Muhassima Hausa Novel Complete

Muhassima Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

MUHASSIMA

 

 

*Mallakar*

 

 

*Zainab Muhammad*

 

*Indian Girl*

 

 

 

*Wannan littafi ba free bane na kuɗine.

 

*Normal group 300*

 

*Special group 500*

 

*V.I.P 1000*

 

 

*10 pages ne free kan ya ƙare ki biya domin shiga sahun masu jin ƙarshen labarin*

 

 

*Mai son biya ya tuntuɓeni a wannan lambar*

 

 

*08143907733 ko 09042626462 *

 

 

*Sai na jiku *

 

1-2

 

*Cikin garin adamawa*

Rugace mai cike da fulani masu kyau ga shanunsu suna ta harkokinsu.

 

Daga can kuma na jiyo ƙarar daka daga wani ɗan gida,hakan yaja ra’ayina na shiga.

A Sanadin Direba Hausa Novel Complete

Ɗakuna biyune a gidan sai banɗaki na kara sannan tsakar gida,yayin da wata mata wacce ba zata wuce shekara 40 ba a duniya kyakykyawa da ita fulanin usuli.

 

Masha Allah na furta lokacin dana kalli inda sautin dakan ke tashi.

 

Wata kyakykyawar yarinyace fara mai kyau na ƙarshen kwatance wadda ba zata wuce 16 years ba,tana sanye da kaya irin nasu na fulani wato riga iya cibi sai zani,hakan ya bawa manyan dukiyar fulaninta damar fitowa sosai ta cikin rigar ta duk da ƙananun shekarunta Allah yai mata baiwa.

 

Tana da manyan booty da hips kamar na babbar mace,Muhassima kenan.

 

Ta share gumin daya ke akan kyakykyawar fuskarta tsabar dakan da take,ta kalli sai tin da wannan matar take cikin gajiya da abin da take.

 

Tace”Wallahi inna nagaji da dakan nan”

 

Inna ta juyo ta kalleta sannan.

 

Tace”To ban da abinki Muhassima ya zaki yi shine fa gatanmu”

 

 

 

Muhassima ta cuno naki,Tace”To Inna dafa gajiya gashi sai naje wannan tallan dana tsana”

 

Inna ta ɗan harareta,Tace”Tun da kin gaji ai sai ki zauna macinyeki matsayin abinci ai”

 

Muhassima ba tai ƙara magana ba saboda ita magana wahala take bata,taci gaba da dakanta ita kuma Inna tai ta faɗanta.

 

Haka Muhassima ta gama dakan ta kwashe ta kaiwa Inna,ita kuma Inna ta haɗa mata fura tare da shirya mata kayan tallan nonon.

 

Ɗaki Muhassima ta shiga tayi kwalliyarta irin ta fulani ta fito ta ɗauki tallan taiwa Inna sallama ta fita.

 

Tana tafiya tana cuccuno baki wanda hakan kamar sarar tace.

 

“Muhassima tsayani”

 

Daga bayanta taji muryar Hanne tana faɗar haka.

 

Ta tsaya har Hanne ta ƙaraso inda Muhassima take.

 

Hanne Tace”Ashe har kin fito ina can ina jiranki”

 

Muhassima ta kalli Hanne Tace”Yau bana son tallan shiyasa ban biyo miki ba”

 

Hanne tai dariya da,Cewa”Kai Muhassima ai ya kamata ki saba da wannan tallan”

 

“Ni ba zan saba ba”

 

Muhassima ta faɗa.

 

Daga haka bata sake magana ba sai Hanne ce take ta zuba.

 

A haka har suka isa tasha.

 

Da zuwansu jama’a suka fara siya.

 

Wani daga can jikin mota ya kwallawa Muhassima kira.

 

Ta ɗaga kai tare da amsawa.

 

“Ki kawo min zan siya”

 

Ya faɗa.

 

Muhassima ta gama sallamar wanda ke tsaye sannan ta ɗauki kayan ta nufi wajan mutumin.

 

Zuba mata ido ya yi lokacin data sunkuya zata ajiye kwayar,ya lashe baki kamar maye tare da zubawa dukiyarta da suka ɗan fito ido.

 

Yace”Ki zuban na ɗari biyu”

 

Ta amsa da to sannan ta zuba ta miƙa masa,ya zo ƙarɓa ya taɓa jikinta.

 

Muhassima tai saurin kallonsa cikin ɓacin rai.

 

Ko kallonta bai ba.

 

Yace”Kije idan na gama zan kawo miki”

 

Haka ta ɗauka ta tafi taci gaba da siyarwarta har ya ƙare mutumin bai kawo mata kwanonta ba.

 

Hanne Tace”Muhassima tashi mu tafi ko?”

 

Muhassima tana waige-waige.

 

Tace”Bari Mudi nake jira ya kawon kwano sai mu tafi”

 

Haka suka tsaya suna jiransa har wasu ƴan mintuna.

 

Hanne ta kalli Muhassima da take ta rarraba ido ko zata ga Mudi.

 

Tace”Kinga ni wallahi Muhassima na tafi sai kin tawo”

 

Kafin Muhassima tai magana Hanne harta fara tafiya.

 

Muhassima tana kiranta taki juyowa.

 

Har yamma ta fara kawo kai shiru Muhassima tana tsaye tana jira,ganin idan ba nemansa take ba ba zata ganshi ba yasa ta nufi shagonsa.

 

Aikwa yana ciki a kwance da alama ma bacci yake.

 

Abin da Muhassima bata sani ba shine yana kallon tawo warta ya kwanta.

 

Rasa yadda za tai Muhassima tayi dan haka ta shiga bubbuga ƙyaure.

 

A furgice irin na wanda ya tashi daga bacci ya wawuro ta zuwa jikinsa ya rungume.

 

Zaro ido Muhassima tayi tana tuna nasihar Inna da take cewa”Muhassima ki riƙe mutuncinki baki da kowa sai Allah sai ni sai ƙannenki,karki bari wani ko da hannunki ya riƙe”

 

A zabure Muhassima ta fuzge jikinta tare da ɗaukan robarta dake ƙasa ta fita a guje.

 

Tana fitowa daga shagon ta ɗauki kwaryarta ta fara tafiya cikin sauri tana waige-waige ga kuma duhun magriba ya kawo kai.

 

Ana kiran sallar magriba ta isa rugarsu ta shiga gida.

 

Tana shiga Inna da hankalinta ke tashe ta taso da sauri ta ƙarɓi kayan tana tambayarta.

 

“Lafiya kika tafi shiru haba Muhassima ke kuwa kin sa hankalina ya tashi”

 

Muhassima ta kauda fuskarta gefe sakamakon kwallan daya tawo mata.

 

Tace”Inna ban fa siyar da wuri bane shiyasa kika jini shiru”

 

Inna tai shiru domin tasan da wuri Muhassima ke sai da tallanta.

 

Tace”Muhassima ki faɗan gaskiya nasan bakya ƙarya”

 

Kuka ya kuɓucewa Muhassima,Tace”Inna wani ne ya siya da kuma naje ƙarɓa shagonsa shine ya rungumeni”

 

(Abinka da fulani su gaskiya da gaskiyane)

 

Da sauri Inna ta toshe bakin Muhassima tare da janta ɗaki ya yin da ƙannanta suke zaune kan tabarmar kara.

 

“Hi shiru kar mutane suji suce kinyi iskanci”

 

Inna ta faɗa tana kallon ƙofar ɗakin.

 

Muhassima ta gyaɗa kai.

 

Inna ta sake,Cewa”Ba yadda zamu yi dana hanaki wannan tallan,amma daga yau na hana ki zuwa tashi ki dinga shiga irin unguwar ma’aikatan nan da suke zuwa daga birni”

 

Da “To” Muhassima ta amsa sannan suka fita zuwa tsakar gidan.

 

Sai da Muhassima tai wanka sannan ta zauna cin abinci tuwo miyar ganye.

Ranar da su Hanne suka biyo mata zuwa dandali cewa tai ba zata ba sai da Inna ta mata magana ta wuce su tafi sannan.

 

Kwalliyar zuwa dandalin tayi sannan ta tashi suka fice tasha kyau duk da kwalliyace kamar me.

 

A hanya suna tafiya Hanne take tambayarta yaushe ta dawo gida, tace bayan ta dawo bata daɗe ba itama ta dawo.

 

Haka suka isa Dandalin wanda ya sha kwalliya ga shi an kunna huta wajan ya ɗau haske,haka suka ƙarasa suna isa filin su Hanne su kai wajan rawa ita kuwa Muhassima gefe ta koma ta zama ƴar kallo.

 

Wasu samari ne su biyu tsaye bakin dandalin suna magana.

 

“Idi ga mutuniyar can fa”

 

“Ai nima na hangota ka san ita ɗin muguwar ƴar ƙauye ce”

 

Idi ya faɗa yana kallon inda Muhassima ke rakuɓe a zaune.

 

Rabe yai ƴar dariya sannan, Ya ce”Yo ai kamata yai ka cire mata ƙauyan cin duk da dai dama duk ɗaya kai dai ta”

 

Idi ya ɗan harari Rabe kafin, Ya ce”Haba ai ni ɗan birnin ne tunda na taɓa zuwa ita kuwa fa”

 

Duk suka sa dariya.

 

Rabe Ya ce”Alqur’an kai shegene yanzu dai kaje muga ya zaku kaya.

 

Idi yai murmushi ya nufi inda Muhassima ke zaune.

 

“Barka da hutawa”

 

Daga gefanta taji an faɗa, zabuta tai ta miƙe tsaye tana rarraba idanu.

 

“Lafiya naga kin zabura menene?”

 

“Inna ta hana ni zama kusa da namiji”

 

Ta faɗa tana kallon inda su Hanne ke a tsakiyar fili.

 

Murmushi Idi yai sannan, Ya ce”Ke nifa ba wani abu zan miki ba sonki nake”

 

Muhassima tai ƙasa da kanta zuciyarta na lugude, ‘Tafa san an ce Idi ɗan iska ne anya kuwa zata sake dashi, gwara dai kawai ta tafi gida’.

 

A ziciyarta take faɗar haka.

 

Bata jira komai ba ta kwasa a guje zuwa gida.

 

Rabe ya ƙaraso inda Idi yake a tsaye suna dariya tamkar cikin su zai fashe.

 

Muhassima ba ita ta tsaya ba sai da ta ganta a gida sannan ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya masu ƙarfi, sai da ta dawo nutsuwarta sannan ta ƙarasa shiga gidan..

 

Inna tana zaune akan tabarmar kaba tana zaman jiran dawowar Muhassima ganin shigowarta yasa ta miƙe suka shige ɗaki domin dare ya fara sosai.

 

A can kuwa dandali bayan an tashi daga wasan Hanne ta nemi Muhassima ta rasa ko da ta tambaya ba wanda ya ganta dan haka ta tafi gida.

 

****

“Soja na na ganka haka lafiya meke damunka”

 

Ya janyota ya zaunar akan cinyarsa sanna cikin damuwa, Ya ce”Matar soja wani aiki aka tura mu wani gari ni kuma naji bana son zuwa shine kawai”

 

Ta ɗan yi dariya, Ta ce”To mene na damuwar?”

 

“Saboda zan tafi na barki”

 

Ya faɗa yana marairaicewa.

 

Ta ce”To idan har dan nice ka kwantar da hankalinka ina nan insha Allah kaje ka dawo ka same ni, wata nawa za ku?”

 

Ya ce”Sati ɗaya me zuwa biyu”

 

Nabeeha tai dariya, Ta ce”Kai amma har ka ɗan ban kunya wallahi, yanzu banda abin ka Muhseen watanni fa kake zuwa kuyi a wani garin”

 

Muhseen Ya ce”Ok kenan ke baki damu da ni ba ai shikenan”

 

Ya faɗa tare da miƙewa zai bar ɗakin.

 

Da sauri Nabeeha ta riƙo hannunsa cikin langwaɓar da kai, Ta ce”Haba yallaɓai waya isa yace haka sorry”

 

Yai ɗan murmushi.

 

(Nabeeha tana iya bakin ƙoƙarinta wajan ganin ta faranta ransa sai da kash ta gaza wajan mu’amalar auratayya domin ta wannan ɓangaran har faɗa suke da ita.)

 

Ya ce”Shikenan na haƙura, yanzu ki haɗan kayana saboda da wurwuri za mu tafi yanzu bari naje gidan Mammy na dawo”

 

“Tam shikenan bari na raka ka”

 

Nabeeha ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa.

 

Mai da ita yai ya zaunar sannan, Ya ce”A’a ki zaman ki aikin dana saki bari yanzu zanje na dawo”

 

Nabeeha Ta ce”To a dawo lafiya Allah ya tsare hanya”

 

Ya amsa da “Ameen” sannan ya fice daga ɗakin.

 

Kai tsaye harabar gidan ya nufa, inda ake ajiye motoci ya nufa ya shiga wata ja yai mata key yaja ya bar gidan.

 

Ko da ya isa gidan Mammy dan suyi sallama addu’a tai masa sosai kafin ya baro gidan.

 

Kafin ya dawo Nabeeha ta gama shirya masa kayansa tsaff da duk wani abu da zai buƙata a cikin akwati.

 

A falo ya sameta tana chat da wayarta, zama ya yi kusa da ita.

 

“Sannu da gida madam”

 

Ta ɗago kai ta sakar masa murmushi sannan, Ta ce”Sannunka mijin madam”

 

Dariya duk suka sanya.

 

Ya ɗan langwaɓar da kai kafin, Ya ce”Madam me zan samu ne?”

 

Haɗe rai Nabeeha tayi kamar ba itace take wannan fara’ar ba, Ta ce”Kaga Muhseen mu bar wannan maganar da kai”

 

Muhseen ya ƙura mata idanu yana mamakinta ace mace bata son ai mata zan cen mu’amalar aure sai kace mara lafiya anya kuwa rayuwa zata iya musu a haka? Shi fa namiji ne mai buƙatar mace a tare dashi ko da yaushe amma gashi ya haɗu da wata kalar mace.

 

Ya sauke ajiyar zuciya, Ya ce”Shikenan tashi muje mu kwanta”

 

“Kaje kai ni ba yanzu zan kwanta ba”

 

Ta faɗa tana kumbure kumbure.

 

‘Ita fa wai har ranta ya ɓaci ikon Allah’ Ya faɗa a ransa.

 

Bai ce mata komai ba ya nufi ɗaki.

 

“Mtsss! Aikin banza duk yadda ka kai da yiwa mutun amma baya gani”

 

Nabeeha ta faɗa bayan jan dogon tsakin da tai.

 

(Ni kwa Zainab da nake tsaye nace anya kuwa Nabeeha rayuwa zata yiwu a haka, ana yin aure ne dan soyayya amma mafi ƙarfin shine mu’amalar dake cikin auran tsananin mata da mijinta.)

 

 

*#Comment and Shares#*

Post a Comment

Previous Post Next Post