Yawon Ta Zubar Hausa Novel Complete
YAWON TA ZUBAR
©️FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).
☀️ ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION.☀️
LAMBA TA TAKWAS.
YA-KA-CI-KA.
Wani sansanyar ƙamshin turare ya daki hancinmu ni da ita hakan yasa muka juyo muna kallon in da wannan ƙamshin yake fitowa,
Wani ƙaƙƙarfan mutum ne ma’abocin zati da kwarjini da haiba riƙe da ƙofar ɗakin, waya kare a kunnen shi yana magana cikin Husky Voice,
Mijin Malama Hausa Novel Complete
Dogo ne samɓal mai siffar tsire,doguwar fuskar shi yalwace take da kakkauran gemu tare da ƙasumba da madaidaicin baki wanda ya ƙara fito da asalin kyawun shi,dara-daran ido wanda ya kewaye shi da siririn madubi ya ɗan zamo shi zuwa kan karan hancin shi mai kama da karas,
Wankan tarwaɗa ne shi a kala ya yi shiga wacce ta fito da asalin zatin shi, Voyel ne kalar sararin samaniya riga da wando har ina hango farar singiletin da ke cikin shi, sai hula Mu haɗu a banki(kalar sararin samaniya) da ya kafa wacce ta ƙara ma fuskar shi kwarjini,
The face looks Familiar tabbas,amma na rasa in da na san shi,ga nin yana kusanto mu yasa na yi saurin yin ƙasa da saboda kamani da ya yi ina bin shi da kallo tattakowa ya yi a ƙasaice har ya iso daf da gadon da nake kwance,
Cikin rawar jiki Nas ɗin ta fara gaishe shi,da hannu ya yi mata alamun ta fice ta ba shi guri a tare da ya amsa gaisuwar da take mi shi ba,jiki na rawa ta fice ya bi ta da wani matsiyacin kallo,
Dawo da kallon shi gareni ya yi ganina zaune daram akan gado ya ce”I Thank god da makuɗan kuɗaɗen da na kashe a kan ki ba su tashi a banza ba tunda da alamu za ki warke za kuma ki biya Ni duk kuɗaɗen da na kashe ko ficika ba zan yafe ba.”
Jin ya dasa aya yasa na ɗago ina kallon shi a sace cike da mamakin rashin imanin da mutumin Na ce”Kai ne wanda ka kaɗe ni ka kawo Ni asibiti?”
“Sam ni ne dai ɗan siyasar da ke burin mallakar wannan jahar tamu,Sunana Ataka Adamu tsohole,na san sunan ba baƙo ne ga duk ɗan jahar nan,ba ni ne wanda ya kaɗe ki ba,wata mota ce ta kaɗe na wani faƙirin talaka yana bigeki ya tsere,hakan ya yi daidai da isowata gurin da jama’ata,
take na yo kan ki bayan wasu mata sun suturce jikin ki da sutura,na sa hannayena masu matukar tsada na cicciɓe ki zuwa cikin motata tare da kirar motar asibiti domin a baki taimakon gaggawa,sun iso da wuri suka sungume ki zuwa cikin nasu motar nan take na umurce su da su je su yi miki duk abinda ya kamata zan ɗauki nauyin komai,ban yi hakan dan ceton rayuwar ki ba na yi hakane saboda dukkanin wani motsi nawa a cikin wannan jahar yana tafin mutane dan haka na cicciɓe ki ne dan shi ne matakin mallakar kujerata dan daga ganin ki daga ƙauye kika fito kuma zan yi amfani da ke dan samun kuri’ar mutanen ƙauyenku amma fa bayan na ɗare zan fanshe.
Take kuwa kwalliya ta biya kuɗin sabulu dan Ƴan Media dake tare da Ni tuni suka baza hotunan ɗaukar ki na yi cikin jini domin nuna ma duniya Ni mai tausayin talakawa ne,
sai dai fa ba nan gizo ke saƙar ba A-Taka ba ya yafiya ko da ƙanƙani sannan na san muhimmancin kuɗi fiye da tunanin mai tunani, saboda wani abu na musamman na rasa ka fin na same su dalilin hakan ya sa duk kuɗin dana kashe mi ki zaki zo ki biyani.
Hawaye na ji na sauka akan kuncina ganin irin yanda tawa ƙaddarar take,sai dai mamakin yanda mutane suka dawo marasa tausayi yanzu lamarin ya daina firgitáni dan haka cikin rawar murya na ce”Da me zan biyaka bayan ko ficika ban da shi yanzu?”
“Lokaci ne kaɗai zai sanar da ke da mai za ki biyani babban gargaɗina dai gareki kar ki sake ki ce zaki tsire,dan na zama miki inuwa ina tare da ke a kowani motsi naki,f,kar ki kuskura ki ketara umurnina saɓanin hakan za ki gamu da babban hukuncin da sai kin yi danasanin haifar ki da aka yi.
Ɗago idanuwana da suka ɓaci da hawaye jage-jage na yi ina kallon cikin idon shi hango iyakar gaskiyar shi yake faɗa yasa na yi saurin kauda idona daga kan shi,tabbas na yi gudun Gara na faɗa ma zago da na san haka rayuwa zata riskeni tabbas da ban baro ƙauyenmu da niyyar guje ma dukan Adayina ba.
Wani irin tafiya yake kamar wani mayunwacin zaki da ya hango abincin shi kafin ƙiftawar gira da bismillah har ya iso gareni ya ajiye min takarda akan cinyata ya juya cikin takun faɗi,
Bin takardar nake da ido na gagara sa hannu in ɗauke ta balle har in ga mai ta ƙunsa na yi jigum ina tuno mawuyacin halin da na tsinci kaina sai dai isar shi bakin ƙofa ya sa shi jiyowa ya ganni zaune kamar an da sa ni ce wa ya yi”Na san ba karatu kika iya ba, dalilin hakan yasa zan miki bayani dangane da abin da takardan nan ta ƙunsa.”
Sauke nannauyan ajiyar zuciya na yi bai jira ce wa ta ba ya ce”Ƙiyasin adadin kuɗin da na kashe miki ne tun daga ranar da na kawo ki har zuwa ranar da zaki bar asibitin nan,na baki su a rubuce ne dan ki san ba ƙananan kudade na kashe miki ba, sannan wannan tattaunawar da muka yi tsakanin mu da ke ya zama sirri matuƙar kika bayyana shi ga wani a ranar zan raba ruhinki da gangan jikinki ta hanyar sawa a miki allurar mutuwa ki mutu.”
Sannan daga yau ki daina magana da kowa kar tsautsayi yasa ki bayyana musu sirrina,ko da kuwa abokan hamayya sun Turo ƴan jarida kar ki amshi gayyatar su k did i make myself clear?
“Yes Sir.”na furta hakan cikin sanyin murya.
Kallo ɗaya ya min ya san na tsorata da al’amarin shi dan haka ya murmusa har sai da fararen haƙoransa mai ɗauke da babban wushirya a tsakiya ya bayyana,
Tabbas sai yanzu na gane shi ne matashin ɗan takarar nan da fastocin shi suka baza birni da ƙauye dan daga barina garin Abuja na fara yin arba da manyan hotunan shi a jikin allon talla da falwaya na mashigar garin namu ashe shiyasa a farkon ganina da shi na ga fuskar ta shi ba baƙuwa ba ce a gareni,tsintar kaina na yi da ce wa”Allah ya hana mi shi mulkin jahar nan alfarman Annabi matuƙar ba zai amfanar da talakawa ba”
Dago ido na yi na ga wayam ba shi ba dalilin sa ashe ya daɗe da ficewa tun bayan da ya gama tsorata ni da kalmomin shi daga ƙarshe ya haske Ni da ƙayataccen murmushin,madadin in ji tsanar shi ta tsartu a raina saboda ababen da ya faɗa min sai hoton Fuskar shi ta fara yi min gizo bayan na runtse idona ina hango kowani motsi na shi tun daga takun shi har yanda yake fiddo zance a yangace kamar mace,da yanda yake wani lumlumshe ido haɗe da murmushin da ya min ya yin ficewar shi, murmushin da zuciyata ta lakƙana mi shi suna da murmushin bankwana nake ƙara hangawa,daddaɗan kamshin turaren shi kawai na ke shaƙa wanda ya bar min tsarabar shi haka kawai na tsinci kaina da addu’ar Allah ya sa ko sau ɗaya ne in sake ganin shi a rayuwata.
Kunyar kaina na ji ya kamani tare da haushin kaina dan haka na yi saurin rufe fuskata da tafukan hannayena guda biyu.
To fah! ko dai Ya-ka-ci-ka ta kamu ne Fans,Ni fa bangane ba.
*** *** ***JAWAHIR.*** ***
Magana yake son yi amma harshen shi ya mi shi nauyi ganin yanda lokaci ɗaya halittar shi ta juye yasa na fasa ƙarar da ya yi daidai da shigowar yaranmu 3 cikin kayan makarantar Islamiyya,
Kallon yanda Baban su ke tari yasa Sukainat saurin rugawa ta je fridge ya ɗakko bottle wata mai sanyi,
Tana kawowa ta yi saurin balle murfin ta kafa mi shi bakin robar a baki ya soma kwankwaɗa cikin ikon Allah kuwa sai tarin ya tsaya cak sai maida ajiyar zuciya da yake yi kamar wanda ya yi gudun tsere,
Haɗa kan yaran shi duka su huɗun ya yi ya rumgume hawayen irin rayuwar da za su fuskanta na rashin wadata ga rashin sabo da hakan ya fara kwarara,
Suma yaran sai suka fashe da kuka duk da ba su san maƙasudin kukana da na mahaifin na su ma,
Ganin suna kuka yasa ya fara rarrashin su,ya miƙe cikin rashin ƙarfin jiki kawai sai ya koma ya zauna daɓas,
fahimtar hakan da na yi yasa na taimaka mi shi muka shige ciki na kwantar da shi akan gado,a niyyata in fita in bar shi ya huta sai dai jin ya kama hannuna ya ƙi cikawa yasa ya na rarrafa na haye kan gadon in da na tsinkayo muryan shi yana min tambayar da ta kusa raba raina da gangan jikina.
*Shiru kwana biyu baku ji ni ba,sabgogi da rashin ƙarfin jiki ya sani a gaba a gafarce Ni.*
Ummu-jidda.