Matsalar Mu A Yau Hausa Novel Complete
MATSALAR MU A YAU
_(Labarin Surayya)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
MANAZARTA WRITES
PAID BOOK
Akwai complete ga masu bukata 07084653262
1&2
Cikin nutsuwa take tura keken guragun da yake zaune. a hankali ta fito dashi kofar gida ta tsaya tana kallonsa da idanuwanta da suke cika da ruwan hawaye. Cikin kulawa da tausayawa yake kallonta ya sauke ajiyar zuciya cike da jarumta yace.”Surayya nace ki daina kuka duk da yanzu yamma ce idan na fita Allah ba zai hana ni abinda zan siya miki littatafan makaranta ba saboda naga kin damu yasa na yanke shawarar fita ko Allah zai sa a dace.”
Kewaye Hausa Novel Complete
Hannu tasa ta share hawayen idonta tace.”Baba Tausayin ka nake ji wallahi baka da koshin lafiya kawai ka koma gida ka zauna na hakura.”
Girgiza kansa yayi da murmushi a fuskarsa yace.”Surayya ai tunda na fito ba zan koma ba sai na fita dama can ala dole nake zama a gida tunda yanzu naji kwarin jikina sai na fita watakila Allah yasa a dace.”
A sanyaye tace.”To shikkenan Baba bari na tura ka bakin titin.” Girgiza kansa yayi yace.”Aa kin san bana so kina bina bakin titin nan wasu mutanan basu da uziri.”
A shagwabe tace.”Na sani Baba yau d’aya ka bari na tura ka.” Murmushi yayi yana girgiza kansa yanzu duk wanda zai ganshi da yarinyar tana turashi sai ya dauka bara sukeyi yasan bai wuce a bashi sadaka ba amma tunda Allah yasa yana iya sarrafa hannayensa to babu abinda zai gagareshi a yanda Allah ya halliceshi a haka yake so ya cigaba da bashi kwarin gwiwar sauke nauyin iyalinsa zuciyarsa a tsaye take sam bashi da kasala da nuna cewa shi din nakasashshe ne dole jama’a su taimaka masa.
Idan yaga ‘yan uwansa nakasassu suna yawo kan titi na suna bara da maula ransa yana baci mutuka shiyasa shi ya d’aura d’amarar neman halalinsa tunda Allah ya bashi rai da lafiya to nakasarsa ba zata hanashi aiwatar da komai na rayuwarsa ba.
Cikin nutsuwa take turashi suna hira sai murmushi yake yana amsa mata. Wani matashin saurayi ya tare musu hanya.
Surayya ta ‘bata rai ta kallashi da fadin.” Bawan Allah menene haka zaka tare mana hanya.”
Shahid murmushi yayi yasa hannu ya sosa sumar kanshi ya d’an risinar da kai da fadin.”Baba barka da yamma.” Malam Habu ya amsa kadaran kadahan sam irin wad’annan samarin basa burgeshi yafi san nagartattun mutane su nemi auran ‘yarshi.
Shahid ya jefe ta da kallon kauna yace.”Surayya ya kwana biyu.”? Gabanta ne ya fadi da sauri taja tsaki ta yi saurin tura keken suka barshi a tsaye a gurin. bayansu yabi da kallo yana murmushi shi dai Allah ya sanya masa kaunar yarinyar a cikin ransa.
Suna kokarin karya kwana ta hango maigadin gidan yana gyara masa kujerar da ya saba zama a irin wannan lokacin. kafin ta dauke idonta ya fito daga gidan yana sanye da farar t-shirt tas had’e da jins blue black idanuwansa sakaye da farin gilashi fuskarsa jiya i yau kamar ko da yaushe dai zama yayi kan kafin ya kar’bi dictionary din dake hannun Haruna Maigadi dake tsaye a kusa dashi. Hannu ya daga masa alamun ya bashi guri. da sauri ya shige cikin gidan tare da sakayo karamar kofar.
Yana kokarin bude littafin ya hange su Tana tura shi a keken yana gargada tare da cijewa da alama yafi karfinta kokari kawai take cikin nutsuwa yake kallonsu yana jin wani irin yanayi a tare dashi…….Ita kuwa wani irin sanyi jikinta yayi gabanta in banda fad’uwa babu abinda yake a duk lokacin da za tayi tozali dashi takan rasa kuzari a tare da ita.
Malam Habu tun kafin su ‘karasa inda yake ya saki fuskarsa sai fara’a yake. A nutse ya mike da littafin a hannunsa ba tare da ya kalleta ba ya miqa mata littafin hannunta na rawa ta kar’ba shi kuma ya ri’ke keken ya cigaba da tura shi Malam Habu na ‘yar dariya yace.” Nuraddin anya ban katse maka uziri ba. Murmushi yayi a nutse yace.”Babu damuwa Malam ina ka nufa ne da wannan yammacin.”?
Malam Habu yayi jim kafin Yace.”Zanje bakin titi ne kwana biyu na dan kwanta a gida ban fita ba.” Shuru yayi na minti biyu kafin yace.” Me zai hana ka koma gida tunda daf ake da a kira sallar magriba Idan Allah ya kaimu gobe da safe sai ka fita.
Shuru yayi yana nazarin maganar da zai fada masa yanzu idan ya koma gida bai sai abinda zai bawa iyalinsa suci da daddare ba da safe da rana matarsa Habiba tayi fafutuka to yana da kyau yanzu shi kuma ya tabuka nasa kokarin.
Ganin yayi shuru yasa ya gane abinda yake da akwai. a sace ya kalli gefen da take tana tafiya salau-salau tamkar ka bushe ta saboda tsabar rama tausayinsu ya ‘kara ratsa shi hakika yunwa da tsananin takura tana damunsu.
Yace.”Malam ina neman alfarma a gurinka.” Malam Habu yace.”Wace irin alfarma kake nema Nura.” Ajiyar zuciya ya sauke yace.”Ka koma gida ka kwanta ka huta gobe idan Allah ya kaimu sai ka fita.”
Malam Habu yace.”Nuraddin nayi maka Alfarma.” Murmushi yayi na jin dadi yace.”Nagode Malam.” Da sauri ya juyar da akalar keken domin komawa gida…………Salo-salo take bin bayansu zanin jikinta sai hard’e ta yake gefe guda kuma k’amshin turarensa dake fita daga jikin dictionary dinsa dake hannunta ya bala’in kashe mata jiki tana tafiya tana sansana littafin tana lumshe ido tamkar bugaggiya haka ta zama aikuwa ba tare da tayi aune ba taji ta facal cikin kwata tayi tsumbul ta kamo kifi ka dictionary din sai yawo yake a saman kwatar……..Cikin wani irin yanayi ta kira sunan mahaifinta nata hawaye kuwa tuni suka ‘kwace mata.
[4/29, 12:33 PM] Bintu Umar Marubuciya: *MATSALARMU A YAU!*(Labarin Surayya)
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSOCIATION
PAID BOOK
Akwai complete document ga masu bukata….07084653262
*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya Dee🥰)_
*5&6*
Yaro ya samu a kofar gidan ya bashi abincin da kudi kimanin dubu biyar yace ya shiga ya kai. bayan yaga shigar yaron gidan sai ya juya ya bar gurin cikin yanayin tafiyarsa ta gwarazan maza irin wanda ba’a nuna su da yatsa.
Suna zaune jugum-jugum! abin duniya ya dame su gabad’ayansu Yunwa ce take sasakarsu dan dai kawai sun saba da ita ne shiyasa basu galabaita sosai ba amma a zahirin gaskiya ita Surayya daurewa kawai take dan har ta fara ‘kananun hawaye kawai dai bata so iyayenta su lura shiyasa ta shiga daki ta kwanta kan ya mutsatstsiyar katifa tana share hawaye.
Jin sallamar yaro a gidan yasa tayi shuru tare dasa kunnenta. Yaro yace.”Wai gashi in ji wani .” Innah ta kalleshi ta kalli kwanakun abincin dake hannunsa tace.” Aminu Anya kuwa anan aka tura ka.”?
Yaron yace.”Eh Innah nan ya turo ni kin ga ma har da kudi yace na bawa Malam.” Yafada yana mikawa malam kudin.
Malam Habu ya mike zaune yana kallon kudin dake hannun yaron yace.”Aminu baka sheda mutumin da ya turo ka ba.”
Yaron yayi shuru yana tunani Yace.”Na sheda mutumin shine mai zama a kofar gidan Alhaji Sabo yana karatu.”
Malam Habu yayi murmushi da fadin.”Dama ai tunda naji yace zai dawo nasan hidima zai yi mana babu komai Aminu jeka abinka.”
Yaron ya kama hanya zai fita Innah ta kira shi da fadin.”Zo ka kar’bi naira goma kasha alawa.” Yace.”Aa Innah ki barshi nagode.” Sai ya ruga da gudu ya fita Murmushi tayi tace.”Aminu kenan babu ruwansa da son kudi irin na yara wasu yaran kuwa koda iyayensu ne zasu aikesu sai sun biya su sannan za suje.
Malam Habu ya kalleta da fadin.”Habiba kin ga hidimar da yaron nan yayi mana ko.”?
A sanyaye tace.”E na gani wallahi malam ni mamaki ma ya hana ni nayi magana Yaron nan Nura yana da kirki ya dauko halin mahaifinsa dama mahaifiyarsa ce mara san mutane.
Malam Habu yace.”Allah kenan shine yake had’a mutum da mutum haka kawai yaron nan yake kaunata hakika da ina da wani abu mai muhimmanci da zan bashi to dana dauka na bashi domin alkairinsa a gare ni.”
Innah Habiba tace.” Gaskiya kam Nuraddin ya cancanci ko wace irin kyauta amma bamu da abin da zamu biya shi face muyi masa kyakykyawar addua kaga yanzu muna zaune cikin halin damuwa da tunanin abincin da zamu ci gashi ya kawo mana harda kudi.”
Yace.”Kudin kuma masu yawa dubu biyar ne.” Innah ta rike baki tana mamakin al’amarin Tace.”Allah ya saka masa da alkairi ya biya masa bukatunsa yanzu gobe idan Allah ya kaimu za muje kasuwa ni da Surayya sai mu siyo kayan abinci idan yaso sai aji dana cefane.”
Yace.”Eh kwarai wannan shawarar taki tayi kyau amma zan dauki dubu daya a ciki domin na siyawa yarinyar nan littafan makaranta.”
Tace.”Malam daka bari an siyi abinci daga baya sai a siyi littafan.” Ya girgiza kansa da fadin.”Habiba kina wasa da karatun yarinyar kina kallo yau ma saboda rashin littafan ya hanata zuwa makaranta bamu da wani abu da za muyi mata a duniya face mu bata Ilimi a rayuwata inaso Surayya tayi karatu mai zurfi sai dai kuma bani da arzikin da zan tallafe ta.” Murya na rawa ya kare maganar
Innah Habiba jikinta yayi sanyi tace.”To shikkenan Malam na amince da hukuncin daka yanke Allah ya taimaka ya bata ilimi mai amfani.” Ya amsa da ameeen ya Allah.
To duk wannan zantukan da sukeyi tana jinsu ita gabad’aya ma ba karatu ne a gabanta ba tunaninta ya tafi kan maganar da taji suna yi akan Masoyinta wai suna cewa basu da abinda zasu bashi ita kam wallahi da zasu dauketa su bashi da tayi tsalle tayi dara a duniya bata da wanda take so kamarsa ita kanta bata san irin kauna da son da take masa ba.
Hawaye ta share tana wani tunani tana ganin kawai zata samu babanta da maganar watakila ya amince da tunaninta duk da tasan Shi d’in ba tsaran auranta bane amma tana ganin idan babanta ya bashi ita ba zai qi kar’ba saboda yanda yake ganin girmansa.
Tana tsaka da wannan tunanin taji Innah na kwala mata kira. A sanyaye ta amsa ta mike jiki a mace ta fito tsakar gidan.
A sabule ta zauna kusa dashi tana ya mutse fuskarta ya kalleta cike da tausayawa yace.”Kin ga Allah ya dube mu ko.” Tace.” Nagani Baba Allah ya saka masa da alkairi.” Ya amsa da “Ameen ya Allah kin ga yanzu a cikin kudin zan baki dubu daya sai ki sayi littafan.” Zumbura baki tayi tace.” Baba ai kudin littafan dubu daya da dari bakwai ne.” Shuru yayi yana nazari yace.”To ki fara siyan masu muhimmanci a ciki insha Allahu cikin satin da zamu shiga zan baki dari bakwai din sai ki sayi sauran.” Shuru tayi domin ba taso hakan ba.
Ya kalli Innah da fadin “Ki zuba mana abincin muci gobe idan Allah ya kaimu idan kun tashi tafiya kasuwar sai ku shiga gidan Alhajin Sabo ku gaishe dasu.
Innah Habiba ta kalleshi da fadin.” Aa Malam kasan fa ni bana san wulakanci mai zai kaimu wannan gidan da ba’a son talaka.”
‘Bata rai yayi yace.”Habiba Umarni na baki bana so kuma kiyi min gardama duk wanda ya wulakanta wani kansa ya wulakanta kuma ba dan kowa za ku shiga gidan ba sai domin wannan yaro.”
Tace.”To shikkenan Malam Allah ya kaimu goben lafiya.” ya amsa da “ameeen ya Allah. kwanukan abincin ta fara budewa a take kamshi ya cika musu hanci Shinkafa ce fara tas da ita da miyar kifi manya-manya sai ‘kamshi miyar take da alama suna amfani da tafarnuwa da sauran kayan gyaran kirki.
Jin kamshin tafarnuwa yasa zuciyarta tashi abin da ta tsana kenan a rayuwarta. Hanci ta toshe tana kakarin amai.”
Innah tace.”To sarkin iyayi da sanabe nasan dai kamshin tafarnuwa ne yasa ki toshe hanci.
Kamar za tayi kuka tace.”Allah Innah amai nake ji ki rufe miyar nan.”
Innah Habiba tace.”Idan kakan amai za kiyi sai dai kiyi amma ba zan rufe abinci nan ba…..Da sauri ta mike daga gurin ta nufi bakin rariya ta tsuguna.
Malam Habu ya bita da kallo yana girgiza kanshi Innah tace.”Malam dan Allah ka rabu da yarinyar nan kaci abincin ka tsirfa ce kawai gashi kiri-kiri ta hana ni girki da tafarnuwa a gidan nan.”
Yace.”Habiba ki rabu da abinda mutum ba yaso ba tsirfa bace ba taso ne saboda haka maza zuba mana abincin ki dauke kwanukan daga wurin.”
Tana tsugune a bakin rariya tana tofar da yawu har suka gama cin abincin Ya kalleta da fadin.”Taso kizo ki fada min abinda kike so kici ma fita na siyo miki.
Ta yunkura ta mike tsaye ta nufi inda yake hannunta ya rike da fadin.” Me zaki ci tunda da akwai kudi sai a siyo miki.” Tayi jim tana tunani tace.”A wara nake sha’awa.” Innah Habiba tace”Surayya bana san shashanci a gidan uban wa zaki samu awara yanzu ga abinci mai rai da lafiya amma saboda tsirfa kina gudu.”
Tana marairaicewa tace.”Can karshen layi Ummiyo tana soyawa dan Allah ki bari naje na siyo.” Tace.” Ba zaki je wannan gurin ba awarar Ummiyo maza ne suke cika a gurin.
Kuka ta fashe dashi da fadin.”To ni Innah ina ruwana da maza kawai ina zuwa zance ta bani idan kuma da layi sai na shiga gidansu gurin kawata Samira kafin azo kaina.”
Innah Habiba tace.”Ban yarda ba sai dai ki nemi yaro a waje ya siyo miki.”
Malam yace.”Eh hakan shi yafi Surayya kar’bi kudin ki nemi yaro a waje ki bashi ya siyo miki ta yanda kike so.”
Hawayen ta goge ta kar’bi kudin daki ta shiga tasa hijabi ta fito. Innah tace.”Kada fa kije gurin nan.” Kai kawai ta daga tasa takalmanta ta kama hanya ta fita daga gidan.
[4/29, 12:33 PM] Bintu Umar Marubuciya: *MATSALAR MU A YAU!*_(Labarin Surayya)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES
*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee Amanar Binta🥰)_
_Lallai Shiga tsakaninmu sai an shirya😕_
PAID BOOK
Akwai Complete ga masu bukata 07084653262
3&4
Kusan a tare suka juyo ganinta tsulum a cikin kwata yasa shi ya mutse fuskarsa kawai sai ya tsaya yana jifanta da wani irin kallo mai kama da harara idonsa akan dictionary dinsa dake jike da ruwan kwata!
Sunkuyar da kanta tayi hawaye na sauka a samam fuskarta. Malam Habu cikin damuwa yace.”Surayya garin ya akayi kika fada kwata da girmanki da komai.”
Murya na rawa tace.”Wallahi Baba ban san lokacin ba.” Girgiza kansa kawai yayi yace.”Ai sai kiyi dubura ki fito gashinan kin jefa masa littafi cikin ruwan kwata.”
Cikin damuwa da alhini ta dauko littafin wai zata fito dashi. ya girgiza kai yana yamutsa fuskarsa yace.”Me kike tsammanin zanyi dashi.”?
Kallonsa tayi yace.”Kawai ki fito ki barshi tunda kinyi min asara dole na nemi wani.”
A sanyaye ta sunkuyar da kanta ta fara kokarin fitowa santsin ruwan kwatar yana mayar da ita gabad’aya k’yamar kanta da kanta take ballantana kuma wani.
Ganin yara sun fara taruwa a gurin yasa ya matsa inda tare da mika mata hannunsa. kallonsa tayi gabanta sai faduwa yake. babu walwala a tare dashi yace .”Rike hannuna ki fito .”
A sanyaye tasa hannunta cikin nashi kawai taji fittt! ya janyo ta waje dama ba wani kwari ne da ita ba da kyar ta iya tsayuwa da kafafunta sabida razana! duk ta ‘bata masa jikinsa…..Hararar gefen ido yayi mata ba tare da yace mata komai ba ya bar gurin.
Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka tabi bayansu jikinta duk ya mutu ga yara sai kallonta sukeyi.
Koda tazo shiga gidan bata yarda sun hada ido ba simi-simi ta shige su tana takure jikinta.
A nutse yace.”Malam ka zaka iya shiga gidan ko.”? Malam Habu yace.”Eh zan iya shiga Nura nagode sosai Allah yayi maka albarka ya baka mace tagari.”
Ya amsa da “Ameen ya Allah Malam ni bari naje gida anjima zan dawo insha Allah.” Malam Habu yace.”To shikkenan Nura a gaishe da mutan gidan.” Yana kokarin barin gurin ya amsa da “Insha Allahu za’a fada musu.”
Kai tsaye ruwa ta jawo a rijiya ta shiga bandaki ta wanke jikinta……Tun kafin ta fito daga bandakin take jin muryar mahaifiyarta tana fad’a. “Sai kace wata yarinya karama saboda shashanci zata jefa masa littafi a cikin kwata wallahi malam ban san abinda yake damun yarinyar nan ba.
Yace.” Nima banji dadi ba na lura shima Yaron ransa ya ‘baci kawai ya ‘boye ne.” Innah Habi ta cigaba da fad’a! wanda ya sanya ta fargabar fitowa daga bandakin tasan halin mahaifiyarta mafadaciyar macace. aikuwa koda ta gama ra’be-ra’ben ta ta fito rufe ta tayi da fad’a wanda ya sanyata kuka tana bata hakuri da fadin.”Tsautsayi ne Innah Habi gabadaya taqi kar’bar uzurinta sosai tayi mata fad’a ta shiga daki taci kukanta ta koshi.
To shima koda ya shiga gidansu kai tsaye gurinsa ya nufa a gurguje ya tsaftace jikinsa ya dauro alwala ya fito ya shirya cikin jallabiya ruwan madara turare yasa a jikinsa ya dauki carbi ya nufi massalaci sai da ya gabatar da isha’i sannan ya shigo gidan.
Nan ya samu ‘yan uwanshi dasu da ‘ya’yansu sun cika falon sai hayaniya sukeyi suna shewa ga kayan abinci nan baja-baja……….Babu walwala a tare dashi ya tsaya a bakin kofar falon yana kallonsu.
Fadila da Yusura da Shafa sukayi saurin sunkuyar da kansu suna gaisheshi a dakile ya amsa yana bin falon da kallo a rayuwarsa ya tsani rashin nutsuwa da kamun kai wai saboda lalacewar zamani iyaye ne da ‘ya’yansu suka zauna suna shashanci a guri daya.
Aunty Jamila ta kalleshi da fadin.” To sarkin Masifa da Miskilanci ka shigo.” ‘Bata rai yayi yace.”Yanzu Aunty Jamila wannan wace irin Dabi’a ce kun zauna tare da yara sai shirme kuke yi.”
Aunty Nafisa ta watsa masa harara da fadin.”To menene a ciki dukkaninsu mata ne idan ba mu zauna dasu ba dawa zamu zauna.”
Hannu ya d’aga mata babu sukuni yace.”Ba dake nake magana ba sabida haka kada ki kara saka min baki a maganata.” Dama can a tsakaninsu basa jituwa yafi shiri da Aunty Jamila.
Tsaki taja ta dauke kanta tasan halinsa baya daukar raini duk da tana gaba dashi yanzu sai yayi mata rashin mutunci kuma ya kwana lafiya shiyasa tayi shuru da bakinta sabida tana jin tsoron ta sake magana ya tsinkata a gaban ‘ya’yanta.”
Guri ya samu ya zauna yana ‘bata rai Fadila ta kalleshi da fadin.”Uncle a kawo maka abinci.”?
Girgiza kansa yayi da fadin.”Hau sama ki kira min Hajia.” Da sauri tace.”Uncle.” Ya kalli Aunty Jamila da fadin.” Ku dubi Time fa takwas da rabi na dare sai yaushe zaku tafi gidajenku.”
Saboda tasan halinsa a tsorace ta fadi maganar.” Kwana za muyi sai gobe da yamma.”
Wani irin kallo yake mata kafin yace.”Me akeyi biki ko Suna da zaku kwana.”?
Shuru tayi masa yace.”Saboda kawai kun samu labarin Abbah baya gari shikkenan sai ku baro gidajen mazajenku daku da ‘ya’yanku shin me hakan yake nufi.”
Tace.”Kaga Nura don Allah ka kyale mu wallahi ni bana san takura da matsala kai ba kai kake auranmu ba amma kazo kana tsara mana yanda za muyi.”
Ido ya zuba mata yace.”Saboda kawai za’a gyara miki kuskuranki shine kike wannan maganar.” Tana kokarin magana Hajia ta karaso gurin tana kallonsa tace.”Babangida haka take kiransa saboda sunan kakanta ne dashi. Ya amsa da Na’am Hajia ya gida.”? Tace.”Lafiya lau Fadila tace kana nema sai nace to Allah yasa kudi zan samu.”
Gyara fuska yayi yana kallonta ta zauna a kusa dashi sai washe baki take tana fadin.” Hausawa suka ce idan kaji kira ba banza ba Allah yasa samuwa ce.”
Girgiza kansa kawai yake yana mamakin halin saon kudi irin na mahaifiyarsa macace mai masifar san kudi da rashin alkairi bata kaunar talaka ya ra’bi inda take kullum tafi bukatar ta zauna ita da ‘ya’yanta gabad’aya ‘kawayenta masu kudi ne bata yarda tayi mu’amula da talaka ba. Akan wannan halin nata suke rigima da mijinta domin shi Alhaji Sabo mutum ne mai saukin hali da taimakawa talaka.
Ajiyar zuciya ya sauke yace.” Idan da akwai abinci inaso a zuba a cikin fulas zan fita dashi.”
Tace.” Ba’ki kayi ne.”? Girgiza kansa yayi.” Sai ta ‘bata fuska da fadin.” To wa zaka bawa abinci kuma da wannan daran.”
Bai da munafurci ko kadai komai zaiyi kansa tsaye yake yi shiyasa yake rayuwarsa cikin kwanciyar hankali…….”Babangida magana fa nake maka kayi shuru kana kallon guri daya.
Yace.”Inaso zan kai gidan Malam Habu ne.” Wani matsiyacin tsaki taja ta waiwaya tana kallonsu tace.”Nafisa kiji wata magana don Allah.”
Ta bude baki za tayi magana ya watsa mata muguwar harara! sai tayi shuru da bakinta tana ya’ke!
Aunty Jamila tace.”To kai haka kawai zaka kai musu abinci ko ro’kar ka sukayi.”?
Ransa a bace yace.” Don Allah bana san surutu wannan abin da kuke sam bai dace ba menene abinci abinda kuka fi karfinsa wannan bawan Allahn yana bukatar taimako ko ya roka ko bai roka ba yana da kyau a taimaka masa.”
Hajia Sabuwa ganin yanda ya ‘bata rai yasa ta kalli Fadila da fadin.” Ki tashi kije ki zuba musu abincin Allah ya kyauta.”
Fadila ta tashi ta nufi kicin din ranta a ‘bace ita kam ta tsani yanda yake nuna kulawarsa a kan mutanan sam bata kaunarsu saboda talaucinsu.
Tana kawo masa abincin bai jira komai ba ya mike ya fita ya basu guri aikuwa suka dasa gulmarsa sai zagin Malam Habu suke shida Iyalinsa Hajia Sabuwa tace.”Gurgu dashi sai muguwar bakar zuciya dole ne na tashi a tsaye akan wannan alakar da take tsakaninsu watakila ma asiri yake masa…….Aunty Nafisa ta dinga tunzurata da fadin.” Lallai da akwai alamun gaskiya a cikin maganarta.
Bintu Umar Marubuciya: *MATSALARMU A YAU!*
(Labarin Surayya)
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
MANAZARTA WRITES ASSOCIATION
PAID BOOK
Akwai complete document ga masu bukata.
*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya Dee🥰)_
*7&8*
Ta jima a tsaye tana duba yaron da zata aika bata samu ba kawai sai ta yanke shawarar zuwa ta siyo da kanta sai dai kuma garin yayi duhu tunda dare ya shiga anyi isha’i gashi babu wutar nepa har ta juya da niyyar komawa gidan ta dauko fitila sai kuma ta fasa dan tasan tana shiga gidan Innah zata hana ta fitowa sai kawai ta kama hanya da sauri take tafiya tana addua Allah yasa kada taje ta samu layi a gurin Ummiyo mai awara.
Aikuwa tun kafin ta karasa ta hango uban layi duk maza sunfi yawa Ummiyo ta iya awara shiyasa matasan samari suke mata layi wasu gidajan ma basa girkin dare kawai sai suyi Awarar Ummiyo suci su kwanta.
Tana boye hannuwanta a cikin hijabi ta karasa gurin.Ummiyo dake kokarin tsamo awara ta kalleta da fadin.” Surayya ina za kije da wannan daran.”?
Jin Ummiyo ta kira sunanta yasa da sauri ya kalli inda take tsaye….Saurin kauda kanta tayi tace.”Ummiyo yau awarar ki nake sha’awar ci gashi naga da akwai jama’a.
Ummiyo tace.”Aikuwa dai da jama’a sai dai ki shiga gurin k’awarki ki jira.”
Girgiza kai tayi tace.”Bari kawai na tafi gida Ummiyo sai da safe.” Ummiyo na kokarin magana ya tare mata hanya. Ta ‘bata rai tana kallonsa.
Shahid ya marairace fuska da fadin.” Don Allah ki tsaya ki saurare ni Surayya wallahi da gaske nake auranki zanyi.”
Gabanta na faduwa tace.”Ni dan Allah ka matsa ka bani guri na wuce naje gida.” Yace.”To zan baki hanya amma sai kin saurare ni.”
Zumbura baki tayi tana kokarin ratse shi ta wuce yayi saurin tare hanyar taja tsaki mai karfin gaske Gidansu Ummiyo ta shiga da fadin.” Don Allah Ummiyo idan kinzo kaina kisa min ta dari biyu.” Ta mika mata kudin..Yayi saurin fadin.” Kada ki karba ki bari zan biya.”
Ummiyo na murmushi tace.”To ke Surayya kinji abinda Shahid yace.” Kudin tasa mata a jikinta tace.”Ni dai bana bukatar kowa ya siya min abu ga kudin ki nan.” Ummiyo ta bita da kallo har ta shige gidan.
Abokinsa Yace.”Shahid amma fa yarinyar nan tana wahalar da kai yarinya sai shegen girman kan tsiya gata ‘yar talakawa wai kai don Allah mai ka gani a jikinta kake bibiyarta.
Shahid ya goge fuskarsa da hankici yana girgiza kansa hakika yarinyar nan na bashi wahala gashi shi kuma Allah ya sanya masa kaunarta a cikin ransa.
Ummiyo ta mika masa ledar awararsa da fadin.”Kai Shahid tunda dai yarinyar nan bata sonka ka hakura mana babu dole.
Cikin ‘Kunar zuciya yace.”Ummiyo ba zan iya hakura da Surayya ba yarinyar ta riga ta shiga raina.” Suraja yasa dariya yana kallonsa da fadin.”Lallai kana da aiki abokina tunda har kake son maso wani.”
Shahid a fusace! ya daga masa hannu da fadin.”Dallah malam saurara waye ya fada maka haka kawai ka shige mu tafi.” Suraja na Dariya yasa kai yana mamakin karfin halin abokinsa kiri-kiri yarinya ta nuna bata sonsa amma ya nace ya kasa hakura.
Surayya kuwa tana shiga gidan ta manta da wani Shahid tunda ta samu kawarta Samira suka dinga hira Samira fitinanniya ce mai san auren tsiya ko a makaranta bata da aiki sai waya da samari da rubuta musu wasikar soyayya Ajinsu daya gurin zamansu daya shiyasa suka san sirrin junansu.
A sanyaye ta kalleta da fadin.” Samira wallahi ina cikin damuwa na rasa yanda zanyi.”
Tace.”Wace irin damuwa kuma haba Surayya kuma sai kiyi shuru ki fada min ko da akwai shawarar da zan baki.”
Shuru tayi tana nazarin maganar tace.”Samira don Allah ki rike min amana kada ki fadawa kowa sirri na kuma ki taya ni addua akan Allah yasa na mallake shi.”
Samira tace.”Wa zaki mallaka.”? Idonta cike da ruwan hawaye tace.”Uncle Nura mana.”
Samira ta shiga tunanin inda tasan sunan. Tace.”Surayya ashe kin fara soyayya ban sani ba kuma waye Uncle Nura kuma.”?
Hawaye ta share tace.”Na gidan Alhaji Sabo.” Samira gabanta ya fadi ta dafe kirji da fadin.” Dan Ubanki ina zaki kai wanda yafi karfin ki Surayya ki tsaya a matsayinki.”
Ta ‘bata rai da fadin.” Samira kin san fa ni ko skull bana son wasan zagi me yasa zaki zagi ubana.”
Samira tace.”Ai abin ne ya bani mamaki dan wallahi ni ban san ma na zage ki ba saboda ganin kina kokarin kai kanki inda yafi karfin ki bayan haka kuma dube ki fa kina yawo kamar sillan kara ina zaki kai wannan gafjejan mutumin sai kace dan dambe.”
Tace.”Samira ni kaina nasan Uncle yafi karfi na ta kowane fanni to ba yanda zanyi da zuciyata da abinda take so wallahi ni kadai nasan irin son da nake masa.”
Samira tayi shuru tana girgixa kanta a gaskiya kawarta tana cikin wani hali dan tasan ko mutuwa za tayi ta dawo mutumin da take so ba zai aureta ba domin yayi mata zarra ta ko’ina zuciya ce dai kawai da bata da azanci ta rasa inda zata kai kanta sai inda aka fi karfin ta.
Tace.”Samira kinyi shuru ki bani shawara mana wace dabara zamu shirya wacce zata janyo hankalinsa kaina.”
Samira ta kalleta sai kawai ta fashe da dariya ita wallahi ma abin mamaki yake bata ai ita duk iya shegen ta akan Samari tana ganin ba zata iya da wannan mutumin ba.
Surayya ta goge hawayen bakin ciki tace.”Aikin banza kawai ina miki magana kin mayar dani mahaukaciya to bari kawai na tashi nayi tafiya ta.”
Samira ta rike hannunta tana kokarin danne dariyar tace.”Zauna don Allah kada ki tafi.” Ta zauna tana jan tsaki. Samira ta nutsu ta kalleta da fadin.” Surayya shawarar da zan baki shine ki daina wahalar da kanki a banza wallahi gwara ki tallafi mai kaunarki tsakani da Allah Shahid yana sonki sosai shi kuwa Uncle Nura son maso wani kike na tabbatar da cewa ba zai aure ki ba.”
Taji wani irin kunci a cikin zuciyarta Tace.”Shikkenan Samira tunda fatan da kike min kenan a matsayinki na kawata wacce nake alfahari da ita shine na kawo miki shawara zaki watsa min kasa a ido nagode.” Murya na rawa ta karashe maganar tana kokarin tashi tsaye.
Samira tace.”To shikkenan tunda kinqi yarda da shawara ta yanzu ya kike so ayi.”? Ajiyar zuciya ta sauke tace.”Ki rubuta masa wasikar soyayya da sunana ni nasan yanda zanyi wasikar ta sameshi.
Samira tace.”To shikkenan sai gobe idan mun je makaranta sai mu tsara yanda za’ayi.” Tana murmushi tace.”Nagode sosai kawata bari na shige na tafi naga dare yayi.” Samira tace.”Aikuwa kin ga karfe goma shaura minti goma.” Gabanta ya fadi da sauri ta kalli agogon bangon dake kafe a dakin Gabanta na faduwa tasa takalmanta da fadin.” Samira sai da safe nasan Hankalin Malam na can a tashe.” Samira tace.”Bari na raka ki hanya.” Mahaifiyarta ta fito daga bandaki da buta a hannunta tace.”Samira ina za kiji da wannan daran.” A sanyaye tace.”Zan raka Surayya han…..Tun kafin ta karasa ta watsa mata harara ba tace komai ba ta ajiye butar ta shige daki.
Ta kalleta a sanyaye tace.”Surayya sai da safe.” Itama jiki a mace ta amsa da sauri ta bar gurin….Lokacin har Ummiyo ta fara harhada kaya ta tashi daga suya tace.”Ai dama nasan idan kuka hadu sai Allah sai yanzu kika fito.”
A sanyaye tace.”Wallahi Ummiyo ban san dare yayi ba bani awarar na tafi.” Ummiyo tayi saurin mika mata ledar awarar da sauran kudin ta karba da sauri take tafiya tana had’a hanya.
Ko’ina shuru abinka da lokacin sanyi ga duhu babu wuta fakal-fakal take tafiya gabanta sai faduwa yake……..Horn da hasken motar ne yasa tayi saurin kaucewa cikin rashin sani ta tsumbula kafarta cikin kwata tayi taga-taga zata fadi ledar hannunta ta fadi a gurin awarar duk ta watse akan kasa.
Cikin nutsuwa ya tsayar da motar domin tuni ya gane itace saboda hasken motar daya haske gurin……….Bude motar yayi ya fito wanda yayi daidai da lokacin da ta ciro kafarta daga cikin kwatar tana yarfe bakin zaninta ta yarfa masa k’azantar a kan kafafunsa dake cikin takalmi mai gidan yatsa…..Ido kawai ya zuba mata yana kallo ita kuma gabanta sai faduwa yake itama idon ta zuba masa tana kallonsa bakinta sai motsi yake……..