Nagartaccen Miji Hausa Novel Complete

Nagartaccen Miji Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Nagartaccen Miji Hausa Novel Complete

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

 

F.C.W.A

 

 

Writing by Fatima Sani Abubakar

(Ammieyn Amatullah)

 

 

GODIYA

 

Dukkan yabo da godiya su tabbata ga ubangijin talikai tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu annabi muhammad da alayen shi da sahabban shi har izuwa ranar tashin ƙiyama.

 

 

GARGAƊI

 

Ban yarda wata ko wani su yi amfani da wani ɓangare na wannan labari ba wannan labari mallakin marubuciya ne Duk wanda labarin yayi shige da labarin shi/ta arashi ne

 

DEDICATED TO

 

MY HASKEE

 

 

Na gaisheki

 

Mom mashkur

 

Haziƙar marubuciya gaskiya alƙalaminki abin kwatance ne alƙalaminki akwai faɗakarwa niahaɗantarwa kina bamu nishaɗi na jinjina miki. Littafin ƴar zaman wanka yana bada nishaɗi.

 

 

GAISUWA TA MUSAMMAN

 

Aisha Aliyu

 

Teema sabo

 

Hafsat lawan

 

Salma Abba Abdullahi

 

Hussaina Muhammad auwal

 

 

NAGARTACCEN MIJI

 

BOOK 1

 

1️⃣to2️⃣

 

Alhamdudilllah an ɗaura auren Aisha muhammad da Aliyu Abubakar akan sadaki dubu ɗari ladan ba ajalan ba sautin da kunnena ya jiyo min kenan ban san lokacin da na saki uban ihu ba tun daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sai farkawa nayi na ganni a kwance bisa gadon asibiti adda ce kawai ke zaune kusa da ni humaira kin farka sannu kai kawai na ɗaga mata hawaye na biyo idanuna kiyi haƙuri humaira babu wanda ya isa ya zaɓawa kansa mijin aure muna tamu allah yana nasa kiyi haƙuri ki karɓi zaɓin kakanki mahaifinki.

 

Ayi Min Adalci Hausa Novel Complete

 

Sai kiga rayuwar ta yi miki kyau amma duk wannan tashin hankalin ba zai kawo miki mafita ba.Humaira ina kika kai hankalinki ina kika kai ilimin ki meyasa kike son fushin iyayen ki akan ki haba humaira soyayya hauka ce idan har kina son mu shirya da ke ki kwantar da hankalin ki ki karɓi auren aliyu da hannu biyu

 

 

Ko dan kiyi rayuwa cikin farin ciki a rayuwarki kin san illar fushin iyaye kuwa humaira ki gaya min menene aibun aliyu da bakya son shi. na miki alƙawarin muddin kika gayan aibun shi zan raba auren shiru nayi nidai a iya hangena yaya aliyu ba shi da wani aibu asalima shi mutum ne me nutsuwa ilimin addini ilimin boko sanin yakama baya son rashin kunya nikam dama rashin kunya a wajena babu wadda ban iya ba harda ta siyarwa nidai kawai adda wlh bana son shi na tsane shi shine silar rushewar duk wani farin cikin da nake cik…. ban ƙarasa faɗan abin da nake son faɗa ba naji saukar duka a bakina Mama ce da shigowar ta kenan ta kai min duka da sauri adda ta tare cikin nuna rashin jin daɗi tace haba mama akan wannan yaron duk kun takura rayuwar yarinya ga wanda take so kun ce ba za ku bata shi ba.

 

Kun yi mata dole ta aure shi amma mene na biyo yarinya har gadon asibiti kina duka gaskiya bana jin daɗin abin da kuke ma humaira mama shiru ta yi nikam kukana naci gaba da yi kamar ba gobe.

 

 

ASALIN LABARI

 

 

Malam Kabiru mai atamfa ɗan asalin garin kabo ne a ƙaramar hukumar yako gari ne wanda allah ya albarkace su da sana’o’i daban-daban mazauna garin allah ya yalwace ƙasar yankin da albarkar noma don duk shekara babu abin da ba sa nomawa sosai allah ya buɗawa malam kabiru a harkar noma duk shekara yana kawo amfanin noman shi nan kasuwar dawanau sosai allah yasa nasibi a kasuwancinshi yana da mata ɗaya Baba Hanne da yara biyar maza uku mata biyu babbar maca ce Harira sai Abubakar sai Muhammad sai Abdulkareem sai auta zainab.

 

Malam kabiru idan ya kawo amfanin gonarshi ya siyar yana yawan shiga kasuwanni ya yi sarin wasu abubuwan na amfanin yau da kullum ya tafi da su ya siyar daga baya sai ya koma siyar da atamfofi nan da nan allah ya ɗaukaka shi daga k’arshe ma sai ya taso gaba ɗayan shi ya dawo dala duk wanda yake zaune a kano yasan dala unguwa ce da ke da yawan jama’a unguwa ce da ke da ɗunbin tarihi.

 

 

 

Babban gida ya siya da wani ƙaton fili duk wanda ke zaune a kano yasan irin gine-genen dala da gwammaja da dai sauran tsofaffin unguwar kano sai dai yanzu da yake zamani ya canza ana sabunta gine-gine bayan dawowar malam kabiru da iyalan shi shago ya kama a nan kasuwar kwari atamfofi shaddoji da dai sauran kayan sawa ya zuba kuma alhmdudillah ya karɓu a cikin kasuwar malam kabiru mutum ne mai gaskiya da riƙon amana.

Sosai yake da abokan cinikayya da dama yaran shi gaba ɗaya ya sa su amakaranta arabi da boko a haka rayuwa take ta rafiya dai-dai gwargwado allah ya rufa masa asiri yaranshi mata daga secondry ya aurar da su harira tana aure a nan unguwar santali tana zaune da mijinta lafiya haka zainab duk lokaci ɗaya ya aurar da su, haka yaranshi maza da suka tashi aure a nan cikin gidan ya yankarwa kowa guri ya yi ginin shi Abubakar a can yako ya auro matarshi Zahira don auren zumunci ne shikuma muhammad ƴar katsina ce ya aurota nusaiba mace kyakkyawa mai sanyin hali abdulkareem ƴar gwammaja ce yake aure Fa’iza shikam bai dace da mace ba don macece me hassada ga ganin ƙyashi, a haka allah ya bawa zahira haihuwa ta haifi ɗanta namiji akasa mishi aliyu babu jimawa kuma nusaiba itama ta haifi nata ɗan Mustapha tun daga lokacin kuma haihuwa ta buɗe a gidan sosai fa’iza ta ɗan jima kafin ta haihu ta haifi mace tun daga lokacin ta dunga haihuwa a kufi a kufi bayan wasu shekaru family ɗin malam kabiru ya cika da ƴaƴa sosai don zahira(addah) bayan aliyu tana da yara shida Mas’ud, usman, kabir (malam)me sunan kakanshi kenan suke kiran shi da malam karima,alima amina

Nusaiba(mama)Bayan mustapha tana da hannatu (amira)saboda sunan kakarta taci, sai N’aima sadiya sai auta aishatul humaira yaranta biyar kenan, fa’iza bayan maimuna ta haifi zainab sai ɗan autanta abdulhakeem.

 

 

Gaba ɗaya ƴaƴan malam kabiru kasuwanci suke a kasuwar kwari suna da shaguna a kasuwar na kansu Allah yarufa musu asiri daidai gwargwado kuma sun tsaya akan yaran su sun basu tarbiyya da ilimi dai-dai iyawarsu yanzu haka mustapha yana aiki da asibitin aminu kano shi kuma aliyu laccara ne a aminu kano college of islamic and legal da ke nan kano

mas’ud yana aiki anan outopedic usman kuma kasuwanci yake a kasuwar kwari yana da shaguna da dama kabir yana aikin soja a nan kaduna ranar da na sanyawa baƙar rana zaune muke gaba ɗayanmu ƴanmatan gidan a palon Inna hira sosai muke baba malam ne ya shigo da yake haka muke ce masa zama ya yai aka ci gaba da hira da shi kamar wanda yake ya jiran haɗuwar mu ya kalli amira ke maza kije sashen iyayenki kice ina neman su gaba ɗayan su har iyayenku mata ke kuma humaira maza kije ɓangaren yayyenku maza kice su same ni anan to nace tare da miƙewa ɓangaren samarin gidan na nufa da yake lokacin zafi ne kuma dare ne duk da akwai nefa haka be hana su fitowa brandar ɓangaren nasu sun zauna ba.idan kaga yadda suke wasa da dariya za ka ɗauka dukan su sa’o’in juna ne saɓanin yaya aliyu da yana zaune amma kuma akwaintakaddu a gaban shi da alamar na test ne gaba na ne ya faɗi tun kafin na ƙarasa sakamakon hango sunana da nayi manne jikin takadda alamar test ɗinmu ne na ɗazu zai makin sallama nayi musu sannan na gaya musu saƙon baba malam gamunan zuwa cewar”yaya mas’ud juyawa nayi naci gaba da tafiya falon inna na koma babu jimawa sai gashi duk sun hallara baba malam ne ya buɗe taro da addu’a sannan ya fara jawabi to alhamdudillah allah ya kawo mu lokacin da nake jira da raina da kuma lafiya ta ba tare da nabar wasiyya ba kamar yadda nasha sanar da iyayenku to yau ku ma na zaunar da ku na jaddadda muku abin da baku sani ba na kuma zartar da hukuncin da ko iyayenku ba su isa su ce min a’a ba bani da burin da ya wuce naga jan zuri’a ta a haɗe kuma awaje ɗaya to alhaɓdudillah dukkaninku ga ku nan maza da mata don haka naga ya dace na ƙara ƴarfafa zumuncin dake tsakaninku ta hanyar ƙulla auratayya a tsakaninku kuma wallahi kun ji na rantse duk wanda bai karɓi zaɓina ba babu shi babu zuri’ata sai dai ya nemi wasu ahalin amma ba dai ni ba. shiru kowa yayi gabanmu na dukan tara-tara kowa na jiran tsammanin warrabika.

 

Kai aliyu kaine babba don haka ta kanka zan fara kamar yadda na lura bakwa haɗa inuwa da himaira na yanke hukuncin haɗa aurenka da ita jinayi kaina ya mugun sarawa bansan lokacin da na fasa kika haɗe da ihu ba nace”ni wallahi baba malam bana son shi ina da wanda nake so kuka nake sosai kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa takaici ne ya kama mama ta kaimin duka tare da cewa” don ubanki rufewa mutane baki mara kinya kin ji shi aliyu yayi magana shi da aka cuta aka haɗa shi da ke fitsararriya adda ce ta janye ni daga kusa da mama tana lallashina kuka naci gaba da yi yaya aliyu ko ɗagowa bai yi ba bare yace wani abu. kai mustpha na’am baba malam kana jina ko eh ina jinka yace” cikin in’ina ga karima nan ita na baka amatsayin matarka mas’ud ga sadiya nan ita na baka matsayin matarka wani sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyar masoyan guda biyu waɗanda suka jima cikin begen juna ɗago kai suka yi tare da sakarwa junan su murmushi samarin ne suka ɗau shewa sai a lokacin suka farga cikin jin kunya sadiya ta sunkuyar da kanta kabir na’am ga na’ima amatsayin matarka godiya nake baba malam na’ima ce ta zabga masa harara usman kai kuma ga maimuna nan na baka matsayin matarka Mami ce tace”gaskiya wlh babu wanda ya isa ya yiwa ƴata auren dole a barta ta samu wanda take so dady cikin zafin rai yace ke fa’iza karna sake jin bakinki akan maganar nan wlh idan ba haka ba sai nayi mummunan saɓa miki shiru tayi don tasan halin shi ku kuma sauran na baku nan da wata uku kowa ya fito da miji kai kuma abdulhakeem kasan baka kai lokacin aure ba.

 

Muhammad rufe mana taro da addu’a rufe taron yayi kowa ya nufi sashen shi zuciya cike da zullumi muasamman ni don kuka kawai nake ɗakin inna na nufa don idan na koma sashen mu mama sai ta min faɗa in banyi wasa ba har da duka don naga sai harara ta take saboda nace”bana son yaya aliyu kan gadon inna na faɗa kuka na saki me cin rai yanzu duk irin son da nakewa Mahmud ya tashi a banza raba mu za’a yi wlh bana son yaya aliyu mezan yi da shi ko me za’amin bazan aure shi ba mutumin da baya sona kullum kushe ni yake kullum baƙar magana ce tsakanina da shi inna ce ta shigo lallashina take haba humaira mene abin kuka a nan yanzu ke kin zaɓi bare akan ɗan uwanki menene aibun aliyu meyasa bakya son shi baki ji kunyar addan ki ba duk son da take miki ai be kai son da takewa ɗanta ba shine kike kallon cikin idanunta kike faɗin bakya son ɗanta a tunanin ki bata ji haushin abin da kika faɗa ba tura baki na yi nace” inna nifa wallahi bana sonshi kema kin san mahmud ne zaɓina ba wannan me fuskar shanun ba. shiru inna ta yi min ta juya baya taci gaba da baccinta nikam saƙa da warwara naci gaba da yi damuwa duk ta addabi zuciyata wayata na janyo ganin tana haskee alamun kira ne ya shigo ɗagawa na yi nasa wayar a kunne sallama akamin amsawa nayi babyna me yake damunki naji muryarki kamar kinyi kuka babu komai my lovly kin tabbata cewar mahmud eh in sha allah gobe ina nan tafe tom nace”cikin sanyin murya anya babu abin da yake damunki nace” babu bacci kawai nake ji to ki kwanta da safe ma yi waya.

 

 

Duk yadda naso bacci ya ɗauke ni abin ya gagara tunani na ta yadda zan rusa wannan mugun baƙin ƙullin auren da baba malam ya ƙulla gaba ɗaya tunani na ya tsaya ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba sai asuba da inna ta tayar da ni na tashi da yake ina hutun sallah kuma bani da lacca da wuri alwala na ɗaura kamar yadda ya zamar min al’ada ko ina period to sai na ɗaura alwala komawa na yi na kwanta bacci ne me nauyi ya ɗauke ni sai kusan goma na farka wanka na yi ko break ban tsaya yi ba na nufi ɓangarenmu da sallama na shiga palon mama ce zaune bisa kujera me cin mutum ɗaya tunda ta ɗaga kai ta kallen bata sake kallon inda nake ba.

 

Zama na yi cikin tura baki kamar yarda ya zama ɗabi’ata mama ina kwana nace da lafiya ta amsa tun daga haka taja bakinta tayi shiru zama na yi na kusan minti talatin kafin abba ya fito gaishe shi nayi ya amsa ba tabo ba fallasa tea kawai na haɗa nasha na kwanta ganin babu abin da ba’ayi na aikin gida ba dama nayi tunanin haka.

 

Don su anty hannatu ba su jirana idan banga dama ba Ina sane nake ƙin fitowa daga ɓangaren inna na jima amma babu wanda yake kula ni,ko jira nazo nayi wani aiki lokacin su anty hannatu sun dawo ƙur’anin da ke hannunsu na kallah hakan ya tabbatar min karatu suka je gaishe su nayi kamar yarda mama ta koya mana gaishe da na gaba da mu, anty na’ima ce tace” wlh zan ci miki mitunci zan miki duka a cikin gidan nan yau baki da lacca da kike zaune kina chating ba’a isa da ke ba kin raina mutane ko mama dake zaune tace”rabu da ita na’ima kin nunan ban isa da ke ba na zuba miki ido naga za ki shirya ki wuce makaranta shine kika kunna waya kike chating shiru nayi ina tura baki nidai anshiga rayuwata wlh duka anty na’ima ta kawon da gudu na shiga room ɗinmu na hau shirin tafiya school ba dan raina ya so ba.

 

share and comment.

[02/05, 11:25 am] +234 903 028 3375: FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION

 

FCWA

 

 

K’UNGIYA D’AYA TAMKAR DA DUBU.

 

 

NAGARTACCEN MIJI

 

 

 

LITTAFI NA D’AYA

 

 

 

NA

 

 

 

 

FATIMA SANI ABUBAKAR

 

 

(AMMIEYN AMATULLAHI)

 

 

DEDICATED TO HASKEE

 

3to4

 

 

D’aki na shiga shiryawa nayi cikin riga da sket na wani material me kalar blue black da pink sai pink mayafi da pink shoes and back pitowa nayi a ciki-ciki nayiwa mama sallama,

 

 

b’angaren inna na nufa a falo na tarar da ita tana kallon tashar aljazeera zama nayi kusa da ita kamar zan yi kuka kallona tayi tace”ina makarantar ke kullum bakya jin magana makarantar ma sai ana fama dake tun kina k’arama gashi har kin girma bakiyi hankali ba.

 

 

 

Cikin jin haushi nace”kema inna kin bi sahun su mama baki da aiki sai fad’a kamar baba malam ni wlh duk kun saka ni a gaba daga jiya zuwa yau kawai saboda nace” bana son yaya aliyu Wlh da gaske nake bana sonshi gwara tun wuri ku warware wannan k’ullallen auren da ake shirin k’ak’aba mini shi tun da kinsan ina da wanda nake so idan kuma kun na ce wlh babu ruwana ehe.

 

 

 

 

 

Na fad’a ina mik’ewa zan fita dama abin da ya kawo ni part d’in inna kenan kuma na fad’a ko ba komai sak’ona zai isa kunnen mutum biyu yaya aliyu da baba malam.

 

 

Komar dani inna ta yi ta zaunar humaira ta kira sunana har sau uku banza nayi duk da ina jinta amma ban amsa ba don duk wani abu da zan fad’a nagama fad’a burina infita shima yaya aliyun zamu had’u da shi,

 

 

 

Inna nifa tafiya zanyi makaranta naga kin janyo ni dak’uwa tayi min ke dan ubanki meyasa bakya jin magana kullum rashin kunyarki k’aruwa take wlh badan nasan Nusaiba ce ta haifeki ba kuma a gida wlh da a asibiti ta haifeki da nace” ke ba jininta bace ke kullum bakya ganin girman kowa to wlh bari ubanki ya dawo zan gaya mishi duk cin mutuncin da kika yi min kuma aure babu fashi tsakaninki da gadanga y’ar jakar uba ana miki gata bakya gani tashi kibani waje fita nayi ina gunguni don wlh nayi alk’awarin kowa sai ya gane antab’a humaira babu wanda zan ragawa.

 

 

Ina fita harabar gidan naci karo da yaya aliyu hucewa nayi ta gabanshi na nufi get zan wuce ke banza nayi naci gaba da tafiya ta humaira ya kira sunana sannan na juya ina kallonshi had’a rai yayi kamar be tab’a dariya ba nima cin kunu nayi gudun kada yaga kamar zan ji tsoronshi .

 

 

 

Kizo nan nace”ko kin zama kurma ina jinka sai dai idan kaine ka zama kurma na fad’a a ciki-ciki me kika ce ya tambayen da alamar mamaki da alamar mamaki afuskarshi sarai nasan yaji me nace” ni babu abin da nace”girgiza kai yayi tare da nunan hanyar part d’inmu ki koma ki saka hijab kamar yarda sauran y’an uwanki ke sakawa idan za su tafi makaranta.

 

 

 

 

 

Hijab kuma to gaskiya malam babu ruwanka da rayuwata kuma ba hijab nayi niyyar sakawa ba.

 

Don haka ka fita aharka…. Kafin nak’arasa fad’ar abin da ke bakina naji saukar wani uban mari yaya mustapha ne cikin zafin rai yace” ke humaira rashin kunyar taki da ake fad’a ta wuce kan kowa ta dawo kan yaya aliyu ko dan kin ji baba malam yace”ya aure ki mara kunyar banza ai ancuci yaya me zai yi da ke fitsararriya ko kinji yace”yana sonki ke kad’ai ce kika fita zakka bazaki iya yiwa iyayenmu biyayya ba to wlh za ki sha bak’ar wuya wawuya ki wuce ki d’auko hijab ku tafi makaranta before jikinki ya gaya miki mara hankali sum-sum na wuce don yaya mustapha akwai zafi idan ranshi ya b’aci ba k’aramin aikinshi bane ya min duka da gudu na shiga cikin falo kan mama na fad’a ina ihun kuka kamar wadda aka yanka ke lafiyarki ta tambayen aunty na’ima ce tace”baki san halin wannan yarinyar bane harara na maka mata.

 

 

 

Mama ce ta sake tambayata mene yaya mustapha ne ya daken saboda nace”wa wancan mugun bazan saka hijab ba ture ni mama tayi daga kanta tare da cewa”mara kunyar banza tashi kiban waje ki kuma d’auko hijab Kafin ni da kaina na miki dukan tsaya,

 

 

 

Ihu na kuma saki ina kiran na shiga uku antsane ni kowa baya sona addah dake ta saurin fitowa daga part d’inta Zuwa namu ne ta k’araso cikin sauri tana tambayar lafiya meya faru?

 

 

Da gudu na nufi addah na rungume ta cikin kuka nace”addah yaya mustapha ne ya maren saboda wancan me shigowar ne yace” dole sai na saka hijab zan fita makaranta.

 

 

 

 

Kallon k’ofar falo tayi ganin aliyu ne ke shigowa yasa tayi murmushi tare da shafa kaina haba humaira kinsan babanku baya son kuna fita da mayafi wanda bai rufe miku jiki ba ke kuma bakya sa babban mayafi ya hak’uri maza d’auko hijab ku tafi makaranta Shi kuma mustapha zai zo ya sameni har gida dani yake zance,

 

Mama kam tab’e baki ta yi tace”addah dama ke kike biyewa shirman wannan yarinyar taki yanzu meye laifin aliyu daga baba malam yace”zai had’a su aure shikenan za ta d’agawa mutane hankali meye laifin yarona ni wlh an cuce shi da aka bashi wannan rasa kunyar yanzu inna ta gama sauken sababi.

 

 

Mama ta fad’a ranta a b’ace hak’uri addah ta bata sannan tace”dan allah maman yara ki bi min yarinya a hankali idan ba haka ba zan d’auke ta daga b’angaren nan gaba d’aya nidai da irin hirar nan na barsu a palo na d’auko hijabina pink na saka ban sake yiwa kowa magana ba na fita daga palon

 

 

Bakin get na nufa fita na yi daga gidan da k’afa na fara takawa bakin titi ko minti biyu ban yi ba motar yaya aliyu ta tsaya a gabana cikin had’e rai ya bud’en gaba kishigo ko ranki ya b’aci banza nayi mishi tunawa da nayi yaya mustapha zai iya fitowa daga gida a kowanne lokaci ne yasa na bud’e gaban motar na shiga tare da buga murfin motar da k’arfi duk da yana jina amma mugun miskilancinshi bai sa ya d’ago kai ya kalleni ba har muka isa cikin school har gaban venue d’in da muke lacca ya kaini sai da nazo fita sannan ya sanyawa motar key.

 

 

 

Ke cikin muryarshi mai rikitarwa yayi min magana amma ko gezau banyi ba don bana jin zan iya kallon inuwarshi ma bare kuma shi kanshi Ji nake kamar na shak’e shi kowa ya huta da d’an tsawa ya sake kirana nan ma na yi banza ina catting da al’ameen a waya.

 

Fisge wayar yayi ya ajiye a kusa da shi humaira duk da naji kiran har cikin jikina amma ban amsa ba.

 

 

Humaira ki shiga hankalinki duk wannan rashin kunyar da kike kinji na furta da bakina ina son ki to kisani kamar yarda bakya sona nima ba sonki nake ba hasalima kaf cikin zuri’armu ke ce yarinyar da bata kwanta min ba sakamakon bakya Ji baki da kunya ko kad’an badan ke jinin mama bace wlh da bazan yi biyayya ba amma kisani darajar mama kika ci har na kasa furta komai amma saboda baki da kunya har nake miki magana kina min rashin kunya bakya ragawa kowa ina jinki kina bawa inna sak’o ta bani ni da malam baba to na karb’i nawa saura Shi idan bakiyi wasa ba sai na b’allaki get out from my motor nonsense,

 

 

rank’wafawa nayi kamar zan gyara hijabina kawai na d’auke wayata har k’irjina yana bugar na Shi sai da na tabbatar na fita sannan nace” to idan ka tashi b’alla ni karka b’allani yarda zan d’oru mummuna kawai da fari kamar zabiya murmushi ne yaso sub’uce mishi amma ya kanne bai yi ba motar Shi yaja ya nufi office nashi cost biyu yake d’aukarmu general english sai kuma yake d’aukarmu nikhah and mirath.

 

 

Venue d’inmu na nufa cikin friend d’ina na zauna da yake sit d’inmu yana gaba kusa da nihla na zauna naulat ce ke tambaya ta na makara eh kawai nace” don yau haushin kowa nake ji bana son yawan magana har muka gama lacca lokacin tafiya gida yayi ban sake ba.

 

Ko da aka tashi ban tsaya jiran kowa ya zo d’auka ta ba.

 

Y’an unguwarmu na bi na koma gida ina shiga a palo na tarar da su aunty hannatu sannu kawai nace” musu na nufi d’aki wanka na yi naci abinci duk da yamma ta yi k’in fitowa nayi na kwanta a D’aki.

 

 

Tunanin yarda rayuwata za ta kasance nake muddin aka tilasta min auren mutumin da bana so kuma baya sona.

 

Bayan kowa a cikin gidan ya fahimci irin soyayyar da ke tsakanina da al’ameen anya kuwa anyiwa rayuwata adalci,

 

Menene laifin al’ameen da har baba malam yake k’inshi yake shirin raba tsakanin masoyan da suka d’au lokaci cikin k’aunar junansu hawaye ne kawai yake bin fuskata zuciyata azabar rad’ad’i kawai take min,

 

Shigowar anty zainab ce tasa ni mik’ewa zama nayi ina kallonta da mama ki me aunty zee za ta yi a d’akinmu matar da ba shigowa part d’inmu take ba.

 

Zama tayi kusa da ni humaira kina mamakin ganina a b’angarenku ko eh nace” cikin d’aure fuska kinsan me ya kawo ni wajanki kuwa a’a nace” ina ci gaba da share hawayen fuskata kina son al’ameen kuwa d’aga mata kai nayi don tambayar da ta yi mini ce ke k’ara karyar da zuciyata nikam a ganina duk wanda ya kwana a family d’in malam kabeeru me atamfa yasan da soyayyata da al’ameen,

 

 

Humaira na’am anty zee na amsa mata kina son na taimaka miki ki auri al’ameen d’inki cikin farin ciki na d’aga kai dafa ni tayi tare da cewa yawwa y’ar k’anwata, ki saurare ni da kyau.

 

Da farko kada kigayawa kowa zan kawo miki wani magani ki zubawa aliyu a cikin abinci daman anan part d’in yake yawan cin abinci da zarar kin zuba mishi ya ci shima zai nuna baya son auren kinga kema dama bakya so idan baba malam yaga aliyu baya so kema haka dole zai hak’ura yace al’ameen ya turo.

 

Sannan kici gaba da kula al’ameen don ba k’aramin so yake miki ba kinsan me nake so dake a’a nace” mata kada ki sake cewa” bakya son auren zan dunga kawo miki magani har afasa auren kinji d’aga mata kai nayi daga haka ta fita ni kuma naci gaba da kwanciya ban fita palo ba har bayan isha’i sallah kawai ke tasar dani haka babu wanda ya min magana.

 

 

 

Kiran al’ameen ne ya shigo wayata ina k’ofar gida ki fito to nace” tashi nayi na wanke fuskata na d’an shafa powder da listip na yafa mayafin abayar da na saka duk da ko rabin tulin gashin kaina bai rufe ba don ana gani plate shoe na saka red kasancewar abayar irin two colour d’in da ake yayi ce yanzu red and black sai mayafin red ne turare na me sassanyan k’amshi na saka a jikina nayi aunty na’ima ce tamin magana banza nayi mata don tafi kowa takura min da masifarta tun daga nesa al’ameen yake k’are mata kallo ganin yadda albarkatun jikinta ke motsawa kamar dagayya take motsawa,

Har sai da na k’arasa amma ya kasa d’auke idonshi akaina ta window na zagaya hure mishi ido nayi murmushi yayi my honey wannan kallonfa na fad’a cikin shagwab’a,

 

Dariya yayi tare da cewa”ai kece my baby kullum k’ara kyau kike kinganki kuwa kamar balarabiyar da tazo daga Quwait dariya muka yi gaba d’aya zagayawa nayi na zauna a front seat hira muke kamar babu abin da yake damun mu don har ga allah mantawa nake da wata damuwa idan ina tare da al’ameen becouse shi mutum ne me barkwanci mutum ne da idan har ya ganka cikin damuwa lallai zai yi k’ok’arin ganin walwala akan fuskarka yanzu ma haka ce ta kasance sai da ya tabbatar babu wata damuwa akan fuskata sannan ya tafi lokacin da na shiga duk suna part d’in inna da yake anan muke dinner ban shiga part d’in inna ba shirin kwanciya nayi na kwanta,

Na jima ina tunani kafin bacci ya d’aukeni.

 

 

Call or chat on watsapp 09166820615

 

Comment and share

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION

 

FCWA

 

 

 

NAGARTACCEN MIJI

 

 

 

 

NA

 

FATIMA SANI ABUBAKAR

 

 

 

(AMMIEYN AMATULLAHI )

 

 

Page 5to6

 

 

 

Tunda aka tsaida ranar bikinmu bana cikin nutsuwata,

duk wani tashin hankali nayi amma abin yagagara kullum cikin kuka nake ko naje school ba wani abu nake ganewa ba.

 

A irin haka muka yi exam lokacin yayi dai-dai watan bikinmu tashin hankali babu wanda ban shiga ba na rame iya rama zuwa lokacin al’ameen shine ya zamar mini d’an’uwa kullum cikin kwantar min da hankali da nasiha yake.

 

Akullum sai nayi yunk’urin barin gidan na tabbata idan naje gidan aunty zainab ba tsira zan yi ba.

 

Ganin kowa acikinsu son auren yake kowa gani yake baba malam yayi dai-dai da ya had’a aurena da yaya aliyu ita kuma umma harira tana santali ko na je can za’a san naje,

 

 

 

A b’angaren aunty maimuna kullum tana zaryar kawon magani nikam zuwa yanzu duk ba wannan ne a gabana ba damuwata yarda gaba d’aya mama bata kulani duk akan nace” bana son auren aliyu ta rantse muddin na rusa aurena da aliyu sai dai na nemi wata uwar ba ita ba abba ma baya amsan gaisuwata bare kuma yayyena.

 

 

 

Addah ce kawai ke sona a wajanta kawai nake jin dad’i sai sadiya dake tausaya min Yau umma barira tun da tazo gidan take zabga masifa ganin yadda na rame na fita daga hayyacina kaf cikinsu addah da mama rasa me bata hak’uri aka yi.

 

 

Mami kuwa sai k’ara zugata take akan kada ta yarda ayi aurena da aliyu tunda na nuna bana so kawai a fasa banza umma barira tayi mata da taga abin nata ba mai ka’rewa bane cikin fusata tace”faiza kimin shuru ba ina nufin afasa auren aliyu da humaira bane a’a damuwata ganin yarda ita humairan ta koma ne bata sake ma kowa magana ba don haushin mama takeji musamman da na gaya mata bata kula ni mik’ewa tayi ta shiga d’akinmu trolleyna ta janyo ta had’an kaya da d’an yawa ko b’angaren inna bata koma ba gudun ta hanata tafi ya dani.

 

 

Bata yiwa kowa sallama ba ta kama hannuna direct gidanta muka wuce umma barira bata rasa komai na rayuwa ba Alhmdudillah gida ne had’add’e tsararre fad’in had’uwarshi ma b’ata baki ne komai yayi daidai da tsarin gidan a main falo maka tarar da triple d’inta mata biyu sai namijin Hasina da haneefa sai haneef sa’annina ne kuma last born d’in umma kareema ne shiyasa jininmu ya had’u da nasu sosai.

 

 

 

manyan yaranta kuwa duk maza ne su uku ne Aminu Usman Habeeb duka sunyi aure da iyalansu dan sun girmi su yaya aliyu,

 

 

Zama nayi kusa da haseena tsokanata ta fara yi da amarya_amarya dak’uwa umma tayi mata haka yasa taja bakinta tayi shiru haneefa kam dama magana bata dameta ba sab’anin haseena sarkin Zuba.

 

Zamana tare da su haseena ba k’aramin d’eben kewa yayi ba jinayi dukkan wani damuwata babu bana tunanin wani auren dole da ake tunanin yi min su haseena basa min zancen aure saboda umma ta kwab’e su da yawan zancen auren haka babu wanda yazo daga gida da sunan nemana amma tana yawan had’a magunguna ta bani da sunan maganin sanyi gaba d’ayanmu har su haseena tasa ake mana guarantee jiki sosai naga na canza jikina yayi kyau duk da dama ni ba fara bace black beauty ce hakan yasa fata ta ta k’ara zama so glowing nazama abin sha’awa ni kaina bana gajiya da kallon kaina.

 

 

 

Sosai nayi mugun canzawa mu’amalata da al’ameen babu abinda ya canza sai ma k’ara shak’uwa da muka yi

 

Yau ta kasance laraba tun da na tashi gaba na ke mugun fad’uwa bana cikin walwala kamar kullum

 

Ko abinci ma da k’yar na samu naci

 

 

Fargaba ce kawai ke damuna duk narasa meke shirin faruwa dani

 

Wajan 1:00pm, sai ga aunty zee da yaranta kasancewar ita bata haihu da wuriba yaranta babban abbas sa’an aunty sadiya ne wadda nake bi sai macen sa’ata ce Nana sai k’anwarta binafa atak’aice y’ay’an aunty zee uku tana aure a Abuja mijinta ma’aikacin gwamnati ne kuma d’an kasuwa yana da kud’i dai-dai rufin asiri,

 

 

Da murnarmu muka tareta sai dai jin sunan da take kira na dashi ba k’aramin d’agan hankali yayi ba, a zuciyata na dinga nanata kalmar amarya kuma dama ba’a fasa aurena da aliyu ba kuma meyasa aunty zee tazo ita da su nana na tabbata wani abu me muhimmanci ne ke sa wa tazo da duka yaran Kallona tayi tare da nunan kusa da ita jiki babu k’wari na isa na zauna kusa da k’afafunta my dogheter da yake haka take kira na da Shi,

 

 

 

Na’am aunty intambaye ki za ki gayamin tsakaninki da allah d’aga kai nayi don zuwa lokacin babu bakin magana sai ido da nake bin kowa da shi kenan baza’a k’yaleni da maganar auren aliyu ba.

 

 

Kina jina my daughter meyasa bakya son d’an’uwanki meyasa kika zab’i b’acin ran iyayenki meyasa bazaki yi musu biyayya ba meyasa bazaki hak’ura da soyayyar al’ameen ba domin ki farantawa iyayenki da kakanninki rai.

 

 

Soyayya ta rufe miki ido kin manta irin d’awainiyar da iyayenki suka sha dake tun kina ciki har zuwa girmanki nayi tunanin za ki kasance y’a mesadaukar da farin cikinta saboda na iyayenta zuwa lokacin kuka nake sosai umma barira kam tuni da tabar wajan zuwa cikin d’akinta dake dawn stair bata tsaya sauraron abin da aunty zee ke fad’a mini ba ita ba aurenmu da aliyu ne bata so ba, ganin yarda duk na birkice ne ke d’aga mata hankali gashi baba malam kaifi d’ayane idan yace” eh to bazai tab’a canzawa ba, haka idan yace”a’a babu gudu babu ja da baya.

 

 

Kiyi min magana mana my dogheter kuka bashi da amfani cikin kuka nace”aunty nidai kawai bana sonshi ni al’ameen nake so daga haka na mik’e da gudu na nufi d’aki wayata na d’auka na kira al’ameen jin muryarshi nayi duk ta dushe kamar wanda yayi kuka arud’e nake tamabayarshi lafiya humaira ya kira sunana cikin fargaba nace” na’am humaira kiyi hak’uri allah bai nufa za mu kasance matsayin mata da miji ba, allah yayi ni ba mijinki bane kiyi hak’uri humaira ki karb’i zab’in iyayenki ki zauna da mijinki lafiya ina miki fatan alkhairi zan ci gaba da yi miki addu’a a kowanne lokaci amma bana tunanin zan so wata y’a mace bayan ke ina sonki humaira kiyi hak’uri yau aka tabbatar min ana kamunku ke da sauran y’an uwanki da gaske baba malam ba zai tab’a canza maganrshi ba nabarki lafiya humaira zuwa lokacin bazan iya musalta halin da na shiga ba nasan nakira sunan al’ameen daga haka bana iya tuna meya faru dani farkawa kawai nayi naga aunty zee namin firfita wani wahallallen kuka ne ya k’wace min ganin abin nake kamar a mafarki sannu humaira kiyi hak’uri mamanki ta ce” muddin baki kwantar da hankalinki kamar yarda sauran y’an uwanki suka yi ba babu ita babu ke idan har kika b’ata mata taro.

 

 

Kiyi hak’uri ga ruwa can a toilet kije kiyi wanka ke kad’ai ake jira za’a muku kamu kinga har la’asar ta wuce jiki babu wadataccen k’wari haka na mik’e na shiga toilet jin furucin da mama tayi wanka nayi ina kuka ina komai haka aka shiryani cikin alkyabba kamar yarda yanzu da yawan amare da ita ake musu kamu nayi kyau sosai amma har lokacin hawaye bai daina zuba cikin idanuna ba.

 

 

. Jin gidan shiru ya tabbatar min da duka sunyi gaba daga ni sai aunty zee kama hannuna ta yi har cikin wata mota ta bud’e bayan motar ta zaunar dani jin wani sassanyan k’amshin turaren man yasa ni kallon gefena aliyu ne cikin dakakkiyar shadda fara taji aiki k’afarshi sanye da wani had’adden takalmi me rufaffen sama hannunshi d’aure da agogo na d’anyan azurfa k’irar dubai hular dake kanshi tayi mishi mugun kyau acikin abin da bifi seconds biyu ba na k’are mishi kallo k’asa nayi da kaina ina ci gaba da share hawayen da ke zuba a fuskata jin motar ta fara tafiya ne yasa na ci gaba da kukana gaba d’aya gaban farar alkyabbar ya b’aci da ruwan hawaye.

 

 

Aliyu mutum ne me tausayi musamman

akan mace baya son kuka ko kad’an ba son humaira yake ba, amma zuwa yanzu ta fara bashi tausayi ganin yarda gaba d’aya ta canza daga humairar da ya sani duk akan aurenshi da ita damuwarshi kada wani mugun ciwon ya kamata da gaske bata sonshi da gaske ta tsaneshi aharabar gidan aka shirya walima wajan ya had’u ba k’aramin kyau yayi ba komai fari ne a wajan b’angaren maza daban haka b’angaren mata.

 

 

Malama zahra’u umar aka gayyato dan ta fad’akar da maza da mata hak’k’ok’in aure da abin da allah ya shar’antawa mace ta yiwa mijinta haka shima miji yayiwa matarshi,

 

 

 

Laccarmu ayau itace me take zaman aure

 

Dukkan yabo da godiya su tabbatta ga sarki da babu kamarshi sarkin da bai haifa ba kuma ba’a haifeshi ba, sarkin da bashi da abokin tarayya a cikin mulkinshi sarkin da ya daidaita bisa al’arshinshi

 

 

 

 

Tsira da amincinshi su tabbata ga shugabanmu annabi Muhammad s’aw da ahalinshi da sahabbanshi har izuwa ranar tashin alk’iyama.

 

 

Y’an’uwana musulmai salamu’alaikum inawa kowa barka da zuwa wannan walima me albarka kamar yarda dukkan wani musulmi yasani kuma ya karanta akwai hak’k’ok’in da aka shar’antawa mace akan mijinta akwai hak’k’ok’in da aka shar’antawa miji akan matarshi.

 

 

Gareku amare ko nace Y’an’uwana mata kusani aljannarmu tana k’afar mazajenmu sai munkasance masu biyayya sannan zamu rabauta da rabo mafi girma ranar alk’iyama duk macen da bata bata yiwa mijinta biyayya ba tayi hasara duniya da lahira sai dai babu biyayya ga abin halitta awajan sab’awa allah

 

 

Y’an’uwana mata kusani tsafta wata muhimmiyar aba ce dake taka rawa wajan zamantakewarmu agidajen aurenmu y’ar’uwa kada kibar gidanki kamar juji ma’ana kada kibar gidanki kamar bola babu gyara ya zamana a koda yaushe idan mijinki ya fita ya dawo yana farin cikin kasancewa da ke kada ya zamana cewa mijinki yafi sha’awar zaman majalista fiye da zama da ke mace y’ar kwalliya ce mace sai da gyara.

 

Menene shi kanshi gayan?

sannan yaya za muyi kwalliya don mu burge mazajenmu?

 

Dafarko idan aka ce miki gyara ya had’a da tsaftar jikinku keda mai gida da yara idan akwai da tsaftar gidanki.

 

Ita tsaftar gida tana farawa tun daga d’akunanki cikin kiching toilet tsakar gida yar’uwa ki kasance mai taimakawa mai gida wajan tsafatace jikinki kada kibada k’ofar da za’a raina mijinki idan ya fita a dunga nuna shi ana mijin wance ne y’ar gayu shikuma dube Shi kamar almajiri to ki gyara kayanki ke kanki ki gyara kanki kada ki dunga barin gashi yana cika miki jiki duk inda kika san ana askewa ki aske ki yawaita amfani da humra da body spray da body splash ya kasance k’amshinki na musamman ne awajan me gidanki sisters kada kibari mijinki ya shak’i wani wari ko k’arni daga gareki.

 

Y’ar’uwa ki iya girki kada ya zamana baki iya komai na abinci ba sai kala d’aya ki iya sarrafa abinci ta hanyoyi da dama iya sarrafa abinci ba dole sai da kud’i me yawa ba.

 

 

 

Y’an’uwana mata kada ki kasance baki iya kissa ba ki iya kissa ba ina nufin kissa ta munafunci ba a’a kissa irin wadda manyan mata suke yi mujinsu ya sosu ya tarairaye su ya shagwab’a su ya gatanta su sannan ita kissa bata amfani sai a had’a da biyayya ki iya kissar kallo ki iya kissar kwanciya ki iya kissar magana y’ar’uwa ki iya shagwab’a zamuyi bayani d’aya bayan d’aya idan kuna biye dani acikin littafin nagartaccen miji

 

Jan hankali garemu mata iyayen giji

 

Y’an’uwana kisani kamar yarda kike son mahaifiyarki haka ya kamata kiso uwar mijinki kamar yarda kike son danginki haka ya kamata kiso dangin mijinki.

 

Yar’uwa meye ribarki dan kin wulak’anta uwar mijinki meye ribarki dan kin hana mijinki yin biyayya ga iyayenshi ki sani baki ci riba ba sai asara me tarin yawa da kika da idan har albarka tabi mijinki kisani tabi y’ay’anki dake kanki idan akasin haka kema ta shafe ki zakiyi ta fuskantar k’alubale na rayuwa

 

Iyayenmu mata babu amfanin ki d’au karan tsana ki kafawa matar d’anki kisani kema kin haifa ba wai baki haifa ba wata K’ila kin aurar kuma kina sa ran y’arki taji d’adi agidan aure duk abin da muka yi wlh za’a yi mana dan haka mu gyara zamantakewarmu mu gyara tsakaninmu da alllah muji tsoron Allah.

 

 

 

 

Bayan anyi addu’a lokacin ana gab da kiran sallar magriba kayan da aka tanada dan d’aurin aure shi aka rabawa jama’a sannan kowa ya koma gida aunty zee duk inda nasa k’afa nan take sa tata kama hannuna tayi ta nufi b’angaren inna dani zuwa lokacin zazazzab’i mai zafin gaske ya rufeni ko ganin gabana bana yi da k’yar na gabatar da sallah ina idarwa aunty zee dole ta tilasta min cin abinci haka nan na daure naci bai fi three spon naci ba magani ta mik’on karb’a nayi kamar zan sha na zubar tare da shan ruwa bana son abin da ya shafi magani ko allura bana son ko d’aya daga ciki har bayan isha’i ban fito ba ana ta tambayar ina humaira amma ina jinsu gaba d’aya duniyar tamin zafi Ji nake kamar zuciyata zata fashe dan tsakanin bak’in ciki ina jin su aunty maimuna da aunty sadiya suna ta kai kawo da abokan wasanmu amma nikam ina kwance ga zazzafan zazzab’i da ciwon kai da ya rufe ni da k’yar nayi sallar isha’i daga haka wani wahalallen bacci ya d’auke ni.

 

 

 

please comment and share

Post a Comment

Previous Post Next Post