Littafan Hausa Novels

Kaunar Uwa Hausa Novel Complete

Kaunar Uwa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

ƘAUNAR UWA

(DABANCE)

 

 

NA

 

AMMIEYN AMATULLAHI

 

PAID BOOK

 

FREE PAGE

 

PAGE 1️⃣TO2️⃣

 

GODIYA

 

 

Godiya ta tabbata ga allah ubangijin talikai wanda bai haifa ba ba’a haifeshi shi ba shi kaɗai ne ubangiji mabuwayi me iko da kowa da komai.Tsira da amincin allah ya ƙara tabbata ga shugabanmu annabi muhammadu (s.a.w)da ahalinshi da sahabbanshi har izuwa ranar tashin alƙiyama.

Roƙon allah ya ba ni ikon kammala rubuta wannan littafi lafiya kamar yarda na fara lafiya allah ka ba ni ikon rubuta abinda al’umma za ta amfana dashi ameen.

 

 

GARGAƊI

Wannnan kabari ƙirƙirarren labari ne ban yarda wani ko wata suyi amfani da wani sashi na cikin labarin ba tare da amincewar marubuciyar ba yin haka saɓawa doka ce ta marubuciya duk wanda na kama da yin amfani da wani ɓangare na cikin labari ba tare da amincewata ba.Zai fuskanci hukunci.

 

 

ARASHI

 

Duk wanda wannan labarin yayi shige da labarin rayuwarshi arashi ne yayi haƙuri labarina ƙirƙirarrene.

Hakin So Hausa Novel Complete

 

DEDUCATED TO MOM MASHKUR.

This entire book is a dedication to you mom mashkur &afra thank God for your love.

You are definitely a person, your generosity and creativity are special. I love you. Fisabilillah Antyna.

May God glorify your pen more and this book is dedicated to you, believe it if you want.

The pen is better than the sword.

 

 

Ka yi wa darajar Allah kada ka raba k’aunar dake tsakanin d’a da uwa.

ka tuna tausayi da shak’uwa da Allah ya sanya tsakanin mahaifiya da d’anta,

kada ka raba tsakaninmu kayi min alfarma kabarni na rayu da d’ana ina sonshi ahaka kada ka raba k’aunar uwa da ɗanta na yarda da dukkan hukuncin da za ka yanken amma kada haka ya sha fi lafiyar jaririn da ko cibi ba’a yanke mishi ba.

 

 

Kuka ne yaci ƙarfina sakamakon ganin kwalin da mahaifina ya d’auka yana shirin sanya jaririn da ko wanka bai samu anyi mishi ba. ji nayi dukkan wani tsoro da fargaba ta fita azuciyata tsantsar k’auna da tausayin gudan jinina da ƙila shi kaɗai Allah ya mallaka min amma saboda rashin tawakkali ana shirin salwantar da ranshi saboda allah ya hukunta zuwanshi duniya to menene laifinshi da har mahaifina ya kasa karɓarshi menene laifinshi don ya zo A matsayin ɗan da aka samu cikinshi ta hanyar fyad’e meyasa duniya ta lalace mutanan kirki sun yi ƙaranci acikinta. na rasa tudun dafawa alokacin da mummunar ƙaddara ta faɗawa rayuwata alokacin da

banyi zato ba.

 

 

Amma mahaifina ya shafawa idonshi toka wayyo rayuwa ni sumayya ina zan saka raina naji daɗi jin fitar mahaifina daga ɗakin da nake ne ya farkar dani daga tunanin ƙaddarar da ta faɗa min,aguje na bishi tare da fisge kwalin da ya saka jaririn aciki na yi, ban taɓa tunanin tsanar da mahaifina yake min ta kai haka ba shin akaina aka fara haihuwar ɗa ba tare da aure ba.

 

 

Mene ribar kashe rai me abbana yake shirin aikatawa ina ji a yanzu ko duniya za ta tattaru akaina bazan iya bada gudan jinina asalwantar da ranshi ba.

 

 

Wallahi ina sonshi ahaka na shirya fuskantar dukkan ƙalubale na rayuwa na shirya dukkan abin da zan gani ko na ji dangane da ɗana Abbah!!! nakira shi cikin amon murya abba wallahi muddin ba za ka zauna da ni da ɗana ba a haka ba na zaɓi barin gidan ka”.

Na zaɓi na shiga duniya na zaɓi dukkan wani ƙunci da zan shiga ayanzu ko agaba amma kasani bazan iya bari akashe Muhammad Anwar ba.

 

 

Ina tantama akan so da ƙaunar da ka nuna min abaya Allah sarki Ammie Allah ya jiƙanki allah ya sa ka miki yabi miki haƙƙinki duk wanda ya yi sanadiyyar rasa ranki Allah kana ganin zalincin da aka yi wa bayinka Allah ka sa ka min kukane yaci ƙarfina tabbas anyi mana zalincin da bazamu manta ba.

 

 

Juyawa Abba ya yi idonshi yana zubar da hawaye nima rungume Anwar na yi zuwa ɗakina tare da ɗaukar sabuwar reza na yanke mishi cibiya ruwa na ɗaura akan wuta sai da ya tafasa sannan na ɗiba wanka na yiwa anwar duk da ban iya sosai ba.

 

 

Amma ina ganin yarda Ammie take yiwa ƙanina Muhammada Anwar ina gama yi mishi wanka na ɗebo kayan murgayi Anwar wanda kafin rasuwar Ammie ta danƙa min da hannunta.

 

 

Allah sarki uwa Allah ne kaɗai yasan ƙaunar da ya sanya tsakanin uwa da yaranta na yi kewarki Ammie ke kaɗai ce kika yarda da ƙaddarar da ta faɗawa tilon ƴarki Ammie allah ya jiƙanki ammie ganin na shiryashi kamar yarda naga ammie na yi sai na kwantar da shi na shiga banɗaki wanka nayi da ruwa me zafi haka na daure ina kuka ina komai na gyara kaina na fito na gyara wajan da ya ɓaci zama nayi ina tunanin rayuwa yunwar da ke ƙwaƙular cikina ce tasa na ɗauki kayan karin da ban iya ci ba ina turawa ba dan daɗi ba banjima ba wani masifaffen ciwon ciki ya murɗeni kuka nake ina juyi tare da kiran sunan Allah don na san babu me fitar da ni ahalin da nake ciki jin Anwar na kuka ne yasa na ɗan janyoshi kusa da ni tare da sanya mishi nono abaki jin zafi ya ziyarce nonona lokacin da ya kama yana zuƙa lokaci ɗaya naji tausayi da ƙaunar dukkan wata uwa tabbas iyaye sai dai addu’ar allah ya biyasu ahankali nake shafa kanshi ina ƙare mishi kallo farine tas sumarshi irinta fulanin usul gata baƙa ƙirin da ita yaron yana da hanci da manyan ido sam ba ya kama dani sai dai kama ta jini.

 

 

Ina sonka anwar ƙaunarka ta musammance yarona Allah ya albarkaci rayuwarka Allah ya yi maka arziƙi da biyayyarshi Allah ya yi maka arziƙi da alƙur’ani allah ya raya mini kai bisa sunnar Annabi Muhammad (s.a.w).

 

 

 

Shiru yayi kamar yana jin abin da nake cewa rungumeshi nayi jimawa kaɗan wani wahalallen bacci ya ɗauke ni.

 

 

Hayaniyar da na ji ita ta tabbatar min da Momy ta dawo kishiyar Ammie tsayuwa tayi a kaina tana ƙarewa Anwar kallo kafin ta hau salati tana kiran Abbana aguje ya fito kamar ɗanta zuwa yayi ya tsaya a kusa da ita.

 

 

 

Abban Rufaida me nake gani a gidanka ɗan shege fa ɗan zina wallahi bazan zauna da ɗan shege ba sai dai kasan abin da za ka yi ko dai aje a yarda shegen yaron ko kuma uwar da ɗan zina subar gidan ko kuma ni inbar maka gidan sai ka zaɓa tsakanin ni da su jikin Abba na rawa ya miƙa hannu zai ɗauke Anwar saurin dakatar da shi na yi na miƙe tare da janyo akwatina na haɗa dukkan abin da nake buƙata na goya Anwar na juya na kama hannun Abbana da yake zubar da hawaye nima hawayen nake na ce”Abba kayi haƙuri na san duk abin da kake ba yin kanka bane Abbana me ƙaunata ba zai taɓa wulaƙanta ni ba Abba a duk inda nake a faɗin duniya addu’arka nake buƙata bazan taɓa mantawa da Abbana ba zan kasance me roƙon Allah ya fitar da kai daga sarƙaƙiyar duhun da ka shiga Allah ya fitar da kai ke kuma ki jira ranar da asirinki zai tonu ki jira ranar sakamako tun a duniya ki sani wannan yaron insha Allahu shi ne mabuɗin tonon asirinki jan trolly ɗina na yi tare da sa mukulli na kulle ɗakin mahaifiyata.

 

Nafita ina kuka tabbas ƙaddara ta riga fata ƙaddarar allah ba ta huce kan kowa allah ne ya jarabce ni kuma shi zai yaye min dukkan damuwata tafiya naci gaba da yi duk da ban san in da zan nufa ba Allah ga baiwarka tana buƙatar ɗaukinka.

 

 

Ban san ina zan shiga ba bansan ina za ni ba tafiya nake ba tare da nasan ina na nufa ba ga duhun magriba ya kawo kai yanke shawarar barin garin gombe na yi ban san ina dangin Ammie suke ba bare na nufe su dangin Abbana kuwa ko giyar wake nasha bazan doshi inda suke ba ko da na je bazan sa mu masauki ba ƙarshe cin mutunci da tozarci ne zai biyu baya atsakaninmu tabbas maraici mugun ciwo ne nayi imani da Ammie tana duniya bazan tozarta ba.

 

 

 

Tashar gombe na nufa ina zuwa naji ana kiran me duguri mutum ɗaya me duguri mutum da sauri na ƙarasa na shiga motar tare da kwance goyon Anwar ina rungume shi a ƙirjina yana ta bacci tunanin ina zan nufa a cikin Meduguri nake nidai bansan kowa ba.

 

 

 

Baiwar allah yaronki yana kuka firgigit na dawo daga duniyar tunanin da na shiga wata” ƴar dattijuwar mata ce ke min magana tare da karɓar Anwar tana ƙare min kallo girgiza kai kawai tayi tana jimanta abin da zai fito da me jego dan da alama haihuwar yau ce duba da yarda taga yaron hannunta ƴar nan gyara ki shayar dashi da alama yunwa yake ji nono nafara ba shi da sauri ya karɓa yana sha duk second ɗaya idan na kalli anwar ƙaunarshi da tausayinshi ƙara shiga raina yake bamu isa garin mai duguri ba sai ƙarfe 12:30am sannan ko da muka sauka atasha rasa inda zan nufa na yi guri na nema na zauna acikin tashar ganin babu mataimaki sai allah kuma nasan zamana cikin tasha a dai-dai wannan lokacin akwai matsala kasancewar duk maza ne babu mace yasa na miƙe tare da sake gyara goyon anwar dake ta tsala kuka babu ƙaƙƙautawa bakin titi na nufa da nufin tsallakawa sai dai ban ƙarasa tsallakawa ba naji anyi sama dani daga haka ban sake sanin inda kaina yake aduniya ba.

 

 

Kallon mutumin da ya kaɗe sumayya nayi ba yaro bane magidanci ne aƙalla zai kai shekara arba’in da ɗaya zuwa da biyu baƙi ne me matsagaicin tsawo yana da kyawunshi dai-dai wanda ilahu ya wadata shi da shi sai dai daga gani yana da hali duba da sittirar dake jikinshi da kuma motar da yake ciki da alamar janshi ake amotar duba da tarda drevan motar ya fito agigice kan sumayya suka nufa yayin da yayi nasarar ɗaukar anwar dake kwance gefen titi cikin hukuncin ubangiji bacci yake ba ta re da ya tashi ba.

 

 

 

rungume Anwar ya yi, a ƙirjinshi tare da buɗe mota ya sanya shi sannan ya kinkimi Sumayya ya sanya ta a bayan mota tare da kullewa drevan ne ya shiga yaja motar Alhaji wane asibiti ya kamata mukaita duba da mun yi nisa da gida cikin nuna alamar damuwa mutumin ya ce”baza mu rasa hospitals agaba ba.

 

 

 

Mu kaita alhayat hospital gaba jaɗan suka isa asibitin cikin gaggawa aka karɓe ta tare da fara bata taimakon gaggawa sai da ya tabbatar anduba lafiyar anwar sannan ƙarin ruwa aka ɗaura mata sannan ta nemi su ɗan bata waje za ta duba sumayya duba da yarda taga jariri sabon haihuwa ahannunta duk wanda yaga yarda sumayya take indai ya san haihuwa zai gane sabuwar haihuwa tayi da ka kalleta sai da ta duba ta ciki da waje ganin lafiyarta ƙalau sai dai buguwar da ta yi da kuma yarda gaban goshinta ke zubar da jini ɗinki ta yi mata agaban goshinta sai ruwan da aka jona mata anwar na hannun mutumin da ya kaɗeta.

 

 

Duk wacce take buƙatar atallata mata hajarta ƙofa abuɗe take za ta iya tuntuɓata ta wannan number watsapp or call 07044509533 or 09166820615.

 

 

 

 

Comment and share please.

Add Comment

Click here to post a comment