Macijin Ciki Hausa Novel Complete
MACIJIN CIKI
MRS SADAUKI
SADAUKARWA ga S REZA
FCWA
*Jan hankali*
*Macizai da ake samu a gidaje ana kashe su ne bayan an kira su sau uku su fita, saboda tsoron kar da su kasance cikin Aljanu, sai dai (nau’i biyu): Al-abtar da dhut-Tafifatan waɗanda ake kashe su koda a gidaje ne saboda Annabi (SAW)kawai ya haramta shi ga sauran macizai. _Al-Bukhari, babin farkon halitta n°3297 da n°3298 da Muslim, babin aminci, n°2233._ *- Al-abtar (الأبتر) shine wanda wutsiyarsa tayi gajere,* *- dhut-tafifatayn (ذو الطفيتين) shine wanda yayi ke zane biyu a bayansa.*
Wajibi ne a kashe waɗannan macizai guda biyu a kowane hali, saɓanin sauran da ake kashewa sai bayan an kira su su fita har sau uku, ta hanyar cewa misali: “Na kira ku ku fita daga gidana” ko kuma wani hukunci da zai yi gargaɗi ne kuma ya na nuna masa cewa an hana shi zama a gidan.
In duk mutum ya yi haka amma macijin bai fita ba,hakan na nufin ba aljani ba ne,in ma shi ɗin ne to bai cancanci darantawa ba a kashe shi.
Amma idan maciji ya kai masa hari, sai a bar shi ya ture shi, ko da a karon farko. Idan har hakan ya haifar da kashe maciji ko kuma a iya dakile harin ta hanyar kashe shi, to a nan muna da hakkin yin hakan, kare kai ne. _Fatâwa Islamiyya juzu’i na 4, shafi na 450 da 451._ _Sheikh Muhammad Ibn Salih Al-Utheymine(r)_
*Page 1*
MACIJI ne! Tabbas idona ba gizau ba ne suke mini,jinjirin maciji ne a gabana.Kashin da nake mugun ji ne ya ɓace ɓat,sai murɗawa ciki haɗi da ƙugi kamar mai jin yunwa.”Sulululu”ya fara nufo inda nake,idonsa ƙurrr kaina ya na kallona,da sauri na rumtse nawa gam haɗi da buɗe dukkan muryata na ƙwala uban ihu tare da neman agaji duk da na san gidan ni ɗaya ce Inna ta tafi kasuwa,Baba kuma ya na can gona tun safe.
Mu Rayu Tare Hausa Novel Complete
Cikin tsoron da ya aure ni nake jiran farmaki haɗi da cizon MACIJIN sai dai ko ɗaya daga ciki.A hankali na buɗe idona da ke shatatar da hawaye,wayam babu macijin.Tamkar wacce ta yi ma sarki ƙarya haka na ci gaba da gwale ido ina duba ko ina na cikin banɗakin wanda ya kasance na kara.
Ina shafar ido na ɗauki butar da ta saɓile a hannuna tun lokacin da mu ka yi gamdakatar da maciji.
Waje na fito na ajiye butar tsakar gida,na shiga ɗaki.Ga mamakina Inna na tarar zaune kan tabarma ta na ƙirga kuɗi.Na ɗan turo baki gaba bisanin nace “saboda Allah Inna ki na ji na ashe duk ihun nan da nake na neman agaji ke ta ƙirgon kuɗi ki ke? Wai yaushe ma ki ka dawo?”
Ba tare da ta ɗago ta dube ni ba ta bani amsa “tunda Allah ya yi ki da shegen tsoron tsiya ba doli ki firgice ba,daga rana irin ta yau kar na sake gani ko ji kin shiga banɗaki da hantsi gatse-gatse muddin ba ni gida”
“Rummacen da na ci jiya ne ya burkuta mini ciki,to in ban zawaye shi ba Inna ya ki ke so na yi ? In tsaya ya kashe ni?” Na faɗa ina mai zama kusa da ita.
Sai a lokacin Inna ta ɗago kanta,mu ka haɗa ido da ita.Yanayin idonta da kallon ya so tuna mini wani abu amma ba ta bani damar yin tunani ba ta jefo mini tambaya “Tuwalle ba ki so mu yi kuɗi ne mu fita daga wannan ƙangin rayuwar?”
Ba tare da yin wani dogon nazari ba na bata amsa da “ina so mana Inna ,ni da nake son mu je can binni kullum mu rinƙa dafa macarandi da naman kaza”
“Yauwa Ramatuwalle na! To muddin ki na son mu je binni doli ki rinƙa yin duk abin da nace ki bar kuma wanda ban so”
“To Inna daga yau zan rinƙa yi” na faɗa ina susar daƙwalon kaina wanda yake jibge da ƴar karen dauɗa kamar mai jegon ƙauye.
“Saura ƙiris ya rage kuɗin da za mu fara sana’a su cika,da zarar sun kammala zan sayo kayan miya sai mu na kasawa a kasuwa” Inna ta faɗa ta na ƙulle kuɗin cikin baƙar leda bayan ta ware ɗari biyu.
“Inna mi za mu ci yau?” Na tambaye ta.
“Oh! Ni Tuwalle kin cika gaggawa kamar zawo! Ungo je ki gidan Mairo ki sayo mana kafa sai mu kwaɗa dama ina da sauran ƙuli”
Na waro ido haɗi da dafe ƙirji nace “Inna wannan matar fa mayya ce!”
Inna ta ce “wa ya faɗa miki mayya ce?”
Cikin son ƙin zuwa aiken na kwaɓe fuska na ce “Allah Inna mayya ce,duk ƙauyen nan babu wanda bai san Mairo na da *MACIJIN CIKI* mai tsotse jinin mutane shi ya sa ba kowa ke shiga gidanta ba”
Ga mamakina sai na ga Inna ta haɗe rai ta gimtse fuska kicin-kicin kai kace Mairo ɗin uwarta ce.
“Daga yau kar na sake jin kin faɗi haka,abin da mutane ke cewa ba doli ya zamana gaskiya ba.Tashi maza ki karɓo mini ”
Jiki a saɓule na miƙe tare da karɓar kuɗin na fita.
Babu wani nisa sosai tsakanin mu da gidanta.Kamar kullum gidan a rufe yake sai da na bubuga ,ina nan tsaye kamar kayan shanya don na fi minti biyar a tsaye sai faman kishin gidan nake.
Har zan juya na ji muryarta “tsaya Tuwalle gani nan!”
Na harari ƙyauren gidan ina gunguni,ta buɗe ta na mai tambayata”Asabe ta aiko ki?” Ta na nufin Innata,kai na ɗaga mata tare da miƙa mata kuɗin nace “kafa za a bani” “ki shigo mana “ta faɗa ni kuwa na yi tsaye ƙiƙam na riƙe ƙyaure a zuci nace ‘ na shigo ki tsotse mini jini ko?’
“Ki shigo ki karɓa” ta ƙara faɗa a karo na biyu ta na mai juyowa ,zuciyata na bugun uku-uku cike da tsoro na shiga amma a tsakar gida na tsaya .
Ina nan tsaye ina jiran ta fito sai ji na yi mage na shafar mini ƙafa.Na yi tsalle na ja da baya,amma abu kamar na tsiya magen nan ta saka yatsunta ta karce ni a ƙafa.
Na yi ƙara haɗi da rugawa na shige ɗaki,tamkar munafuka haka na yi tsaye cikin ɗakin ina rarraba ido.
Abun da ya bani mamaki shi ne yadda Mairo ta buɗe labulen ɗaki ta shigo,alhalin dama tun can ta na cikin ɗaki.
‘To yaushe ta fita ? ‘ ban sani ba.
Fuska a haɗe ta ɗauki leda ta zuba mini kafar,ta miƙo mini tare da mini wani kallon irin kamar ya ki ka gani? Gobe ma ki sake.Amma da yake ni ɗu ce ban fahimci komi ba haka na karɓa,na zo na kawo ma Inna .
Da dare ina bacci,ƙafata ta ishe ni da zugi.A doli na tashi zaune,na fara sosa gun.Jin tamkar ana ƙara mini zafin ya saka ni fashe wa da kuka.
Baba da ke can ƙurya ɗaki shi ya fito ya na mai hasko ni da fitila “lafiya mine ne?” Ya tambaye ni,ƙafar na nuna masa da sauri ya zauna ya na mai tambayata “mine ne ya ji miki?”
Shiru na yi don har ga Allah na manta magen Mairo ta yage ni.
“Bari sosa wa kar ya yi jini” ya faɗa tare da fara tofa mini addu’a.Cikin ikon Allah na ji komi ya tsaya,hakan ya sa na raɓa gefen Inna wacce ke ta yin bacci kamar matatta.
A gaban idona Baba ya haskata da fitilar hannunsa,duk da akwai hasken ƙwan fitila aci balbal.Kai ya girgiza ya ce “Allah shirya!” Ban san mi ya gani ba ko mi yake nufi da hakan ba kawai dai na lumshe idona.
Kwaramniya ko nace haniyar su ce ta tashe ni daga bacci.
Ban san mine ne ya haɗa su ba,haka ban san farkon rikicin ba kawai tashi na yi na ji su na faɗa da junansu.
Na buɗe na zomayena na fara sauraren masayar yawunsu.
Inna ce ta ke faɗar “babu ruwan ka da rayuwata,ka yi taka in yi tawa.Ina ce dai abincin da za mu ci ka na baƙin cikin kawo wa,ni ce dai wacce ka ke kira da mayya,bokanya nake fita nake nemowa”
Baba ya katse ta “ki ke nemowa ko ki ke satowa? To bari ki ji wlh daga yau in na sake ganin mugayen halayen ki sai kin bar gidan nan”
“Ai wlh sai dai kai ka bar shi amma ni zama daram”
“Asabe ki ji tsoron Allah,ki kasance uwa ta gari wacce ƴarta za ta yi koyi da ke”
“Na ƙi na zama,wai Audu da ka ke kuri ka ke tunƙawo kafin ka zama malami ina ce kai ne Sarkin may….”
Tarin da na yi ne ya saka Inna yin shiru,sai duk suka juyo suka zuba mini ido kamar masu son sanin tun yaushe na tashi.Fahimtar haka ya saka na fara murza ido,kamar wata ƙaramar yarinya na fara kukan sangarta tare da tashi ta na nufi ƙofa.
“Kar ki buɗe ɗaki safiya ba ta yi ba” cewar Baba.
“Ruwa zan sha” na faɗa a shagwaɓe,Inna ta harare ni ta mai cewa “su kuma ruwan da ke cikin moɗar ƙarfe”
Na sosa ƙeya tare da zuwa na ɗauki moɗar ƙarfen wacce dama kullum a cike take da ruwa saboda ko da mutum ya ji ƙishi.
Baba ya koma can ƙurya ɗaki,ni kuwa ina gama shan ruwan na kwanta.
Tsawon lokaci da kwanciyata sai na ga Inna na leƙon fuskata,da sauri na lumshe ido kamar mai yin bacci.
“Tuwalle? Tuwalle? Tuwalle?” Ta kira sunana har sau uku amma na yi shiru kamar ba na jin ta.
Ƙarar buɗe ɗaki na ji wanda ta yi shi a hankali,ban san ina ne Inna za ta je ba kawai dai na samu kaina da bugawar zuciya da sauri da sauri.
An ɗauki kamar minti goma da fitar Inna ,sannan na tashi zaune.Sauraren zuciyata nake wacce ke ce mini na fita na ga mine ne Inna ke yi,sai dai kiciniya da hargowar da kunnuwa suka fara jiyo daga waje ya katse mini hanzari.
Da sauri na sake komawa na kwanta,tamkar ana taron biki haka nake jin tsiminiyar mutane.Ina nan kwance ina tunani ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.
Washegari
Ina farkawa na fita,idona ba su gama buɗe wa taram ba na nufi banɗaki ko buta ban ɗauka ba.
Kamar jira yake na tsugunna,MACIJIN da na gani jiya ya sake ɓullo wa ta cikin zana……
MACIJIN CIKI
MRS SADAUKI
SADAUKARWA ga S REZA
FCWA
*Page 2*
MACIJIN ya ƙure ni da tsanwayen/kori idonsa kamar dai jiya.Daga inda nake tsugunne fitsri sai ratata yake mini kai kace raƙumin da ya shanye ƙoramar ruwa.
Tamkar wacce aka shuka,na kasa tashi a gaban idona ya yi sulululu ya wuce.Tsawon kamar minti biyar na miƙe,ashe fitsari da zawo ne na yi ba tare da ni kaina na sani ba.
Ina kuka na fita daga ɗan kewayen zanan da ya kasance banɗaki,ruwa na samo na wanke jikina.
Ina shiga ɗaki na tarar da Inna kwance ta rufa da bargo ta na maida numfashi kamar dokin da ya gama tsere.
Jikinta na faɗa jikinta ,ina kuka da sauri kuma na janye tare da ƙoƙarin yaye bargon da ta rufa sai ta riƙe shi gam ta na mai juyo da fuskarta amma ba ta buɗe idonta ba.
“Inna? Inna mi ya same ki? Ina ƙafafun ki?” Na yi tambayar ina laluba can ƙasan ƙugunta sai dai wayam ba alamun ko ƙafa sai wani abu mai taushi da na ji gudan ƙatoto.
Cikin wata irin murya wacce ban santa da ita ba ta ce “je ki dubo Baban ki”
Ambaton sunan Baba ya saka na maida dubana da ƙofar shiga ƙurya ɗaki,ƙunnai haɗi da alamun jan ajiyar zuciya kunnuwana suka jiye mini.
Da sauri na shiga,cikin mawuyacin halin na tarar da Babana.Ban san lokacin da na fara yin kuka ba ina kiran “Baba? Baba?” Tuni idonsa sun kafe,sai bakinsa da yake motsawa kafin wani lokaci tsit babu gurnani babu numfashi.
Daga bayana na ji Inna na tambayata “ya jikin nasa?”
Na juyo ido shaɓe-shaɓe da hawaye na ce “Inna tun yaushe Baba ya fara rashin lafiya ba tare da na sani ba?”
Ba ta bani amsa ba kawai sai gani na yi ta matsa kusa da Baba,idonsa ta shafa tare da luluɓe shi har izuwa kai sannan ta ja hannuna mu ka fita.
“Allah ya yi ma Baban ki rasuwa!” Shi ne abin da Inna ta faɗa mini,ko kaɗan ban ga alamar rauni ko ƙunci a tattare da matar da ta rasa mijinta sai ma wani farin ciki.
Tamkar saukar guduma haka na ji,ihu da kururuwar da nake shi ya jawo hankalin maƙwabta.
Kafin wani lokaci mutanen ƙauyenmu sun hallarci zana’izar Babana.
Tamkar sabuwar amarya haka ƙawayen Inna suka kewaye ta su na ta shan hirar su,ban san mi su ke cewa ba amma ban ga alhini a fuskokinsu ba.
“Kai Asabe mijin nan naki ya cika taurin rai,yaƙi kamar ba gobe! ”
“Ki bari ni har sai da na sare na zata ba za mu iya kai shi ƙasa ba”
“Yanzu dai ke ma kin huta da alaƙaƙai!”
“Ba ki ji sanyi a ranka ki ba da ya zamana babu wani wanda ya san sirrin ki?”
Abokan Asabe ne ke tattaunawa game da yaƙin kashe mijinta da suka taya ta a jiya wajen kashe mijinta Audu.Shiru ta yi ta na saurarensu,rabin hankalinta ya na kan Tuwalle wacce ke can zaune a rakuɓe ɗan nesa da su.Fahimtar haka ne ya saka Mairo cewa “wai mine ne? Ko ita ma Tuwallen ki na so ta bi Babanta ne?”
Da sauri Asabe ta dubeta,ta wani taɓe baki “hum! Duk wannan abin da naka don waye nake yi? Saboda Tuwallen ne! Saboda ina son gobenta ta yi kyau.”
Mairo ta ce “ai na ga kamar kin damu ne sosai sai kallonta ki ke”
“Eh ina tausayinta ne,na san za a ɗauki lokaci kafin mutuwar ta fita ranta”
“Wannan ai ba damuwa ba ne,akwai wani magani da nake da zarar ta sha shi to shikenan za ta sakin ranta ta ci gaba da walwala ” ɗaya daga cikin matan mai suna Bintoto ta faɗa.
“Mutanen ƙauyen nan sam ba su da kara dubi duk sun watse ko awa ɗaya ba ayi da kaudo gawa ba ” cewar Salame,Bintoto ta karɓe da cewa “saboda sun ga Mairo ne ,kin san kusan duk tsoronta ake a ƙauyen nan”
Cikin jin haushi Mairo ta ce “ina ce dai ba ni ɗaya ba ce mayya ,duk ɗaya nake da ku”
Duk suka yi dariya, Bintoto ta ce “to ai taki ce ta fito a fili,sam ba ki iya takun saƙa ba”
“Ku yi shiru” cewar Asabe.
Na gaji da zama cikin rana,hakan ya sa na tashi tare da nufo inda suke.A gaban idona Inna ta yi masu alama da hannu,duk da banda tabbaci amma na fi tunanin kamar ba ta so na ji hirar da suke.
Ban wani tsaya ɓata lokaci ba,ina zuwa na zauna kan tabarma tare da yin kwanciya na ɗora kaina bisa cinyar Inna.
“Ƙatuwa da ke shi ne ki ka wani zo ki ka yi kwance kan ƙafafuwanta” cewar Salame cikin sigar wasa ta yi maganar ta na ƴar dariya.
“Duka nawa take? Shekaru sha uku ɗin,kar ku takura ma auta ta” Inna ta faɗa ta na ɗan bubuga bayana.
“To ku tashi mu tafi sai in mun haɗe zuwa dare ko?” Mairo ta faɗa ta na mai tashi tsaye, Allah na gani sam na tsani matar nan.
Duk sauran tashi suka yi su ma,hira suke a jirkice wacce sam ban kanta ba balle ƙafafu.
Su na fita,sauran matan ƙauyenmu suka fara shigowa su na yi ma Inna ta’aziya.
Haka dai aka yi ta shigowa na tsawon kwana uku bisanin ƙafa ta tsana.
Hum! Ban san a ina Inna ta samu kuɗi ba kawai dai na ga ta yo sayayyar kayan miya.Irin su magi,garin kwaki,gishiri,tafarnuwa da dai sauran su.
Bayan ta gama ƙulle kayan miyar cikin leda sai ta zuba cikin faranti.
“Zo ki shiga gidaje ,ko Allah yasa kin yi cinaki.” Inna ta faɗa ta na kallona,na turo baki ina jin haushin yadda Inna sam ba ta damu da mutuwar Baba ba.
“Zo na aike ki gidan Salame ,ki ce mata maganin da tace za ta bani na aiko ki amsa” Inna ta faɗa cike da kulawa,na miƙe tsaye tare da kakaɓe burgujejen bujena.
Har zan tafi sai kuma Inna ta tsayar da ni “ungo ki kai mata daudawa da gishiri ,ki ce na fara sayar da kayan miya” na karɓa kafin na fita.
Ina tafe ina waƙa har na kai gidan Salame,sallama na ta yi ba a amsa ba.
Daga can cikin banɗaki ta ce “ina wanka ne ki jira ni” kan wani gutun ƙunƙu na je na zauna ina rera waƙa tare da wasa da kare ina yin zane.
Kamar daga sama na ga ƙatuwar tsutsa ta na fitowa daga wani ɗan rame alamu gidanta ne.
Yadda take shiga ta na fitowa ya ɗauki hankalina,ta saka kanta domin komawa cikin ramen kawai sai na saka karen da nake wasa da shi na cake bindinta tare da danne shi.
Ta ji zafi ne ko kuwa mine ne oho! Kawai dai na ga ta fitar da kanta daga cikin ramen tare da kiciniyar janye bindinta.Cike da mugunta na hude ledar gishiri na fara zuba mata a jiki,na sani sarai tsutsa ba ta son shiga gishiri.
Yadda take birkiɗoɗoniya shi ya fi komi yi min daɗi,sai ƙara juyata nake ina zuba mata gishirin.
Sam ban jin tawowar Salame ba,sai saukar muryarta na ji “mine ne ki ke haka?” Da sauri na jefar da karen ina cewa “Ina kwana Inna Salame ? Inna ce ta aiko ni ”
Ba ta amsa gaisuwar da na yi mata ba, sai kallon ƙasa da take yi ni ma na kai idona nan na yi tozali tsutsar nan a kwance kamar dai ta mutu.
“Da ta aiko ki sai ta ce ki zo ki yi mugunta?” Ta tambaye ni cikin zafin rai.
Sarai na fahimci abin da take nufi,amma ni ban ga wani aibu ba a nan don na cutar da tsutsa tunda ba Ɗan cikinta ba ne.
Ta ja tsuki ta shiga ɗaki,ba ta jima ba ta fito hannunta riƙe da leda.Ta miƙa mini na karɓa,sai nace “ga kayan miy…” Cikin haushi ta katse ni”na ji don Allah! Wuce ki tafi”
Yadda ta wakice ni sam ban ji daɗi ba, wannan ya saka na fita a guje.
Inda na yi sakarci da na zo gida maimakon na baiwa Inna labarin komi sai na yi shiru da bakina ashe babban kuskure ne.
Dare ya yi amma sam na kasa rumtsa wa saboda raɗaɗi da azabar da duk jikina ke yi mini.
Kuka kawai nake ina susar ko ina,bisanin na tashe da Inna .
Fitila ta haska mini,sai na ji ta na salati tare da ambaton sunan Salame….