Karsashi Hausa Novel Complete

Karsashi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ƘARSASHI!

 

 

 

 

*NA*

*RASHEEDAT S DIRECTOR*

 

 

 

 

( _Book 1_)

 

 

~Free page~

 

 

( _Bismillahirrahmanurrahim_)

_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_

 

 

 

🅿️1

 

 

 

 

 

 

 

Dandazon matasa ne ke cike tap a filin kwallon dake cikin wata makarantar kwana, hayaniyar mafiya yawa daga cikin dandazon matasan ne ke tashi suna faɗin

” *LOCKY* sai ka sha *LOCKY* sai ka sha!.”

dai-dai lokacin wani matashi wan da a kalla shekarun sa bazasu wuce 19to20 years ba, cikin kwarewa haɗe karsashi, ya buga k’wallo tashi ga cikin raga.

Namijin Zuma Hausa Novel Complete

 

wani irin ihu filin ya kaure da shi kan kace me y’an’uwan sa matasa da suke buga ƙwallon y’an team in sa suka d’aga shi sama suna ihun murna da faɗin.

“Locky Locky Locky!!.”

cikin matukar farin ciki da tsantsar jin daɗi.

tuni filin ya kacame da hayaniya baka jin komai bakin mutane sai kalmar sunan Locky ke fita daga bakin su.

fuskar matashin da ake ta kira Locky sai fidda annuri yake ya na d’aga hannunsa sama wa muta ne.

har suka fito daga cikin filin kwallon duk in da ya gilma sai mutane sun mika masa hannu sun gaisa tare da yi masa kirari.

can gefe suka karasa shi da y’an team ɗin sa da sauri coch d’in su ya iso in da suke da murmushi d’auke a kan fuskarsa ya rungume Locky yana bubbuga kafad’ar sa cike da jinjinawa da yabawa hazaka da kokarin sa wan da a yau ya sha musu kwallo uku.

yana matukar alfahari da shi dan duk san da za’a buga wasa to kuwa tabbas cikin amincin Allah sai ya cimusu wasan da kyauta mai tsoka.

suna tsaye suna shan ruwa da huta gajiyar da suka kwaso, wani yaro dake kusa da Locky ya ciro wata kwaya daga cikin aljuhun wandon sa ya afa a bakin sa kana ya kora da ruwa.

sauran ragowar kwayar ya mikawa Locky yana faɗin

“Locky gashi ka kora.” karb’ar kwayar yayi ya wasar da su kasa, ido yaron ya ware ya ce

“Zubarwa kayi na baka abin da gaba idan kacigaba da sha zaka ciyo mana kwallon duniya shine zaka zubar?.”

bayan keyar sa ya sotso yace

“Anwar kana da damuwa bana yanayin da zan iya shan wad’an nan abubuwan.”

kafad’a Anwar ya d’aga kana ya kunna sigarin da ya ciro yanzu ya kai bakin sa yana zuka,

Sagir dake gefen Anwar ya ce “Ai dai kasan wannan bazai tab’a shigo wa gari ba gara ma ka daina damin kanka.”

baki Locky ya tab’e, kana

a sannu ya mika hannu ya zaro sigarin da Anwar ya kunna ya kai nashi bakin yashiga zukarta a hankali..

da mamaki Anwar ke kallon sa dan a sanin sa da shi ko sigarin baya sha,bare kuma kwaya, duk da yawancin abokan su suna huld’a da irin wad’an nan abubuwan, a cewar su wai yana kara musu kuzari wajen buga kwallo.

sai dai shi Locky sam baya shan komai, ko da sun nima da ya sha ma wai dan ya kara kwazo kan wanda yake da shi, sam baya sha.

sai gashi yau ya karb’i sigari da hannun sa yana sha.

dariya Anwar da Sager sukayi, Anwar ya ce

“Mutumin fa yafara shigowa gari.”

hararar su Locky yayi

gaba ki d’aya lissafin sa da hankalin sa baya gun, da sauri-sairi yake zukar sigarin yayin da gaba d’aya lissafin sa yayi nisa…

 

Kamar daga sama yaga motar ta sharo kwana da mugun gudu,

daga bayan ta can wata mota na biye da ita, cikin hanzari yazare sigarin bakin sa yayi wurgi da shi, kana cikin azama ya nufi in da keken sa ke kafe, cikin sassarfa ya haye kan keken da iya karfin sa yake gudu kan keken ya rufawa motar baya, hanyar barin wajen gari motar ta nufa bai kuma fasa bin sa ba, sai dai a wannan karon ya sauka a kan titi gefen hanya yake bi wato ta kasa,

d’aya motar da take bin d’aya na gaban ne ya sauya hanya,

shiko bai fasa bin motar da ya sa a gaba ba,

har suka fice daga cikin gari suka fara shiga jeji, ta cikin bishiyoyi da ciyayi yake bi batare da ya bar wan da yake bi d’in ya gansa ba.

ganin motar tana kokarin gangara wa ta cikin daji, da sauri ya gangara da keken sa bayan wata katuwar bishiya ya b’oye a bayan bishiyar.

motar ta isa can kusa da wani kogon dutse wan da ya ke cikin motar ya fito da sauri ya buɗe bayan but d’in motar, yaciro wasu manyan ganamasgo guda biyar yarika kinkimar su yana kaisu cikin kogon dutse d’in nan yana saka su ciki.

sai da ya zuba su duka sannan ya juya yarika tsinko ciyayi yana rufe bakin kogon da shi har ya rufe shi gaba d’aya,

kana mutumin ya koma cikin motar da sauri yabar gurin.

numfashi Locky ya sauke daga in da yake b’oye yana ganin duk abin da yake yi…

 

Mutumin yabar gurin dakamar minti 10 Locky yafito daga gurin da yake b’oye, dai-dai lokacin sautin karar bindiga ke tashi,

ji kake tau-tau har sau biyu.

da sauri cikin azama ya haye kan keken sa ya nufi in da yake jiyo sautin harbin ke tashi.

tun daga can nesa yake hango motar mutumin da ya biyo sa a baya tsaye a tsakiyar titi, shi kuma mutumin yana yashe a tsakiyar titin cikin jini.

wasu mutane suna tsaye a kansa rike da bindigogi yayin da fuskokin su ke rufe da bakin kyalle.

cikin hanzari suka shige motar su suka bar gurin da mugun gudu.

ido ya kurawa motar nasu daga in da yake tabbas wannan itace motar daya gani tun da fari yake biye da motar mutumin.

da sauri ya kara gudun keken sa, kafin ya iso gurin tuni motar tabar gurin.

yana iso wa gurin cikin matukar tashin hankali ya diro daga kan keken,

yazube guiwowinsa gaban mutumin tare da d’aura hannayensa a kai yana salati, wasu hawaye ne masu matukar zafi suka shiga wanke fuskarsa.

da karfi yashiga jijjiga mutumin yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarsa.

wani irin mike wa yayi cikin azama, abun hannun dake daure a hannunsa mai d’auke da harafin(L) da babban harafi abun hannu ne na musamman wan da ake kera wa na musamman da kuma harafin da kake so a kera maka da shi a jiki. (L) yana nufin Locky kenan.

mab’allin jikin abun hannun

ya rike jikin rigar mutumin cikin matukar da muwa da tashin hankali, bai tsaya cire abun hannun nasa ba ya zare hannunsa abun hannun ya makale jikin rigar mutumin,

shiko Locky cikin zafin nama ya haye kan keken sa yabi bayan motar mutanen da sukayi kisan, da tuni sunyi nisa can nesa yake hango su.

gudu yake yi a kan keke da iya karfin sa,

duk da sunyi masa nisa sosai baisa yafasa binsu ba.

har sukayi nisa da gari sosai can suka sauka kan titi suka bi hanyar kasa,

tafiya sukayi me nisa har suka iso wani gida dake cikin jejin shi kad’ai a tsakiyar dajin.

har kuma lokacin Locky nabiye da su,

suka kashe motar suka fita dukansu suka shiga cikin gidan.

daga can nesa da gidan Locky yafito daga in da yab’oye, ganin sun tsaya gudun kada su ganshi.

cikin hanzari ya karaso gidan da suka shiga ta bayan gidan ya aje keken sa, a hankali cikin sand’a yashiga gidan, yana lab’ewa da tafiyar sand’a har ya shige cikin gidan.

 

Ta jikin windon wani d’aki dayaji magana ciki, ya make jikin windon tare da kasa kunnen sa.

wayar sa ya ciro daga cikin aljihu, yad’an d’ago hannunsa sama ta jikin windon yana d’aukar video’n su dakuma nad’an sautin maganarsu,

dai-dai lokacin da yaji a na fad’in

“Mun gama da shi yana can kwance mutacce, amma mun duba cikin motar sa sama da kasa babu kud’in nan ciki.”

da karfi cikin karaji a ka ce

“Me yasa kuka kashe shi batare da kun karb’i kud’in ko sanin in da kud’in suke ba!, oh my god kun b’ata mana shiri, ai kin banza kukayi kun kashe shi bayan kuma baku karb’i kud’in ba,

ina kud’in yake matsiyaci a ina ka aje su, ka mutu banza bansan in da ka kaisu ba,

ku wasu irin marasa lissafi ne da zaku kashe shi batare da kun karb’i kud’in ba, ina ya kaisu to!!!.”

ya karashe maganar cikin karaji sosai.

kamar daga sama muryar mai magabar yado ki kunnen Locky,cikin kad’uwa da jin muryar mai maganar ya d’ago tare da leka windon, idanunsa ya sauka kan mai maganar, yana tsaye sakiyar wad’an da sukayi kisan nan yana ta kaiwa da komowa yana cigaba da fadin

“Kun yi shirme da kafin ku kashe shi kun tirsasa shi ya fad’a muku in da kud’in yake tun da baya tare da shi, to ma ina yakai kud’in bayan dasu ya fita a mota!.”

d’aya daga cikin makisan ya ce

“Abin da yasa muka kashe shi take batare da tunanin komai ba sabo da munsan da kud’in yake tafe,

bayan ya sheka kuma muka duba motar babu kud’in.”

“Ku shiga gidan sa da daddare ku bincika ko ina ya shammace mu wata kila ya baro sa a gidan, ku tabbatar da kunzo min da kud’in, duk wan da yakawo muku gardama ku kashe shi.”

su ka ce “To oga.”

da sauri Locky yayi baya yana save din video d’in daya d’auka a wayar sa, ya jefa watar cikin aljihu cikin sand’a ya sulale ya fita a gidan…

keken sa ya haye cikin hanzari yabar gurin da mugun gudu, yayin da zuciyar sa ke wani irin tafarfasa.

daga can yarika jiyo jiniyar ‘yan sanda,

mutane ya hango cike a kan mutumin da aka kashe, ‘yanjaridu nata d’aukar hoton gawar, yayin da ‘yan sanda keta faman korar mutane su samu sugudanar da aikin su.

jiki a santaye ya karaso gurin, yayin da yake jin gaba d’aya duniyar tayi masa zafi zuciyar sa kuwa naci gaba da wani irin tafarfasa.

wani d’an sanda ne ya sunkuya kan gawar yakai hannu ya ciro abun hannun dake makale a jikin wuyan rigar mutumin da aka kashen,

ido ya kurawa abun hannun yana jujjuya shi a hannunsa.

a fili ya furta “L. wane ne shi duk yan da akayi shi yayi wannan kisan!

babban abun hannu ne wan da ba a samun irin sa a kasuwa sai dai a kera maka shi, duk yanda akayi zai kuma kera wani irin sa.”

wani irin bugawa kirjin Locky ya yi, cikin hanzari yayi baya da hannunsa wan da ke sanye da d’aya abun hannun irin wancan, wan da dama guda biyu ne a hannun sa d’ayan ne ya makale jikin rigar mutumin.

d’an sandan ya mikawa d’an uwan aikin sa abun hannun tare da fad’in.

“Daga kan wannan za’a fara bincike da wannan zamu sami nasarar kama shi.”

suka d’au gawar suka saka cikin motar asibiti da yanzu ta iso gurin sannan suka yi gaba…

 

Locky yaja keken sa zuciyarsa a jagule ya nufi cikin makaranta wan da acan yake da zama cikin hostel,

yana isa direct d’akin su ya wuce wan da su hud’u ne ke kwana ciki, shi da abokansa Anwar Sagir da kuma Bashir.

yana shiga d’akin yashiga fatali da kayan cikin d’akin yayin da idanunsa suka kad’u sukayi jajir, sai huci yake,

d’aya abun hannun sa ya cire yajefa shi cikin jakar shi.

sai kuma cikin hanzari kamar wan da aka zabura yayi in da su Anwar suke ajiye kayan shaye-shayen su ya d’auki kwalaben da kwayoyin yarika afawa a bakin sa.

su Sagir ne suka turo kofa ganin halin da yake ciki da sauri suka iso in da yake, Bashir daya ruko sa yana fad’in

“Kai Locky an fad’a maka da haka ake fara shan kwayar so kake kwakwalwar ka ya tab’u?, muma da kaga muna sha ai ba irin wannnan shan muke masa ba,

ko munsha babu mai gane munsha wani abun sai dai kai da kake tare da mu, dan bama sha yanda zai fidda mu daga hayyacin mu,

sai dai kawai musha dan muji karfin jikin mu tare da nisha d’i.”

 

Hannun sa ya fiske daga rukon da Bashir ya masa, yakuma kai wata kwayar bakin sa.

da sauri su ka shiga tattara magungunan su ganin da gasken sa yake narkawa cikin sa, kada ya kashe kansa ko ya haukata kansa a kamasu.

 

Zube wa yayi saman katifar sa tare da dafe kansa da hannayen sa biyu,

duk tambayar duniyar nan da su Anwar ke masa kan abin da ke damin sa dan sun hango damuwa sosai tare da shi, wan da yayi sana diyyar shan kwayar da yayi, amma yaki ce da su komai. suna cikin masa tambayoyin ma sukaga bacci yayi gaba da shi.

Sagir ya ce

“Anya bazamu d’auke shi mu kai shi

Pharmacy a duba shi ba kada fa kwakwalwar sa ya tab’u dan yasha kwayoyin nan da yawa.”

“To amma taya zamuyi mu fita da shi idan a ka ganmu dole za’a tambayi abin da ya faru da shi kaga mu ma baza’a kyale mu ba.”

Bashir ya fad’a cike da jin tsoron abin da zaije ya dawo.

Anwar ya ce “Kuma gaskiya haka ne mudai nemo wata hanyar.”

haka sukayi ta sakawa da kwance wa sakanin su, shiko Locky yana ta kan sharara baccin sa…

 

Sai bayan sallar magriba ya farka kamar wanda aka zabura, Anwar ne kad’ai cikin d’akin su Bashir sun fita nima masa magani ganin baccin nasa yayi yawa, sun fara tsoron abin da suke zargi ne ya faru, wato ya haukace kokuma zai mutu.

da sauri Anwar ya taro shi ganin ya mike zunbur ya nufi kofa yana kokarin fita.

ya ce “Locky dakata dan Allah kada ka fita karufa mana asiri.”

yana maganar ne cikin jin tsoro dan gani yake kamar haukan ce yayi zai fita ya gudu.

Locky da har lokacin idanunsa suna nan jajir kamar d’azu ya dube sa ya ce

“Bani hanya na wuce.”

Anwar ya ce “Amma Locky kana cikin hankalin ka dai ko?.”

wani mugun kallo ya watsa masa kana ya ce

“Kai ka haukatar da ni.”

bangaje sa yayi yayi waje da sauri.

Anwar ya bud’e baki yana bin bayan sa da kallo ganin yana cikin hayyacin sa.

a haka su Bashir suka iso suka same sa tsaye bakin kofar,

suka ce ina Locky’n ya ce da su ya fita,

hankali tashe Sagir ya ce “Sai ka barshi ya fita yanzu kasan bolar da zamuje mu nemo shi?.”

Anwar ya ce “Wlh lafiyar sa lau cikin hayyacin sa ya fita, nayi mamakin karfin kwakwalwa irin nashi.”

gabaki d’ayan su suka rika jinjina karfin kwakwalwa irin na Locky, ace duk tulin tarin kwayar da yayi ta narkawa cikin sa a ce ya tashi tsaf batare da wani nakaso a tare da shi ba…

 

Shiko Locky yana fita keken sa yahau yanufi dajin da mutumin da aka kashe d’azu ya b’oye wasu ganamazgo cikin kogon dutse,

babu tsoro tare da shi duk da kuwa lokacin guri ya rufa yayi duhu,

a kan keken nan yarika kinkimar manyan jakukkunan nan da d’ad’d’aya yana fita da su daga cikin dajin ya canza musu wajen b’uya.

cikin sati guda ya nima wa kud’ad’en gurin ajiya na musamman wato banki bayan yayi wani cuku-cuku na musamman.

 

Bayan shekara shabakwai……..!

 

 

 

 

Mommyn Twins ce

Post a Comment

Previous Post Next Post