Kuskurena Hausa Novel Complete
KUSKURENA
“`Gidan karamci, rubutu don ci gaban al’umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.“`
*RUBUTAWA*
*BEENTU*
Sadaukarwa ga kanwata,wanna labarin gaba daya sadaukarwa ce agare ki.
Safiyah Naseer ki yi yadda kike so Blood.
P-1/5
Kamar yadda sakani suke juya zuwa mintina su Koma su juya zuwa awani daga nan zuwa kwanaki.
Lokutan sun kasance tamkar Jan su ake haka kazalika kwanan ki rayuwa ka ke karewa ba zaka tabbatar da hakan ba sai ka juya ka gan ka acikin kabari.
Allah ka yafe mana zunuban mu kasa muyi karshe Mai kyau.
*MALLAM SULAIMAN MAI ALO*
Sai Naga Bayanki Hausa Novel Complete
Shahareren Mallamin makarantan Alo
ne mai dauke da dinbim almajira dake zaune a anguwan liman dake Zaria.
Matan shi biyu da Yaya shida,inda uwargidan Hadiza shi ke da guda biyar maza hudu mace daya.
Abbas ne babba sai shu’aibu sannan Sadiya sanna yan biyu Hassan da Usaini.
Amaryar shi Hauwa’u na da ya daya tilo Fatimah wace ta kasance ta fita zaka cikin yayan gida.
Kasancewar gidansu na malamai ya Sanya su tashi da karatu addini fiye da boko duk da dai shima ba baya ba .
Mallam ya kasance mutum be Mai tsanani akan yayan shi mussanman su da suka kasance mata Wanda ya kance suna da matukar rauni.
Fatima yarinya ce kyaukawa Dan babu inda ta baro mahaifiyarta wace ta kansace shuwa.
Ita kadai ce ta fita zaka a cikin yaran gida duk inda daukan magana yake tana gurin haka ‘kida da rawa kamar dangin dujal haka take kullum zai nuna nima din ya ce mai yanci agidan su tamkar ko wani da dake takama da gidan uban sa.
Dogon tsaki na ja kafin na mike,hijjabi na dake rataye saman kofar dakin mu na fige tare da fita daga daki.
Ina fita kuwa naci karo da Ussain yana ja min rigata daga igiyar shanya ban yi wata wata ba kuwa na kwatsa mai mari.
Ihu yasa wanda ya ja hankalin mutanen gidan gaba daya suka fito suna tambayar ba’asin kukan nashi.
Ko ajiki na kuwa Ina jin shi yana mayar da zance,caraf kuwa Sadiya ta amshi da fadin”Wallahi Yaya Abbas ita ce ta kawai ta dinga zabga mai mari akan ya ja mata riga”ta zabga min harara.
Kallon sama da kasa na mata”ko zaki rama masa ne mandiyya?
Caraf kuwa ta amshe”kin fi karfin a rama m……
“Kai dalla ya ishe ku mallamai “Ya Abbas ya katse mu cikin tsawa.
“Zaku tashi ku bar nan ko sai na bi jikin ku yanzu”.
Cike da takaicin juna mu kama gaban mu.
Daki na Kuma Ina kunkuni,tun shigowar ta take bin ta da kallo zuciyar ta cike take fam da tarin takaicin ta gefe Kuma addu’ah shiriya take mata.
“Kalan rayuwar da kika zaba ma kanki ke nan ko Fatimah?
Shiru nayi Ina sauraran Ummin”ki yi hakuri”.
Murmushi tayi mai sauti”Na yi Zarah! Allah ya shirya min ke”.
Cike da jin dadi na amsa”Amin Ummi na”.
Hira muka shiga yi inda kusan duk rabi nasiha ce take mata akan gyaran halayenta.
Shigowar Umma ce ta katse mana hirar”Ina kwana Umma”.
Na gaidata,amsa min tayi cikin sakin fuska sosai.
Fitowar Mallam yasa duk muka mike muka fita zuwa tsakar gida.
Bin mu yayi da kallo kafin ya maida idon sa cikin nawa inda nayi saurin yin kasa dashi.
“Kina ji na ko kar ki sake na dawo cikin gidan na iske baki nan idan kuma hakan ya kasance zan yi mumunan saba miki don kuwa duk hukunci da na yanke Miki kar ki yi kuka da kowa”.
“To”kawai na iya cewa cikin halin ko in kulla don na saba jin haka sai dai da duk kan alamu wannan karan babu daga kafa alamarin Mallam.
Fita yayi inda muka bishi da addu’ah dawowa lafiya.
Daki na koma nayi kwanciyata,muryar aminiyata Safina na jiyu ta na gaida su Umma da ke tsakar gida.
Cikin zumudi na mike zan fita har na ke kofa mu kayi karo da ita.
Cikin farin cikin ganin juna muka rungume juna,bata gurin zama nayi.
“Kawata two daz kin buya”cewar Safina.
“Hmmm! Ke dai bari kawai kawata Mallam ya samin takunkumi”
“To! Ya za’ayi yanzu gobe bridal shower din Hajara”.
“Ke don Allah”
“Wallahi kuwa”.
“Hmmm aikuwa duk yadda za’ayi sai na je”.
“Allah ya ha naki sa’ar zuwa”caraf Sadiya ta amshe da fadin haka wace ke kwance ta jiyo duk hirar ko Fatima bata lura da ita lokacin da take kwance har Kuma zuwan Safina duk basu farga da ita ba adakin.
“Mtswwww! Ni fa kinga shishigi ne bana so ko Ina ruwan mutum da ni”.
Ta fada tana fincikar hannun Safina suka yi waje.
Cigaba da ta taunawar yadda gobe zasu yi ta fita daga kafin Safina ta tafi.
Saka da warwara Kafin daga bisani ta samawa kanta mafita.
*******************
“Haba Ahmad ka dinga sanyawa zuciyarka salama man,kana ganin dai bayan kai da yan uwan ka banda Wanda zan kalla in ji sanyi a raina so kake damuwa tai maka yawa har sai ciwon zuciya ya kama ka na fadi ka mutu”.
Wata yar farar dattijiya ke fada,wace kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa duk da yanayinta kadai zai nuna maka tana cikin rufin asiri.
Kansa na kasa Yana sauraron fadan da mahaifiyarsa ke Mai.
Cikin sanyi murya ya ce”Don Allah ki yi hakuri Umma shi damuwa yin kansa ne ba naka ba”.
“Ummm! Ahmad kenan,duk da hakan ya kamata ka sanyawa zuciyar ka sallama”.
“Insha Allah Umma”.
Gyada kanta take cike da tausayin sa tun sa’a da ya rasa aikin sa ya ke cikin tarin damuwa da kunci duk da ita ma karfin hali kawai take don tasan watan tunar asirin su ne ya kama don dukan su day aikin nashi suka dogara.
Mikewa yayi santalelan saurayi ne fari tass ba za’a Kira shi da dogo ba ko guntu Yana sa tsayi daidai misali fuskarsa na kewaye da kyaukwan saje da dogon hanci hade da madaidaicin baki, kyaukwa wane kyau nai kyau ba rin kyau dinn sosai ba.
Kai tsaye dakin shi ya nufa dake da ga soron gidan.
Kwance yayi akan katifarsa zuciyar shi tamkar zata fashe don haushi,shi damuwar shi ba korar shi da aka yi ba aa kazafin da sukq jefe shi dashi ne tafi taba zuciyar da Kuma gidan jiya da su ke dusar komawa.
Ahmad Adam Sale da ne na biyu gurin Mallam Adam da mahaifiyar Zainab su biyar ne Mata uku sai su maza biyu Shine babba cikin mazan sai kaninsa Aminu,bayan yayar sa Farida sai Saliha sanna autar su Amira.
Asalin sun yan jahar adamawa ne,tun da aka kawo mahaifinsa almajiran ci Zaria tun daga Bai koma gida ba sai biyo shi da matar shi suka yi.
Suna da rufin asiri daidai na su inda duk sunyi karatu daga arabi har boko mahaifinsu ya rasu tun kafin cikin Amira na karami,hakan yasa nauyin gidan ta koma kan Ahmad duk da lokacin ba wasu shekaru ne dashi ba.
Haka rayuwar take gwara yau fari gone tsuma har ya kammala karatun shi lokacin Kuma bikin yayarshi Farida ya tashi duk da dai ita ma mijin nata ba Mai karfi bane sai dai rufin asiri.
Bayan Kamala service dinshi kam ansha fama inda da kyar ya samu aiki awani kamfani hada takalma,sosai aikin ya taimaka mai inda ya canza wa kanen shi makarantan daga na gobnati zuwa ta kudi.
Kwatsam a sake daukar Sabin ma’aikata,Wanda ya zo na masa da tarin kallubale kasancewar zuwa hasabibiyar Ramlat da zai iya goge ta cikin tarinhin rayuwar sa.
Tun da ta nuna masa tana son shi yaki ta shiga rakurawa rayuwar sa har ranar da kaddarar barin aikin sa ta same sa.
Shigowa tayi cikin office din bashi yayin da shi kuma Yana duke yana duba agogo shi.
Jin saukar hannu yayi akan mazaunan sa an kai mai wani
irrin cafka,arazane ya waigo,tozali yayi da ita tana binshi da wani irrin kallo Mai cike da tsantsar sha’awa.
A zafafe ya dago tare da zabga mata mari,cike da furgici da razana ke kallon shi hannuta dafe da kumatun ta.
“Ke wace irrin kariya ce dabba ce Maya kawai”.
Kallonsa tayi”Ahmad ni ka mara?
Masa da kasa ya kalleta”E! Zaki rama ne”.
Dariya tayi”bazan rama ba Amma sai kayi nadamar hakan Kuma a yanzu zan nuna maka aikin dabba Kuwa”.
Tsaki yayi”dallah gafara Mallami fice ki bar min office kafin yanzu in nada Miki duka”.
Dariya ta Kuma sake fiye dana farko”kai ka isa ka daken in ba ma so da Bai da adalci ba Ina ni Ina kai office Kuma yau zanga ni da kai wa zai barshi.
Kafin yayi wani yin kuri ta ya ge rigarta tari da cikume wuyar rigar sa kokarin finciketa yake inda take sakin ihu da Kururuwar neman taimako.
Kafin Mai har an cika office din duk Wanda ya shigo sai yayi turus ita Kuma ganin bukatar ta ta biya ne yasata dungulewa a gurin dare da fashe wa da kuka.
“Amma ba ka kyautawa rayuwar ka ba Ahmad cin zarafin har a gurin neman halaliya tirda kai wllh”
Cewar Manager company.
“Yallabai wllh b…..
“Don Allah rufe min baki Mallam boyeyen halin ka ne ya bayyana,haka dai kamar ba za ka aikata ba, ka zo office dina yanzu ka saman”.
Zama da mutane ba ka gane Mai son ka da gaskiya sai kaddara ta afka maka.
Na jiyu muryar Zainab tana ba da bayanin karyar da ta riga ta kintsa,acewarta dama yasa ba nemanta ganin ta ki yarda yayi kokarin afka ma ta yau.
Sanadin barin aikin shi kenan bayan tarin bacin suna ta da janyu Mai.
Hakan da bata duk wani farin ciki da cusa Mai tarin bakin ciki da damuwa acikin zuciyar sa.
**********************
Tun da safe na ke fakar ido Allah Allah ne in samu dama in fice don bani son bidirin yau din nan ya wuce ni.
Kamar kullum yau jadda rashin fitar Mallam ya min na dau amsa ne kawai Amma Kuma fita kam yau babu fashi sai na yi shi.
Misalin karfe uku gidan yayi tsit nayi zirfif na fita bayan na leka na tabbatar da babu kuwa a tsakar gidan.
Cikin saure nake har na fice daga layin ba tare da na hadu da kowa ba.Wani karfafan ajiya zuciya ta sauke kafin ta nufi titi.
Bata jima da tsayuwa ba ta samu mashin zuwa low-cost inda za’a yi bridal shower din.
Tun kafin ta karasa gidan sautin kida ke ratsani cikin sauri na karasa aikuwa yanmata ne jirgib ko wace ta yi kwalliyar cikin anko.
Waigawa na shiga yi ko zan ga Safina.
Da ga can na hangeta,cikin sauri na isa gare ta.
“Wayyo kawata”.
Ajiyar zuciya na sauke mai nauyi”Hmmm!Ina kika shiga ne?
Na fi minti goma Ina neman ki”.
“Ke dai bari kawata,kawai Ina chart da Habibi na ne”.
“Ummm su Habibi manya”.
Dariya muka sake cike da jin dadi da nishadi,sauyin kidan da ya canza ne yasa ni fita cikin filin,gaba daya na manta da wani sharidin Mallam ko hukuncin sa.
*************************
Mikewa yayi daga kwance,jin sautin Kiran Sallah Mangariba daya Kara de unguwar.
“Umma na tafi masallaci” ya fada cikin daga murya yadda zai kaima Umma dake cikin daki.
Cikin sauri ya nufi fita masallaci.
Kiran sunan shi da aka yi ne yasa saurin waigawa ganin abokin shi Jabir yasa shi tsayawa.
Musabaha suka daidai isar su massalaci.
Jeruwa suka suna taba hira jifi jifi.
“Yauwa! Na tuna Babanmu ya sa ni aiki ko zaka dan zaga da napep din tawa?
Wani irrin farin ciki ne ya lulube zuciyar sa,dama duk tunanin shi inda zai samu kudi abin da za’a karya dashi da safe.
Cikin murnan da ya kasa boyewa akan fuskar shi ya amsa wa Jabir tare da Mai tsantsan godiya.
Dai dai kofar gidan su Jabir din suka tsaya bashi makulin yayi gida, Ahmad kam daukan napep din yayi don ya dan zagaya.
*******************
Shiru kawai yayi yana bin iyallan nashi da kallo,kallo daya zaka Mai ka fahimci tsarsar bacin ran dake kwance aka kamilaliyar fuskar shi.
Babu abin da Ummi ke yi sai hawayye domin da ta San duk laifin kanta zai juya gefe guda Kuma tana tunanin taurin kai da rashin tsoro irrin na Fatima.
“Wallahi na gaji da dauko min magana da zubar min da mutunci da yarinyar nan ke yi,sai ka ce ita kadai na haifi duk unguwar nan gulma ta da zunbe na akayi to wallahi yau kam ta kaini bango”.
Masifar shi ta katse ta daga tunanin da ta tafi.
Umma ce ta katse shi cikin bada hakuri inda ita Kuma tayi tsiitttt ta jiyu shi,mugun tsaki ya ja tare da ficewa daga gida.
Gaba daya gidan yayi tsiitt tamkar babu mutane agidan sai bi da tsoran fushin Mallam.
*******************
Tashin hudubar shadain(kida),yasa bamu san anyi Sallah Mangariba ba ballanta sallan isha da ake ta Kira a masallatai.
Sai karfe 9 kafin Dj yana sepikun shi,dan kari sai lokacin da tsure tare da tuna gargadin Mallam tsoro,fargaba tashin hankali duk suka diran min lokaci guda.
Baban tashin hankali na satar fitan da nayi cikin sauri na fusgo hannu Safina na nufi get da ita.
“Lafiya kawata?
Cikin sauri na girgiza mata kai”babu lafiya Safina,ban san hukunci da zan tarar agida ba”.
Hawayye na ji suna bin fuskata inda yayi dai dai da murdawan da marata tayi.
“Innallilahi wa’inna illahi raji’un”.
Burgi Safina ta ja tare da kallon na cikin furgice”Fatima lafiya”.
“Babu Safina Period ne”.
Na fada kawai Ina fashewa da kuka shafff na manta da lokacina kenan don tsabar zumudin son zuwa biki,Baban tashin hankalin ya ke zuba min tamkar Mai barin Dan tayin ciki.
Cikin sauri Safina ta rike ne zuwa Bakin titi lokacin kam jinin ya fara zuba min hakan yasa na Kara volume din kukan da na keyi.
*************************
Ba laifi tun da ya fito ya samu passengers kasancewar dare yasa ta samu alheri ba laifi.
Cikin nutsuwa yake tukin shi farin cikin ne shinfide akan fuskarsa,sauke passenger kenan na kokarin barin wajen,ya hange su suna tsadai shi.
Tsayawa yayi cike da tausayi da ka nesa Yana tunani ko Mai nakuda ce ganin yadda yar uwar ta ta rikota tana duke rike da marar ta.
Cikin hanzari ya nufe su sai sannu yake jera musu fada mishi inda zasu shiga kawai sukayi ba tare da tambayar kudin su ba.
Fatimah kam ban da kuka babu abin da take yi zuwa yanzu duk jikinta ya baci ga azabar ciwon mara.
Ta na jiyu sanyayar muryar Mai adaidatan dake ta jira Mata sannu jifi jifi.
*************************
Yana daga zaune aka dakalin da yake zama don biyawa daliban shi karatu.
Zuciyar shi mugun tafasa yake don Yana jiyu gulmar su Mallam Sani mokanci shi akan sun ga Fatimah ta shiga adaidatan saurayin ta bayan sun gama badalar su a kan titi.
Cize leban shi yayi Yana jin kamar ya fashe da kuka ko zai samu sasaucin dake zuciyar sa.
Yayi zurfi cikin tunanin irrin hukunci daya dace da ita ya jiyu karar parking din nepep a kofar gidan.
Cikin hanzari ya daga kanshi caraf idon shi ya sauka akan ta kawata rike da ita kasancewar fitilan napep din akune ta ke.
Dukan su babu wanda ya lura da Mallam dake tsaye ba yana bin su day wani irrin mugun kallo ganin dai tabbass gashi saurayin nata dai shi ya dawo da ita.
Kokarin fitowa take inda Safina ke rike da ita,wani irrin jiri ne ya kwashe ta inda tayi baya Kwata Kwata Safina bata gama tsayawa da kafafon ta ba duk suka yi baya,cikin zafin nama ya fito ya riko su gaba daya,inda Fatima ta tafi gaba daya ta fada kan fadadan kirjin shi.
Sallatin da su ka ji an rafka ne ya ankarar dasu mutanen dake kewaye suna bin su day kallo.
Cikin azama ya zame ta daga jikin shi,yayin da Safina ta rike ta.
Fusgeta yayi a fusace ya shiga zabga Mata mari
“Haba Mallam! Ai duka bashi ba ne masalaha ka fara duba halin da take cikin man”fada Ahmad yana isa kusa da Mallam don ya amshe ta.
A fusace Mallam ya kai mai mari”wato kun gama lalacewar da zakuyi ka dawo da ita ko? Tare da cikuma wuyan rigan sa.
Tsammm yayi yana bin shi da kallo cikin rashin fahimtar abin da Mallam ke fadi.
Daga muryar da yake ya dawo da hankalin mutanen kansu ciki kuwa har da su Umma dake cikin gida.
Kafin ka ce mai unguwa ta cika makil ana bin mu da ido. Mallam ya Ahmad fam kamar Wanda ya cafke barawo.
Beentu
[05/05, 5:34 am] +234 701 497 9567: *KUSKURENA*
*Beentu*
P-5/10
*Noble Writers Association*
Wani irrin kuka ya sake kubce min ganin yadda na ja ma mutumin da ko taba gani na bayi ba cin mutunci da Kuma tozarci.
Saukar wani lafiyayen mari da na ji ne ya san ni dauke wuta difff daga kukan da nake.
Bin Ummi da ta wanke fuskata da mari na ke waxe babu abin da take sai huci kamar wata mayuwanci maciji.
“Kin cuce ni Fatimah! Kin ha’inci ni haka Kuma kin wulakantan tarbiyar da muka gina ki akai”.
Cikin matsanaicin kuka na ke girgiza kai”Ummi wallahi ba h…..
“Zaki rufewa mutane baki ne ko Kuma zaki cigaba da fitsarar naki”.Ya Abbas ya tari numfashi na cikin tsananin fushi alamar Yana gab da kai min duka.
Gaba daya kan shi ya gama kulewa tunani wace irrin kaddara ce Kuma ya sa shi daukan su a napep din for the first place ma mai yasa ya amshi ta daga gurin Jabir.
Bin su kawai yake da kallo kamar wani soko musanman kwallar rigar shi da Mallam ya cafa ya rige ta kam kamar wani ya rike wani kwarto.
“Haba Mallam ka sake ki shi man mu bi komai ahankali duba da yadda ka tara ma kanka jama’ah ga Kuma halin da yarinya ke ciki”.
Cewar Umma tana kokarin kwantar wa da Mallam hankali.
Shaf shi ya manta da wanzuwar ta wajen cikin sauri ya sake wuyan rigan Ahmad tare da karasawa inda take.
Turusss yayi duk wani zafin rai da nufin kai mata wani wawan duka ne ya tsaya cakkk ganin halin zubar jinin data ke ciki.
Sake kamkame Safina nayi Ina cigaba da kuka mai matukar tausayi ga wanda ke saurara burina bai wuce Mallam ya tausaya min ba.
Tarin nadama zuwa party nake tare da jin tsanar duk wata bidi’a acikin raina.
Zuciyar shi ya ke jin kamar ta tsaga kirjin shi don tsabar bugun da take,Allah shine masa’ni Yana matukar son Fatima cikin yayan shi fiye da duk sauran ya kan yi tunanin ko don son da yake wa mahaifiyar ta ne,taurin kai da kafiya irrin nata ke jin tsananin haushin ta.
Yasan dai tana da rashin ji,sai dai ko kusa baiyi tunanin rashin jin nata har ya kai haka ba.
Bin jinin da ke jikin ta yayi Bai san lokacin da wasu zafafan hawaye suka zubu da kwayar idon shi.
Jiri ne ya shiga daukan shi,inda cikin zafin nama Abbas ya rike shi tare da dakawa mutanen dake kewaye da su tsawan da ya sa su barin wajen.
“Don ubanki kina tsaye awajen ba za ki shige gida ba?.
A tsorace na rike Safina gam tsananin tsorn Yayan nawa na kama ni.
“Ta shiga wani gida Abbas?.
Cak na tsaya Ina bin Mallam da kallo Wanda ke girgiza kanshi cikin tsananin takaici.
Ahmad dake kokarin wucewa don shiga napep dinshi ya bar gurin ya tsaya cak,zuciyar shi fal takaici wannan tsohon,haka kawai ya ke jin zuciyar shi na ingiza don tsayawa ya ga yadda zasu yi.
“Mallam kayi hakuri ka barta ta shiga daka cikin ko dan halin da take ciki”.
Maganar Liman ya katse shi daga tunanin da ya tafi.
“Wallahi!Wallahi!!Wallahi!!! Rantsuwa uku kenan yarinyar nan bazata shigar min gida ba bayan ta gama yawon ta”ya kai karshen maganar tasa a matukar fusace.
Sautin kukan Ummi hadi da na su Sadiya ke tashi,duk da ita din yar uwar tsama ta ce amma tafi kuwa jin wannan furinci na Mahaifin su.
Cike da magiya Liman ke cigaba da ba Mallam hakurin”Babu inda zata shigan min ta bi shi lalatacen daya gama abin da zai yi da ita sanna ya dawo da ita.Iba ma ta raina ni ba har ni zata kawowa raguwar kazatar ta cikin gida wato Mallamin sakarai ta wuce ta bishi su daura daga inda suka tsaya”.
Da hazanri na ja jikina daga na Safina zuwa gaban sa cikin durkusa wa aka guiwarta”Mallam in kana ma Allah ka min rai hakuri Wallahi ban aikata abun daka ke tunani ba hasalima yau na fara ganin wanna bawan Allah,ko sani shi ba yi”.
“Ke dallah rufe mana baki”ya Abbas ya fada ya na Mai shurina tare da nufar inda Ahmad ke tsaye ya harde hannuwansa jikin keken shi.
Gadan gadan yayi kansa da nufin cakumar su cikin zafin nama ya matsa mai tare da dujewa.
Ganin suna neman dambe yasa Liman saurin shiga tsakanin su”Yaro yi hakuri maza ta da keken ka,ka tafi”.
Kallon datijjon yayi tabbas da bai San girman furfura ba da ya make shi ya ga abin da ya taka.
Kokarin shiga adaidaitan sa yake karaf sautin muryar Mahaifin yarinyar ya duke kunuwan shi,cikin matukar Kaduwa ya jiyu.
“Abbas! Kyale shi Bai dai laifi ita ce ta janyu shi don haka kar ka ga laifin sa.
Mai da duban shi yayi kan iyallan shi”ku wuce ku shiga gida”.
Sum sum na mike na dusa kofar gida,cikin zafin nama na jin an fuzgu ni.
“Gidan wa Zaki shige mandiyya?
“Mallm don Allah ka y…..
“Kada ki kuskura maza koma inda kika fito Kuma wallahi naji kin je gidan wani dangi ban yafe miki ba Kuma ko da wasa kada ki kuskura in gan ko Mai kama da ke ne a cikin gida na”.
Tashin hakanli ya dirar min na San halin Mallam Sarai tamkar yunwa cikina.
Mutum ne shi Wanda indan yace E to e din ne haka idan yace Aa.
Muryar Ummi na ta farkar dani daga duniyar tunanin Dana tafi.
“Haba Mallam wannan wani irrin hukunci ne?
Juyuwa yayi kanta azafafe”tambayata kike wani irrin hukunci ne wannan?
Kin manta abun da nace da ita kenan kafin in fita?
Kuka duk su Umma ke yi hata yan biyu dake da karacin shekaru kuka suke.
“Haba Mallam kayi hakuri man idan ka kure ta cikin Daren nan Ina zata?
Anya ka mata adalci kuwa?
Ka kyautawa mahaifiyar?
Idan rai ya baci hankali baya gushewa ya aiki da hankali da illimi ala’ranma”
Liman ya fada cikin tausasa harshen shi do San tausar zuciyar mallam din.
Ahmad kam ganin abin na su bana karewa ba ne yasa shi yunkuri buga adaidanta shi yai gaba.
Cikin sauri Liman ya tsaidashi ganin Mallam na Mai magana bai ji shi ba.
“Tabbas zan mata afuwa Amma da sharadi aurwn wannan takadirin a yanzu yanzu”.
Wani irrin bugu zuciyar shi tayi aure ina yaga halin riketa ko ba wannan ba ma haka kawai bai san yariya ba ake kokarin kakaba mai.
Bayan duk yanzu agaban shi ake nuna halayarta.
Bai farga ba daga duniyar tunanin da ya tafi ya jiyu Liman ya rike hannun shi gam zuwa kofar gidan Mallam.
Gaba daya gabobin shi sun sare tamkar sarafa jijiyuyin shu hadi da tunanin shi ake,ya kasa yin wani tunani balle ya tabuka ma kanshi wani abu gaba daya kwakwalwar shi atunkushe ta ke.
Bai dawo daga tunanin da ya tafi ba sai da Liman ya taba shi tare da tambayar sunan shi.
Firgit ya dawo hayyacinsa tare da saurin rike hannun Liman zuwa gefe.
“Baba! Gaskiya akwai matsala don ni dai bani da halin rike mace,hasalima ni ke daukan dawainiyar mahaifiyata da yan uwa na Kuma ni yanzu haka ba aiki ne da ni ba”.
Cikin kankan da kai Liman yace”Yaro kar ka samu damuwa ni nan zan biya maka sadakin”.
Cikin tsantsar damuwa ya ce”Baba wallahi akwai matsala yadda San Lau ta gidanmu haka kazal kum…..
“Jahadi zaka yi yaro ka tseratar da ita daga cikin fushin iyayye,ka Sanya ta amazaunin kanwarka”.
Shiru yayi kawai Yana tunanin yadda zai yi da Umman shi duk da dai yasan bata da matsala ko kadan
“Menene sunan yaro”.
“Ahmad”ya fada cikin sarkewar harshe.
“Wani barayi ka ke! Atakaice dai gidan ku da inda muke da tabbacin samun ka,sannan kada ka damu da kai na zan bika har gidan din yiwa mahaifiyar taka bayanin komai”.
Tabbas Mallam ya daure shi da jijiyuyin wuyan shi.
Sha biyu dai dai aka daura auren Ahmad da Fatima a jimilar sadaki naira dubu hamsin.
Wani irrin sanyi ne ya shiga bin jikin shi tamkar ana kwara mai ruwan kankara.
Ko kadan Bai jin akwai wata laka ajikin shi ba.Hakan yasa shi zama kan dakalin da yake zaune.
************************
Duk wani abu da sukeyi Ina daga tsugune Ina jiyu su.Nayi kukan har hawayena sun kafe,dole na koma yin na zuci.
“Ga sadakin ki nan”Mallam ya fada ya miko min kudin.
“Ke Sadiya maza shiga ki hadu mata kayanta! Ka da ki sake na ji kin yi wani mugun abu Kuma da zarar kin kashe auren ki nemi wanj uban ba ni ba.Sannan kada na ga kafar ki a gudana sai in ni na neme ki”.
Yana gama fadin haka ya baza rigar shi tare da shigewa gida.
Matsuwa kusa Dani su Ummi na su kayi,rungumeta nayi Ina fashewa da ni irrin kuka”kinga illar rashin jin magana da taurin kai ko Fatima?
Yanzu wa gari ya waya?
Kuma wannan jinin na jikin ki fa?.
“Wallahi Ummi ban aikata komai ba wata na ne ya zo kawai.Don Allah ki yafe min na yi kuskure bazan sake ba”.
Dawowar Sadiya janye da jakata inda Ya Abbas ke bayan ta dauke da ghans masgo dina ne yasa ni saken sabon kuka.
Kiran da Mallam yayi musu me yasa muka kamkame juna Sadiya muna fashe da kuka kamar ance mana Mallam ne ya mutu.
Cikin dauriya ya Abbas ya raba mu inda Umma ke min alkwarin zuwa suga inda zan bude sabuwar rayuwa.
Babu abun da nake sai kuka har muka shiga adaidaitan da Liman,Tafiya kawai muke har muka isa daida kofar wani gida.
Kadawa yayi lokacin karfe 1 daidai.
“Allhmdllh!Umma gashi nan”muryar wani matashi ya sauka a kunne na.
“Bissimillah Baba mu shiga ko?
Cikin zumudi dattijuwar ta riko shi adai dai sanda na fito.
“Kana lafiya Ahmad?
Ina ka je?
“Lafiya klau Umma,Ina tare da baki”
“Baki Kuma?
Lafiya?
Ganin yadda ta furgice yasa shi sakin Mata murmushi”lafiya lau”.
Juyawa yayi inda muke tsaye da Liman.
“Baba Bismillah”.
Ba tare da ya jira cewar Umma ba ya shiga da su ciki.
“Ahmad lafiya kuwa?
“Lafiya klau Umma.Bari inga Faruk in zo”.
Binsa tayi da ido har ya shige gidan su Faruk din.
Iso tayi Mana zuwa cikin gida.
Haske kwan wuta dake tsakar gidan ne ya haska mu hakan yasa ta bi ta da kallo ganin yadda jiki gaba daya ya baci da jini, ga idanuwan ta a kumbure alamar ta ci kuka har ta gaji.
Wani irrin tsoro ne ya dirar wa zuciyarta”Ya Allah kasa ba abin da na ke tunanin ba ne”.
“Bismillah Baba mu shiga daga ciki”muryar Ahmad ya dawo da ita daga tunanin da ta fada.
Shiga pallon Umma suka yi,inda kowa ya nemi gurin zama Fatima kam rakube take daga jikin kofa.
Kallon kanan sa tayi”ku bamu guri ko”.
“Aa Umma bar su! Zama duk ya shafe su”cewar Ahmad.
Gyada kai tayi,gaisawa suka yi da Liman inda Fatima ma ta gaisheta kan aduke akasa.
Duk wani abun daya faru Mallam ya kwashe ya sanar da Umma duk abin da ya sani da Wanda ya gani.
Idan Ahmad ya daura da daukan su day yayi a keken sa.
Kanta kawai take gyadawa cike da dunbin mamaki”To Hajjya kinga Da dai na kowa ne don Allah ga amanar Fatima duk abin da tayi na kuskure a tsawatar mata,tsarin Allah tun kafin ka San da wanzuwarka aduran duniya ya gama tsara maka rayuwa,Ina so ki dauki wannan a matsayin rubutaciya tun daga rabbi samawati,Allah ya kaddara ita din matar shi Kuma ta wannan hanyar ce sillar haduwan su cikin inuwa guda,ki Sanya ta mazaunin yarki na San kin San halin da uwa kan shiga idan Allah ya jarabe ta akan Yaya don Allah ga ta nan ki rike ta da Amana tamkar ya cikin ki”.
Murmushi kawai Umma ke yi zuciyar ta a cunkushe ta ke ta rasa ma wani irrin tunani ne ya dace tayi.Har ga tayi alkawarin rike ta tsakani da Allah don da da dukiya ba’a musu mugunta Bata San inda nata yayan zasu fada ba.
“Ba komai Mallam insha Allah Fatima zata zauna dani kamar mahaifiyarta don da ita da Ahmad duk yaya na ne,Allah Kuma ya shirya mana zuri’a”.
Cikin jin dadi da ya bawa da dataku irrin na Umma ya shiga zabga Mata godiya.Kiran sallah da akayi ne ya sa su mikewa suka fita bayan Liman ya yiwa Fatima nasiha tare da jan kunnenta.
Ba tasan tarin godiyar da za ta masa ba tabas Liman ya cika makoci na gari.
“Tashi ki shiga daga ciki man diyata”muryar Umma ya katseta daga duniya tunanin data tafi.
Cikin Jan jiki na dawo tsakiya dakin na zauna”Saliha kaita dakin yayanku ki zo”maida kallon ta tayi kan Fatimah ganin jikin ta duk a bace,sanin kanta me yayansu bai son kazanta.
“Tsayiwar mai kike haka?
“Umma! nace ko zata kintsa?