Hakin So Hausa Novel Complete
HAKIN SO
BY MSS TEEMAH
Bismillahi rahamanin rahim
DUKAN YABO DA GODIYA TATABBATA GA ALLAH (S A T) ALLAH KAYI DADIN TSIRA GASHUGABANMU ANNABINMU ANNABIN RAHAMA DA ALIHI DA SAHABEINSA BAKI DAYA DAGANAN HAZUWA TASHIN ALKIYAMA
TSOKACI
WANAN LITTATAFIN KIRKIRAREN LBRNE BAN RUBUTASHI DAN TOZARCI KOCIN MUTUNCIN WANIBA
WANAN LBRN YANA KUNSHE DA ABUBUWA KALA KALA CIKI HARDA CIN AMANAR SOYAYYA DA KUMA SON MASO WANI AKACE KOSHIN WHL SAI SOYAYYAR GASKIYA DA MAKIRCI DA KUMA DANA DANI
HAKIN SO
page 1️⃣_-_2️⃣
Farkon lbrn
Jini Daya Hausa Novel Complete
______________ wata matashiyar yarinya Nahango dabazata wuce shekara 17 zuwa 18 ans sanye take da kayan buzaye Riga bakace wadda takawo mata harga guwawo Tana daure da Zane baki gashin Nan nata anmusu kitso guda biyu yarinyar farace sosai gatada dogon hanci harbaka GA manya manya idanuwa farare tass Kamar madara GA gashin giranan nata Yayi baki sosai gatada Dan karamun baki Idan baka saniba sai Kace Jan baki ne tassa abakinta amma batassa komaiba abakinta yarinyar dei ba’acewa komai sai dei tubara kalla Masha allah kyau Kam Allah yabatashi gatada diri Humm abundei ba’acewa komai, tafe take Tana rera waka Kamar Haka ” (auren buzuwa jidaline auren buzuwa da Kwai tsada da mai rakumi da akala sai mai turkudi kwanin tsada) wakar take rerawa cikin nishadi saboda wakar na bala’in burgeta, takawo dede wani shagone tahadu da balkissa yar gidan Inna talatu, yarinyarce tace ma balkissa yau Wana kama yau banga ubanda zei hanani CIN ubankiba balkissa” balkissa tace,”ni yau banajin fada iheesan saurima nake inna talatu tace nayi sauri nakai mata filawanta, iheesan tace” Kan uban can me kika mayardani wato kina nufin ni masifaffiyace Ko aiko zakiga masifa kinsan dama inada cikinki ranan da kika cemun Wai kakata mayyace kika gudu Ko kuma yanzu kika cemun masifafdiya, balkissa tassan Sarai iheesan Dan zata iya CIN ubanta Kamar yadda tafada Dan ita bata ima iheesanba yanzune tafara Dana sanin abunda tacewa iheesan din cikin yanayin ban taussayi tacema iheesan Dan Allah Kiyi hakuri bazan karaba dayake iheesan duk abunta Idan kagamata da allah zata Dena, Nan take tacema balkissa shikenan n’a hakura amma Kissani Idan kika Kara wllh bazan hakuraba balkissa tace ” bazan ma karaba insha Allah zan kiyaye, iheesan hanyar gida tanufa Tana Dan sauri sauri Dan sai alokacin ne ta tuno da gargadinda mama Tama mata akan kada tadade Gashi kuma ta dadike
Tahoua
Wata haddadiyar Mota Nagani Tayi parking à gaban wani katoton wurin shakatawa wani hadadden saurayi Nagani Yana saukowa daga cikin motar Masha Allah kawai nafurta Dan Naga saurayin kyakyawane sosai nakarshe ma kuwa sanye yake cikin riga da wando dinki haussa ne,
Kara yaji wayarsa nayi da alama Tana neman temako zarota Yayi daga cikin aljuhun wandonsa sunan KAMAL Nagani anrubuta da manya manya haruffa, wayar yadaga banji kome Kamal yace massaba saiji nayi yace”OK pas de problème
Sanan Ya katse Kirran, shiga cikin filin shakatawar Yayi Yana shiga ciki yazauna saman wata tebre me zaman mutun biyu ya zauna wani Dan gugun Wajen ya Kira yace massa” inason akwawo mun Kofi, kukun yace “angama oga, baifi minti 1 ba yakarassaba Wajen mutunen yace” GA Kofin inda ka bukata angama amsa kofin in Yayi Yana sha ahankali ahankali
Masarauta
Uncle Ibrahim ne yake cewa inna “kinga ciwon Sarki sai gaba gaba yake abun yakici yaki cinyewa me zei Hana mu fita dashi kassar waje mugani koza’adace, inna tace massa” a’a kabarshi kawai tunda kaga tun ba yanzuba anata fita dashi kassar waje Amma abun sai gaba gaba yake ni anawa ganin me zei Hana mugwadayi na gargajiya mugani koza’adace, shidei cewa Yayi badamuwa mugwadayin nagidan to, wayarsace ta fara riging alamu Tana neman temako duban wayar Yayi yaga sunan yarima asaman fuskar wayar, dauka Kiran Yayi daga can naji ance massa”
DUKA DUKA ANAN ZANDAKATA MUHADU DAKU AKASHI NAGABA INDA ZANKAWO MUKU CIGABANSA INSHA ALLAH
BYE BYE NABARKU LFY
MARUBUCIYA TEEMAH
: HAKIN SO
BY MSS TEEMAH
Bismillahi rahamanin rahim
HAKIN SO
page 3️⃣_-_4️⃣
Dagacan cikin wayar naji yarima nacema uncle Ibrahim Allah yayiwa zeinaba rassuwa, Inna lillahi wa’inna ilaihin raju’un wanan wace irin massiface Haka, inna takalleshi gabanta na faduwa tace ” Ibrahim wani abone yafaruda Muhammad? in Kassan cewar ita Haka take kiransa, uncle Ibrahim yakalli Inna cikin jajayen idanuwanshi wa’anda suka sake Kala tun Lokacin Da yarima yafada mishi rassuwar kanwar tassa kwaya daya tile, sanan yacema Inna yanzu yanzu Nan yarima yake fadamun cewa Allah yayiwa rintse idanuwansa sanan yakarassa Maganar Allah yayiwa zeinab, inalillahi wa’inna ilaihin raju’un kawai Inna taketa fadi yayinda hawaye suketa zarya assaman fuskarta, uncle Ibrahim tashi Yayi yabar wajenda Inna take bei wani tseotsayaba Yayi préparer in kayanshi dan bazei iya zaman Koda na minti 3h neba Agarin
Kauyen kinfiyawa
Zaune take asaman kujera yar tsugunno Tana kuka me ban taussayi da cinrai duk wanda yakeda Imani Idan yaganta Tana irin wanan kukan to saiya taussayamata, kuka take na taussayin kanta da kanta, Ammi ce ta fito daga cikin daki ta kalli yarinyar tace mata”keh Fatima Dan ubanki uban me kikeyiwa kuka” au baki ma kammalamun wankinaba kintsaya sai kuka kike yau wllh Ko kukan jini zakiyi to saikin mun wankina Dan ubanki “kallon Ammi Fatima Tayi sanan tace mata Ammy wllh yunwa nakeji tun jiya da dadare rabona Dana ci abunci Dan Allah Ammy katemaka kiban abunci naci, Inna tace mata bazan Bayarba kuma kitashi kimun aikina tun Kafin na lahira yafiki Jin dadi, Fatima ita dei yaukam Saidei akasheta Idan kasheta Ammy zatayi wllh bazata iyayin komaiba mudin bataci abunciba tsakar yunwar da takeji Idan tatashi tsaye jiri jiri take gani, ganin Haka da ammy Tayi yassa ta daukko Mata marar tuwo wanda Ko Dan shekara 5 akabama tuwon tsabb zei iya cinyeshi, ballatanama ita da yanzu zata Kai shekara 19 Ko kuma dei 20 ans, Haka ta dauki abincin taci bawai issarta zeiyiba kawai dei tarage yunwar da takeji ne, Tana Gama cin abunci tatashi ta wanke hannunta sanan Tasha ruwa, ba laifi yanzu batajin yunwar sosai, bawai takoshi bane Aa Saidei yunwar datakejice ta Dan rage yanzu Kam tassamu Dan karfi, wanke kayan Tayi tass tashanya ronkonta daya Allah yassa ammy tace sun wanku da kussan Kullun Idan tayiwa ammy wanki sai ammy tace bassu wankuba bawai bassu wanku bane a’a tsabar luguntar ammy ce” botiki ruwa ta dauka da niyyar zuwa Rafi dobo ruwa Dan tacika randa da ruwa, tafiya take ahankali yake tafiya cikin sanyin hali
Agadez
Iheesan ce kwance abakinta tana tunanin kalmarba balkissa tataba wadamata akan kakarta mayya ce Tana so ta tambayi kakartata shin da gaskene balkissa take Amma kuma Tana shakkar hakan, zuciyarta ce tace mata me zei Hana Kiyi buncike da kanki tunda kina tsoron Tambayarta? Iheesan tace to Taya zan Yi Hakan? zuciyarta tassake ce mata ta hanyar Yi abunda maye beiso ? Tace to Menene abunda beiso din? Zuciyarta tabaya amsa da “kin mata abunda kikaji malam mussa Yana fadama larai akan” maye inda yace mata maye bayason ana nuna massa yatsa wato kashedi, kuma maye bayason Jin iskan tazarar gari, baya son Jin iskan habbatu sauda, zuciyarta tace mata to tanan Zaki tantance Idan ira din manyace Ko kuma dei Aa, Iheesan tace to a Ina zan samesu ne,? Zuciyarta tace mata ki siyo mana, juyo muryar kaka Tayi Tana kiranta, Iheesan! Iheesan !Iheesan wai kina Ina daga can cikin daki Iheesan tace Inna ganinan zuwa kaka, fitowa Tayi waje kaka tace mata”amshi kudinan kije kissiyomun magi Wajen iliya me shago amsar kudin Tayi tatafi tassiyo, da saurinta harda gudu take hadawa dashi saboda Tayi sauri ta dawo, aiko batafi minti 3 ba tadawo inda kakz take Tana
Hura wuta,cema kaka Tayi gashi kaka tamiko hannunta da niyyar karba Nan take kaka Tayi wata iriyar zabura, kaka tace keh Iheesan Wanne irin iskancine wanan yazaki sakamun Abu cikin tsakiyar yatsanki,? Iheesan sai kallon kaka take Tana mamakin yadda ta zabura jikinta sai wata iriyar ruwa yake aje magi din Tayi sanan Tayi ficewatta zuwa dakin ta
DUKA DUKA ANAN ZANDAKATA MUHADU DAKU AKASHI NAGABA INDA ZANKAWO MUKU CIGABANSA INSHA ALLAH
NICE TAKU HAR KULLUN MSS TEEMAH
NABARKU LFY
Add Comment