Kewaye Hausa Novel Complete

Kewaye Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

ƘAWAYE

 

*REPOST*

 

*(Wannan book din ba sabo bane zanyi reposting ɗin shi ne haɗe da yin ƴan gyare²)*

 

 

*Mallakar*

AUTAR MAMA

 

*ADABI WRITER’S ASSOCIATION*

 

 

*Shafi na ɗaya*

 

*_NIGERIA_*

 

*KANO STATE*

 

Duk wanda yasan garin Kano yasan garine da ya tara ƙabilu daban – daban a ciki, gari ne mai cike da ni’imomi kala – kala sai dai muce Allah ya ƙara albarka ga wannan gari da ma duk sauran garuruwa dake faɗin duniya Allah ya tabbatar mana da zaman lafiya mai ɗorewa Ameen.

Gudu da Waiwaye Hausa Novel Complete

A kullum burina shi ne na ƙayatar da masoyana da daɗaɗan litattafai toh yauma gani ɗauke da wani sabon littafi mai taken *ƘAWAYE* wanda ya kasance 50% ɗin shi true life ne, 50% kuma fiction.

 

*G/ƙaya*

 

Mazauna garin Kano ga waɗanda suka unguwar gadon ƙaya, sun san unguwace dake ɗauke da masu kudi da kuma masu ƙaramin ƙarfi, toh haka ce ta kasance ga waɗannan ƙawayen Khadijah da Amina.

 

*Wacece Khadijah*

 

Khadijah ta kasance ƴa ga Malam Sani, su biyu iyayensu suka haifa daga ita sai ƙaninta Mus’ab, Mahaifinsu malamin primary ne a wata makarantar gwamnati, mahaifiyarsu sunanta Fatima suna ce mata Umma tana sana’ar ɗinki da kitso, tare suka haɗu suke rufawa juna asiri, Mahaifinsu na burin yaga yaransa sunyi karatu, asalinsu ƴan garin gwarzo ne, neman kuɗi ya kawo su garin Kano, duk a nan Kanon aka haifi Khadijah da Mus’ab, Khadijah yanzu nada shekaru 11 a dunia Mus’ab kuma 8yrs, Khadijah macece me faran² da son jama’a sosai kuma tana da surutu. Khadijah tana da haske amma ba chan ba, hancinta bai da wani tsaho amma yayi daidai da fuskarta haka ma idanunta madaidaita ne masu ɗauke da gashin ido dai dai misali bakinta bai da girma tana da kyau dai-dai nata sai dai muce Ma sha Allah. Khadijah bata da ƙawar da ta wuce Amina domin har iyayensu ma sunsan juna sosai, makaranta ɗaya suke zuwa boko da islamiyya. Wannan kenan.

 

*Wacece Amina?*

 

Amina Ishaq sunanta, su uku iyayensu suka haifa, babbar yayarsu Sadiya sai Abubakar sannan ita Amina ƴar auta, mahaifinta yana da kudi Alhamdullilah ma’aikacin banki ne mahaifiyar kuma business woman ce, sunan mahaifiyarsu Salma suna kiranta da Mama, Amina bata da akwai yawon surutu sosai ga babu kawaici da haƙuri, Amina fara ce tas hancinta yana da tsaho lebanta baida girma sosai tana da dara²n idanu ga cikar gira tana da kyau Masha Allah dan tafi Khadijah amma kasancewar Khadijah ta fita gayu da kwaliyya mutane sai suka Khadijah tafiya kyau but natural beauty Amina ta fita. Amina tana da ɗan kiɓa kaɗan saɓanin Khadijah siririyace. Amina bata da wata ƙawa da ta wuce Khadijah domin duk da yarintarsu sun iya ƙawance. Amina shekarunta 12, babbar yayarsu kuma 22 an kusa bikinta sai Abubakar me 18. Mahaifiyar Amina buzuwar Nijar ce mahaifinta kuma ɗan Kano ne. Wannan kenan.

 

Kamar kullum idan Amina ta gama shirin makaranta ta kan biyawa Khadijah haka ma Khadijah, idan ta gama nata shirin, toh yau Khadijah ce ta shirya da wuri,… Kular abincinta ta ɗauka ta kalli mahaifiyarta dake yankan atamfa tace ” Umma na tafi”. Ɗago kai Umman na ta tayi tace ” Allah ya bada sa’a sai kun dawo”. Da toh Khadijah ta amsa sannan ta gyara hijabinta da jakarta ta fita daga gidan, a hanya suka haɗu da Amina dake riƙe da lunch box ɗinta, baki Khadijah ta wanshare tana kallonta tace ” Laaa Amina sabon uniform ki kayi?. Murmushi Amina tayi tace ” Eh ai na faɗa miki Yaya Abubakar yace ze ɗinka min kala biyu tunda mun shiga Jss 1″. Dariya Khadijah tayi tace ” Nima zance Umma ta ɗinka min”. Murmushi Amina tayi tace ” Yawwa kinga sai muyi anko ko, kuma a ɗinka miki da wuri kinga Sir Bashir yace zuwa next week za’a dena zuwa da kayan gida”. “Toh zan faɗawa Umma”. “Ok toh muje”. Amina ta faɗa tana yin gaba, bayanta Khadijah tabi su na hira har suka isa makarantar dayake bata da wani nisa, an kusa gama assembly sannan su ka isa, dan haka dole suka jira aka shiga class sannan suka nufi cikin aji. Desk d’insu ne a gaba su biyu kowacce ta ajiye jakarta ta fito da littafin maths saboda shine first period ɗin da zasuyi a yau. Suna zaune malamin maths ya shigo ya gama abinda zeyi Basic science ta shigo itama ta gama sai English ta gama nata sannan IRS sai da sukai 4 subjects sannan aka kaɗa lokacin break. Litattafan su suka sa a ƙasan loka, Khadijah ta fito da kulan abincinta dake ƙasan desk tace “yau nawa za’a fara ci, jiya da mukaci naki na koma da nawa gida Umma faɗa tayi min”. Murmushi Amina tayi tace ” Toh shikenan kinsan yadda za’a dinga yi yanzu?. Kai Khadijah ta girgiza alamar a’a. ” Idan nazo da abinci Monday toh ke sai kizo dashi Tuesday”. Dariya Khadijah tayi tace ” hakan yayi”. Buɗe kular abincin Amina tayi. Macaroni ce jollof sai kifi guda ɗaya, murmushi ɗauke akan face ɗinta ta ɗauki cokula guda 2 daga lunch box ɗin ta ta miƙawa Khadijah ɗaya tace “muci”. Su na ci suna hira har abincin ya ƙare, ruwa Amina ta ɗauko daga jakarta ta miƙa wa Khadijah tace ” Sha ki rage min”. Ƙarbar jarkar ruwan Khadijah tayi tasha sannan ta miƙa wa Amina ragowar. 45mins ne daman lokacin break ɗin, basu wani fita ko ina ba, duk da sauran ƴan ajin ana ta kiransu da su fito suyi ƴanta. Lokacin da aka tashi daga makaranta sai da suka tsaya sukaci abincin Amina sannan suka dawo gida. Amina na shiga gida ta ajiye jakarta a kan dining ta fara kallon palonsu da ba kowa, “Mamaaa!”. Shine sunan da take kira da ƙarfi, wata mata ce da bazata haura 48yrs ba ta fito daga wani ɗaki tana sanye da atamfa me kyau da tsada, daga ganinta kaga inda Amina ta ɗauko fari, ” Har kun dawo?. Mama ta faɗa tana kallon Amina. Turo baki Amina tayi tana zama aka tiles tace ” Eh Mama ina Aunty sadiya?. Murmushi mama tayi tace ” Ai ta tafi rabon kai sample na katin biki”. Amina kamar zatayi kuka tace ” Na ce fa zamu rakata ni da Khadijah”. Mama ce ta ƙara so inda take ta ɗagata tace ” Bana hanaki zama kan tiles ba? Kuma ai yanzu islamiyya zaku tafi ko?. Hawayene ya biyo kan fuskar Amina a hankali tace ” ai bazamu ba”. Ajiyar zuciya Mama ta sauke tana share mata hawaye tace ” Sorry toh, kije ki yi wanka ga abinci chan kici sai kiyi shirin makaranta, weekend ranar Lahadi sai in kai ku shopping ke da Khadijan ko?. Cikin farinciki Amina ta washe baki tace “Toh, ni sai na dawo zanci abinci munci a makaranta”. Daga haka ta wuce ɗakin da Mama ta fito da gudunta. Ƙarfe uku saura ta fito cikin sky blue well ironed uniform ɗinta kallon Mama tayi dake zaune a palo tana danna na’ura me ƙwaƙwalwa hannunta riƙe da jota da pen. “Mama na tafi”. Ta faɗa tana wucewa. “Zonan Amina”. Juyowa Amina tayi tana kallon Mama sannan ta ƙaraso inda take, hijab ɗinta ta cire mata gashinta me santsi da laushi ya zubo sai sheki yake. “Ina vest ɗinki? Baki san kin fara girma ba? Kar na ƙara ganin kin fita baki sa vest ba kinji? Kuma ki ɗauko ɗankwali ki daure kanki, idan kin dawo sai na miki kalba”. “Toh” Kawai Amina tace tana komawa ɗaki.

 

Khadijah kuwa tana shiga gida wanka ta farayi sannan tayi wanke² ta shirya cikin uniform ɗinta gogaggu kuma sababbi kamar na Amina. Turaren Umma ta dauka ta fesa ta dauki jakarta dake sip ta kalli Umma da ta hau kan keke tana ɗinki tace ” Umma na tafi”. “Ungonan”. Umma ta faɗa tana miƙa mata nera 50 “ki ɗauki 20 ki bawa Amina 20 ki dawo min da goma”. Khadijah na murmushi tace ” Toh umma mungode”. Murmushi Umma tayi har ya bayyanar da hakorin gwal ɗin dake bakinta, ” Allah ya bada sa’a ayi karatu banda wasa”. Khadijah na murna ta fito, a ƙofar gidan su Amina suka haɗu. Hamsin ɗin hannunta Amina ta kalla tace ” Waya baki kudi? Murmushi Khadijah tayi tace ” Umma ce tace in ɗauki 20 in baki 20 in dawo ma ta da goma”. Murmushi Amina tayi cikin farinciki tace ” Allah sarki Umma, mungode”. Suna hirar abinda zasu siya da kudin suka iso makaranta lokacin ana dukan makara, basu wani ɓata lokaci ba sukaje akai musu suka shige aji ko wacce ta fito da Alqur’aninta suka fara tilawa…….

 

 

Ƙarfe 5 da rabi na yamma aka taso su, sai da suka tsaya siyan fitsarin bature sannan suka dawo gida kamar karsu rabu. Khadijah na shiga gida ta cire uniform ɗinta ta ninke ta mayar sip ta sanya doguwar riga ƴar kanti da hula ta fito tsakar gida ta kalli Ummanta dake kan keke tace ” Umma wai ke bakya gajiya ne?. Murmushi Umma tayi tace ” Khadijah kenan, kinsan idan sallah ta matso ai tela baida wani sukuni, wannan ɗin kunan tun bayan sallah karama aka kawo min, so nake na ƙara sa su na fara naku ɗinkin na bikin Sadiya tunda kafin babban sallah ne”. Murmushi Khadijah tayi tace ” Allah yayi miki albarka umma na”. Dariya Umma tayi cikin jin dadi tace ” Amin Khadijah kema Allah ya sanya albarka cikin rayuwarki, kiyi sauri ga abinci can a kitchen kici sai ki kai markaɗen kayan miyar nan”. “Toh umma bari na fara kaiwa kar yamma ta ƙara yi, kinsan idan akai magariba basa yin markaɗen, kuma ba yunwa nake ji ba, wai Mus’ab be dawo bane?. Khadijah ta ƙarashe maganar tana kallon gidan. “Eh kinsan yau Litinin sai sun tsaya a Rauda saboda hadda anayin isha’i zaki ganshi, yanzu ma Abban ku ma chan yaje ya kai masa abinci”. “Ok bari naje”. Khadijah ta faɗa tana janyo hijabinta a igiya, markaɗen ta ɗauka ta fita bayan tayi sallama da ummanta.

 

Amina kuwa tana komawa gida abinci ta fara ci lokaci Aunty Sadiya ta dawo sun gama kwasar drama. Cikin tsokana Aunty Sadiya tace ” Kinga ranar lahadi idan zaku je shopping sai mu tafi tare ko?. Kallon Mama Amina tayi tana kwaɓe fuska tace ” Mama kinganta ko?. Kafin Mama tayi magana Abubakar yace ” Don’t mind ur sister ni ne zan kai ku shopping ɗin babu inda zata bi mu”. Dariya Amina tayi ta kallesa tace ” Give me five”. Hannu ya daga suka tafa suna dariya. “Aje acire uniform smell_smell girl kawai”. Aunty Sadiya ta faɗa dan ta ƙara kunno Aminan”. Turo baki Amina tayi sai kuma ta ɗaga hammatarta ta kai saitin hancin Abubakar tace ” Yaya ina wari?. Dogon numfashi Abubakar ya ja yana wani lumshe ido sannan ya buɗe yace ” Ni daɗin khamshi kike kamar turaren almiski”. Sai a lokacin Mama tayi dariya tace ” Ni da yar me duguri”. Murmushi Amina tayi tana kallon Mama tace ” Ai nima idan na girma kamar Aunty Sadiya zan dinga yin khamshi kamar yadda akewa Aunty Sadiya turare take khamshi ko Mama”. Kafin Mama tayi magana Aunty Sadiya tace ” Chab Waye ze miki turare irin nawa?. “Ni mana”. Abubakar ya bata amsa yana kallonta. Dariya Aunty Sadiya tayi sannan tace ” ah muna turare dai ko?. Ɓata rai Amina tayi tana kallon Aunty Sadiya tace ” Ni ba ruwana dake”. Daga haka ta wuce ɗaki tana kumbure². Girgiza kai Mama tayi a fili tace ” Allah ya shirya”. Da Amin Aunty Sadiya da Abubakar suka amsa suna dariya.

 

Ƙarfe 9 da kusan rabi sannan Mus’ab da Abban su suka dawo gida, a tsakar gida duk suka zauna saboda an ɗauke nefa ga zafi da alama hadari ne ma a garin. Tuwon da Mama ta zubawa kowa Khadijah taje ta ɗauko ta kawo musu suka fara ci. Mus’ab ne ya kalli Mama yace ” Mama an bamu hutun sallah, sannan saura izu hudu mu haɗe”. Murmushi Khadijah tayi tace ” Kai Dan Allah?. Dariya Mus’ab yayi yace ” Wallahi Yasayyadin mu yace kowa ze kawo dubu 1 na haɗa kuɗin walimar hadda sannan makaranta zata yi taron sauka za’a kawo dubu goma”. “Masha Allah yaro ze riga yayarsa sauka”. Abba ya faɗa yana shafa kan Mus’ab. Ɓata rai Khadijah tayi tana kallon tuwan gabanta kamar zatai kuka tace ” Muma ai saura izu 20 mu haɗe”. Dariya Umma tayi tace ” Saura ko uwar tafiya?”. Shuru Khadijah tayi tana ɓata rai. Abba ne yayi murmushi yace ” Yi hakuri Dejalle kema kun kusa ai Allah ya hore ranar walimarki nayi miki bajinta”. Sai a lokacin ta washe baki tace ” Amin Abba”. “Abba nifa?. Mus’ab ya faɗa yana lashe hannu. ” Kaima haka yanzu ai an biya maka kudin sauka ko sannan na siya maka shadda na walima da hula da takalmi harda rago ma ko? Dariya Mus’ab yayi yace ” Eh Abba, Allah ya kawo kudi”. Amin suka amsa suna farinciki.

 

Washe gari Khadijah da ciwon cinya, baya da mara harda gudawa ta tashi, bakwai da ƴan mintina Amina ta shigo gidansu tana shirye cikin uniform ɗinta, gaida Umma tayi dake haɗa karin kummalo a kitchen umman ta amsa fuska sake tana tambayarta ya mutan gidan. “Umma ina Khadijah?. Amina ta faɗa tana kallon ɗakinsu. “Ayyah yau Khadijah bata da lafiya bazata iya zuwa makaranta ba”. Rau_rau Amina tayi da ido tana kallon ɗakinsu Khadijan. “Shiga mana”. Umma ta faɗa tana kallonta. Da sauri ta ajiye jakarta da lunch box dinta ta shiga ɗakin, kwance ta ga Khadijah a kan gado sai murƙususu takeyi, hawayene ya fara zuba a idanunta da sauri ta ƙarasa gadon tana taɓa jikin Khadijah tace ” Sannu Khadijah”. Sai kuma ta fashe da kuka, da ƙyar Khadijah ta iya kiran sunanta… Cikin tsananin ciwo bayanta ya riƙe ta ce ” Amina fitsari nakeyi a kwance ki kaini banɗaki”. Da ƙyar Amina ta iya ɗagata me zata gani jini ajikin kayan ƙawarta, ihu tasaka tana sakin Khadijah, wani ihun ta kuma kurmawa hakan yasa Umma ta shigo da sauri dan su Abba da Mus’ab sun jima da fita, “Umma Khadijah zata mutu haihuwa za tayi”. Amina ta faɗa tana nunawa Umma jinin dake bedsheet. Kallon Khadijah data dena murƙususu jin ance zata haihu tayi sannan ta kalli Amina tace ” yi shuru hakannan ko? Zauna nan”. Umma ta faɗa tana nuna mata kan kujerar mirror. Zama Amina tayi jikinta na rawa, ganin Umma ta juya wajen Khadijah yasa ta fita da gudu ta ɗau jakarta da lunch box ɗinta sai gida, kuka take kamar wadda uwarta da ubanta suka mutu. Kiciɓis sukai da Abubakar dake kan mashin a ƙofar gida ze tafi makaranta dan yau lectures ɗin safe gareshi. Da mamaki ya kalleta yace ” Ke me haka? Wucewa tayi ta barsa a tsaye hakan yasa shima ya dawo cikin gidan ya ajiye mashin ɗinsa ya shigo palo… Kwance yaga Amina tana ta gunjin kuka kamar zata mutu Mama da Aunty Sadiya Harda Baba suna tsaye a kanta amma taƙi cewa komai, Baba ne ya kalli Mama yace ” ɗauko min bulala”. Ba musu Mama ta ɗauko wayar caza ta miƙawa Baban. Ɗagawa yayi kamar ze daketa da sauri ta tashi zaune tana goge majina da hijabin ta tace ” Khadijah ce”. Sai kuma tayi shiru, “Me ya samu Khadijan? Abubakar ya faɗa yana kallonta. Kuka ta kuma sawa ganin tanason ɓata musu lokaci yasa Baba zula mata chaja, sosa gurin ta farayi ta mike da sauri tana kuka tace ” Baba Dan Allah kayi hakuri”. “Me ya samu Khadijan kinyi shuru”. Mama ta faɗa tana kallonta. Sai data goge majina sannan ta ce ” Mutuwa Khadijah zatayi Mama”. Zaro idanu Abubakar da Aunty Sadiya sukai da mamaki Mama tace ” Mutuwa kuma?. Cikin tsananin kuka tace ” Mama haihuwafa zatayi tana can sai fitsarin jini take”. Ta ƙarashe maganar tana sakin wani kuka. Sim² Aunty Sadiya tayi ɗaki dan ta harbo jirgin, tsaki Baba yayi ya ajiye chazar hannunsa ya ɗauki jakarsa ta aiki ya wuce, “kai kuma me kake jira?. Mama ta faɗa tana kallon Abubakar”. Shafa kai yayi yana murmushi yace ” Nothing mother na Wuce”. Sai da mama taga fitarsa sannan ta janyo Amina jikinta suka zauna ta ciro tissue a kan Centre table ta goge mata fuska still hawaye na ƙara fitowa cikin rarrashi Mama tace ” Stop crying kinji Queen of beauty? Khadijan ki ba mutuwa za tayi ba kuma ba haihuwa zatai ba”. Cikin rawar murya Amina tace ” Me zatayi toh?. Murmushi Mama tayi ta ƙara janyota jikinta sannan tace ” Khadijah ta girma yanzu ta bar sahun yara, Khadijah ta fara jinin al’ada wanda yawancin mata munayinsa”. Cike da yarinta Khadijah tace ” Mama kema kinayi?”. Murmushi Mama tayi tace ” Shi wannan jinin da kika gani a wajen Khadijah idan mace ta fara shi toh alamune na mace zata iya ɗaukar ciki…… Nan Mama ta zauna tayi wa Amina bayani sosai sannan ta ƙara da kuma daga yanzu daga ke har ita ba ruwanku da maza kinji ko, kar ku bari namiji ya kiraku kuje banda wasa da maza idan ba haka ba ciki zaku ɗauka a dinga muku dariya ko da kuwa hannunku namijin ya taɓa”. Kai Amina ta girgiza kamar ba zatai magana ba sai kuma tace ” Mama ni kuma yaushe zan fara?. Kuncinta Mama taja tace ” Ko yaushe yana iya zuwan miki kema”. Murmushi Amina tayi tace ” Toh”. “Toh muje a cire kaya yau nasan ba batun zuwa makaranta ko? Aunty Sadiya da fitowarta daga ɗauki kenan ta faɗa tana murmushi”. Dariya Amina tayi ta nufi ɗaki da sauri dan ta cire kaya ta koma gidansu Khadijah………..

 

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

 

Bazan juyi sharing ko wani group ba ga link na group Dina ayi joining.

 

Autarmama ce

Post a Comment

Previous Post Next Post