Cikin Waye Hausa Novel Complete
CIKIN WAYE?
Wallafar
Maryam Shehu tijjani
ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Dukkan yabo da godiya su ƙara tabbata ga Ubangijin da ya sake bani damar dawowa a wannan karon tare da sabon littafi na wanda nake fatan zai fadakar kuma ya nisha ɗan tar
Page 1&2
Tun daga k’ofar gidan nake jin kakarin amai wanda ke nuna alamar mai yinsa ba ƙaramar wahala yake shaba. Gida ne ma dai dai ci cikin unguwa ta masu ƙaramin ƙarfi, duk da haka a cikin layin ma yafi ko wanne gida lalacewa domin kofar gidan ma ta karye sai jingina ta akai, a sannu a hankali na tura kaina zuwa cikin gidan, wacce take aman na samu tsugunne a bakin rariya sai faman haɗa gume take ga wani irin rawa da jikinta yake, tsayawa nayi ta k’are mata kallo Yarinya ce sosai domin bazata wuce shekara sha bakwai ba.
Nisan Kiwo Hausa Novel Complete
“Bari malam yazo yau sai kinci ubanki acikin gidan nan, kullum idan nace karuwan cinki kike tafiya sai a karya tani to sai kiyi bayanin inda kika samo cikin idan kuma aruwa kika sha ne to sai muji, yo to Allah na tuba idan yar gidan Luba batayi ciki ba ai wallahi bata bar miki gado ba dama kuma ance kyan ɗa ya gaji uwarsa..
Tunda wannan matar ta fara magana Yarinyar bata ɗago kanta ba dake sunkuye ba abinda kake ji sai shashshekar kukanta.
Da sallama ya shigo gidan hannunsa rik’e da baƙar leda, “dama kai nake jira yau dai gashi Allah ya toni asirinta, kullum ina cewa yawonta take zuwa an ganin dan ba ni na haife ta ba, to gashinan dai ta kwaso ma abin kunya dan bazansa kaina aciki ba, Malam wanda tun da Baba Ramma ta fara magana ya daka ta da ƙarasowarsa cikin gidan tsaya wa yayi ya zubawa Umaima ido take tsugunne gabansa cike da bak’in rai ya ce
“Umaima waya miki ciki? Cikin tsoro da fad’uwar gaba domin bata san wanda ya mata ba hasalima bata sani ba cikin ne koko kawai Baba Ramma sharri take nemanta da shi dan haka murya na rawa ta ce “wallahi Baba ban san cikin waye ba..
Wata irin suya zuciyar shi ta kamayi domin bai taɓa tunanin Umaiman zata kwasomai abin kunya haka ba, dan haka cikin ɓacin rai tare da kunar zuciya ya ce
“Umaima bazan tsine miki ba amma abinda nake so da ke ki haɗa kayan ki ki barmin gida na yafe ki kije ki raini dan shegen da kika dakko amma ba a gidana ba,
A matukar tsorace Umaima ta ɗago tana duban mahaifin nata sai dai kafin tace wani abu ya shige dakinsa kuka ne ya kwace mata mai taɓa zuciya
Baba Rammamma wacce kwata kwata hukuncin da malam ya ɗauka bai mata daɗi ba domin kuwa so tayi ya zane Umaiman kafin kuma ya bita da tsiniwa amma duk da haka taji sauki ta wani ɓangaren tunda ya kore ta daga gidan ,”to ai sai a haka sauran tsunmo karai abar gidan kinga kin samu damar yin yawanki ba mai saka miki ido amma wallahi Allah ya wadaran naka ya lalace Umaima duk tarbiyyar da aka baki
Sarai Umaima tasan Baba Ramma da biyu take wannan maganar domin ba tun yau ba ta daɗe da sanin cewa ta tsane ta
Kayan ta wanda ba su wuce kala biyar ba ta haɗo cikin wata leda ta sako hijjabin ta da ya gama kodewa sabida rana ta nufi hanyar fita daga cikin gidan ba tare da tasan inda ta nufa ba
Tunda ta baro gidan take tafe kwakwalwar ta cinkushe da tunani tun tana kuka har ta daina sabida hawayan ya ƙafe ba wanda ta sani a duk garin Kaduna domin Mahaifin ta ba dan Najeriya bane asalin sa dan Niger ne sana’a ce ta kawo shi Nigeria har yayi aure ,mahaifiyar ta kuma kafin ta rasu tana yawan faɗa mata ita yar asalin Mali ce fadan boko haram shine ya barota da ƙasar ta har ta hadu da malam iro wato mahaifin ta sukai aure
Ganin ta rasa wajan zuwa ne yasa ta yanke shawarar tafiya gidan da take aikatau duk da bata kwana yanzu idan yaje bata san me zata ce musu ba ga matar gidan masifaffiya,tana wannan tunanin har ta karasa kofar gidan tsayawa tayi tana karewa gidan kallo babba ne sosai gashi ya tsaru iya tsaruwa cike da tunanin abinda zata faɗawa mutan gidan ta fara kwankwasa kofar gidan mai gadin gidan ne ya leko ganin Umaima ce yasa ya bude yana tanbayar ta lafiya dan yasan da safe kawai take zuwa ba tare da taji abinda yake cema ta ba ta wuce zuwa cikin gidan ,kai tsaye falon mutan gidan ta shiga bayan ta aje ledar kayan ta awaje
Zaune ta same su kan table din da aka tana da domin cin abinci ,duk kansu suka juyo suna kallon ta cikin rawar baki ta fara faɗin “ina wunin ku ,kasan cewar komai ƙanƙantar yaro agidan in dai kina aiki a ciki sai kin gaishe shi domin arzikin su kika zo ci cewar Hajiya Bilki matar gidan kenan
Mutum daya ne acikin su ya amsa gaisuwar ta da alama shine mai gidan dan haka yace “lafiya mai ya kawo ki yanzu? Cike da tsoro Umaima tace dama ƴan gidan mune sukayi tafiya shine na dawo zan dinga kwana
Shiru kowa yayi ya cigaba da cin abincin sa idan sun kula ta ko kujerun falon sunyi magana tana nan tsugunne har suka gama “to zaman me kike daba zaki tashi kibar nan ba..cewar Hajiya Bilki ,cikin sanyin jiki Umaima ta tashi tayi waje bangaren da masu aiki suke kwana ta nufa jiki ba kwari ga matsanan ciyar yunwa da take cinta……..✍️
Mai son shiga group domin yin comments ya min magana idan kasan baza kai ba Please karma mutum ya min magana. 08144054353
Amaryar Royar Star ce
Add Comment