Gamon Jini Hausa Novel Complete

Gamon Jini Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

GAMON JINI

 

*NA FATIMA MOH’D GURIN*

*GUREENJO*

 

*E.W.F*

 

*PAID BOOK*

 

*FREE PAGE FOUR*

 

*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*

 

*****

 

Da sauri Amah ta mike tsaye tana cewa

“Barka da shigowa Hajiya Babba”

Tsaki ta ja tare da cewa

“Ba shi na tambayeki ba… waye ke da matsalar kwakwalwa nace ko Asma d’in ta fara dod’e miki kunne ne Uwar tuzuru?”

Dukansu kai suka dukar suna jin zafin zagin mahaifiyar tasu da ake yayinda shi Abrar gabad’aya ya sa a ranshi sbd shi ne ake iya ciwa Amah zarafi, Auren nan kam dole ne? Mukarrama ita ce macen da ya ta’ba so Allah be yi ya aureta ba ya ce ya kare so ya rufe baabin soyayya suna tunanin wasa yake?

Shi fa ba yaro bañe at his age of 42 yaci ace ya za’barwa kanshi abinda yake ganin shine daidai da rayuwarshi ya ma wuce ma…

My Little Sister Hausa Novel Complete

Yana ji Amah zata fara magana ya katseta

“Patient d’in khalid ce”

Harara ta banka mishi tare da jan tsaki, tace

“Dama Muhammad ne ya matsa min In zo In dubaki a cewarshi baki da Lafiya se kuma na zo na tadda kin saka d’ima d’iman yara a gaba kina basu abinci daga Katon Tuzuru se fand’ararre, kai kuma dena Kallo na da idanu kaman na mayu”

 

Ta dakawa Maher tsawa, da sauri ya dukar da kai, fita tayi tana mitar itakam Muhammad ya auro mata zuriyar mayu en anace gashi Saude bata da zuciya kwata kwata kaman ta yar kare ya lashe, duk abinda suke mata bata nuna ta damu sam…

 

Ajiye spoon d’in da be kai ga kaiwa bakinshi bane yayi yana shirin Mikewa Amah da kanta ke kasa tana juya chokali cikin abinci tace

“Lamido ina me umurtar ka da ka zauna ka ci abincin nan ka bani plate..”

 

Had’e rai yayi kaman be ta’ba Sanin me dariya ba ya fara cin abincin, duk zuciyarshi Amah Bata rene shi da rashin kunya ba, ta samu wani irin tarbiya daga iyayenta wadda ya iya lankwasa shi tun yana karami, ta san yadda take bi dashi sede In be yi motsi gabanta ba ta san abinda yake nufi, ita ce kawarshi tun daga randa ta fara fahimtar halinshi da Allah ya hallice shi da kayanshi…

 

Har suka gama cin abincin ba wadda ya sake magana, parlor suka dawo Amah ta umurci Maher ya zo da ruwa da kanta ta ‘ballo magungunan ta bashi a tsaye ya sha yana me duba time a wayarshi baya so d’aya ya mishi a gidan sam, sbd jin gidan yake kaman kurkuku, kofa ya nufa yana cewa Amah

“Se na dawo”

Be kai ga fita ba Tace

“Lamido…!”

Dakatawa yayi tare da juyowa, Mikewa tayi ta nufi d’akinta se yabi bayanta sanin magana ne take dashi, Khalid yace

“Aah za’ayi sirri uwa da d’a”

Abdulkadir yace

“Kai kam idan yayanmu na nan me kake nema ne da Amah… duk hankali da kulawarta na kanshi, ni tun Ina kishi har na gaji na kyale”

 

Sadiq ne dake ta kallon jabir dake ta ciccin magani yace

“Ya J, ya akayi ne naga kaman ranka a ‘bace ko Hajiya babba ce?”

Duk hankali suka mayar kanshi seda yayi tsaki akallah biyar kan yace

“Ni ce ban yi sa’ar mata ba ko haka duka matan suke ne?”

 

Aisha da suke wasa dashi sossai tace

“Kanwata ta sake laifi kenan Uncle J?”

Kaman yadda yaranta biyu ke kiranshi,

Ze yi magana Abdulkadir yace

“Shhhh… kayi mata nasiha karka kasance me fad’an sirrin gidan ka a ko da yaushe yawan korafi ma matsala ce, hajiya Maman Aslam(Aisha) an kasa kunne don aji gulma ba”

Dariya suka kwashe dashi, Ita kuwa ta fara cewa

“Kai kuwa me bamu sani ba Uncle A? Kaga gwara karka ‘Bata bakinka ni da Uncle J kaman 5&6 ne ko ka hanashi magana anan se naji”

Ruqayya matarshi ma ta saka baki akan ai Sumayya kam ko J be fad’a ba ita zata fad’i mutum cikinshi sam ba rike sirri, raha suka ci gaba dayi tsakaninsu… wadda wannan kaman farilla ne in an had’u ba Amah da Uncle Moh(Abrar) kaman yadda yaran kannen suke kiranshi, kaman zasu d’aga gida da hira da Tsokana…

 

“Amma Amah banga dalilin amincewarta kan Amatullah ta zauna gidan nan ba… Abbu da yafi chanchanta ya sani zaki iya sanar mishi kan a sállame ta shima d’in if he didn’t welcome her here se na sama mata wani wuri… ba shikenan ba?”

 

Kai ta gyad’a ta de San idan Hajiya babba tace ‘a’a’ babu yadda suka iya da Abbu ko yaya mahaifiyarshi ce, kallonshi tayi tace

“Lamido batun zaginka da ake da tuzuru, can’t you let anything Go and start again? Ka duba kaga Abdulkadir yaranshi 3, khalid yaranshi 2, matar Jabir kaninka na Uku da ciki, banda ma yaran Hajiya Yaya da suka fi d’akin nan tara jikoki… yanzu kai daad’i kake ji da zaman haka?”

 

Yadda yayi kasa sossai da kanshi ya kuma d’inke fuska ya so Bata dariya, be saba ci mata dry ba sam ganin tana murmushi se ya fuske yana Mikewa yace

“Amah zan je Asibiti”

“Hmm”

Tace kan ta d’aura da

“Allah ya tsare”

Fita yayi be kula su Abdulkadir ba, a kofar fita yaci karo da Nadra rike da basket ta ci kwalliya cikin wata Straight Gown na purple less ta kafa d’auri, ba karamin kyau tayi ba musamman yadda purple lipstick ke shining a lips d’inta da manyan idanunta da suka ji Kwallin asiri mad’au…

 

Tasbihi yayi a sadda kamshin turarenta da yaji yana son fin karfin kwakwalwarshi ya riske shi ba tare da ya kalleta ba ya nufi fita, gabanshi ta sha wadda hakan ya tilasta mishi kallonta bakinshi na cigaba da karatu cikin suratul baqara…

 

“Malama lafiya?”

Ya watsa mata tambayar yana me kallon cikin idanun ta, mamaki ne ya kamata tare da shakka da kwarjininshi, a sanyaye ta matsa sbd kaifin idanunshi yafi karfin hankalinta, ba tare da ya kara second ba ya fice ya barta sake da baki… a cewar bokanta sede idan Abrar be yi ido biyu da ita ba gashi for the first time kenan a rayuwarta da ta kalli tsakiyar kwayar idanunshi sede ko

Kusa ko alamu kwallin idanunta kaman be yi tasiri ba, bare kamshin turaren…

 

“Nadra ya kike tsaye karaso mana…”

Amah ta fad’a daga cikin parlorn wadda hakan ya katse mata hanzari daga lissafin da take na anya ba da gaske bañe da Hajiya Yaya tace tsafinsu ya ci uwar nasu..?

 

Karasawa tayi tana dukar da kai cike da kissa irin nata ta ce

“Amah Sannu ashe jikinki ya tashi wlh ban sani ba dake na je rano jiya na dawo da dare…”

Murmushi Amah tayi tace

“Da sauki Ai Nadra Allah dae ya sa lafiya tafiya Rano ba sallama..”

 

Fuskan tausayi tayi kaman zatayi kuka  tace

“Mama ce ba lafiya, amma taji sauki ma ba don Ina da test yau 4-6 ba da se Gobe zan dawo”

Adu’ar samun lafiya sukayi wa mahaifiyarta da ta kasance kanwa ga Hajiya yaya, ta amsa tana cewa su Abdulkadir Ina Kwana cikin jam’i, da lfy suka amsa mata…

 

Ta gama fi’ilinta da duk sun san ba don Allah bane harda d’auko plate wai Zata sawa Amah abincin da ta girka mata da kanta, sede amma ta mata nuni da dining akan yanzu suka sauko, bata ji daad’i ba har a fuskanta ya nuna Aiko ganin haka yasa Amah sa Aisha ta kai mata kitchen zata ci anjima… ta zauna a cikinsu kad’an dukda hiransu kawai suke ba tare da sun tanka ta ba… daga karshe ta fice cike da jin haushin rashin samun nasararta…

 

Allah kad’ai ya san wahalar da tasha a Rano jiya akan kwalli da turaren nan amma duk a banza… bazata saduda ba kaman yadda bazata hakura ba se taga tarwatsewar rayuwar Abrar.

 

Dafe kanshi da ya Sara yayi a kasalance ya d’ago ya zubawa Dr Alpha dake mishi bayanin ciwon Amatullah idanu, juya maganganun kawai yake, Nyctophobia, Anthropophobia and daga karshe ita d’in SS ce sickle cell patient…

 

Ganin yadda damuwa ya bayyana karara a fuskanshi yasa yace

“Ka kwantar da hankalinka zata samu sauki In Shaa Allah.. Nyctophobia Tsoron daré an fi samunsu wurin yara sede matasa ma ka iya kamuwa dashi musamman idan ya gamu da abinda yafi karfin tunani da kwakwalwa kuma cikin dare.. zata dinga samun wahalar bacci da dare kai ko tunanin duhu tayi zata firgice… wasu masu karamin kwakwalwa kam ma ko film na tsoro suka gani suna iya developing ciwon.. dole zata dinga samun wahalar had’iye abu, bushewar baki, jiri, harda amai da kuma ciwon kai…”

 

Saurarawa yayi yana kallon Abrar da idanunshi ke wani wurin kaman Baya sauraranshi jin Shiru ya sa ya juyo ya kalleshi yace

“Uhmm I’m listening”

Ajiyar zuciya ya sauke kan ya ci gaba…

“Shi kuma Anthropopobhia tsoron mutane, irin tsananin tsoro da anxiety, duk masu wannan ciwo suna tsoron shiga cikin jama’a Sannan suna tsoron idanu wato kallo bazasu jure ko wani kallo ba idan har ya zurfafa, Sannan suna samun attack a duk sadda a ka tuhume su da abinda basu aikata ba wato to be judge, duk abinda Nyctophobia yake causing haka wannan ma sede wannan harda tumor zata iya developing idan tana yawan samun attack, da kuma bugun zuciya…”

 

Yanzu kam idanun Abrar a lumshe Allah me girma yarinyar da bazata wuce 18 bane da waennan ciwuka.. me ya ta’bata haka, me ya faru a rayuwarta da ya firgitata haka? Jin shirun dr Alpha ya sa ya bud’e idanun da suka birkice ya watsa mishi yayi gyaran murya kan ya ce

“Wani irin taimako zaku iya Bata?”

 

Cike da mamakin Abrar yace

“Zamu d’aurata akan medications Sannan akwai therapist da zata ke gani, Ana exposing d’inta to people ku da kuke tare da ita ta samu 100% kwanciyar hankali daga gareku a kiyaye duk wani attack in shaa Allah zata samu sauki… kuma ku taimaka daga wurinku… yanzu ga wannan, Folic Acid ne da polygam shi kuma na sickler d’inta zata dinga sha kullum guda d’ai d’ai Sannan Please sanyi, tsananin zafi, yawan anfani da ruwa duk a kiyaye zata jima bata samu attack ba… in Shaa Allahu”

 

Kar’ba yayi tare da Mikewa ya mika mishi hannu sukayi musabaha da kyar ya lalu’bo “thanks” ya ce mishi kan yayi waje, da kallo Dr Alpha ya bishi yanzu duk wannan bayani da ya gama takarkarewa yayi da abinda ze bishi kenan? Ta’be baki yayi tare da d’age kafad’a…

 

*****

 

Sanye da Maroon shadda wadda ke ta Maiko da kyalli an mishi d’inkin bubu me d’uke da Adon bakin zare, dukda ta tasamma shekaru hamsin da hud’u amma se ka zaci ‘yar talatin ce, sbd yadda fatarta yake a murje da hutu, kud’i ya ‘boye shekarun nata, Amah kam ba de ado ba.. sarka da abin hannu dake hannunta ma kad’ai abin kallo ne, parlorn nata ba kowa duk sun watse bayan ruqayya ta gyare mata parlorn sanin yadda ta tsani kazanta kuma Hindu bata nan, wani corridor dake cikin parlorn nata ta nausa a karshenshi Akwai kofa tsararriya murd’awa tayi ta shige…

 

A tankamemen parlon Abbu ta fito wadda corridor d’in yayi linking d’inta da sashen Abbun kaman yadda na Hajiya Yaya ma haka, hakanan kuma na Aunty, mata ta uku ga Abbu hakan ya baiwa sashen Abbun wani shape da zaka d’auka sashukan hud’u a dunkule suke sun saka shi a tsakiya dukda ko wani sashe da asalin mashigarshi wadda ko kusa bakon wannan ba Lallai ya ga na wannan ba.

 

A zaune dattijon yake dukda ya tasamma sittin da wani abu sam a fuska ba zaka ce hakan ba, sbd Allah be yi su da saurin furfura ba daga kan kyakyawar gashin dake saman kanshi har zuwa sajenshi bak’i ne sid’ik ba furfura ko guda d’aya, sanye yake da glass fara da ya kara fito da kyaunshi da kuma zatinshi jarida ce hannunshi yana dubawa sede jin bud’e kofar yasa ya d’ago kallonta ya ci gaba dayi kyakyawar murmushi na wadatuwa a fuskanshi…

 

“‘Dawisu sarauniyar Ado.”

Ya furta yana ajiye jaridar tare da maida hankalinshi kachokan kanta, murmushi ta saki tana zama dab dashi tace

“Barka da wannan lokaci ranka ya dad’e”

Cikin muryarshi me cike da dattako yace

“Yauwa, ya jiki hope kin samu afuwa? Ban shigo ba a tunani na hutawa kike”

 

Sanin ba cika zuwa sashensu yayi ba idan ba mamallakiyar sashen na cikin hali na ciwo ba yasa tayi murmushi tace

“Alhamdulillah, tafe na ke da wata alfarma,ban sani ba ko ni da babana bamu kyauta ba..”

Dukda hankalinshi na a kanta hakan be hanashi sake tattare natsuwarshi ba yana sauraronta..

 

Tiryan tiryan ta mishi bayanin Amatullah da abinda ya wakana daga jiya zuwa yau, kan ta karasa ta lura da rashin walwalar fukarshi, a sanyaye ta gama zuciyarta na adu’a…

 

Baki ya bud’e da shirin magana suka ji muryar Hajiya Yaya

“Wasu tarukucen kuma za’a kwaso mana gida..? Mun san halinta da tarbiyarta? Wa ya sani ko Aiko ta akayi da mugun nufi cikin ahalinmu don baze shafe ku ku kad’ai ba har da mu Tsintacciyar mage de Bata mage ehe,don haka inda ya tsintota chan zai maidata ba nan ba kam”

Rashin walwalar fuskan shi ne ya karu ba tare da ya kalleta ba yace…

 

****

 

*Ko kin shirya mallakar Wad’annan TAURARI Guda biyu😉 Da Naira Dari biyar kachal zaki mallaki gawurtattun littatafan nan guda biyu…

 

*GAMON JINI Na Fatima Muhammad Gureen (Gureenjo)*

 

*Da Kuma*

 

*SABABI Na Amina Ibrahim (Oum Ameer)*

 

*Akan Naira D’ari uku kuma zaki mallaki Guda d’aya cikin biyun, karku manta mun shirya tsab domin Nishad’antar daku, fad’akar daku da kuma Nishad’antar da ku masoya, Mallaki naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali er uwa👌*

 

Zaku iya biya ta account number kamar haka

3118518476

First bank

Fatima Muhammad Gurin

Se a turo shedar biya ta wannan layin

09039206763

Note: Banda Recharge card.

 

 

 

 

Post a Comment

Previous Post Next Post