Gudu da Waiwaye Hausa Novel Complete
GUDU DA WAIWAYE…..!!!
(Shi ya kawo mugun zato)
Bilyn Abdull ce
Page 1
MALAM Rabi’u Shema, cikakken bakatsine jinin rumawan asali da ALLAH ya azurta da wani sirrin ƙyau mai fita da kwarjini.
Ya fitone da ga yankin karamar hukumar Dutsamma dake jihar katsina, a wani ƙauye da ake kira Shema, danginsa uwa da uba duk sun fitone daga wannan yanki.
Sanadin ƙaddarar neman na kaine ta dalilin kasuwanci ya tsinci kansa a garin kano, shi kaɗai ya fara zuwa kafin daga baya ya kawo matarsa mai suna iya ladi.
Ƴaƴansu huɗu a duniya, maza uku mace ɗaya.
A yanzu haka da shekaru suka shuɗa gidan Malam Rabi’u ya zama family house mai ɓangarori huɗu.
Ginine irin na mutanen da, shiyyasa ya kasance gida babba da har ƴaƴansa Uku duk suka sami gurbin zama da iyalansu a cikinsa.
A yanzu haka dai ALLAH ya azurtashi da jikoki daga tsatson waɗannan ƴaƴa huɗu da zasu iya kaiwa kusan ashirin da huɗu, harda ƴaƴan ƴarsa mace Marwa dake aure acan garin Dutsamma kuma guda biyu.
Huguma A Rubuce Take Hausa Novel Complete
Duka ƴaƴan malam Rabi’u ALLAH baisa sunyi karatun boko ba har suka kai minzalin hankali, amma sunada ilimin addini gwargwadon iko.
Babban ciki mai suna Hamza shine ya fara auren matarsa ta farko Ruƙayya, wadda ya koma gida ya auro ɗiyar zumu, wato ɗiyar gwaggonsa ƙanwar mahaifinsa.
Ruƙayya ta tare a kano tare da mijinta Hamza annan cikin gidansu, ya gina ɗakuna biyune da bayi ya katange wajen, Ruƙayya tana samun soyayyarsa data iyayensa mai tsafta harma da ƙannensa.
Sai da Ruƙayya ta shekara uku a gidan sannan ta samu ciki, bayan ya kai haihuwa ta haife ɗiyarta mace wadda taci suna maryam.
Haihuwar Maryam da watanni biyu Muktar yazo da batun sake aure.
Hankalin Ruƙayya ya tashi ƙololuwa, hakama iyayensa suka nuna sam basu yardaba.
Yashiga damuwa sosai, saboda yanason Suwaiba, kuma harma sunyi alƙawarin aure, da farko yaso ya haƙuran amma sai ya kasa, yaje can gida Shema ya sanar ma mahaifin Ruƙayya halin da ake ciki.
Mahaifin Ruƙayya yazo kano, inda ya wanke Ruƙayya da faɗa tas, sannan ya koma nasiha a gareta, hakama iyayen Hamza ya samesu ya nuna musu suyi haƙuri su barsa tunda yanaso, da yaje gefe yana aikata abun banza gara ya auro yarinyar zaifi kwanciyar hankali.
Badan su iya ladi sun soba suka amince akai auren Suwaiba da Hamza.
Suwaiba dai asalin iyayenta ƴan dawanau ne, amma yanzu suna nan zaune a cikin garin kano, bata da damuwa sam, dan tunda ta tare gidan Hamza batajin daɗin kowa sai shi, iyayensa da ƴan uwansa basa sonta, ƙiri-ƙiri suke nuna mata fifiko akan Ruƙayya.
Danne zuciyarta tayi tamkar bata gani, takuma kwantar da hankalinta tana musu biyayya su duka, wannan halayyar tatace ta saka suka fara sassauta mata, har itama Ruƙayyar kanta.
Koda yaushe zakiga Maryam maƙale da Suwaiba, dan tanada son yaran tsiya, tun Ruƙayya na ƙwacewa bisa zugar matar Yusha’u harta hakura ganin Suwaiba bata taɓa cutar da Maryam ɗinba, lokacin ma da Ruƙayya zata yaye maryam sai Suwaiba ta amsheta ta yayeta, tundaga wannan lokacin kuma zaman Maryam ya koma hannun Suwaiba.
Kawaicin ɗan fari yasa Rukayya ta ƙyale mata.
Cikin hikimar ALLAH kuma sai Suwaiba da Ruƙayya suka fara laulayin ciki a tare, Rukayya na biyu, Suwaiba na farko, tare sukaita laulayinsu har ALLAH ya saukesu lafiya, sai dai Ruƙayyace ta fara haihuwar ɗiyarta mace, taci sunan Rahama, bayan kamar sati biyu dayin suna sai itama Suwaiba ta haihu, amma ita namijine.
Itama ranar suna yaronta yaci suna AHMAD, Suwaiba mutum ce mai azabar kawaici, sai yazam har akan Ahmad halayyarta na nan, dan sam yitake kamar ba ɗantaba, dukda kuwa tana ƙaunarsa sosai, wani lokacin tana zaune zaita kuka amma tai biris dashi, har sai Ruƙayya ta shigo ta ɗaukesa tana mata faɗa, ko bashi nono sai Ruƙayyan ta tsaya a kanta wani lokacin.
Wannan kawaicin da takeyi mai tsanani a kansa yasaka Ruƙayya maida hankalin kula dashi da Rahama, sai suka taso tamkar wasu tagwaye, idan ka ganshi hannun Suwaiba to nono zaisha.
Maryam kam ta zama ƴar ɗakin Suwaiba, itace tamkar uwarta, itama Ruƙayya tana kawaici akanta, dan bata faɗar koda sunanta kamar yanda itama Suwaiba bata faɗar sunan Ahmad.
Ahaka yaran suka fara wayo har zuwa yaye, sai zaman Ahmad ya koma wajen Ruƙayya gaba ɗaya, kamar yanda Maryam take hannun Suwaiba.
A wannan karon sai Ruƙayya ta fara samun ciki kafin Suwaiba, sai da cikinta yakai kusan wata bakwai sannan Suwaiba itama ta fara laulayi, a wannan haihuwarma dai Ruƙayya mace ta haifa, wadda taci suna Sakina.
Su Ahmad sunyi murna sosai an haifa musu ƙanwa, sai nan nan suke da ita dukdama bawani wayone dasuba lokacin.
Bayan haihuwar Sakina da kusan wata taƙwas itama Suwaiba ta haife ƴarta mace, itama taci suna Raheenat.
Ƴaƴa zun fara cika gidan malam Muktar, dan haka sunayen iyayensu ya fara ɓuya, Ruƙayya ta koma Ayyah, Suwaiba kuma Gwaggo.
Tun daga kan Sakina Ayyah (Ruƙayya) bata sake haihuwaba, sai Gwaggo (Suwaiba) ce ta cigaba da haihuwa, tayi Mudanseer, Abubakar, Fa’iza, Sadiya, sai auta Zainab.
Daganan ne haihuwar ta tsaya itama, yaransu sun taso kansu a haɗe, inba sanar maka akaiba baka taɓa sanin ƴaƴan wance da wance, tare suka haɗu wajen gina ƴaƴansu a tarbiyya, sun gina gidansu bisa ƙyaƙykyawan tsari mai birgewa duk da sheɗancin kishin sauri da suke fuskanta lokuta da dama.
Sai ƙanin Hamza mai suna Yusha’u, shima dai matarsa ɗaya da ƴaƴa biyu, shima a cikin gidan ya gina nashi ɗakin matarsa ke zaune, shima sai ya ja katanga iya sashensa kamar yanda Hamza yayi, ya auri matarsa mai suna Ɗausiyya (Gaje) kusan tare da auren yayansa hamza na biyu, hakanne ya saka Gaje ɗaukar kishin duniya ta aza akan Suwaiba tamkar mijinsh ɗaya, dan komai na auren Suwaiba yafi nata.
Taso saka ruɗani a zaman Suwaiba da Ruƙayya, su haɗe kai su ware Suwaiba a gidan, amma sai UBANGIJI ya hana hakan, babu irin munafircin da batai musu, sai yazam ko saɓanin ya shigo tsakaninsu baya wani daɗewa suke fahimtar juna.
Lokacin da riƙon Maryam ya dawo hannun Suwaiba ba ƙaramin baƙin ciki Gaje ta shigaba, taita zuga Ruƙayya akan ta amshe Maryam, amma sai ALLAH bai ƙaddara hakanba.
Abinda kuma yazo ya sake haɗa ƙiyayyarsu Haihuwar namiji da Suwaiba tayi, wato Ahmad, dan kusan tare itama Gaje ta haihu dasu, sai dai itama mace ta samu kamar Ruƙayya, wadda taci suna Binta.
Nanma Gaje ta so ta cusama Ruƙayya ƙiyayyar Ahmad sai hakan bai faruba, dan kuwa Ahmad ma sai ya dawo hannun Ruƙayyan gaba ɗaya.
Tunda Gaje ta fuskanci bazatai galabar ɓata zaman Ruƙayya da Suwaiba ba sai ta koma kishi dasu gaba ɗaya, kullum burinta ta yaya zata ƙuntata musu kota haɗasu faɗa.
Sukam watsar da lamarinta sukayi tankar basusan da zamanta a gidanba.
Ahaka zaman nasu yaci gaba da tafiya har Ilyasu ɗa na uku wajen su malam Rabi’u yayo nasa auren shima.
Ilyasu ya auro matarsa mai suna Sailuba, tunda Sailuba ta tare a gidan sai Gaje ta shiga jan ra’ayinta da cusa mata tsanar su Ruƙayya (Ayyah) a zuciya, a hankali itama abun ya fara tasiri a ranta, sun ware kansu su biyu, bakajin cikinsu sam a gidan, sannu a hankali sai suka fara jan ra’ayin mazansu ma.
Daga nan ne fa zumincin iyalan malam Rabi’u yaso fara tangal-tangal.
Hankalinsa ya tashi lokacin da ya fahimci daga inda matsalar ke neman fitowa, dan haka ya tara ƴaƴansa duka huɗu har Marwanatu autarsu da itama tai aure acan dutsamma.
Ta inda ya shiga ba tanan yake fitaba wajen banbamesu da masifa akan sheɗancin matansu dake nan lalata zumincinsu.
Jikinsu kuma duk sai yayi sanyi, dan tabbas sun fahimci kuskurensu sosai, haƙuri sukaita bama iyayen nasu.
Iya Ladi tace ita sam bazata haƙura ba sai Yusha’u da Ilyasu sun ƙara aure, danta fahimci matsalar daga wajen matansu take.
A take Ilyasu ya amince zai ƙara auren, amma Yusha’u sai ya bada haƙuri akan shifa baida ra’ayin sake mata bayan matarsa Gaje.
Iya Ladi tace aikuwa bai isaba, ƙara aure ya zamar masa tilas, tadai bashi lokaci yaje ya nema wadda taimar daga lokacin har tsawon shekara uku.
Kwanaki kaɗan dayin wannan Zama, zancen ƙara auren Ilyasu ya taso, zai auri wata yarinya anan ƙasan layinsu mai suna Zubaida.
Bayan Ilyasu ya ƙara aure a nanma sai Gaje taita tunzura Sailuba, sam zaman lafiya yaƙi tsakanin matan Ilyasu saboda munafurcin Gaje.
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya a wannan family, a cikin gida ɗaya har kawo yanzu da duk sun mallaki hankulansu, ƴaƴansu duk sunyi girma, yayinda tsufa ya kama Malam Rabi’u sosai, hakama iya ladi, dukda dai ita Alhmdllh jikinta da ƙwari tunda komai tana iyayima kanta.
Hamza talakane mai ƙoƙarin neman na yau da gobe, yanada wadatar zuci da bai amince ya zauna roƙoba, duk wahalar sana’a yana ƙokarin ganin yayi ya samawa iyalansa abinci, da abinda zai kula da iliminsu, dan ya tashi zuciyarsa nason ƴaƴansa suyi karatun boko, amma ga sauran ƴan uwansa sam ba haka baneba, sun tsani ilimin boko, a ganinsu watsa tarbiyyar yarane kawai, inda yana da kyau da iyayensu suma sun sakasu ai..
Hamza yasha zaunar dasu ya fahimtar dasu banbancin zamanin yanzu da nasu daya shuɗe, sai dai sam sunƙi fahimtarsa, hakanne ya sakashi ƙyalesu kawai.
Shi ƴaƴansa Suna zuwa makarantar boko ta gwamnati tamkar sauran yara, sannan da yamma suje islamiyya, da dare suje allo.
Rayuwa ta shuɗa inda malam Hamza (Baba) ya fara aurar da ƴaƴansa, Maryam ita aka fara kaiwa ɗakin miji, sai Rahama da suka tashi sa’anni da Ahmad, daga nan sai Raheenatu.
Shima Yusha’u ya aurar da Binta, wanda bayan bikin da kwanaki kaɗan yace zai kara aure.
Tashin hankali kenan, da ga mama Gaje, wadda tai tsalle ta dire akan bai isaba, ita tafi ƙarfin zama da kishiya wlhy.
Rigima tayi rigima har takai Yusha’u ya saki Gaje da cikinta ɗan wata bakwai.
Wannan shine sanadin barin Gaje gidan, shikuma yayo aurensa.
Daga nanne suka sami zaman lafiya, kowa ya koma mutunta ɗan uwansa a gidan.
Amaryar Yusha’u ta sinkuto masa ɗiya mace bayan shekara ɗaya, wadda taci suna Umm-Rumana.
Ƴaƴan Baba Hamza mata daya aurar Dukansu iyakarsu sakandire aji uku yake musu auren, dan haka Ahmad ne ya fara wuce aji uku na sakandire a gidansu.
Ahmad ƙyaƙyƙyawan yaro mai cikar halittar asalin rumawan katsinawa, komai nasa mahaifinsane, yanada ƙwazo a makaranta ga rashin hayaniya, dan sam da wahala kaji ance ga abokin faɗansa, inhar kaga yayi faɗa to ankaisa maƙurane, dan yanada zafin zuciya idan aka kaishi ƙarshe, sannan idan yay fushi da abu Ayyah ce kawai ke iya lankwasashi cikin sauƙi.
Dan Ahmad ɗan gatan Ayyah ne sosai, duk abinda kaga Ahmad ya nema ya rasa sai dai idan Ayyah bata da ƙarfin siyensa, shima kuma saitayi ƙokarin saya masa makamancinsa, harya fara zama saurayi komai nashi yana ɗakinta, tsakaninsa da mahaifiyarsa kuwa gaisuwace kawai, dan kallonsa ma bata iyayi saboda kunyar ɗan fari.
Ya daɗe baisan ba Ayyah ce ta haifesa ba, da yasani kuman ma bai damuba, abinda kawai ke bashi mamaki kawaicin mahaifiyarsu, dan sam bata sakewa dashi, tun abun bai damunsa harya ɗan fara damunsa, amma daya ƙara hankali sai ya fuskanci ba sonshi bane batayi kawai al’adace irinta hausawa, tunda itama Ayyah ai bata kula yayarsu Maryam, komai sai gwaggo.
Tun Ahmad na sakandire aji ɗaya suka haɗu da Samina, an tashi makaranta sun nufo gida shi da su maryam sai suka iske yara na damben faɗa a wani lungu.
Maryam tayi ƙoƙarin rabasu amma ta gaza, hakan yasa Ahmad ɗaukar ƴar bulala ya tsutstsula musu a ɗuwawu, dole suka rabu kowa na shafa wajen yana kuka.
Yarinya ɗaya a cikinsu sai ta maido faɗan akan Ahmad daya dokesu, tsayawa yay kawai yana kallonta da mamaki, dan alokacin shekarun nata bazasu gaza bakwai ba, inma sun wuce sai dai ƴan wattani.
Kuka take kashirɓan akan saita rama dukan da yay musu, ta kama ƙasan rigarsa ta riƙe tana kai masa duka da ɗan hannunta.
Shi dariyama ta bashi, dan haka ya tsaya yana kallonta yanayi, ganin da gaske take sai Rahama ta kamata ta janye tana dungure mata kai, nanko yarinya takuma daddagewa ta fasa musu kuka harda zagi.
Sunyi mamakin rashin kunyarta, suka wuce suka barta tana cigaba da zaginsu.
Washe gari sun taho makaranta suka gamu da yarinyar jiya da ko sunanta basu saniba, tana ƙyalla ido taga Ahmad saita samu dutse ta jefa masa, aiko sai akan goshinsa, kafin kace kwabo sai jini.
Dole aka kaisa ƙyamiz daga nan makaranta, yarinyar kuwa ta tsere gida basu sake ganintaba.
Bayan kwana huɗu Ahmad ya samu sauƙi ya koma zuwa makaranta, a randa ya koma yakuma yin gamo da yarinyar nan a hanya ana faɗa da ita.
Tsayawa kawai yay yana kallonta, ya kula batajin magana sam, tana ganinsa ta kwasa da gudu zata tsere, amma saiya cafkota, kuka ta saka masa da magiyar yayi haƙuri.
Shiko ya zare mata idanu yana faɗin, saiya rama zubar masa da jini da tayi.
Sosai take kuka tana tsalle da bashi haƙuri, shiko ya tsaya kawai yana kallonta.
Ganin bazata nutsuba yasashi fadin, “Kinga nutsu na fasa ramawar”.
Tsayawa tai tana share hawayenta, tace, “Da gaske ka haƙura?”.
Kansa ya ɗaga mata alamar eh.
Hakan ne yasa ta nutsu, sai kuma takai hannu tana taɓa masa ciwonsa inda aka saka bandejin, dukta marairaice alamar jin tausayinsa.
Hannun nata ya janye yana murmushi, yace, “Kinga ai ya warke, yaya sunanki?”.
“Samina” ta faɗa har yanzu hankalinta nakan goshin nasa data fasa.
“Suna mai daɗi” ya faɗa yana miƙewa riƙe da hannunta, cikin makaranta suka karasa yana tambayarta ajinsu, sashen ƴan firamari ya kaita, saida ya kaita har cikin aji, ya ɗauki naira ɗaya ta ƙwandala ya bata a cikin kuɗin taransa naira uku da Ayyah ta bashi.
Tun daga wannan ranar sai yazam kullum Samina saita zo wajen Ahmad, tun su Rahama na mangareta har suka bari, dan shaƙuwace ta fara shiga tsakaninsu a hankali, harma takai ga Ahmad yasan gidansu Samina, dan anguwarsu ɗaya, sai dai ba layinsu ɗayaba, tsakanin makarantar su Ahmad da gidansu Samina babu nisa, shiko Ahmad gidansu da akwai ɗan nisa da makarantar.
Haka suka kasance a tare, idan Samina ta taho makaranta bata shiga sai ta jira Ahmad yazo, dayake makarantar firamare din kusa take da sakandire ɗin, shikuma shine zai kama hannunta ya rakata har ajinsu yakuma cire ƙwandala ya bata a kuɗinsa na tara.
Shaƙuwar dake tsakaninsuce tasa har Ahmad yasan gidansu Samina, wadda ashe bai saniba ƴar uwarsace ta jini.
Dan kuwa Samina ɗiyar Mama Gaje ce tsohuwar matar Yusha’u ƙanin Hamza daya saki da ciki.
Ashe bayan fitowarta ta haifi Samina sai tai aure a can garin Bauci, kuma da Samina ta tafi sannan tana jinjira, haihuwarta biyu acan zaman yaƙi daɗi ta kashe auren ta dawo kano da Samina, dan wancan mijin ya kwace ƴaƴansa.
Tunda kowa ya fahimci hakan a gidan sai ya fara jan Samina jikinsa, yayinda Ahmad yaytama Kawunsa Yusha’u naci akan ya dawo da mama gaje mahaifiyar Samina gidan dan ALLAH.
Da taimakon Ahmad daya kama kafa dasu Iya Ladi Mama Gaje ta sake dawowa gidansu, inda Samina da Ahmad suka kasance ƙarƙashin inuwa ɗaya.
A wannan karon Mama gaje da shirinta ta dawo gidansu Ahmad, dan kuwa sai da ta gama mallake zuciyar kowa musamman Malam Rabi’u da Iya Ladi.
Dawowarta kuma gidan ya sake ɗaukar sabon salon zama, sai dai kowa na dannewa da kawaici saboda yanzu akwai ƴaƴa a tsakani.
Da taimakon Ahmad dukan yaran gidansu suka samu shiga makaranta a yanzu, musamman ganin ita Samina tanayi tunda ba’a gidan ta tashiba.
A haka har Samina itama ta shigo sakandire ɗin dayake maza da matane a haɗe, hakan ya saka shaƙuwarsu ta sake ƙarfi mai ban mamaki, tana aji ɗaya yana aji biyar, amma ko yaushe suna tare, hakan yasaka abokansa suka fara kiransa da suna Sharukhan baban soyayya.
Page 2
………….Yakanyi dariya kawai, dan a sannan ba soyayyar bace a tsakaninsu, duk da dai ta musu kamu basu saniba.
Tun ana yaya da kawa har abin ya fara rikiɗa yana zama soyayya, soyayyarma mai ƙarfi da shaƙuwa, kowa ya san da hakan a cikin iyayensu kuma duk da iyayen Ahmad mata basuso hakaba saboda mugun halin Mama Gaje.
To Amma ya zasuyi da hukuncin UBANGIJI? Dole suka ɗauke idanunsu suka koma musu addu’a da fatan ALLAH yasa kar Samina tayo gadon halin Uwarta.
Bayan Ahmad ya kammala sakandire saiya fara bin mahaifinsa kasuwa wajen sana’arsa ta saida yadikan maza da huluna, amma sai baban yace da hakan ai gara ya koya koda sana’ar ɗinkice ko wani abun.
Ahmad ya aminta da hakan ɗari bisa ɗari, dan haka yashiga wani shagon koyan ɗinki anan bayan layinsu kusa da makarantar su samina.
kusancin da suka samune ya kara sake ƙullesu sosai, dan kullum daga gida Ahmad da Samina tare suke tahowa, saiya rakata makaranta zai dawo shago wajen aikinsa.
Sannan da an tasosu daga makaranta komi yake a shago sai ya ajiye ya rakata har gida, wataranma sake biyoshi shagon ta keyi, data shiga gida babu daɗewa zata fito wajensa su koma tare..
Ƴan shagon kan musu dariya, musamman da suke ganin sunyi ƙanana, badai za’ace za’ai musu aure a wannan shekarunba.
Lokacin da Baba ya fahimci wannan shashancin nasu sai yaytai ma Ahmad ɗin faɗa, yakuma ce karya sake ganin Samina ta bishi shago bayan ta dawo makaranta.
Yaji faɗan baba ya dakatar da Samina, amma dukda hakan wataran saita ɗan zagaya a ɓoye taje, musamman ranar weekend da babu karatu.
Shekararsa ɗaya a shagon aka yayesa, zuwa lokacin kuma ya kware a aikinsa sosai dan ya nuna ƙwazo matuƙa.
Ayyah ta fasa ɗan asusunta da takeyi da ribar kayan sana’arta ta siya masa keken ɗinki, yayi murna sosai, hakama yan uwansa sunyi farin ciki, wani ɗakin dake cikin gidan aka fasama kofa ta baya aka saka masa keken ɗinkin, sai yazama shike ɗinkama baba yadika ana kaiwa kasuwa a siyar ɗinkakku, sai kuma masu kawowa da yakemawa, harma na mata yana dan jagulawa dukda bai wani ƙwareba saboda dinkin maza ya koya.
A hankali hannunsa ya fara faɗawa akan dinkin matan ma, kafin kace mi komai ya zama Alhmdllh, harma yana taimakawa gidansu da abinda ALLAH ya hore masa, gefe kuma yanama Samina hidima sosai dasu ta karatu da buƙatun yau da kullum.
Ganin yasamu madogara kuma yana samu Alhmdllh sai yay aniyar komawa karatu.
Kowa ya bashi goyon baya, dan haka ya shiga kokarin neman gurbi a jami’ar b.u.k.
Ya samu shiga jami’ar B.U.K, dayake takardunsa sunyi ƙyau sosai, kuma a lokacin tsadar rayuwa batakai hakaba sosai.
Komawarsa makaranta yasakashi sake zama busy, ko ɗinkima sai yayi da gaske yake samu yaɗanyi, ga kuma aikin yana samu, ganin zai iya korar customers ta wannan hanyar sai ya fara koyama ƙaninsa Mudanseer shima, aiko Alhmdllh Mudanseer ma sai ya maida hankalinsa sosai, sai ya zam yana taimakawa Ahmad ɗin da wasu ayyukan.
Tunda Ahmad ya shiga rayuwar Samina ya fara canjata sai baba Yusha’u kejin daɗi sosai, dan abubuwa da yawa sai Samina tabar biyema mahaifiyarta, dan a hannunta ta tashi, lokacin da mama Gaje ta dawo gidansu Ahmad sai tarbiyyar Samina ya banbanta dana sauran yaran gidan.
Daɗin hakan da Baba Yusha’u ya jine ya sashi zaunar da ƴan uwansa duka a gaban iyayensu su iya ladi, aka kuma kira masa Ahmad da Samina, a gaban kowa ya kuma sake damƙa ma Ahmad amanar kula da Samina, tare da alƙawarin aura masa ita a duk lokacin da suka kai munzalin girma, ya kumace ko bayan babu ransa bai yarda wannan alƙawarin ya tashiba.
Murmushi kawai Ahmad yayi kansa a ƙasa saboda kunya.
Yayinda sauran ƴan uwa da tsoffi su malam Rabi’u wannan abu yay musu daɗi, dankuwa koba komai zumincin ƴaƴansu zai ƙara danƙo da ƙarfi.
Albarka kowa ya sakama abin, tare da addu’ar kaiwa lokacin da rai.
Tun daga wannan lokacinne kuma Samina bata kula kowanne namiji, kowa yasan an mata miji Ahmad, hatta da danginsu na Shema kowa yasan hakan.
Mama Gaje dai batace hakan bai mataba, bakuma taji a ranta zuwa nan gaba idan Samina ta sami wanda yafi Ahmad zata hanata barin Ahmad ɗinba, idan kuma Ahmad yayi arziƙi dama ta dawo hannunta, dan kuwa sai yanda tayi dasu Ayyah akansa.
Tunda Ahmad ya gama secondary ya koya ɗinki yana kama ƴan kuɗaɗe sai nauyin Samina ya kusan koma kansa, shine duk wani bukatunta na makaranta, shine dinkinta da bukatun yau da kullum na ɗiya mace, hatta dasu kayan ciki na mata bai gazaba wajen bata kudin saye.
Wannan hidima da yake da ita sai ta ƙara saka mata girmansa da ƙaunarsa a zuciyarta, bata da hira sai ta Ahmad, duk wani namiji a idonta mace ne, Ahmad ɗintane kawai take kallo da gashin arziƙi, shine kuma kawai nagartaccen namiji a idonta.
Bayan samina ta gama secondary lokacin Ahmad na shekararsa ta ƙarshe a jami’a sai yake bata shawarar komawa karatu.
Lokacin suna zaune a ƙofar gidansune a shagon ɗinkinsa suna hira, dama mafi yawan lokuta anan suke hirar tasu.
Kallonsa tayi da ɗan murmushi ta dukar da kanta ƙasa saboda kunyarsa, cikin muryarta mai cike da yanga tace, “Haba Hubby, kamar ka manta yanda al’amuran suke a gidannan namu, idan nace zan cigaba da karatu yanzu a ina baba zai samu kuɗin ɗaukar nauyina?, kullum ana haɗa na masara da ƙyar a ina za’a samo na karatu kuma?, sannan a ziri’ar mu kaf babu macen data taɓa gama secondary sai nifa, shima da taimakonka, saiko ƙannenmu uku mata da ayanzu suma zasu kammala, iyayenmu ma bazasu amince naje jami’a ba nima nasani”.
Murmushi Ahmad dake kallonta da tausayawa yayi, ya sauke ajiyar zuciya har lokacin idonsa a kanta, a hankali yace, “Samie na ai komai na ALLAH ne, indai kina da ra’ayin karatun baki da matsala, dan ba baba zamu dorama wannan nauyinba, nine zan ɗauki nauyin matata da kaina, kinga insha ALLAHU idan ubangiji ya shige mana gaba sanda zaki kammala ƙila koda karamin aikine na samu, sai maganar aurenmu ko, kodama baki gamaba inhar aka samu ɗan abin rufin asiri sai mu rufama kanmu asiri a wankemu a miƙamu daga ciki kowama ya huta”.
Maganarsa ta ƙarshe ce ta sakata jan hijjab ɗinta ta rufe fuskarta saboda kunya tana ƴar dariya.
Shima dariyar yayi mai sauti yana shafa kansa, yace, “Sorry bazan sake bama matata kunyaba, ammafa randa aka kaimin ita zan cire kunyarnan dukanta insha ALLAHU”.
Babu shiri Samina ta tashi ta gudu zuwa gida, duk kiran da Ahmad yake mata akan ta dawo su karasa magana kasawa tayi, dole ya haƙura ya ƙyaleta.
Daya shiga gidan suka haɗuma da sauri ta kauda fuska taƙi kallonsa, lokacin suna a tsakar gida itada su Rumana suna shafa kurkur a fuska.
Murmushi kawai yay yana ɗauke kansa, dan baya wasa da yaran gidan, idan ka cire Samina babu mai yawan ganin haƙoransa a cikinsu.
Duk sannu sukai masa, ya amsa kamar yanda ya saba, sai da yazo gab da shiga sashensu ne suka haɗa ido da Samina data saci kallonsa.
Ido ɗaya ya kashe mata yana murmushi, tai saurin ɗauke kai tana murguɗa masa baki.
Shigewa yay yana maijin nishaɗi da ƙarin kaunarta a ransa.
Da daddare Samina take sanarma mahaifiyarta yanda sukayi da Ahmad.
Mama Gaje da daɗi ya lulluɓe ta washe baki tana rungume Samina.
“Yo Samina wannan kuwa abin amincewane da guduma, damacefa tazo mana, ai wannan yaro bamusan abinda zamuce masaba a rayuwa, ALLAH dai ya saka masa da alkairi, yakuma kaimu lokacin aurenku, dan kuwa Suwaiba ta haifama Ruƙayya, niko Ruƙayya ta rainar mini”.
Duk da Samina bata fahimci zaurencen mahaifiyarta na ƙarshen maganarba Babu kunya ta amsa da amin, dan tana tsananin son Ahmad da har takai batajin kunyar yin duk wani abun daya shafesa a gaban kowa, iyayensu maza kawai take iya ɗagama ƙafa akan Ahmad.
Hatta kakanninsu Iya ladi da baba Rabi’u bata jin kunyarsu akan Ahmad.
Sai washe gari Ahmad ya samu saƙo a rubuce daga wajen Samina akan amsar cigaba da karatunta.
Yaji daɗin hakan sosai, a ranar kuma ya samu su baba da batun su duka harma da kakanninsu.
Da farko dai tsoho mai ran ƙarfe malam Rabi’u har yace a’a, danshi kam baiga dabara ba a wajen nan sam.
Amma sai Ahmad yayta lallashinsa da nuna masa ra’ayinsa akan matarsa tai karatu mai zurfi, tunda yanzu suna da dama saita fara kafin shi yaɗan samu madogarar da za’ai hidimar aurensu, in yaso ita saita ƙarasa karatun a gidansa.
Fatan alkairi yay musu, tunda ya fahimci Ahmad nason lamarin, bai kamata a katse masa hanzariba matsayinsa na babba namiji a gidan.
Kwana biyu dayin zancen Ahmad ya amshi takardunta ya tafi dasu makaranta.
Tun daga ranar Ahmad yashiga faɗi tashi wajen ganin ya samawa Samina gurbin karatu, kasancewarsa mai ƙokari a makarantar yasashi kusanci da mafi yawan malaman cikinta, ta hanyarsu ya samawa Samina gurbin karatu.
Lokacin da labarin hakan yazo mata tayi farin ciki harma ta rasa ina zata saka kanta dan daɗi.
Hakama iyayensu kowa yaji daɗi, babu kuma wanda ya nuna rashin dacewar hakan, dan a ganinsu Ahmad ɗin yanada ra’ayin matarsa tasamu karatu mai zurfi shiyyasa ya maida Saminar makaranta.
Sauran ƴan uwantama ƴammatan gidan sun tayata murna da wannan cigaba, koba komai suma zasu saka ran cigaban tunda aka fara daga kanta.
Nauyin karatun Samina daya dawo kan Ahmad sai ya sa abubuwa suka sake masa yawa, dan kuɗin shigarsa basu kai nauyin ɗukar hidimar da yakeyiba, gashi dai-dai da kuɗin mota wannan sai Samina tazo wajensa take amsa. Ga nauyin karatun Mudanseer ma shine yake bada mafi yawan ƙarfinsa, dukda mahaifansu na taimakawa tanan ɓan garen.
Kuma a gefen hidimar gidama baya zuba ido baneba, yanayin ƙoƙarinsa wajen taimakon mahaifinsu.
Wannan abubuwan da sukaimasa yawane ya sakashi fara tunanin faɗaɗa neman kuɗin nasa, akuyarsa da ya saya Ayyah na kula da ita yace zai saida ya zuba kayan ɗinki na saidawa, saboda akuyar ta haifi yara biyu sai Ayyah ta amince masa aka saida, da kuɗin akuyar yaɗan sayo kayan su zare da wasu ƙananun abubuwa irinsu allura, almakashi, zips da sauransu ya zuba a shagon, teloli dake cikin gida da masuma shagunan dake kusa sai sukanzo sukan saya anan, kamar wasa sai ALLAH ya sakama abin albarka ake ciniki, idan duk suna makaranta sukan ɗan ɗebo kayan sayarwar a ajiye cikin gida, duk wanda yazo saya sai yayi sallama a bashi.
Ahmad bai tsaya ananba kawai, har komawa yay idan ya taso makaranta ya sari lemuka ya ɗora a kansa yana zuwa bakin titi saboda motoci masu wucewa, wani lokacin kuma biredi, ko kayan fruits haka.
Da waɗannan sana’oi da wahalhalu Ahmad ya cigaba da kula da karatunsu shi da Mudanseer da samina, sauran ƙannensa ma yakan basu gudunmawa, hakama yayunsa dake gidan aure sukan taimaka masu da abinda ALLAH ya hore musu.
Ahmad ya kammala degree ɗinsa ya samu yay bautar ƙasa, daga nan kumane ya dawo zaman gida sosai, dan babu dai maganar aiki.
Yaci gaba da sana’oinsa na ɗinki da saida kayan ɗinki, zuwa yanzu kuma hannunsa ya faɗa sosai ya ƙware, ɗinkuna yake na zamani masu birgewa, duk wasu samari ƴan kwalisa da ƴammata zaka samu ɗinkinsu ya fitone daga shagon Ahmad, wanda aka fi sani da Ahmad sharukhan, idan ɗinki yaɗan kwanta saiya koma sana’arsa ta sai da lemo da ruwa, kokuma kayan fruits.
Yanzu dai haka takai Ahmad yana hayar keke napep ne, yay ɗinkinsa da yamma ko dare, da safe zuwa la’asar yana neman taro da kwabo da adaidaitarsa a gari.
Matsala ta farko data fara shigowa tsakanin Samina da Ahmad shine, bayan barinsa makaranta Samina tayi sabbin ƙawaye, sanda yana nan koda yaushe suna tare, sai dai lokacin karatune zaka samesu ba tareba, duk wanda ma yake mu’amula dasu yasan suɗin masoyan junane.
Samina tun tana secondary takanyi karatun novels ɗin hausa, rayuwar jin daɗi da dukiya da akeyi a novels na ƙayatar da ita, har wani lokacinma takanyi addu’ar ALLAH ya buɗama Ahmad ɗinta shima yay arziƙi ya gina musu ƙaton gida, ya narka musu kayan alatu da jin daɗi, su ringa hawa motoci na alfarma ita dashi.
A wancan lokacin burin nata bai taɓa kaita ta nemi canjin Ahmad da masu irin suffar jaruman littafiba, shiɗin dai takema addu’ar ya samu su mora.
Takai koda Samina ta karanta littafi sam bata wani damuwa da ɗaukar darussan rayuwa ko ilimin da littafin yazo dashi, ita kawai soyayya da kayan ƙawane ke ɗaukar hankalinta da ƙara faɗaɗa burinta, tama kai inhar buk bana masu ƙazamin arziƙi bane ƴan gayu batason karantawa, data fara karatun taji ana faɗin jarumin littafi nashan wahalar neman nakansa sai buk ya fitar mata akai ta ajiyeshi, tafi son taji ana suffanta ƙyawun jaruman littafi tare da dukiyar da tunani bazai iya musaltawa ba, to takanji kamar tai tsalle ta ganta a buk ɗin saboda shauƙi.
Haɗuwarta dasu Nafy ne ya fara nuna mata hanyar samun cikar wannan burin nata, tun tanajin haushin kushe mata Ahmad da sukeyi akan talaucinsa har zuciyarta ta fara rawa da aminta da maganarsu.
Dan kuwa dai sunyi nasarar fara tsundumata shafe-shafen mayukan bilicin, dukda kuwa tanada haskenta gwargwadon iko, sannan Samina ƙyaƙyƙyawace babu laifi.
Ƙananun burikan Samina sun fara faɗaɗa, dan yanzu kowane biki saita san yanda ta ƙwalkwali Ahmad kuɗin ankonsa. Ada bata kula kowane saurayi sai Ahmad, amma zuwa yanzu kam ai samari babu iyaka take kulawa, dataga kazo da ƴar kalar manyan mutane babu wani jan aji take miƙa kanta.
Tun Ahmad na zuba mata idanu akan ƙananun sabbin ɗabi’unta harya kasa haƙuri ya tuhumeta akan bilicin data fara, ya tabbatar masa shi bama ya ra’ayin farar mace, yafisonta da kalar fatarta choco color, alokaci haƙuri tabasa, ta shirya masa ƙaryar ba bilicin baneba, kayan gyaran jikine irin namu na gida take amfani dashi.
Cayay kosu ɗinne tabar amfani dasu sai sunyi aure ya yarda da ingancinsu.
Ta amsa masa da to, amma tana bama su Nafy labari sai suka zugata akan ai ba aurenta yakeba, taci gaba da abinta, gashinan harta fara zama big girl shine zata wani biye masa, inharfa bazata cire tsoron Ahmad a rantaba to bazata taɓa wayewaba ta zama cikakkiyar ƴar jami’a balle shima ta maidoshi kan hanya su shinfiɗa ƙyaƙyƙyawan rayuwa irinta jaruman littafi.
Page 3
………..Da waɗannan shawarwarin dukkan ginin Ahmad ya fara rushewa ga tarbiyyar Samina, ta fara biyema ruɗin su Nafy, idonta ya fara buɗewa da rayuwa ta manyan yara masu aji, duk wani dandalin wayewa suna wajen matsayin manyan baƙi masu lokaci, wannan damar samarin jami’a ƴan ƙwalisa da lectures suka samu wajen shiga jikin su Samina, sai ga ƴaƴan manya masu abin magana a aljihu sun fara kutso kai cikin rayuwarsu.
Tunanin Samina ya fara bata cewar lallai Ahmad bazai zama dai-dai da burinta na rayuwar Jaruman novels ba, saboda har lokacin dai ana nan jiya iyau, buga-bugar sana’a ce dai kawai a samu na yau na gobe sai an fita nemansa, suturar kirki wannan ta shiga taro Ahmad bashi da ita, gaba ɗaya kayan nasa duk yadin (Tashi sama sallau) ne, idan ƙananun kaya ka gansa dasu ma dai na gwanjone ba sabbi ba, ƙyawune kawai Ahmad ɗin zai iya mata burga dashi.
A samarinta kuma na yanzuma akwai waɗanda zasu iya linkashi ƙyawun, ga kuɗi na gaske suna mata wasa dasu, wanda suka fara lulluɓe zuciyarta dana mahaifiyarta wajen mance alkairin Ahmad a garesu.
Duk tsiyar da Samina ke aikatawa mama gaje ta sani sarai, kwaɗayin abinda Samina ke kawo musu na ciye-ciye ne ya lulluɓe idanunta ruf.
Idan cikin samarin Samina wani yace zaizo bata kawoshi gidansu, sai dai ta kaisa can gidan kakanninta da suka haifi mama gaje.
Hakan yasa Ahmad baisan mi Samina ke aikatawa ba, dan bai taɓa kawoma ransa zata kula wani saurayi bayan shiba, musamman da yasan akwai alƙawarin aure a kansu da ƙaunar juna mai ƙarfin gaske.
_________________________
A yanzu haka Saminar na gidan kakarsu, taima Ahmad ƙarya Inna mari bata da lafiya dan kawai tasamu taje wani bikin ƙawarta da za’ayi.
Sai dai tsoron kar wani yakai masa gulma yasata kiransa a waya ta sanar masa cewar zataje wajen kamun bikin ƙawarta.
Bai musa mataba ya barta, amma yace ta jirasa yazo da mashin ɗin Sufyan zai kaita.
Hakan ba ƙaramin haushi ya bataba, amma yaya ta iya dashi.
Shiri take da sauri-sauri gudun kar Ahmad yazo ya sameta a gidan…… Dan tafison su tafi tare dasu Nafy, kiran da taji Iya kishiyar kakarta Inna mari na ƙwala mata daga waje yasa gabanta faɗuwa, tasan dai yanzu haka Ahmad ne yazo.
“Samina!, Samina!!, Wai Samina baƙya jinane kokuwa lalatar takice ta motsa ne?”.
Ta sake jiyo muryar iya daga tsakar gida.
Cikin cuno baki ta fito daga ɗakin dake can cikin wani lungu tana gyara ɗaurin ɗankwalinta ture kaga tsiya tana kumbura fuska.
“Kai Iya, irin wannan kira haka saikace na mafarauta, ɗan kwalifa nake ɗaurawa saboda su Nafy zasuzo yanzu mu wuce, mi kuma zan miki?”.
Baki iya dake tsaye bakin murhu tana ƙokarin hura wuta ta riƙe, “Samina anya wannan rayuwar ta dace dake kuwa? Baƙya ganin kinason wuce gona da iri? Yanzu nan kodan yaron nan Ahmad ai ƙyaɗan sassauta wani abun, wlhy kibar biyema lalatattun yarancan su Nafisa karsu kaiki su baro”.
Baki Samina ta ɗan taɓe tana gyara zaman gyalen kafaɗarta, “Iya nifa wlhy banajin daɗin irin maganganun nan naki, ni mi nakeyi mara ƙyau a rayuwata dan ALLAH?”.
“Ba nace kina wani abu mara ƙyau bane ba Samina, Inason dai ki tsaya matsayinki kodan Yaronnan da ya gama wahalar duniya a kanki, karsuje su hure miki kunne akan ɗabi’u mara amfani”.
“A’a Atine, anface ka fadi alkairi ko kai shiru, dan Ahmadu yaymata wahala sai akace bazata mori ƙuruciyarta ba? Naga ba aure aka ɗaura musu ba alƙawarin auren ne kawai ko?”.
Wata dattijuwar tsohuwa mace dake fitowa daga bandaki ta faɗa tana ƙokarin ajiye butar hannunta.
Su duka kallonta sukayi.
Iya tace, “Amma dai Mari ai kowa yasan dama ALLAH shine yake yanda yaso ga mutum, amma kinsan ta yaro ƙyau take bata ƙarko, tunda har da alƙawarin auren, wataranama ɗaurawa za’ayi kamar yanda muke fata
“Uhm Atine, mubar wannan batunma dan ALLAH, dan yanzu ba lokacin yinsa bane, ni dai abinda nasani kawai shine bazamuyima yarinya auren doleba, idan tace Ahmad takeso zamu bata, idanko ta kawo waninsa shima zamu bata”.
“Hakane Mari”.
Iya ta faɗa tana ɗauke kanta daga garesu ta koma ƙoƙarin hura wutar data fara.
Daga Samina har inna Mari kakarta harar Iya dake duke sukayi.
Samina ta maida kallonta ga kakar tata tana murmushi, “inna mari bara naje karsu Nafy suyita jirana, kinsan za’a fara kamun ƙarfe uku na yammane”.
“To Samina ALLAH ya tsare, a dai dunga kula saboda ƴan saka ido, kana rayuwarka baka damu da kowaba saikiga anata ƙokarin taɗo ƙafarka da harshe, bayan ko MANZON ALLAH ma yace mu kiyayi harsunanmu”.
“Humm Inna ai mutanen duniya ba’a iya musu, sunfi son kullum su ganka jiya iyau, kuma idan arziƙin kayi sune zasu fara zakalkalewar kai nasune”.
“Maganarki na kan hanya wlhy ƴar albarka, kedai jeki karki makara”.
“Okey my sweet kakus bye”.
“Duk da ban iya turancinba Samina, nima bye”.
Ficewa Samina tayi tana dariyar zancen kakar tata.
Itama inna mari ta shige ɗakinta tana ƙyalkyata dariyar sake ƙular da kishiyarta iya Atine.
Murmushi kawai Iya tayi, tasan duk ita akema habaicin, ta girgiza kanta tana nemawa abokiyar zaman nata da jikarta shiriyar ALLAH, tare da fatan ganewa kafin guri ya ƙure musu.
Kamar an saita Samina na fitowa daga ƙozajjen soron gidan kakanninta da Ahmad ta fara cin karo zaune bisa ɗan dandamalin dakalin dake ƙofar gidan maƙwafcinsu.
Ta tsaya tsam tana ƙarema kwalliyarsa kallo, tabbas Ahmad ƙyaƙykyawane, shiyyasa duk rashin tsadar kaya sukan zauna masa a ƙyaƙyƙyawar surarsa suyi ɗas.
Ba wani kayane mai tsada a jikinsaba, hularsa ƙube da ita kaɗai ta iya saninsa dashi ta ƙarshen gayunsa ya saka, ta zauna ɗas akansa, inda daga bayan ƙeyarsa kwantacciyar sumarsa ta jinin fulanin rumawan asalin katsinawa ta bayyana, sai yadi mai ƙarancin kuɗi mai kama dana ƴan makaranta kalar ruwan shanshan bale, takalmansa ƴan saƙe suma masu ƙarancin kuɗi, sai agogon fatar da itace ta saya masashi naira ɗari huɗu ɗaure a hannunsa da zoben azurfa a yatsansa, kayan sun ɗauki guga, dan haka suka kwanta luff tare da ɓoyewar tsufan da suka fara a idon mai kallonsa, ƙamshin turarensa yake mai ƙarancin kuɗi, amma akwai daɗi ga hancin mai shaƙa.
Ganinta ya sakashi miƙewa yana ƙawata nutsatstsiyar fuskarsa da murmushi na musamman.
“Barka da fitowa tauraruwar mata ma’abociyar haske da walwali”.
Samina ta kallesa a wani yatsine tana cuna baki gaba, ba tare data amsa masa kalmomin yabonsa ba ta maida murtani da faɗin, “Kai yaya, dama zakazo ɗin amma kaki kirana ka sanarmin kuma? Gashi nacema su Nafy su jirani a gidansu saimu tafi tare”.
Murmushi yaɗanyi duk da yanda tai masan ya bashi mamaki, “Yi haƙuri Samie na, banzo danna hanaki ƙyautata zaman tareba, nazone dama na kaiki basai kinsha wahalar jiran abin hawaba”.
Yanzu kam sosai ta juyi ta kallesa, cikin waro masa manyan idanunta tace, “Ka kaini kuma yah Ahmad? Da wane motan?”.
Huci yaɗan fidda mai ɗaci, dan ta fara ƙokarin janyo fusatarsa da wannan salon rainin wayon data ɗakko, amma kasancewarsa sonta na ɗawainiya dashi saiya sauke numfashi da ƙokarin hadiye dukkan fusatar tasa ya saki murmushi a karo na babu adadi.
“Banda abunki Samina ina naga mota, wannanma mashin ɗin Sufiyanu ne na aro danna sauƙaƙa miki wahala”.
“Tofa, to ALLAH yay mana maganinta ita wahalar, karka damu na hutar dakai, kaje kawai zamu tafine dasu Nafyn tunda kaga na musu alƙawarin binsu dan ALLAH”.
Wani irin bugawa yaji zuciyarsa tayi, sam baya ƙaunar alakar Samina da su Nafyn gidan ɗan-majillisa, amma ya kula yanzu dukkan hankalinta yana ga mu’amulantarsu. Ganin zata tafi yay saurin tsaidata ta hanyar faɗin,
“Okey to babu damuwa tunda kin samu abokan tafiya, ga wannan kozaki buƙaci wani abu a wajen”.
Har tayi niyyar wucewarta saita dawo baya jin ya ambaci kuɗi, babu kunya tazo ta amshe kuɗin dayake miƙomata canzazzu ƴan hamsin-hamsin rabin bandir ɗaya.
Godiya tai masa cikin ladabi, ta tura kuɗin a jakarta tare da sakar masa murmushi duk dan dai hankalinsa ya kwanta da barinta ta wuce ita kaɗai.
Ta ɗaga masa yatsun hannunta guda biyu alamar bye cike da wani salo.
Da kallo kawai ya iya binta tamkar wani soko, ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya yana nufar roba-roba mashin ɗin dayazo dashi kalar jaa, hawa kawai yay ya zauna yana kallonta harta ɓacema ganinsa, yanda take tafiyarta cikin yauƙi da yanga sai sonta ya kuma nunkuwa a ransa, yanason Samina so irin mai tsanani ɗinnan, dankuwa dashi ya girma a zuciya tun baima gama sanin ma’anar SO ɗinba.
Ya ɗauki kusan mintuna talatin a wajen kafin ya hau mashin ɗin yabar anguwar da tunanin ina ya dace ace yaje, dan shidai a yanzu ya koma majalisar abokansa dariya zasuyi masa, yanda ya fito yana ɓare-ɓaren jiki zaije yakai Samina, sai gashi Samina ta watsa masa ƙasa a ido, bayan kuma dama kullum abokansa na nuna masa yanzu Samina ta canja, ta fara fin ƙarfinsa amma sam yaƙi fahimtarsu balle ya yarda da batunsu.
Yawo yaytayi a gari, sai da ya fahimci man ciki yayi ƙasa kafin ya koma gida.
Ya iske abokansa na hada-hadar shiga sallar magriba a massallaci, dan haka shima yay haramar yin alwala domin samun jam’i.
Bayan an idar duk suka fito ɗai-ɗai zuwa majalisarsu da suka kafa a ƙofar gidan su Yakubu abokinsu, saboda baranda dake wajen, shikuma yakubu yanada shagon littatafan hausane da yake bada rancin da saidawa.
Hannu suka shiga bama juna suna gaisuwa, Ahmad ya miƙama Sufyanu key ɗin mashin ɗin yana faɗin, “Broth nagode, ALLAH ya bada ladan zuminci”.
Amin suka faɗa a tare, yayinda Sufiyanu dake amsar key ɗin ke faɗin Sharukhan ɗinmu nazata fa sai dare zamu ganka ALLAH, Amma kunyi saurin dawowa kaida gimbiyar taka”.
Murmushin yaƙe Ahmad yayi kawai, ya kishingiɗa kusa da Musa yana bama Sufiyanu amsa da, “Ai ba yaune ainahin bikinba fa, kamu sukayi yau shiyyasa, sai jibinema ɗaurin auren, kasan mata da shegen son bidi’a, shiyyasa a kullum ake ƙara nisanta talaka da samun aure cikin sauƙi”.
Cikin damuwa Rabilu yace, “Maganarka gaskiyane wlhy Ahmad, ba gamunanba, acikinmu nan wanene bai isa aurenba, kuma duk munada ƴammata amma babu kuɗin yin auren, to wai muma fa kenan dakeda sana’oi munkuma ɗanyi karatun, inaga waɗanda basuda sana’ar babu karatun kumafa”.
Salisu daya zabga tagumi ya wani marairaice fuska yana harɗe kafafunsa dake lilo a ƙasan benci, “Abokai wlhy bidi’oin biki suna taka rawar gani wajen ɗora mata a burin auren mai hannu da shuni, tana kuma jefa rayuwarsu a garari harma da ƙara yawaitar fyaɗe, yanzu irina masu ƙarfin sha’awa idan baka danne zuciyarkaba ai tuni zaka afkama ƴar wani ka jefa kanka a halaka da ƴan uwanka a damuwa ko”.
Lumshe idanu Ahmad yayi a hankali, dan maganar Salisu ta sosa masa inda ke masa ƙaikayi, yace “Uhumm” kawai ba tare da ya ƙara komaiba.
Hakane ya saka Sufiyanu da Yakubu dake kusa dashi kallonsa.
“Sharukhan yaya dai?”.
Ameenu da tun ɗazun baice komaiba ya faɗa yana kallon Ahmad ɗin shima.
Buɗe ido Ahmad yay da suka canja launi zuwa jaa, yay murmushi kawai yana girgiza kansa.
Hakanne yasaka su cigaba da hirarsu akan matsalolin aure da burikan da mazan da ƴammata ke dorawa saboda son gasa da masu kuɗi keyi lokacin bikinsu.
Sallar isha’ice ta tadasu a majalissar, dukansu suka dunguma zuwa massalaci, akabar waɗanda zasu sake alwala irinsu Ahmad.
Bayan sun idar da salla zama sukai islamiyyar da suka tsarama kansu kamar yadda suka saba a kowanne dare, malam Sulaiman ne malaminsu, wato limamin massalacin, bayan ƙarin karatu yay musu nasiha kamar yanda ya saba.
Ƙarfe tara da rabi dai-dai suka fito, kowa daga nan gida ya shiga domin cin abinci.
Tsakanin gidansu Ahmad da majalissarsu gida biyar ne, hakan yasakashi takawa a hankali suna tafiya shida Salisu da shima gidansu ke maƙwaftaka da nasu Ahmad, suna isowa kowa ya shige.
Gidansu Ahmad gidane na talakawa irin masu ƙaramin ƙarfinnan sosai kamar yanda kukaji tun a farkon labarin, ginine irin na zamanin daya shuɗe, duk da dai yana mulmule da suminti har jikin bango, amma kallo ɗaya zakaima gidan ka fahimci ingantaccen ginin daya samune yasaka sumintin daɗewa bai zabtareba, saika shiga soro biyu kafin ka iso ainahin tsakar gidansu, amma a shiga farkon gidan zakaci karo da turken awakine da mahaifansu mata ke kiwo, sai kejin kaji daga gefe wanda baida nisa sosai da ƙofar banɗakinsu.
A shiga farkon gidan ɗakunan kakanninsu da aka zagaye da katanga zaka fara iskewa, sai sashen Baba Iliyasu daga bangon gabas, sai sashen Baba Yusha’u mahaifin Samina daga can Bangon arewa, suna kallon sashin kakanninsu, sai sashen iyayen Ahmad a bangon yamma suna kallon sashensu baba Iliyasu.
Tsakar gida zaka fara tararwa, sannan kabi siririyar hanyar da zata sadaka da ainahin sashen da matan Baba Hamza mahaifin su Ahmad suke.
Ya shafa kan tunkiyar daketa ɓara kuka saboda rashin ganin ɗanta kusa da ita, “K dan ALLAH ki rage ihunan, tunkiyarnan sam baki da hankali akan ƴaƴa, inama ya shiga shima uban ɓarnar” Ahmad ya ƙare maganar yana leƙa ƙasan kejin kajinsu kozai gano ɗan jaririn ragon tunkiyar.
Can kuwa ya hangoshi kwance, dan haka yasa hannu ya zaƙulosa ya kai gabanta ya ajiye kafin ya shige ainahin cikin gidan da sallama.
Mahaifiyarsa da ƴar kunya ke tsakaninsu saboda shine na fari a gabanta ya fara cin karo tana ɗibar ruwa a tulun dake ƙasan barandar ɗakunansu cikin kofin silba.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tamkar batama gansaba, sai ƙannensa dake zaune a tabarma da fitila a gabansu sun baza littatafaine suka amsa masa, sai kuma Ayyah matar babansu ta farko dake riƙe dashi a ɗakinta data amsa itama daga cikin ɗakinta.
Ya gaida Gwaggo data gama zuba ruwan harta ɗora a tiren data shirya abincin babansu tana shirin ɗauka zuwa ɗakinsa, sau ɗaya ta amsa ta ɗauki tiren tai gaba abinta, yaɗan bita da kallo yana kauda kansa a lokaci ɗaya…..
Ayyah dake fitowa ta katsesa da faɗin, “Ɗan albarka ka dawo?”.
Murmushi yay mata yana ƙarasawa gabanta da cewa, “Eh Ayyah na, ina yini?”.
“Lafiya lau ɗan albarka, kaga tashi ga abincinka nan yau miyarka nasaka akai dole a gidannan, maza kaci karya huce, ga manshanu nan dana soya maka ɗazun”.
Cikin faɗaɗa fara’arsa ya miƙe yana faɗin, “ALLAH ya saka da alkairi Ayyah na, ya jiƙan malam ya ƙara muku nisan kwana da lafiya”.
Amin ta faɗa ita da ƙannensa.
Baba dake daga can ɗakinsa duk suna jinsu shi da gwaggo, ba yaune suka fara ganin hakanba, dan soyayyar Ayyah da Ahmad ALLAH ne kawai yasan iyakarta, amma ba mutumba, inhar ba faɗa maka akaiba bazaka taɓa ɗauka ba itace ta haifesaba.
Saman tabarmar da ƙanwarsa Sadiya ta shinfiɗa masa ya zauna, tuwone na jar masara dayaji dahuwa ta ma’iya, sai miyar tafasa da akayita da gyaɗa sai ƙamshi takeyi, ya buɗe kwanon langa ɗan ƙarami da manshanun ke a ciki ya zuba, tare da barbaɗa yajin daddawa da shikuma ke a robar cingam.
Laumar farko daya kai ya lumshe idanu saboda daɗin da miyar tayi, Zainab dake ajiye masa ruwa tai ƴar dariya ciki-ciki, “Yah Ahmad kaji miyar ta haɗu ko?”.
Idanunsa ya buɗe ya ɗaga mata kai kawai batare da yace komaiba.
Ayyah dake ƙoƙarin kunna redio ɗinta tai saurin faɗin, “To akku, ki tashi masa akai yaci abincinsa cikin salama”.
Baki Zainab ta kumbura tana barin wajen, hakan yay dai-dai da shigowar Mudanseer ƙanin Ahmad ɗin.
Sallama yay suka amsa, ya ajiye ledar hannunsa gaban Ayyah yana cewa, “Ayyah gashi nan inji Yaya Maryama, tace gobe insha ALLAHU zama tazo gidan”.
“Karma tazo” Ayyah ta faɗa rai a jagule.
Ɗago ido Ahmad yay ya kalli Ayyahn, kafin ya maida kan Mudanseer dake ƙoƙarin zama kusa dashi.
“Miya faru kuma da Yaya Maryaman?”.
“Yaya abinda kasani kullumne dai, faɗa suka sakeyi da kishiyarta shikuma jakin ya daki yaya maryama ɗin, amma sai batazo ta faɗaba tai shiru, sai ɗazunne Inna Haule tazo da zancen gidannan”.
Shiru Ahmad yay kamar bazai tankaba, ya tsame hannunsa daga abincin da yakeci yana ture kwanon silbar gefe, miƙewa yake shirin yi Ayyah tace,
“Ɗan albarka dama ka zauna kaci abincinka, itafa ta zaɓama kanta wannan rayuwar, mizaisa ku zauna kuna ɓata ranku a banza, maza koma ka zauna ka karasa ci”.
Komawa yay ya zauna, danba tarbiyyarsu bace jayayya da maganar manyansu, Mudanseer ya ɗauki ruwan dake gaban Ahmad yasha tare da wanke hannunsa, cikin kwantar da murya yace, “Yah Ahmad babu tayine? Bayan ga ƙamshin manshanu inaji ya cikan hanci ɗan gatan Ayyah”.
Hararsa Ahmad yayi, amma baice komaiba, hakanne ya saka Mudanseer ɗin yin murmushi ya saka hannu suka cigaba dacin tuwon, wanda a yanzu Sam Ahmad baya wani ci sosai saboda damuwar halin da ƴar uwarsa take ciki.