayi bako ,Kodayake ai batasan kaba Shiyasa daidai lokacin da take zama tsugunnuwa yayi yagaisheta ta amsa cikin fara’a daman naxone wajan Abba kuma naga bayanan.
“Eh Wallahi bayanan kunyi saɓani amma baisan xaka xoba ko eh ban faɗa masa ba ah to Shiyasa ,kungaisa da kanwar taka ne ?kasan shekaran jiya tadawo bakusan junaba hafsat na’am ummi kixo to ummi fitowa tayi ta zauna kusa da ummi gani ummi ,dama yayankine nace kixo ku kara gaisawa dashi ɗan wajan aminin babankune násan baki sanshi ba dagowa tayi da niyar kara gaidashi lokacin yadago aiko suka hada ido jitayi baxa ta iya kallonshi ba saboda kwarjinin da Allah yayi masa saurin sunkuyar dakai tayi tace inayini? lpy alhmdllh yafaɗa yana me mikewa da faɗin ummi Ni zan tafi Saida safe ,tun yanzu Abdallah eh wllh akwai aikin da xanyine acan kasuwan tace to Allah yabada Sa’a amen ya amsa yana mai fita hafsat ta kalli Ummi tace nikam daman wannan ne dan baba muhd din dakike faɗa ?
Eh shine ai dayake baki sanshi ba ko dawani abunne? murmushi tayi tace ummi babu komai to shikkenan
Washegari ummi suna zaune da Alhaji Ibrahim tana masa tausa Abba yace nikuwa akwai wata magana dana keso namiki ko shawarar danai tayi?
Ummi tace inajinka Alhaji,daman tunani nayi naga hafsat tagama karatunta yakamata ace tafito da mijin aure Amman kinsan mai nakeso ?ina sha’awar naga ta auri Abdallah.
” murmushi Ummi tayi tace Alhaji kamar kashiga xuciyata wllh Nima ina wannan tunanin kuma kasan lokacin da Abdallah yazo gidan nan hafsat har tambaya ta take wanene shi Amman fa naga kamar sonshi take , murmushi Alhaji yayi yace aikuwa xanwa mahaifinsa magana barama yanxu nakira sa ,kiranshi yayi yafaɗa masa komai shima Alhaji Muhammad yaji dadin maganar haryake cemai daman suna da shirin zuwa shida mai dakinsa murmushi yayi yace Allah yakawo ku lpy amen suka amsa suka yanke wayar.
_______Alhaji Ibrahim shi yayiwa Abdallah maganar beyi musu ba ya amince SBD shi Mutum ne mai biyayya ansa ranar bikin wata biyu ana igobe Abdullahi yake shedawa Alhaji Ibrahim cew iyayenshi xasuxo gobe murna sukaitayi shima Abdullahi yayi murna sosai dan rabon shi da ganin iyayen nashi anyi wata biyar saidai yayi musu aike.
” ranar da xasuxo Alhaji muhd yayiwa Alhaji Ibrahim waya yace suna hanya ba ai awa daya ba yaga an sakemai waya haryana cewa Ummu ina gama sun iso yana daga wayar yaji wata murya wani daram yana cewa kasan me wayan nan dakacen bangaren ake cewa daman ke wayan ne yayi hatsari kuma Allah yayi masa rasuwa innalillahi wainnailahi rajiun abinda yafaɗa ya saki wayar saiji kake tasss tafashe wayar Abdallah yana zaune awajan shima yana jiran mahaifinsa ummuce take cewa Alhaji lpy
Shiru yayi mata yakasa cewa komai sumbatu yafara yana cewa shikkenan na rasa aminina,ai jin haka tuni Abdallah yafaɗi asume ,arude sukayo gurinsa ruwa hafsat ta debo tafara zuba masa dan kuwa Alhaji Ibrahim baiyi tunanin dauko ruwan SBD ruɗani ba ajiyar xuciya yasauke daya buɗi ido yace dan Allah kuce mafarki nake ba gaske bane ba yafaɗa cikin kuka shima Alhaji Ibrahim kawai dauriya yake cikin karfin hali yace Abdallah kayi hakuri Allah yakarbi abinsa yanxu dai tashi muje mudauko su .
Bayan sundauko su akayi musu wanka akayi musu sutura aka kaisu gidan gaskiya.
Nan Abdullahi yarame yayi baki Saida aka hada masa da rubutu Sannan ya fara dawowa daidai
Bayan kwana arba’in Abdullahi yafara zuwa kasuwa dan kuwa daman andaga ranar biki ankara wata daya akai.
Lokacin biki yana ta karatowa akayi biki babu wani bidia aka kaita unguwar G,RA bayan shekaru biyu amarya tahaifi santalelen ɗanta mai suna Imran.
Bata kara haihuwa ba Saida akayi shekaru shidda Sannan ta haifi khadija ana cemata jawaheer yarinya taci sunan kakarta tagurin uba daganan kuma takara haihuwar abeed tundaga nan bata sake haihuwa ba
Ci gaban labari.
Tsokaci!!!!
Zamu dunga posting na sati ma’ana kwana bakwai kenan, Sannan idan sati yazagayo zamu maimaici SBD wanda basu samu karantawa ba susamu damar karantawa .
Plz Share it and comment.
Add Comment