Gidan Aunty Hausa Novel Complete
GIDAN AUNTY
A heart touching love story
Story & written
By
Aysha galadima
( mss Lee)
UK WRITERS (Unique kingdom writers)
Sabuwar marubuta masu tafiya da saban salo me kayatarwa.
Littafina kirkirarran labarine banyi dan cin zarafin wani no ko wata ba, duk Wanda labarina ya zo daya da nashi yayi hakuri rashin sani ne.
Yadda na fara littafinnnan a Sa’a Allah ya bani ikon kammalashi..
Bismillahir rahmanirrahim…..
Paid book
Book 1
Free page
1
TAHEE!!! TAHEE!!! “Naam oumma “ cewar wata yarinya wacce kallo daya zaka mata kasan bazata wuce 16 to 17 years ba, ta fito daga cikin wata kofa da kallo daya zaka mata kasan daga kitchen take, sabida flour da ya Dan bata mata jiki.” Har hanxu baki gama kwabin ba , kinsan abbanku ya kusan dawowa kuma kinsan inyazo ya taddaku haka ran mune zai baci duka ko!”kiyi hakuri oumma na kusa gamawa TAHEER nake jira ya taimakamun …”bata kammala magana ba sukaji anshigo falan ko sallama babu, Mai da hankalinsu sukayi kan kofa . Wata yarinyace itama da bazata wuce 15 to 16 ba a tsaye sai faman ya tsine take kamar wata babba, kura mata ido TAHEE tayi dan jiranjin mai zatace, dan tasan zuwan ameerah ba alkairi bane. Kamar kuwa ta shiga zuciyarta , “maryam dake da TAHEE wai Kuzo inji abba…, bata kammala maganar ta ba sabida saukar marukan da taji a waje maban banta. Kuka ta saki mai kara tana jiyowa. Karo taci da TAHEER da TAHEERA a tsaye sai faman huci suke saki, TAHEER ne ya soma magana “sau nawa zan fada miki duk lokacin da Kika kwaso rashin kuryarki ki dunga ajje ta a waje kafun ki tako mana daki, mahaifiyar Tamu kike dan baki da kunya “, kuka kawai ameerah take dan ba karamun zafin marin tajiba, dafe kuncinta tayi dagudu ta bar dakin .
Akida Ta Hausa Novel Complete
Kallansu oumma tayi cikin hade rai,”sau nawa zan ja muku kunne kudinga hakuri da mutanan gidan nan, ko so kuke kudinga ganin raina yana baci” , kamar hadin baki TAHEER da TAHEERA suka ruke kunnuwansu ,”oumma kiyi hakuri bazamu sake ba “, Daman ta San halinsu, dungure musu kai tayi, atare suka saki dariya dan dama sunsan ba fushi tayiba.
Kamo hannayensu tayi tare da hadewa waje daya , TAHEE!! Naam oumma! TAHEERA ta amsa mata, maida kallanta tayi wajan taheer shima ta kira sunansa, amsa mata yayi shima yana kallanta. Numfashi oumma ta saki kafun ta soma magana cikin Sanyi , “ku kadai Allah ya bani, banaso kuna saurin fushinnan, inaso ko bayan raina kuzama masu kaunar juna kunji, ku zama masu hakuri da kawaici, Musamman Kai TAHEER , kafi saurin hawa”. Murmurmur taheer yayi tare da dan sosa keya, oumma kiyi hakuri, hararar wasa tasakar masa daman anan kafi kauri wajan bada hakuri. Kema taheera ki shiga taitayinki , hada ido Taheer da taheera sukai tare da hada baki , oumma kiyi hakuri bazamu sake ba .
Girgiza kai oumma tayi kawai, basuyi wata wata ba suka rungumeta, hado kansu tayi su biyun ta rungume a jikinta. Suna cikin zamannan sukajiyo bugun kofa da karfin gaske , duk mimmikewa sukai tsaye, bakowa bane face abba sai faman huci yake bayansa kuma mamy ce hannunta rike dana Ameerah sai faman cika take . Baiyi wata wata ba ya tsinkawa oumma mari, Maryam sau nawa zan fada miki ki fita harkar yata,me yasa bakyajin magana, Tom bari kiji na fada miki na gaji da wannan halayen naki, ki tattara kayanki kije na SAKEKI.
Kafun na dawo gidannan banaso naga fuskarki data yan iskan yayanki , sannan fuuu ya bar wajan. Shewa mamy ta saka toh maza maza azo abar mana gida tunda anzama bazawara, budar bakin ameerah sai cewa tayi da Yayan zawarawa sanin cewa ba mai tabata tunda uwarta na wajan , sai da mamy ta gama babatunta da zafesu tasss sannan takama hannun yarta sukabar wajan.
Zubewa umma tayi a kasa zuciyarta na faman ta farfasa ga kuncin da zuciyarta ke mata, fashe wa kawai tayi da kuka, TAHEE ma zubewa tayi a kasa tana kuka sosai, TAHEER ne mai dauriyar cikinsu yake lallashinsu, abun yayi masa ciwo sosai, asaki mahaifiyarsu agaban idansu dan basu da gata. Abbu nayi kewarka , ALLAH YAJIKANKA ABBU!! Shima sai ya fashe da kuka , haka suka kwashi kusan minti 15 suna abu daya , ganin sunki daina kukan Yasa oumma tsayar da nata kukan, tashiga lallashinsu.
Ganin sunyi shiru yasa ta mikewa, daki ta shiga ta tattaro musu Kayan sawarsu cikin jakunkunansu, sannan tasa taheer yasamo mata motar akurki dan kwashe mata kayansu, ba jimawa kuwa sai gasu, lokacin abba ya fita shiyasa mai akurkin ya shigo ya taimaka musu suka kwashe kayan.Mamy na labe ita da wata kawarta sai faman kwasan dariya suke , bayan sun gama kwashe komaine suka fito waje , oumma ta janyo kofar bangaransu Wanda ko cokali datasan natane bata bar musu shi ko daya ba.
Awaje ta tarar da mamy ta fito sai habaici take tana kwasar dariya kawarta na tayata, sabida rashin tarbiyya har ameerah ce ke kiransu zawarawa da yayan zawara wa uwarta na biyemata. TAHEER da TAHEERA kuwa suna gefe sun cika bamm ji suke Idan suka kama ameerah ba abunda zai hanasu lallasata .
Kamar oumma tasan abunda ke ransu takamo hannunsu suka fita , saida suka fita oumma ta fara tunanin ina zasu koma da zama.
Ba yadda ta iya dole su koma BUNKURE da zama , Wanda ba tsoran komawa take ba , aah yadda rayuwar yayanta Zata koma , batasan abunda zai kuntata wa yayanta, ganin tsayuwar ba mai anfani bace yasata yiwa me motar magana , bawan Allah bunkure zaka Kai mu nawa zan baka, 7k zaki bayar. Haba bawan Allah kadan duba mana, shikenan ku kawo 6k , kallan TAHEE da TAHEERA tayi da su shiga , ko wannansu jiki a sanyaye yashiga inda abunda suka tsana shine zuwa bunkure yadda ake gallazamusu suda mahaifiyarsu, ba adau lokaci ba suka fara tafiya kowa yayi jigum ba meyiwa wani magana kowa da abunda Ke cin ransa.
ASALINSU…..
➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
GARIN LAGOS
Wasu dankara dan Karan Motocine kefaman zuga gudu akan titi, duk Wanda yazo wucewa sai ya tsaya motocinnan sun wuce tukunna sabida tanbarin da motocin ke Dauke dashi .Duk uban motocinnan basu tsaya a ko ina ba sai a NAHYAN HOSPITAL, one of the best hospital in Nigeria , ba karamun hospital bane da kallo daya zaka masa kasan ba karamun kudi aka kashewa asibitin ba , Kai tsaye wajan parking space suka nufa , cikin wani irin slow motocin suka tsaya , Wanda hakan ba karamun birge masu wucewa yayi ba . Bude motocin akai , wasu blacks American ne suka fito daga cikin motocin ko wannensu sanye da bakin suit da sunglasses,fuskarnan ba fara’a kwata kwata , yayin da hannunsu ke dauke da bindigogi. Daya daga cikinsu ,Wanda ya kasance kamar ogansu ne ya nufa wata black tinted Lamborghini sai faman sheki da daukar ido take.bude kofar motar yayi sai da aka dau kusan 40 seconds kafun ya zuro da kafarsa Guda daya , tubarkallah Masha Allah , wani irin takalmine a kafarsa kamar na sarauta, fatar kafarshi sai faman daukar ido take, wacce take fara kal cikin takalmin kafarsa, an dau kusan 2 minutes kafun mamallakin kafar fitowa. Oh my god , tubarkallah masha Allah , tabbas Allah madaukakin sarki yayi halitta anan, ba kowa bane face TAHNOON , one of the youngest billionaire kenan, daga tsohon president zayed Al_Nahyan, irin su ake kira one in thousand,dan guy din ya hadu tako ina ba Karya. Sanye yake cikin kuftan sai faman maiko da daukar ido take , wacce ta kasance blue colour , bakaramun kyau tayiwa surar jikin saba , wacce ta kasance kakkar fa, kallo daya zaka masa kasan yana motsajikin sa ,farine irin asalin fari mai shegen kyau da tsari, yana dauke da wasu irin sexy eyes fari tass dasu, kwayar idanshi ba Baka bace sannan ba brown bace ,wasu irin idanuwane dashi mai ladaftar da makaryaci, Wanda idanuwansa ba karamun tafiyar da yan mata yake ba, hancinshi dogone ba irin over dinnan ba, amma dogone da yayi matukar yiwa fuskarsa kyau , bakinshi dan madaidaicine Wanda ya kasance pink colour , yana da saje a fuskarsa wanda ya hade da gyaran fuskarsa. Kallo daya zaka masa kasan irin mutanan nanne da ake Kira half cast , ta ko ina gayen nan ya hadu, cikin taku da kasaita ya fara tafiya , Wanda da yawa mutane suke wa kallan girman kai, musamman in ya hadu da kasaitarsa da muskilanci , dan ba karamun miskili bane na bugawa a jarida, amma a hakan ba karamun tafiya yake da imanin mutane ba .
Direct cikin premises din hospital ya nufa , duk inda ya wuce sai ma’aikata da majin yata sun gaishesa , daga musu hannu Kawai yake ,yayin da wadannan kattin ke binsu a baya , Daidai wata kofa naga sun nufa wacce ta kasance ta glass , kai tsaye wannan mutumin dazun ya bude masa kofa , lifter ce a wajan , shi kadai ya shiga wajen tare da wannan mutumin , yayin da Sauran suka tsaya . A flour 4 suka tsaya inda yakasance bakowa a wajan ( abun mamaki sai na tarar da wannan kartun sunja layi kamar masu jiran karban sadaqa😂), duk inda ya wuce sai sun Sara masa . Daidai wata kofa suka tsaya , anan ma wannan mutuminne ya bude masa kofa , tafiyar muntuna 2 biyune ya kaisu wata kofar , wata koface tsararriya a wajan me shegen kyau , direct cikin kofar suka shiga , babban office ne iya tsaruwa office dinnan ya tsaru, daga gefan hagunsa wasu dan ubansun cushion chairs ne masu shegen daukan ido ash colour , medium carpet din office din ma ash colour , daga gefan damansa kuma wani gadan duba marasa lapiya ne , daga inda kake kana iya hango table dinshi sai faman daukan ido yake ( irin na yan gayun nan😂), wajan sai faman daukar kamshi da sanyin freshener yake . Samun waje yayi kan daya daga cikin cushion chairs dinnan yayi tare da crossing legs, kallan mutuminnan yayi , cikin husky voice dinsa ya fara magana ,”zaki” shine Sunan da naji ya Kira mutuminnan Wanda in ba natsuwa kayi ba bazaka taba Jin mai have ba, “yes sir “Cewar zaki , “yaushene meeting dinnan”, “sauran few minutes sir “cewar zaki, jinjina masa kai kawai king Yayi tare da Mika masa wasu files karba zaki yayi tare da Sara masa tare da ficewa daga office din , duk wannan abun da yake fuskarshi kwata kwata ba annuri a ciki , ba a dau dogon lokaci ba daya daga cikin wayoyinsa ya fara ringing , sai da ta kusan katsewa sannan ya dauki wayar dake kusa dashi akan center table din gefenshi , UKTI shine sunan da ya bayyana akan screen din wayar , ajiyar nunfashi ya sauke ganin me kiran, dauka yayi cikin kamilalliyar muryarsa, “Assalamu alaikum”Shine abunda yace , ya dau sakanni kafun ya sake cewa komai, “masa’ul khair ukti( barka da Yamma yaya)”, bansan mai akace masaba amma ganin yadda ya natsu zai tabbatar maka da magana ce me mahimmanci suke tattaunawa,ya dau kusan 10 minutes yana wayar wacce ba abunda nakeji a ciki kasancewar cikin larabci yake maganar , baka Jin sautin muryarshi sai bakinsa dake motsawa, a haka zaki yazo ya tarar dashi , sannan suka dunguma zuwa inda aka kebanceshi dan yin meeting . Sun dau kusan 1 and half hours suna tattaunawa game da asibitin da kuma tsare tsaren da za a sake , basu sukabar NAHYAN HOSPITAL ba sai wajan karfe 5 na yamma, Kai tsaye NAHYAN ESTATE dake cikin BANANA ISLAND suka nufa .
GIDAN AUNTY
Dedicated dis page to my masoyiya ‘yar fillo ta zara’u our star lady ! I heart you
PAID BOOK
BOOK 1 📕
……………..بسم اللهً الرحمنً الرحيم
Free Page 2🦋
WACECE TAHEERA
TAHEERA yarinyace yar kimanin shekara 17 da dan biyunta TAHEER Wanda suke tsananin kama kasancewarsu yan biyu. Mahaifinsu Malam Mohammad nada wadatarsa kafun yasamu karayar arziki ,yarasu shekaru biyar baya , Wanda a kazo har gida akwai wa kisan gilla, kisan da haryanxu ba’a san ko suwanene ba , yana da mata guda daya me suna maryam wato oummansu taheera , haifaffiyar buzuwace fara tass da ita daga kasar Niger , anan suka hadu da mahaifin su taheera, Wanda yazo kasuwanci kasar. Mahaifiyarsu marainiyace wacce iyayenta suka rasu bata da kowa sai yayanta Wanda tun lokacin baya daya fita da daddare ba’a karajin labarinsaba .
Bakaramun wahala da gwagwarmaya suka shaba arayuwarsu , tun bayan rasuwar mahaifinsu taheera , kasancewar dangin babansu basu so ya auretaba, sun so ya auri yar dangi amma malam Muhammad ya nuna baya Santa maryam yakeso . Bakaramun wuya maryam Tasha ba a hannun dangin mijinta, babu me kaunarta sai KILISHI, wacce ta nuna mata so, ta tallafi yayanta har bayan mutuwar yayanta. Kilishi kanwace ga Malam Mohammad wacce suka hada baba dashi kasancewar shi kadai mahaifiyarsa ta haifa sai yan uwa . Ba karamun rawar gani ta taka arayuwarsu ba sabida irin yadda take temaka musu.Itace mace kwallinkwal da take fadar magana aji atake a wajan dalilin Auran wani hamshakin me kudi da take a Garin Lagos , shiyasa duk dangi akejin maganarta.Bayan shekara biyu da rasuwar Malam Mohammed, Malam bashari yanuna Yanasan auran maryam amma kememe maryam ta nuna bazata iya aure ta bar ‘ya’yanta ba , ba irin magiyar da Malam bashari beyiba har maganar tazo kunnen hajiya kilishi, sanin cewa bazata iya yiwa hajiya kilishi musu ba yasa ta Amince amma da Sharadin tafiya da yayanta. Wannan abu beyiwa Malam bashari dad’i ba amma haka yabar abun azuciyarsa. Hajiya kilishi ita ta dauki nauyin kome da kome na bikin maryam, tundaga kan kayan daki da sauransu, shiyasa ba karamun ganin girman matar takeji ba. Shiganta gidan bashari ba karamun wahala Tasha ba ita da yaranta, sabida tsangwaman da ake nuna wa ‘ya’yanta hatta abinci baya bawa ‘ya’yan maryam , ko ta tanbayeshi dalili kaitsaye ze ce mata sabida bashine ubansu ba. Wahalar dasu d’in da yake ne yasa maganar har taje kunnen kilishi Wanda takirashi tayi masa tatas harda i’kirarin zata kulleshi sannan ya saduda. Malam bashari yana da matarsa daya kafun ya auro maryam, asabe kenan wacce suke kira da mamy, mamy wata irin muguwar matace da batasan zaman lapiya , duk wani kulli kulli da tashin hankalin dake faruwa a gidan harda sa hannunta, da farko taso kullum su dunga danbe amma ganin maryam bata biye mata yasa ta canza taku take biyowa ta bayan malam bashari.yar ta d’aya Ameerah , yarinyace fitinanniya bata jin magana , ga rashin kunya a cikinta , Ameerah ta tsani y’ay’an maryam kasancewarsu farare tass kamar ka taba namansu ya fashe wani irin kyaune da su da baki baze musaltaba musamman tahee da take da asalin gashin buzaye har kugu, kasan cewar mahaifiyar su buzuwa mahaifinsu kuma bafulatani . Dalilin da yasa mamy da yarta suka dauki Karan tsana suka dora musu, dan ko ita mamin tasan maryam ta wuceta akomai amma sabida harsada da kyashi taki barinta, a haka har suka kwashe tsawan shekaru uku kafin yanxu rabuwarsu da Malam bashari.
➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
BANANA ISLAND unguwace ta wane da wane da ta amsa sunanta, a jere motocin suke tafiya , tun kafin ayi horn sojojin dake gadin first gate suka wangale musu kofa, tare da Sara musu, wata iriyar koface a wajan kallo daya zaka mata kasan ba Karamun makudan kudi aka kashe akanta ba, cikin kwarewa motocin suke tafiya harsukazo gate 2, nan din ma wani abun kallo ne , karamun titi ne a wajan sai kananan shukokin dasukayiwa wajan kwawanya, wajan bakaramun haduwa yayi ba , minti uku kacal yakaisu main gate din gidan inda yafi ko ina tsare sabida sojojin da ke ke waye da wajan .sanin Wanda yake cikin motar yasa ba bata lokaci aka wangale musu gate , wow !! Wow !! Wow !! Shine abunda bakina ke furtawa tunkan na karasa shiga nasan bakaramun gida bane wannan, dan filine a wajan me dauke da korayen shukoki inda yayi wa wajan kwawanyaw, babban estate ne me dauke da part part na musamman, duk inda ka kalla zaka ga alamun hakan sabida giftawar da masu aiki keyi lokaci lokacin cikin shigar uniform Dinsu . Kai tsaye wani babban glass building motocin nan suka nufa Wanda yakasance daban cikin buildings din , Daidai parking lot din building din motocinnan suka tsaya , ba bata lokaci duk suka fito daga motar, yanxun ma zaki ne ya bude masa kofa, sea da ya dau tsawan lokaci kafun ya fito gaba daya daga cikin motar, Sara masa sukayi a tare , ba Wanda ya kalla a cikinsu sai ma kara tsuke fuskarsa da yayi , a hankali ya fara tafiya cikin takunsa kamar bayasan taka kasa direct main door ya nufa , still zaki na biye dashi har cikin farlon da ya gama haduwa , direct wata kofa ya nufa , shi kuma zaki files din hannunsa ya ajje tare da ficewa gaba daya daga cikin building din.
WANENE TAHNOON
TAHNOON Wanda ake wa lakabi da KING , shalele kuma mafi soyuwa a wajan mahaifinsa , saurayine Matashi dan kimanin shekara 33 a duniya . Mutumne me matukar dukiya , kasaita da kuma miskilanci , bayasan raini ko kadan,baya shish shigi da shiga sabgar kowa , King babban muskiline Wanda da yawan mutane ke yiwa kallan girmankai, dan da wuya kaji yayi dogon magana da mutum, yawancin maganarsa da idone,king ya kammala karatunsa na likitanci a kasar turkey, a yanxu haka doctor ne shi babba daya karanci bangarori na lafiya, mutum ne shi me temako da sanin darajar mutane , amma in ba zama kayi dashi ba bazaka taba sanin hakan ba. King na da babban asibiti mai suna NAHYAN HOSPITAL, asibitine da yake temakawa marasa karfi duk da kasancewarsa asibitin kudi.wannan dalili yasa mutane ke ganin girmansa da kimarsa.Wanda duk Garin Lagos da ke wayanta zaka samu talakawa nazuwa Neman temako, Hakan yasa talakawa ke mugun sonsa da kaunarsa. Ko guri zaibi zakaga manya da yara na daga masa hannu tare dayi masa kirari, hakan yasa yayi suna sosai a fadin Nigeria dan ba Garin Lagos kawai yake temakawa ba , shiyasa da yawa masu kudi basa sanshi.
Mahaifinsa zayed-al-nahyan babban dan siyasane Wanda har mukamun shugaban kasa ya ruke , kuma hamshakin me kudine dayayi Fuce a kasar Nigeria gabaki daya da ke wayanta. Alhaji zayed mutumne adali me temakon jama’arsa,shiyasa ake matukar girmamashi, Adalin shugaban kasane Wanda har yanxu mutane suke kwadayin ya kara shugabantarsu.tsohon shugaban kasa yana da mata biyu, matarsa ta farko Itace hajiya suhaima, hajiya suhaima balarabiyar dubaice daga ita sai yayanta da kanwarta iyayenta suka haifa, macace me matukar miskilanci da kawaici, ga tarin dukiya da Allah ya bata , ga ilimin addini Dana zamani. Hajiya suhaima yayanta 4, Babban d’anta sunanshi mohammed amma Allah yayi mishi rasuwa shekarun baya da suka wuce sai ‘yarta ta biyu samreen suna kiranta UKTI , tayi aure yanxu tana saudiya ita da mijinta, sai king da autarsu zoya.
Matarsa ta biyu Itace hajiya kilishi , kamilalliyar mata wacce tasan ya kamata , macece me matukar wasa da yara , baruwanta Sabida kyautatawar ta yasa yawancin yayan gidan suna part dinta. Yar ta d’aya zulaiha wacce ta rasu tun tana yarinya. Suna rayuwane da familyn su cikin da Kaunar juna, tare da kakarsu dasuke kira Dada. Dada masifaffiyar matace gata da rigima ta bugawa a jarida, amma hakan besa ta wulakanta kowa ba , mutumce me temako da san jama’a, duk cikin jikokinta tafisan king duk da yawancin lokuta cikin rikici suke da ita , sai uncles Dinsu guda biyu uncle musaddiq da uncle salim, suma ko wannansu na rayuwa agidan tare da iyalinsa. Uncle musaddiq na da mata biyu hauwau wacce suke kira da mamy tana da ‘ya’ya 3 , kabeer , ihsan, sumayya sai matarsa ta biyu kubra ana ce mata momy tana da ‘ya’ya 2, haroon , firdausi(feedy). Uncle salim kuma matarsa daya mai suna amina ana ce mata aunty , basu da ‘ya ko daya sai ‘yar rikonta mai suna amrah, sabida duk dan data haifa baya dadewa suke mutuwa sai kanwarsu zarmeen wacce take aure a abuja da danta sha’aban.
Cigaban labari…
➰➰➰➰➰➰➰➰
Sai gabanin yamma suka karaso bunkure , lokacin ba karamun jigata sukayi ba, daidai babban gida na kasa daya kasance kamar family house suka tsaya , nan yara suka fara taruwa , ga yan birni , ga yan birni Wanda labari har ya fara karadewa . Nan mutanan gidan suka fara leke dan ganin ko suwanene, mutanan da suka ganine yasa su fara kuss kuss ana tuntsurar dariya , duk wannan abun da ake taheer and taheera na gefe, itama oumma duk jikinta a sanyaye yake harta kammala biyan mai mota kudinsa bayan ya temaka musu ya sauke musu kayansu . Tun a soran gidan suka fara cin karo da kwano, ga Shara a wajan. Oumma ce tayi sallama yayin da taheer da taheera ke bayanta,gaishe da su oumma da su tahee sukai ganin babu raya yanxu agidan ma duk an aurar dasu sai wa ‘inda ba a rasa ba, cikin izgili da wulakanci suka fara amsa musu gaisuwar tasu, tare da habaice habaice kowa na fadar albarkacin bakinsa . Wata tsohuwa ce ta fito daga wani daki gashin kanta duk yayi furfura da kar take iya tafiya,”wa nake gani kamar maryama da bankadaddun ‘ya’yanta, me ya dawo daku kuma , ko da yake daman kun saba zuwa ba nosis (notice).”to Nide wallahi babu ruwa na ga dakin kucan ba Wanda yake shigarmuku sabida hajiya kilishi ta Hana, amma wallahi bazaki takurani ba,”wai ma tsaya uban me ya kawo ku wannan karan kuma “, sun ku yar da Kai oumma tayi dan kwata kwata ta kasa magana ma, taheer da taheera kuwa ko wannansu hade rai yayi, in akwai abunda suka tsana a zagar musu mahaifiya. Tabe baki kaka ta bawa tayi” oh ni ‘yasu kujimun muna furci daga tanbaya sai ki wani fara sum sum da kai sai kace wata muna fuka”.tun tsirewa mutanan gidan sukayi da dariya, yayinda ko wa ke tofa albarkacin bakinsa. Ganin abun nasu ba me karewa bane yasa oumma mikewa tare da nufar dakinta Wanda ya kasance na hajiya kilishi ne mallaka musu,dakine a ciki da falo harda d’an kewaye da aka d’anyi mashi daga waje.Balefi kusan duk cikin gidan babu inda ya kai nasu kuma kilishi ta Hana kowa kwace musu acewarta wata rana in suka zo zasu dunga zama a ciki. Shigarsu cikin ‘bangaren sai da suka d’auki tsawan lokaci suna gyaranshi dan ba karamun daud’a yayi ba, suna gamawa duk sallah sukai suka mimmi’ke ga yunwa sunaji amma ba daman cin abinci sabida sunsan ko zasu mutu mutanan gidan bazasu basu ko ruwan shaba. Haka suka zauna oumma da tahee suna daki d’aya yayinda taheer kuma yake shinfida a falo dakin. Cab cikin dare lokacin da kowa ke hutawa wani ba’kin haya’kine ke tashi kad’an kad’an kafun daga baya wannan bakin ya bace batt…, can dakinsu taheera kuwa wani abune kamar silver yake faman she’ki a jikin taheera yayin da fatarta ke d’auke da wannan silver d’in kamar na maciji, kafun wani lokaci ta rikid’e tare da dawowa katuwar macijiya, ko munti 2 batai ba jikinta ya kuma dawowa Daidai, sai nan ta kara dawowa wannan macijiyar, daidai gabanin asuba jikinta ya dawo daidai, kwata kwata babu alamaun wannan macijiyar.
Add Comment