Tafiya Akan Ruwa Hausa Novel Complete
TAFIYA AKAN RUWA
BY: Mubarak A Kamba
*_Zamani Writers Association_*
~~“`(We’re Here To Educated, Motivated And Entertain Our Readers)~“`~
Sadaukarwa: Wannan Labarin Sadaukarwa Ne Ga Ƙungiyar Haɗakar Marubutan Jahar Kebbi (HAMJAK)
( ~Tsokaci: Labari Ne Da Aka Ƙirƙira Domin Faɗakar da Ɗalibai Masu Karatu Na Kowanne Fanni, Primary, Secondary Ko Kuma University.~
~Labari Ne Akan Wasu Ƴan Makaranta Da Suka Shiga Gasar Karatu A Tsakaninsu. Gasar Karatu Ne Yayi Sanadiyar Haddasa Ingantacciyar Soyayya, Da Fitinanniyar Ƙiyayya Haka Kuma Shi Ne Sanadiyar Warwarewar Matsalar Wani Babban Al’amari Da Ya Faru Wanda Ya Kawo Rabuwar Zuri’a Ɗaya )~
Page: 1
Sauri yake kada ya ƙara lokaci sosai, duk da yake ya rigada ya makara, amma baya so ya ƙara lokaci fiye da wannan. Mahaifiyarsa Hadiza ta ce, “Kana wannan saurin sai kaje ka manta wani abin kuma in yaso ka dawo nema ko Salim?” Tana ƙare masa kallo a yayin da yake haɗa kayan jakarsa. Ba tare da ya ko kalli gefen da take ba ya ce, “Oh My Goodness! Mama ya kike so ne, na fa makara just pray for me, i have an English test kuma wannan malamar tana da tsauri sosai wallahi. I just need your pray.”
“Toh shi kenan, kai kasani addu’a kuma ba lokacin da ba nayi, Allah ya maka arziƙin gamawa lafiya.”
Kamal Ne Hausa Novel Complete
Ya ɗauki school bag ɗinsa zai fice ta kalle shi ta ce, “Dakata Yaro! Da na faɗa maka zaka iya mantuwa, ai sai ka ɗauki maganata a banza, to gashi tun yanzu ma ka fara mantawa.” Da tsantsar mamaki tare da tsumayi ya ce, “To me na manta?” “Ina kuɗin da zaka hau adaidaita sahun iyyeh?”
Shiru yayi na ɗan lokaci kana ya wuce ɗaki inda ya saba ɗauka da take ajiye masa. Duk da haka dai bai sa shi nutsuwan ba, yayi saurin fita ƙofar gida. Cikin nasarar Ubangiji ya tarar da mai adaidata sahun a kusan ƙofar gidan ya tare shi. Ba inda ya tsaya da shi sai ƙofar makaranta.
Salim? Waye Salim?
Yaro ne mai matuƙar hazaƙa a kowane irin al’amari. Yana da tsabta sosai, wanda tsabtarsa ne yasa sauran ɗaliban ke masa kallon mai jiji-da-kai. Tun da Salim ya taso a rayuwarsa ba wani ɗan uwa ko ƴar uwarsa da ya sani na dangin uwa ko uba. Bai san wani ƙani ko yaya, ko wata auntynsa ba. Salim mahaifiyarsa ce kaɗai ya sani. Da yake yaro ne ƙarami wanda bai fi shekara sha shida ba, yasa bai taɓa damuwa da dole sai ya san ahalinsa ba. Idan ka cire mahaifiyarsa to babu wani abu da ya fiso sama da karatu. Ba shida wani aboki namiji ko macce ko a makarantarsu balle kuma cikin unguwa.
A daidai ƙofar makaranta mai adaidaita sahun ya ajiye shi yana sauri ya fita ko kuɗin mai adaidata sahun bai biya ba, ai kuwa da sauri ya fito yana dakatar da shi. “Wai kai saurin me kake ne, ka bani kuɗina ne?” Ji yake kamar ya hamɓare shi ya wuce yayi wani tsaki tare da ciro kuɗi aljihunsa ya damƙa masa ko canji bai tsaya karɓa ba ya shige school ɗin.
Wuce mutanen da ke tsaye wurin kawai yake bai damu da kowa ba har ya isa ƙofar ajinsu. Babban abinda ya ƙona masa rai yayi matuƙar ba shi haushi, shi ne yadda ya ga class ɗin nasu fayau ba kowa a ciki. Nan kuma tunaninsa ya rabu gida biyu ya gaza tantancewa an kammala Test ɗin ne ko kuwa dai an fasa ne?
Yana tsaye cikin wannan tunanin ne wata yarinya Cristian wato Xayyeeshert ta same shi tsaye. Kallo ɗaya ta yi masa ta nazarci tsayin da yake yi ta ce, “Oh! Salim are you surprised for the Test shifted right?” Cike da tsantsar mamaki ya ce, “Did you mean the Test has been shifted?” “Yes of course the test is shifted till after breakfast, i think as you are very serious student you already knew that.”
Sai a wannan lokacin ne hankalinsa ya kwanta yayi murmushi ya ce, “Thank you for the information Xayyeeshert I thought the Test has been done, because I knew I became a very late due to some crasis i face at home. But where are the class members has gone? “Some of them has gone to read their book perfectly, some of them goes to take breakfast, while the rest has gone to do their fact issues.”
Daga nan suka rabu yana mata godiya ya wuce Library kai tsaye domin ƙara karatu kamar yadda sauran ke yi. Wannan shi ne karon farko da zai fara rubuta wani abu mai kamada jarabawa a makarantar, domin kuwa bai fi wata biyu da samun admission ba a makarantar.
***********
A can wani sashen cikin makarantar, a wani ajin da bakomai a ciki sai wasu ƴan kujeri wanda ɗalibai suka saka aciki ne ƴan mata uku ne zaune a ciki su ma dai lokacin rubuta test ɗin suke jira. Ummita, Hilfat da kuma Fathil ne.
“How that be possible, duk wannan tsantsar so da yake mata a ce idan ya dawo daga ƙasar waje zai daina sonta, haba dai ai kema dai kinsan hakan ba zai yi yu ba. Wallahi ba zan yarda ba.” Hilfat ta faɗa yayin da take kallon Fathil dukansu suna zaune akan kujera ɗaya. Ita ma ɗin ta kalleta ta ce, “Ba wani abin mamaki ba ne, tunda kinga fa ba shi da lafiya ne, ya samu taɓin hankali ne, ba mamaki idan aka yi masa wannan aikin ya manta da ita.”
Ummita kuwa dake zaune a gefe tana karatu ta ce, “Allah yasan kuna damuna da wannan shegen labarin, even director of this film ma baisan me yakamata yayi don ya ƙayatar daku ba, shi ne har kuke wani surutu akan wannan banzar film. Idan zaku yi karatu guys mu yi karatu pls if not kawai mu fi ce mana.”
“Yawwa there’s something very special i want Us to discuss dama ina son mu haɗu ne. Gaskiya fa yakamata mu ƙaro other genders, because I want us to rule the whole entire school, kuma idan muna son haka dole ne mu ƙaro yawa da ƴan saffa-saffan guys.” Hilfat ta faɗa tana saurarensu, chewing gum a cikin bakinta tana taunawa ƙa-ƙas. Ummita kuwa da ke tsaka da karatu ta rufe littafin ta dawo da hankalinta gare su. “Am! Hmm! You are right Hilfat, but how can we do that?” Ta faɗa tana jinjina wannan discussion.
Fathil ta ce, “Eh tabbas fa, wannan ma tunani ne mai kyau, i think the only way to complete the task, shi ne zamu fara neman smart guys, ba kawai duk wanda muka samu ba.” “Ke dallah, zancen da nake shi ne tayaya zamu jawo su a jiki, ni fa ba wanda ya isa na same shi na faɗa masa ina son mu yi abota da shi a makarantar nan, ba zan iya bawa kowa damar da zai rena min hankali ba.” Ummita kenan gwanar ji da kai.
“To shi kenan ku bari kawai nasan me zan.” Hilfat ta faɗa. Tana washe haƙora tsabar farin cikin yadda take hango wannan abin nasu zai yi kyau.
Wace ce Ummi? Wace ce Hilfat? Kuma Wace ce Fathil?
Ayi Hakuri da gajeren typing a gaba zan ƙara yawan Page
Add Comment