Kamal Ne Hausa Novel Complete
KAMAL NE
*Page 1️⃣*
Wasu mahaukatan gidaje ne guda biyu, suna kallon juna kai kana kallon gidajan kasan masu shi sunci sun tada kai da kudi, ko cikin unguwar ma wannan ɓangaran ya fita daban, saboda wajan shiru babu hayaniya kowa na safgar gabansa cikin gidajan su.
Se kukan tsuntsaye da sansanyan kamshin frannai me dadi kakeji cikin hancin ka. Ɗayan gidan me kallon gabas na kutsa kai ciki, ina shiga na kara tabbatar da lallai akwai arziki, saboda yadda gidan ya tsaru babu karya, tamkar ba a ƙasar hausa ba, ko ina franni ne kore shar me haɗe da pink colour, duk sun kewaye cikin maƙareran gidan mai girman gaske, ga ma’aikata nan na kai komo, ɓangaran ajiye motoci na kalla na jinjina kai saboda a ƙalla motoci sunkai 20 kala-kala babu kalar da babu, wada naga me wanke motocin gidan ya cire mata riga yana gogewa ce ta tafi da imanina, saboda kyanta baƙa ce sudik kirar *range rover 2020* baƙin sai sheki yake, baki na riƙe ina so naga mamallakin motar ko nace wanda zai shiga motar nan, da sauri na kutsa kaina ciki kofar wani hamshaƙin parlo na tsaya ina karema kofar glass ɗin kallo ta yadda zan iya bude wannan kofar ta glass, wani ɗan madanin baƙi na gani jikin glass ɗin a manne, nayi saurin dannawa ai kuwa kofar glass ta bude haka ya nuna min cewar daga ciki ba a saka mata security ba.
Bakon Lamari Hausa Novel Complete
Kai na danna cikin parlon sai da numfashina ya kusa ɗaukewa saboda Wani irin sanyi da wani carpet da ƙafata ta shige, da kuma sassanyan kamshin dadi da ya daki hancina… Tunani na ya katse dai-dai lokacin da nayi tozali da wani hadaddan gay, a ƙalla zai kai kima nin 30 years sanye cikin Suit baƙake, wanda suka masa mahaukacin kyau, yana saukowa daga saman wani haɗadɗan bene, cikin kuzari da zafin nama yake taka matattakalar bene ɗin, hannunsa riƙe da wayoyi masu tsada guda biyu, yana kallon tsadaddan ɓaƙin agogon hannunsa na zallar fata, haka takalmin ƙafarsa baƙi ne shima na zallar fatane wanda ake masa adon zamani sai mahaukacin kudi, dan yana ra’ayin irinsa duk da ɗingisawar da yake, sai ka lura zaka gane yana ɗingisawa, ma’ana duk haduwarsa ƙafarsa ɗaya da rabi ce, amma yana ƙoƙarin take hakan dogo ne ƙaƙarfa me murɗadɗan jiki, ba fari bane tas haka zalika ba baƙi bane, wato chocolet colour ne yanayin sa tamkar ɗan ƙasar Ethiopia, yanada manyan idanu da gashin girar ido gazar-gazar, yanada dogon hanci me dan fadi kaɗan, bakinsa madedeci me ɗan fadi shi ba karami ba shi ba babba ba, lips dinsa ya ɗan sa Ja kaɗan, kyakyawar fuskarsa kewaye take da saja ga wata yar ƙasummba gashi ma’abucin fara’a wanda hakan yay mugun ƙara ma kyakyawar fuskarsa kyau… Yana dab da saukowa naji murya wata mata tana tafa hannuwa cikin muryata mai dadin sauraro, tana cewa”Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!! Yanzu *Kamaluddeen* saboda Allah saukowar ganganci kake , baka duba yanda kafarka take salon ka gangaro ka samu tashin hankali haba ɗa ɗaya tamkar da dubu…” Da gudun sa ya ƙaraso yana sakin murmushin da ya zame masa jiki, dan sam shi bayada tsuke fuska mutum ne mai faram-faram da jama’a. matsalarsa ɗaya tsani raini ƙo dede da kwayar zarra, baya zama waje ɗaya da mutumin da zai rainashi ko wanene. Jikinta ya fada ya rungumeta cikin amon muryashi me daɗin sauraro yace”Oh my Umma nah ɗanki jarumine fa , good morning ummah…”Abbu ne ya katse masa magana, ta hanyar dora masa cup ɗin hadaddan tea a baki yana murmushi yace”Oya sha wlh baka fita haka ba dan naga kayi lati.” baki Kamal ya turo yana lumshe tsumammun idanunsa ya kurbi tea ɗin kaɗan.. Dariyar wata matashiyar budurwa ce kyakywa me kyan diri tana kama da Kamal sosai sai de ita baƙa ce, itace ta katse su tana tafa hannuwa, itace ta dawo dasu daga duniyar lallashin Kamal da suke, Ummah ta janye shi jikinta ta kamo hannunsa tana dariya tace”Samha kin fiye sa idanu wlh.” Samha ta zumburo baki tana bubbuga ƙafa tace”Allah nima se an lallasheni zanyi breakfast.” Kamal ya watsa mata wani shu’umin kallo na yarinya nasha gabanki, ya mata gwalo, baki ta turo gaba tana kallon Abbu zata fara kuka. Abbu ya kama hannunta yace”Haba Samha nah Oya muje kiyi breakfast kema.” ya faɗa yana janye da hannunta, suna biye dasu Kamal har kan wani makeken dining are. Suna isa ummah ta zaunar dashi cikin dubara da Abbu suka samu yasha tea ɗin kadai Samha kuwa sai da taji ba guri, tana tsokanar Kamal baibi ta kanta ba ya miƙe saboda ya makara, ya rungume iyayansa yay masu kiss yayi masu sallama ya fita, a gaggauce. Samha ma ciki ta shiga ta fara shirin tafiya school.. *Kamal* yana fitowa ma’aikatan gidan suka fara kwasar gaisuwa, ya rinƙa amsa masu cikin sakin fuska. Kai tsaye gun motar da Garba ya goge masa ya nufa cikin takunsa na kasaitaccan namiji, Garba na biye dashi yana cewa”takawarka lafiya ƙasaitaccan namiji Jika ga Amadu jinin Ali zaki ɗa ɗaya tilo ga *Alhaji Abubakar kan giwa mai Nasara*, zanso naga wace mai sa’arce Allah zai kashe ya bata tauraron Miji abin nunama sa’a…” Kamal hannunsa ɗaya ya ɗaga masa alamar dakatar dashi, ɗayan hannunsa ya tura cikin lallausar sumar kansa yana sakin murmushi yace”uhumm Garba Allah shiryeka , Oya buɗe min mota na wuce irin wannan koɗawa haka…”Wayarsa ta katse masa magana, sakamakon ringing ɗin da take, ya kalli screen ɗin wayar yaga sunan *Sageer* na yawo saman screen ɗin wayar, picking ɗin call ɗin yay ya kara a kunnensa. Garba ya bude masa motar yana cewa”Yallaɓai ko dai na kirawo dire ba?” Kamal bai masa magana ya shige ya rufe motar yay mata key ya fizgeta da karfin gaske kamar zai tashi sama, ya nufi bakin tamƙameman get ɗin gidan yana horn. Ya’u ya gaishe sa ya buɗe masa kofa a guje ya fice daga gidan. Dirving yake sosai kamar ya tashi sama ransa ya ɓaci jin cewar yay lati har dalibansa sun fara shiga aji bai iso ba abinda ya tsana kenan a rayuwarsa. *Maryam Abacha American University Of Niger* Ciki Kamal ya danna hancin motarsa, iya haduwa University nan ta hadu ba karya kallo ɗaya zakai maya kasan ta haɗa ƴaƴan manya da kuma akasin hakan, babu ƴan ƙasar da babu cikin Makarantar nan ƙabila daban-daban. Yana shiga ya nufi parking spece yay parking ya kwashi wayoyinsa da laptop ya fito ya rufe motarsa ko Office ɗinsa bai nufa ba ya nufi ajin da yake koyarwa yau direct ya shiga, dan ba wani jimawa zai ba 1 hours kawai ke gare shi.. Can ko cikin ajin da Kamal zai zo, class ɗin hayaniya ce ta ɓarke sai ihu da shewa kakeji, tamkar ba yan Jami’a ba sai kace wasu ƴan JSS 3 saboda Hatsabiɓiyar yarinyar nan dake ajinsu sam bata ganin ta girma. *Mubina* matashiyar budurwa ce kyakyawa, tsaye take tana kwatanta tafiyar *Kangiwa* sai ihu suke suna zugata, farace sul ƴar siririya doguwa kyakyawa mai diraran jiki ga hips da boobs ƴar kimanin 20 years, masha Allah kyakywace sosai kallo ɗaya zaka mata kasan ta haɗa jini da larabawa, tanada doguwar fuska me ɗauke da dogon hanci da karamin baki, idanunta dara-dara farare tas lumsassu tamkar tana jin bacci, gashin idanunta gazar-gazar haka zalika girata me kyau, tanada gashi amma ba dogo ba sosai ya dai sauko kafadarta gashi da santsi, tana da dimples sharan kumcinta na dama wanda ko magana take sai ya loɓa duk inda kake neman kyakyawa *Mubina* takai, saide ta cika siririya sam batada jiki ko misƙala zarratin, saide akwai kyan diri da surah idan ka kalli hips ɗinta da boobs ɗinta zakasha mamki, suna tsantsar kama da muny roy ƴar india tamkar an tsaga kara, banban cinsu da muny tafi ta fari kaɗan da gashi dan Mubina batada dogon gashi sosai ya dai sauka kafadarta kuma ba baƙi bane ba maroon colour ne. Sanye take da wani tsadaddan material baƙi ɗinkin doguwar riga yayi mata kyau matuka, gashin kanta yasha kwalliya wasu irin ribbon ta ɗaure rabi rabin ta zubo shi saman fuskarta. Ƙafarta sanye da wani hills mai mutikar tsini tasha kunshin jan lalle yayi mata mugun kyau, zakayi mamakin yadda take takunta cikin nutsuwa hankali kwance da wannan takalmin me uban tsini.. Juyowa tayi ta kalli sharan da Basma take zaune kusa da window, sai raraɓa idanu take. Cikin daddadar muryata tace” Kunga tafiyar Kangiwa gurgu idan yana sauri. ” ta faɗa tana karkace ƙafa tana tafiyar Kamal sak wlh tamkar shine yake tafiyar, tako haɗe face babu wasa tamkar Kamal ɗin. Haba ai sai ihu da shewa suna tafa mata sai zugata suke tana hura hanci ita ƴar iska. Basma kuwa ranta ya ɓaci sosai kawai dan bata son Mubina ta kirta mata rashin mutunci ne yasa tai shiru, amma tayi alkawalin ko da ta hango Sir Kangiwa bazata faɗi ba yau sai yaci ubanta, ya koya mata hankali dan duk raharsa baya ɗaukan raini sam bai taɓa sanin Mubina na cin duduniyar saba a munafurce take, duk da yasan yarinyar tantiriyace bata gabansa tunda bata shiga sabgarsa ba. Mubina tace da Basma” Kifa rinƙa duba hanya kar gurgu ya ritsoni wlh bazan taɓa yafe maki ba.” ta faɗa tana dariyar mugunta. Nazir yace “Haba Baby babbar yarinya kiyi kawai me ya isa yayi dake ai kina wuta wlh…” Ai bakinsa ne ya ƙame sakammakon hango Kamal da yayi yana dab da shigowa class ɗin. Cikin sauri yace Baby ki ankare.” a mugun sauri Mubina ta kwasa a guje saura kadan ta fadi na kusa d ita ya riƙeta, ta nufi gun Basma gurin zamanta ta zauna tai sauri ta yafa yalulun gyalanta tana maida numfashi, ta takarkare ta dirkama Basma duka a bayanta, tace”karamar ƴar iska , wlh yau da me rabani dake sai Allah.” ta faɗi tana zabga mata harara. Nan take kowa ya kama kansa suka nutsu kowa ya ƙoma mazauninsa, shiru kakejin class ɗin tayi. Basma ta kumshe dariyar duk taji zafin dukan, tana mamkin rashin kunyar Mubina ga tant
iranci ga tsoro. Kamal da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin class ɗin gabaki ɗaya suka miƙe suna gaishe sa”good morning sir” Hannu ya ɗaga masu kowa ya zauna ya nufi gurin zaman sa. Ya sunkuya zai zauna karaf a kunnesa yaji an karkace murya ance” Jirgar ɗan gurgu” da sauri ya ɗago yana zaro idanu cike da mugun mamaki, dan wannan shine karo na biyar a cikin ajin nan ana faɗi masa haka, sam sai yaji kamar kunnensa ne dan suna bashi girman sa, har tantiriyar yarinyar nan. Ya kallesu cike da mamaki tabbas ya gano duk ranar da ya shigo ajinan sai yaji an faɗi wannna kalmar ta gurgu ƙasa-ƙasa sau ɗaya. Baiyi magana ba, ya bisu da kallo wanda su kuma sun cika da tsoron cewar karfa yace a fito da wacce ta faɗa Mubina ta zame masu annoba dan tayi alkawalin duk wanda ya faɗa zata bashi mugun mamaki sharrin da zata kulla masa sai an korashi daga makarantar. Ɗaya bayan ɗaya ya rinƙa bin daliban da kallo duk sun sadda kansu, gashi wasunsu basajin ko hausa ma. Ya kalli ɓangaran su Mubina, Basma jikinta har rawa yake karaf suka haɗa idanu da Mubina Sai kif-kif take ta tsareshi da idanu babu wani ɗar da zai nuna itace ta faɗi, da sauri tace “Wlh sir dole a ɗauki mataki nima naji a kan kunnena ance maka…..🙊”Ni kabani aikin ko jinnu ne sai an fito dashi , dan abun ba a cikin aji bane daga wajane…”Hannu ya ɗaga mata kansa ya ɗauke daga kallonta, saboda tsaf ya gano yarinyar ce, kuma daman sam tun shigowarsa makarantar bata masa ba sam batada tarbiyya da kamun kai amma Zaiyi bin cike ya tabbatar da cewar itace take cemasa gurgu abinda Allah ya halilcesa dashi, ba saya yayi ba, tabbas zai koya nata hankali. Bai sake magana ba kuma ya boye ɓacin ransa ya koya masu abinda ya kawosa ajin tsawon one hours. Yana gamawa ya fita, Direct Office ɗinsa ya nufa. Yana shiga hadaddan office ɗinsa ya shiga toilet bai jima ba ya fito ya zauna saman lumtsumemiyar kujera tana juyi dashi ga sanyin Ac kamshi na tashi, ko ina laptop ya kunna ya shiga wani aiki yanayi yana duba agogo, yaga 12 tayi. Knocking ɗin kofar akayi, tsaki yaja ya miƙe ya nufi kofar ya murza key ya buɗe, idanu hudu suka yi da wata matashiyar budurwa tsaye face ya haɗe yace lfy?” Cikin kisisina da malle tayi fari da idanu ta kara matsowa kusa dashi har sunajin numfashin juna, tace”Sir nazo ma da labarin wacce take faɗama sunan da bakaso ne…” Cikin fushi ya daka mata tsawa!! Ya matsa gefe yace”kiyi gagawar fiti tun ban canza maki kamanni ba bana son gulma natsani mace maras kamun kai, get out my Office.” a tsorace ta fita jikinta na rawa. Kamal ya dafe kansa yazo ya warci key ɗin motarsa ransa a mugun ɓace ya fito ya rufe kofar ya fito. Anan farfajiyar makaranta jikin wasu bishiyoyi ya hango Mubina ita da yarinyar da ya kora yanzu, idanu ya zaro cike da mamki, Mubina tana magana tana dariya, tana riƙe da hannunta, kansa ya kauda ya nufi gun motarsa, yana maijin tsanar yarinyar a ransa, yana ciza lips ɗinsa. Yana zuwa ya buɗe motar ya shiga ya fizgeta da karfin Gaske, ya fice daga makarantar. Sageer da fitowarsa kenan daga aji ya hango Kamal ya fita, ya girgiza kai hayaniyar su Mubina ce tasa Sageer ya juyo ya kallesu ya saki murmushi yana faɗin “Baby Mubina kin haɗu ta ko ina Allah ya mallaka min ke. A matsayin uwar ƴaƴana.” ya faɗa yana kallonta har yayi nisa kafin janye idanunsa daga kallonta gudun kar ta ganshi ta tsira masa rashin kunya dan so yake a sannu ya janyota jikinsa. *KAMALUDDEEN KAN GIWA MAI NASARA COMPANY* Nan naga Kamal ya cinna hancin motarsa ciki, yana shiga ya nufi gun parking yay parking ya fito wayoyinsa hannunsa fuskara a sake ɗauke da sihirtaccen murmushi, nan ma’aikata suka fara kwasar gaisuwa yana amasawa cikin sakin fuska ya saka kai ciki.
Add Comment