King Zaid Hausa Novels Complete
King Zaid Hausa Novels Complete
KING ZAID
(A touch and romantic story)
Paid book (na kudi ne)
——free page 1️⃣
……..Magic club hadadden club ne dake birnin London, yawanci bakaken fata ne (Africa) suke zuwa club din……waka mai sanyi ke tashi, mata da maza suna rawa…wasu kuma suna aikin shan barasa da wiwi da shisha, daga gefe kuwa dandalin chacha ne….Laila matashiyar budurwa ‘yar shekara ashirin da hudu ‘kwararriyar ‘yar chacha ce, a tarihin chacha na magic club babu wanda ya taba cinta, hakan yasa a kullum take alfahari da jin kanta ita din wata ce ta musamman……
Haka yau ma ya kasance ta biga chacha da mutane uku ta cinyesu, yanzu bigawa take yi da mutum na hudu, ‘Kawarta Chuchu na zaune gefenta tana kallon yadda wasan yake kasancewa
“I checked” Laila ta fada sannan ta biga katin ‘karshe…cikin tsananin farin ciki Chuchu ta ce wow, that is good my gal
Cikin alfahari Laila ta shiga fadin “waye kuma zai iya ja dani, Ko baku da zarra ne?”
Shuru babu wanda ya tankata yasa Laila ta mike tana tattara kudin data ci a chacha tana zubawa a jaka “Kawata tashi mu tafi, babu wanda yake da zarran biga chacha dani”
Tashi Chuchu ta yi…suna ‘kokarin barin wurin suka dakata
“Ki dawo mu biga wasa”
A hankali Laila ta juyo ta sauke kallonta a kan wani dan matashin saurayi da bai wuce shekara talatin ba, ya yi matukar haduwa fiye da tunanin mai karatu, dogo ne sosai, farine sosai kamar ka taba jini ya fito, bai da ‘kiba amma yana da kakkaurar ‘kirji, idanunsa masu dauke hankali, komai na Zaid na musamman ne
Littafin Gidan Uncle Hausa Novels Complete
“Idan kina da zarran biga chacha dani, ki dawo ki zauna” cire Europes ya yi ya zube a kan tebirin chacha
Smile Laila ta yi ta ce da alamu kai Bako ne a Magic club baka san wace ce Laila ba
Shima smile ya yi ya zauna yana fadin “hakazalika baki san wanene Zaid ba”
Cikin isa Laila ta koma ta zauna sannan ta fito da kudaden jakarta gabadaya ta zube a tebirin chacha
Nan take Zaid da Laila suka shiga biga wasa
Sun kai wani lokaci suna biga wasa Zaid ya ce Check…sannan ya biga katin ‘karshe
Cak Laila ta sha jinin jikinta ganin Zaid ya ci chacha
Kowa a wurin mamaki ya shiga yi, nan aka shiga tafawa Zaid…. Zaid juyawa ya yi ya tafa da abokinshi Yusuf suna dariya
A take idanun Laila suka canza launi zuwa ja, ranta ya yi matukar ‘baci sosai
Kallonta Zaid ya yi yana smile sannan ya ce kin ga abinda nake fada miki ko, Zaid ba sa’anki bane, wasa ya ‘kare
A take Laila ta shiga cire tsarkarta na diamonds da dankunnayenta na diamonds ta zuba a tebirin chacha tana magana “Ka dakata, wasa bai ‘kare ba, ni kadai ce mai nasara a koda yaushe, babu wanda ya isa ya yi nasara a kaina”
Smile Zaid ya yi sannan ya ce Ina son mutum mai confidence, to muje zuwa
Nan suka shiga biga chacha a Karo na biyu….abin mamaki Zaid ya ‘kara lashe wannan wasan, Laila ji ta yi kamar ta hadiye rai ta mutu tsabar bakin ciki amma bata karaya ba, yanzu wayar hannunta ‘kirar IPhone15 ta saka inda a wannan karon ma Zaid ne ya ‘kara cinyewa
Yanzu aje makullin motarta ta yi tana kallon Zaid dake kallonta yana smile ta ce na fada maka ni ce mai nasara a koda yaushe, na saka mota ta, muje zuwa
Nan suka shiga biga wasa inda a wannan karon ma Zaid ne ya ‘kara yin nasara
Chuchu kallon Laila ta yi ta ce Laila ki bar wannan wasan, yau nasara bata tare dake, mu tafi kawai
Laila zubawa Chuchu idanunta da suka canza launi ta yi ta ce ban yarda da fadiwa ba, ba zan taba fadi ba, nasara na tare dani
Zaid ya ce yanzu me zaki saka, ta ‘kare miki, baki da wani abin daya rage miki, bari nasa a kawo miki barasa ki sha ko zaki ji sanyi a ranki
Cikin ‘bacin rai Laila ta ce akwai abin daya rage min na saka
Zaid ya ce mene ne wannan?
“Na saka kaina, idan har a wannan karon ka yi nasara, na mallaka maka jikina, ka yi duk abinda ka ga dama dani”
Zaro ido Chuchu ta yi cikin tsoro tana kallon Laila ta ce kinsan me kika ce kuwa? Magana kike yi a kan jikinki….
“Eh na sani, Ina sane da abinda na ce”
Smile din mugunta Zaid ya yi yana ‘kara kallon Laila, sai yanzu ya fara tantancen yanayin halittarta…..ta hadu sosai, ‘karamin bakinta yake kallo mai matukar jan hankali sannan ya dawo kan ‘kirjinta, tsayayyun nonuwanta sunyi dai dai a cikin blouse din jikinta, lasar lebansa ya yi na ‘kasa, a lokacin wani sha’awarta ya shiga fisganshi
Nan suka shiga biga wasa, a wannan karon Laila ta dage sosai tana son ta yi nasara amma Zaid ya nuna mata bata kai inda yake ba a duniyar chacha
Zumbur Laila ta mike, hawayen da suka cika a idanunta suka shiga bin kan kumatunta, girgiza Kai ta shiga yi tana fadin “impossible, impossible”
Chuchu rike Laila ta yi tana fadin “Laila mu gudu”
Zaid na kallon Laila cikin tsananin sha’awa ya ce relax ‘yan mata, Karki tayar da hankalinki
‘Kokarin juyawa Laila ta yi zata gudu Zaid ya yi saurin rike mata hannu yana fadin “Ina zaki je kuma?”
‘Kokarin fisge hannunta ta shiga yi tana fadin “ni ka ‘kyaleni, an ce maka ni shasha ce da zan baka jikina?”
Mikewa Zaid ya yi yana kallonta sannan ya ce mecece ke Idan ba shashasha ba, kin manta kinsa kanki a chacha kuma na cinyeki, yanzu dake da jikinki duk mallakina ne, abinda na ga dama shi zan yi dake
Cikin fushi ta ‘kwace hannunta daga nashi, Kallonshi take yi da jajayen idanunta da hawaye ke fita daga ciki, nuna shi ta yi da yatsa ta ce kai Kasan ni wace ce? Har kai ka isa ka mallakeni, ka fadi ko nawa kake so zan baka amma Ba za ka taba samun jikina ba
Kallon tarin kudade da diamonds da sauran kayan da suke tebirin chacha ya yi, tura mata ya yi zuwa gabanta yana fadin “ga kudadenki, ga wayarki, ga diamonds da makullin motarki bana bukatarsu, what I want is you, i just wanna fuck you bitch”
Cikin ‘bacin rai ta daga hannu zata koda masa mari ya yi saurin rike hannun, kallon kallo suka shiga yi a tsakanin su
“Ko a mafarki Kar hannunki ya yi kuskuren taba fuskar Zaid” Zaid ya fada yana kallon idanun Laila
“Kaima kada ka ‘kara dangantani da karya”
‘Karamin dariya Zaid ya yi ya ce to me ce ce ke Idan ba karya ba, karuwa mara tarbiyya, kina da sunan daya wuce wadan nan dana lissafo?
Wani irin kallon ‘kiyayya ta shiga binshi dashi, ji tai duk duniya babu wanda ta tsana kamar shi…batare data ce komai ba ta juya tai hanyar barin Club din, Chuchu na biye da ita
Zaid kalmasa hannayensa ya yi a bisa ‘kirjinsa yana binta da kallo, yanayin yadda take juya duwaiwukanta na ‘kara tayar masa da hankali, cikin wani yanayi ya kalli Yusuf yana fadin “gaskiya ta hadu sosai, ita kawai nake bukata”
Yusuf ya ce amma ya zaka barta ta tafi free
Zama Zaid ya yi yana fadin “ka manta wanene Zaid kenan, ai tunda na ji kwadayinta dole saina sameta, nasan zata yi dadi sosai”
Zaid da Yusuf suka cigaba da harkokinsu
****
Chuchu da Laila katafaran gidansu suka wuce, Laila dakinta ta shiga cikin tsananin ‘bacin rai, kai tsaye ta je ta bude durowa ta dakko fodar ibilis (cocaine) zama ta yi kan kujera ta zuba fodar ibilis a table sannan ta shiga shaka tana samun sauki daga radadin da zuciyarta take mata, haka ta cigaba da shakar fodar har bacci ya dauke ta a wurin
Washegari da sassafe Chuchu ta shigo ta sameta kwance kan kujera, tashinta ta shiga yi
“Laila! Laila!”
Bude ido Laila ta shiga yi a hankali, idanunta sun yi jawur, kallon Chuchu take yi sannan ta rike kai tana ‘kara tuno abubuwan da suka faru jiya
“Ki tashi ki shirya mu tafi makaranta” Chuchu ta fada tana kallon Laila
Girgiza Kai Laila ta yi ta ce A’a babu inda zan je, ki tafi kawai
“For how many weeks bama zuwa makaranta, kin manta munyi alkawarin Ba za mu ‘kara maimaita shekara ba”
Laila mikewa ta yi tana fadin “I’m not in the good mood, babu wanda ya taba cina chacha, koda yaushe ni ce a sama, amma wannan dan iskan matsiyacin ya zo ya dawo dani ‘kasa, sannan ni yake kira da karuwa mara mutunci”
“Ki manta dashi Laila, shi matsiyacine, bai san wacece ke ba, Karki ‘bata lokacinki a kanshi”
Wasu hawaye suka shiga zarya daga idanun Laila tana fadin “da ciwo a kira mace da karuwa, ni da ban taba sanin wani da namiji ba a duniya shine sai ya ce min karuwa, Kinsan dai duk rashin jina ko saurayi ban taba yi ba”
Cikin tausayi Chuchu ta jawota jiki ta shiga rarrashi “ki yi hakuri Laila, please ki kwantar da hankalinki, kada kisa wannan tunanin a zuciyarki, Kinsan dai a kowani lokaci Ina tare dake”
Haka Chuchu ta cigaba da rarrashin Laila har ta samu ta kwantar da hankalinta sannan ta je kitchen ta hada mata breakfast ta kawo mata, Bayan Chuchu ta kammala breakfast bathroom ta shiga ta yi wanka bayan ta fito ta shirya cikin wani ‘karamin riga mara nauyi da tsawonshi ya tsaya dai dai rabin cinya, fadawa ta yi kan gado ta kwanta
Chuchu ce ta turo ‘kofa ta shigo cikin shirinta tsaf na tafiya makaranta..ganin Laila a kwance yasa ta ce Laila baki shirya ba, lokaci fa yana tafiya
Cikin marairaicewa Laila ta ce please ki barni yau, na yi miki alkawarin gobe zan je, please
Chuchu ta ce to shikenan, amma ki kula da kanki, sai na dawo
Smile Laila kawai ta yi, Chuchu ta yi tafiyarta
Laila sai juye juye take yi a kan gado ta ‘kasa bacci, Zaid ke ‘kara fado mata a rai, ji take kamar ta yi hauka, ‘kara jin tsanani ‘kiyayyarshi take yi a zuciyarta…..hankalinta komawa ya yi kan bibbiga ‘kofar dakin da ake yi
Sauka ta yi daga kan gadon tana ‘karamin tsaki sannan ta je ta bude, cak ta tsaya tana kallon Zaid cikin tsananin mamaki
Mu hadu a page 2
Taku ce M. Jaruma Luxury
Add Comment