Mu Rayu Tare Hausa Novel Complete
MU RAYU A TARE
True life story
Zainab Habib (Mom Islam
Free
Page 1-2
Zaune take gaban mahaifiyar tata wacce ta kasance mahaukaciya, Iffat yarinyar ƴar shekara huɗu, tunda ta fara wayo ta gano basu da gidan daya wuce bola, inda taga mahaifiyarta take zama koda yaushe.
Iffat yarinya ce mai wayon gaske, gata da surutu, tana gyarawa mahaifiyarta zani wanda ya buɗe ana ganin ilahirin cinyoyinta, taji ance “kee yarinyar mahaukaciya ungo”
Mar’Adams Hausa Novel Complete
Kafin ta juya taji saukar abu a gabanta, a hankali takai dubanta tare da kunce baƙar ledar dake ɗauke da abinda mutumin ya jefo mata, tana washe baki tace “Umma tuwo ne miyar kuka zakici?”
Umman ta karɓe ledar tare da ajiyewa a gabanta, ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya, tunda Iffat taga Umma ta kusa cinye tuwon, ta janye ledar tare da rugawa da gudu, tana gudun tana cin tuwon.
Umma ta miƙe tana wasu irin yaruka wanda Iffat ɗin ta gane me take faɗa amma sam taƙi kula Umman,
UNGUWAR DALA, DAKE CIKIN GARIN KANO.
“Haba Wasila tun ɗazu na kawo cefane amma naga ko tukunya baki ɗora ba?”
Cikin yanayin rashin jin daɗin gane halin da take ciki na hura wutar tace “malam tun ɗazu nasa yara su kwasomin makamashi, wlhi har yanzu basu dawo ba gashi gawayin sam yaƙi kamawa, ko uffan bece ba ya juya yana tsaki, Juwairiyya ta fito riƙe da ƙugu tace “baba..”
Har ya kusa kaiwa bakin ƙofa ya juyo, cike da nuna kulawa yace “ƴar baba ya akayi?”
“Wlhi bacci tasha, har sai da naje na tashe ta , tasan yanzu ƙarfe ɗaya na rana ne, muna jin yunwa amma taƙi ɗora abinci saboda mugunta, baba ni dai na fasa cin abincin”
Malam Yusuf ya dawo da sauri tare da cewa “haba ƴar baba, idan kikace bazakici abinci ba, ki gayamin me zakici?”
Cikin shagwaɓa Juwairiyya tace “baba Fate nakeson sha”
Malam Yusuf yace “ke Hajara, sauke tukunyar shinkafar nan ki ɗora fate”
Cikin ɓacin rai Hajara tace “haba malam gashi nayi sanwa har da kayan miyar, amma zaka ce in sauke?”
Eh ki sauke ki auni masara mudu ɗaya akai ɓarji ga nera hamsin”
“Juwairiyya zoki miƙa niƙan”
“Taɓɓ wlhi nikam yunwa nakeji baba kai dai ka tafi kawai tunda ka faɗi abinda za’ayi”
Malam Yusuf ya wuce yana cewa “ƴar baba kenan”
Yana fita Hajara ta kalli Juwairiyya dake girgiza tana kallon Hajara, cikin tuhuma Hajara tace “idan alkairi kike ƙullawa zaki gani, idan sharri kike ƙullawa duk zaki gani”
Kafin Hajara ta ƙara magana, Juwairiyya taje tai saurin zubar da sanwar abincin da Hajara tayi…
Idan har naga ya samu karɓuwa posting kullum, idan naga akasin hakan to sai sati-sati,
Cikin gadara Juwairiyya take cewa “kin kashe mahaifiyata kina neman mallakemin mahaifi, to ta Allah ba taki ba,”
Cikin tsananin ɓacin rai, Hajara taje ta wanke Juwairiyya da mari, zuciyarta na ƙuna tace “karkiga ina biye miki ba tsoranki nakeji ba, muddin kikace zaki dinga jifana da munanan kalamai wlhi sai nayi maganinki”
Juwairiyya na tsaye riƙe da kumatu, tana bin Hajara da kallon raini,
Kamar inda malam Yusuf ya bata umarnin aunar masara hakan tayi, a gajiye take tafiya har ta isa bakin ƙofar gidan hannunta riƙe da ƙwarwar da ta auno masara, kafin ta ƙwalawa ɗaya daga cikin yaran da suke wasa a ƙofar gidansu ta hango an ɗauke wutar nepa, cikin baƙin cikin hakan, Hajara tace “nepa basu da tabbas ya zanyi nikam?”
Ta wuce gida tana riƙe da ƙwarya a hannunta.
Ko sisi bata dashi bare ta ƙirƙiro dafa wani abun, ruwan sanwar da zata mayar dashi fate, Juwairiyya ta kifar, bata da zaɓin da ya wuce ta koma ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido, kana kuma ta jira hukuncin da malam Yusuf zeyi mata.
HUDA
zaune take a ɗan madai-daicin ɗakinsu wanda ya kasance ɗaƙi ɗaya ne suke amfani dashi, kasancewar gidan nasu babu wasu yawaitar ɗakuna, a hankali Huda take bin kowanne sashe na fuskarta tana shafa jar hoda ƴar zazzage, Umma dake tsakar gida ta ƙwala mata kira tare da cewa “Huda yanzu fa muna ƙarfe goma ne na safiya, tun tuni kike kwalliya sai kace mai sauya fata, kin daɗe gurin wanka yanzu ma bakida niyar fitowa naga kamar?”
Da ɗan ƙaramin bakinta na tsiwa tace “Umma gani nan, na gama kaya zansa”
A gurguje Huda tasa doguwar riga ta material wanda yayi mata kyau, duk da ya tsufa,
Tana sanya mayafi ta fito tana cewa “umma nagama ke nake jira”
Umman ta gyara zaman kular data ajiye abincin da bokiti wanda yake ɗauke da robobi da cokula, kana da omo da soso, sai ɗan ƙaramin bokiti mai ɗauke da jar miya taji mangyaɗa, Huda tace “Umma wlhi kafin in ƙarasa bakin titi ina gajiya, kodai inje in taro me mashin ne?”
Kafin Umman tayi magana, daga can waje sukaji ƙarar mashina, Umma tayi waje da gudu tana gyara ɗaurin zani, tana leƙawa ta ƙwala wa me mashin ɗin kira, me mashin yace “yana jira”
Umma ta dawo cikin gida ta samu har Huda ta kwaso kayan, Umman ta tayata miƙo ragowar, kana ta kunto bakin zaninta ta miƙawa Huda nera ɗari tace “Allah ya kiyaye hanya, saura inji kin dawo kince wani yaci be baki kuɗi ba, wlhi sai na lahira yafiki jin daɗi, dan bazaki mai dani…
Mai mashin yai saurin figarsu da gudu, sbda ya gaji dajin kalaman Umman, ya girgiza kai.
Tana isowa gidan mai, kafin takai ga sauka daga kan mashin samarin gurin suka taso suna shewa suna sauke mata kayan abincin, Huda ta miƙawa me mashin kuɗinsa ya wuce, ta kalli samarin tana murmishi tace “kodai kunci kun ƙoshi ne shiyasa kuketa yimin dariya?”
Ɗaya daga cikinsu yace “mun isa ai bamu isa muci abincin wata yarinya anan ba, dole naki zamu jira,
Huda tasa dariya, ta gyara zaman kayan a cikin wata ƴar rumfa, kana ta nemi gefen dogon benci ta zauna, sha biyu na rana, mutane suka fara zuwa, tana zuba musu, harda samarin gurin, wani saurayi yaci abinci be bata kuɗi ba, ta miƙe tsaye sbda taga ze tafi tace “malam baka bani kuɗina ba?”
Cikin masifa da tsageranci saurayin yace “na ƙarfi ne naci kuma bazan bayarba”
Huda tace “kaje kaci nacan wlhi sai Allah ya sakamin”
Saurayin ya ɗaga hannu ze mareta, wani daga cikin wanda suke siyan abincinta ya taso yana cewa “amma baka da imani, kaci abincinta ka hanata kuɗi, har Kanada ikon dukanta?”
“Eh ance baza’a bada ba ko Kanada abinda zakayi ne?”
Mai kare Huda yace “eh yanzu ma kuwa”
Kafin wanda ya shigarwa Huda ya zaro bel, saurayin ya gudu,
Huda ta fashe da kuka gashi abinci ya ƙare, tsabar tunanin kuɗin hannun wannan saurayin ta cikawa mutane abinci,
“Kiyi haƙuri Huda, nawa ne kuɗin wancan ɗan iskan gayen?”
Huda tace “ɗari uku”
Saurayin yace “ga ɗari biyar ki ajiye a gurinki, gobe zanci abinci”
Huda tayi godiya, sai a lokacin taji mugun sanyi a ranta, ta tattara kayan abincin, harda robobin da bata wanke ba ta tari mashin ta wuce gida.
IFFAT
Yamma tayi sosai, ga wani gagarumin hadari ya haɗa, Iffat ta kamo hannun Umman ta tana cewa “Umma zomu samu gida, ruwa ze jiƙaki”
Mahaukaciyar sai wasu irin abubuwa take, tana ta fizge-fizge, da soshe-soshe, Iffat ta tattaro ƙarfinta ta turo Umman nata, kafin ta kamo hannunta sunata tafiya, a barandar wani gida suka zauna, Iffat ta kalli sama, tace “Umma ruwan ya fara zubowa”
Kasancewar ba magana mahaukaciyar takeyi ba, yasa ta ƙurawa Iffat ɗin ido kamar me shirin yin magana, me gidan ya fito yana ganinsu, ya haska fitila, kana yace “ke riƙe hannun mahaukaciya kuyi wani gurin, tsabar iskanci ku rasa inda zaku zauna se nan gurin?”
Iffat tace “malam ka bawa Ummana abinci dan Allah yunwa takeji”
Cike da masifa yaci gaba da cewa “dalla tashi anan yunwo”
Iffat ta kamo hannun Umman ta suka bar gurin, suna cikin tafiya, wani mutumi ya kira Iffat, a tare suke tafiya da Umman nata har suka iso gurin Mutumin, ya miƙawa Iffat dubu ɗaya, kana yace “jeki cikin kasuwa ki siyo muku kayan shayi”
Yasan suna cikin tsananin jin yunwa, sbda yana gani aka koresu.
Iffat ta karɓi kuɗin kana ta ruga a guje tana fara’a, duk da ana shirin kiran sallahar magriba,
A hankali wannan mutumin ya fara tunkaro mahaukaciyar yana wani irin murmishi, daga karshe ya cafke ta ya sanyata a motarsa wacce ya parkata can nesa dasu, motar babba ce irin Sharon ɗinnan, ya tura mahaukaciya a ciki yabar anguwar da ita,
Tana ta buge- bugen gilashin motar da surutai, hakan besa yaji tsusayinta ya ajiyeta a kusa ba, sai da ya iso can bayan gari, gurin babu mutane sai gonaki, hanyar ma, ba kasafai mutane suke Bin ta ba, sai uzirinsu ya kawosu, bayan yayi parking ya kwantar da kujerar gaba tare da kallon baƙin tinted baƙi na gilashin motar, kana ya cire rigarsa ya kuma cire wandonsa, ya rage saura gajere.
ALHAJI AUWAL
Babban ɗan kasuwa a Bauchi, birni da ƙauye babu wanda be san sunansa ko labarinsa ba, ya shahara sosai yana uku daga cikin masu kuɗaɗen NIGERIA.
Zaune take a katafaren parlonsu, wanda yake fidda ni’im taccen sanyi da sanyayyayen ƙamshi mai kwantar da hankalin wanda ya shaƙar, yarinyar ƴar shekara goma sha biyar ta fito hannunta riƙe da tsadaddiyar waya I phone 13pro, a yanayin inda tayi da fuskarta dole abin zai bawa mai karatu dariya, a hakan wai fushi takeyi, cikin girmamawa taɗan risina, sakamakon ganin fitowar Abban nata, “good morning Abba”
“Morning how are you?”
Cikin shagoɓa Amani tace “Abba ina lafiya sai dai akwai wata ƴar matsala”
Cike da nuna kulawa Abban yake kallon ta kana yace “my lovely daughter meke faruwa?”
“Abba inason kayi aure, tun bayan rasuwar Ummi ko maganar aure bakayi, ko jiya ma sai da mukayi shawara da bro Mahaboob da aunty Aseela da Inaya, sukace ya dace”
Abba ya nemi guri ya zauna tare da zuba mata idanu, kafin yace “zanyi shawara amma kafin nan meyasa kikeson inyi aure?”
Amani ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta, kafin ta buɗe tace “Abbana kodan ta dinga yi maka abinda kakeso, kaga duka abokanka sunada mata kaine kawai baka da ita”
Abba yace “shi kenan naji, amman nikam dalilin da yasa naƙi aure, banason in auri matar da zata dinga takura muku”
Amani tace “Abba karka damu”
IFFAT
Da gudu ta dawo tana cewa “Umma ga kayan shayin, kinga me shayin ma har a kofinsa ya zuba miki”
Shirun da taji ne yasata sake leƙa inda suke kwana, wato gefen bola taga wayam babu Umman, cikin ɗaga murya, tana shirin yin kuka tace “Ummaaaa naaa mahaukaciyataaaa”
Duk da haka babu wanda ya fito bare yasan ga halin da take ciki, hankali a tashe Iffat ta fara zagaye unguwa tana ƙwalawa Ummanta kira, sam ta gagara zama tasha shayin sai yawo takeyi dashi a hannu…!
Save and chart 08141799224 Mom Islam
MU RAYU A TARE
True life story
Mom Islam
Page 3-4
Tana cikin tafiya tayi karo da ƙaton dutse wanda yai sanadiyar kai ta ƙasa, cikin kuka Iffat ta taɓi bakinta wanda yakeyi mata zugi, hannun nata ta kalla, ganin jini ya sanyata fashewa da kuka tana yarfe hannaye, daga can gefe shayin da bredin ya zube, bredin ne dai beyi komai ba, dan haka ta miƙe tana karkaɗe jikinta ta, kasancewar garin yayi duhu, yasa bata hango kofin ba, ta riƙe bradin taci gaba da tafiya tana kuka.
A hankali mutumin ya raba mahaukaciya da zanin jikinta, idan mai karatu yaga mahaukaciyar nan, wlhi bazai fara tunkararta ba, duba da inda jikinta yake fitar da tiririn wari, marar daɗi,
A haka ya faɗa mata ya dinga sukuwa a kanta, daga ƙarshe ya wani shigeta da ƙarfin bala’i har ƙafafuwansa na rawa, kafin ya ɗaura mata zaninta kamar inda ya ganta, shima ya mayar da kayansa, yasa tissue paper ya goge gurin ya fesa turare, kana ya bar gurin da motarsa,
Suna tafe yana waya, sai cewa yake “ai nasamu na kwashi gara duk da mahaukaciyar ba wata babba bace amma wlhi tayi daɗi”.
Kafin mutumin yayi parking a inda ya ɗaukota, ya waiga ko ina baiga kowa ba, kana ya ajiyeta tana dukansa, harda cafke masa riga, yai saurin ƙwacewa ya ƙara da gudu, tare da shigewa mota.
Iffat kuwa tayi nisa da anguwar sosai, saboda tsakaninta da inda aka dawo da mahaukaciya yakai nera ɗari, babu wanda ya ganta ya taimaka mata, haka ta dinga tafiya har, takai bakin titin anguwar da suke, wato ɗorayi, tana kuka ta nufi bakin titi ko waigawa batayi ba, sai ji kake ƙuuuuu…ƙiiii…, kafin kace me, wanda basu ga tsayuwar yarinyar ba duk suka hallara a gurin, sakamakon ƙugin motar da suka ji,
Kowa sai ambatar “innalilahi wa inna ilaihir raji’un” yakeyi, a gigice mamallakin motar ya fito, hankalinsa a tashe yana cewa “ku taimaka ku samin ita a mota wani ya biyoni mu kaita asibiti”
Wanda ya taya mai motar sa Iffat a mota, shine yabi mai motar suka wuce asibitin Murtala.
Suna isa aka karɓesu cikin kulawa, sakamakon jinin da yake kokawar kwaranyowa jikinta, aka wuce da ita ɗakin gaggawa,
Sosai suka fara bata kulawa ta musamman, kafin suka sanar musu da cewar “dole zata iya kaiwa gobe, bazai yiwu a sallameta a yau ba”
Hakeem ya danna number Hajiya babba, cikin wani irin yanayi na damuwa yace “Hajiya babba nayi hatsari a hanyar ɗorayi, nidai banji ciwo ba, amma yarinyar taci ciwo, bazan dawo gida yau ba sai zuwa gobe, dan Allah ki sanarwa da Hajiya ƙarama da Dady”
Cike da nuna kulawa Hajiyar tace “Allah ya cigaba da karamin kai yarona”
Hakeem ya amsa da “Amin”
Kafin tace “muma goben zamu taho da izinin Ubangiji”
Yace “Allah ya kawoku”
Bayan an gama gyara Iffat, barci mai nauyi ya ɗauke ta, doctor ya kira Hakeem zuwa office, cikin azama Hakeem ɗin ya bishi, anan ne doctor yake tambayarsa “ina iyayen Iffat?”
Hakeem ya sunkuyar da kansa ƙasa, kana yace, “sir a bakin titi na ganta, banma lura tana gurin ba, kawai ƙarar motata ne ya fargar dani, na tambayi wani mutumi wanda suka taimaka min gurin kawota da sanyata a mota, sunce basu santa ba”
Likitan ya girgiza kai kana yace “gaskiya bazan ɓoye maka ba, yarinyar ta samu ciwon taɓuwar ƙwa-ƙwalwa, ba komai zata iya fahimta a yanzu ba, sai dai nan gaba insha Allah idan kuka kiyaye maganin da zamu ɗoraku akai, abubuwan zasu dinga warwarewa a hankali, sannan a kiyaye ɓata mata rai..
Jikina yayi sanyi kunason mucigaba??