Siddika Hausa Novel Complete

Siddika Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

SIDDIƘA

 

 

Ayush

 

 

_Elegant Online Writers_

 

 

_I seek for Allah’s guidance in writing dis book, Ya Rahman make my hands to write GOOD and detain it to write WRONG, Ya Shaafii grant Shifaa to d sick ones, Ya Rahman have mercy to d Dead ones, Ya Allah satisfy our needs. Ya Hayyu ya Qayyum_.

 

 

****

_Chapter 1&2_

 

Ta kai kusan minti sha biyar a titin nan amma babu alamar abin hawa sai motoci ne suke wucewa jefi-jefi, ga hadari yana ta haɗuwa a garin a hankali duhu yake mamaye haske yayin da bishiyu sai kaɗawa suke alamar iska tana sauka akan su, daga gefen da take tana kallo kwanar da take facing ɗinta wani gida taga an wangale gate ɗin shi mota tana fitowa, tafiya ta ɗan fara yi domin ta kaucewa kwanar da take kallonta, tafiya take a hankali a hankali har ta yi nisa da wannan kwanar kuma babu alamar abin hawan dai, motar nan ce tazo ta wuceta ita kuma tana tafiyarta cikin nutsuwa, a haka har wajen da ta tsaye da farko ya ɓace mata kasancewar tayi tafiya mai nisa.

 

Matsalar Mu A Yau Hausa Novel Complete

 

Tsayawa tayi tana lalubar jakarta sakamakon ƙarar wayarta da take ji a ciki tana ringing, ko da ta ciro wayar kiran yana dab da katsewa cikin sauri ta ɗaga tare da yin sallama tana mai kuma dakatawa daga tafiyar da take yi, tana cikin wayar ne motar nan ta dawo har ta wuceta kaɗan sai kuma matuƙin motar ya dawo dab da inda take a tsaye sauke glass gin motar yayi, a daidai lokacin kuma ta gama wayar tana shirin mayar da ita jaka.Fitowa ya yi daga cikin motar yana mai zagayowa inda take cikin kwantar da murya da kamala yayi mata sallama, Amsawa tayi cikin yanayin tsoro, ganin hakan ne a tattare da ita yasa ya ce mata“Ko kina buƙatar taimako ne?dan naga tin ɗazu baki tafi inda zakije ba and ga hadari a garin yana haɗuwa alamun ko yaushe ruwa zai iya sauka kuma kina ƴa mace shine naga bai kamata in wuce ba, shiyasa na zo na tambaye ki”. Cikin ranta take tunanin anya wannan ba mai satar mutane bane to shi ina ruwan shi da tafiyarta da rashin ta, amma wani ɓangare na zuciyarta yana ce mata ki faɗa masa halin da kike ciki wannan mutumin yana da kalar Mutanen kirki in sha Allah zai taimake ki. Shirun da yaji ne ya saka shi sake ce mata“Ba wai takura miki zan yi ba kawai dai u look so tiredness and in need of iconic”. Ce wa tayi“ Abin hawa nake jira”. Ce mata yayi“In ba zaki damu ba let me drop u at ur abode”. Shiru ta yi sai kuma cikin sauri tace“Ohk, No. 43 Lamiɗo Crescent”. Gyaɗa kai yayi sannan ya zagaya yashiga mota itama buɗe gidan gaba tayi ta shiga a zuciyarta tana karanto duk addu’ar da tazo mata saboda Allah ya kareta daga faɗawa cikin masifa.

 

 

 

 

 

Tana cikin addu’ar ta duk da addu’ar bata fito fili ba amma gaba ɗaya hankalinta da natsuwarta yana ga addu’o’in da take yi, ƙarar wayarta taji alamun kira jakar ta sauke daga kafaɗarta tana mai buɗewa tare da ciro wayar wadda kiran ya katse bin kiran tayi ana ɗauka tayi sallama,wayar tana kare a kunnenta idanunta suna kalle-kallen hanya, cewa tayi “Maama yanzu zan dawo in sha Allah”. Daga nan ta ajiye wayar. Basu k’ara tafiyar minti goma ba sai ga ta a ƙofar gidansu ajiyar zuciya ta sauke, sai da ta fita daga motar sannan ta leƙo ta window tace“Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi”. “Amin, mention not”. Shine abinda ya faɗa, daga nan ta juya ta nufi gate ɗin su ta fara knocking ba daɗewa mai gadi ya buɗe mata har zata shiga sai ta tsaya ta juyo taga ko yana nan ko ya tafi amma ganin shi tayi bai tafi ba ɗaga mai hannu tayi alamar waving shima hakan yayi mata sannan ta juya ta shiga cikin gida shi kuma tana shiga ya ja motar shi ya tafi.

 

 

 

Tana shiga a parlour ta samu Maama wacce tana tsaye da waya a hannunta, cikin sauri ta k’arasa wajen Maama tana rungumeta tare da cewa “Finally Allah ya dawo miki da ni lafiya Maamata”. Maama tace “Alhamdulillah sannunki *SIDDIƘA* Allah ya tsare ki,in sha Allah next week tare da Zainab zakije dan hankalina baya kwanciya ko kad’an idan kika tafi ke kaɗai duk da Allah ne mai tsarewa amma mutum ma dole ya kula”. Siddiƙa tace “To Allah ya kaimu ko dan ki samu natsuwa zamu tafi tare”. Maama tace “Yawwa, now go and refresh urself after that sai kizo muyi magana”. Da to Siddiƙa ta amsa sannan ta wuce sama domin ta yi abinda Maama ta umarceta.

 

 

 

 

_A week later_

 

At precise lokacin da ya ganta wancan satin haka yau ma, sai dai yau su biyu ne, kuma garin babu hadari cikin sauri ya zo ya wuce su ya shiga kwanar su ya danna horn mai gadi ya buɗe ma sa yana shiga yayi parking motar ya fiton ya nufi gate ya fita a daidai kwanar ya tsaya kuma yana facing ɗinta dan shi yana daga tsallake itama haka, kamar da wasa ta ɗaga kai ai kuwa sai suka haɗa ido cikin wani irin yanayi suke kallon juna, ɗan zare ma sa idanunta tayi, murmushi yayi yana mai shirin tsallakowa dan ya iso garesu. Cewa tayi “Aunty Zainab kinga wanda nake faɗa miki”. Daidai lokacin ya ƙaraso wajen su, Gaishe da Aunty Zainab yayi cikin ladabi amsa mai tayi cikin fara’a, Siddiƙa ma ta gaishe shi amsa mata yayi tare da faɗin “How’s ur work? ”. Da tarin mamaki ta kalle shi sai kuma tace “Alhamdulillah”. Daga nan tayi shiru shi kuma Aunty Zainab ya tambaya abin hawa suke jira ne ko kuwa wani abun suke so, Aunty Zainab tace masa yanzu za’a zo ɗaukar su, bata gama ba shi amsa ba mota tayi parking a gaban su, Sallama suka yi mishi sannan suka shiga motar kamar ranar nan haka yau ma aka yi ko da Siddiƙa ta shiga motar sai ta juyo suna haɗa ido ta kalle shi sai ta ɗaga mai hannu shima hakan yayi mata daga nan suka tafi. Tsallaka titi yayi ya shiga gida a zuciyar shi yana son ya san wani abu dangane da wannan _Classy dame_ ɗin dan tin ranar da ya fara ganinta ya saka mata wannan sunan *_(Classy-dame) _*.

#Comment&Share

#SIDDIƘA(a true life story & an extremely pleasing nvl).

#Ayush

Post a Comment

Previous Post Next Post