Beelal Book 2 Hausa Novel Complete

Beelal Book 2 Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BEELAL*

*BOOK 2*

 

NA

 

 

 

MAMAN AFRAH

 

 

*FCW*

 

 

Book 1 free

Book 2 paid 300

 

Ki biya ta asusun bankin Fa’iza Abubukar unity bank 0020281885 shaidar biya 09030283375

 

 

Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai yadda na fara lafiya Allah sa na gama cikin nasara

 

 

 

Free Page1️⃣➡️2️⃣

 

 

 

*LAGOS*

 

 

 

 

Kwana biyu suka yi a hanya suka sauka a garin Lagos, tun da suka sauka a garin Lagos a tasha, Idrisu ke tsangwamar Beelal saboda wai ba ya sauri kwata-kwata ba ya duba larurar da ke tare da yaron, ta nakasar, da ke tare da shi, haka kawai yake jan hannunsa ƙiii suna keta mutanen da ke cikin tashar motar da aka saukesu. Babu wani wanda ya lura da su kowa sabgar gabansa yake, Beelal kwa banda hawaye babu abin da ke zarya a fuskarsa ga wata azababbiyar yunwa da yake ji.Dan tun da suka taho bai ci wani abincin kirki ba, sai dai Idrisu ya sayi cincin ko fanke ya bashi kaɗan ya cinye sauran. Sai da ya samu machine suka hau, Beelal ɗin ne ya fara hawa sai shi ma ya hau bayansa haka suka zo unguwar da Idrisu ke zaune. A ƙofar wani shago da ke wurin aka ajiyesu ya fitar da kuɗin mai machine ɗin ya biya.

Meenah Ameen Hausa Novel Complete

” Kai gurgun mage ka ga inda nake kwana dan haka ba wai a kyauta nake zaune a ciki ba, biya nake dan komai da kake gani a Lagos na kuɗi ne ba kamar can gida bane inda muka baro fa, ka san a can ne wani ma zai iya bada kyautar shago dan kawai mutane su zauna a sadaka wasu har gida suna iya bawa mutane su zauna kyauta, dan haka sai ka zage dantse wajen neman na kai” Cewar Idrisu yana yiwa Beelal wani kallo.

 

“To Baba zan …

 

“Ko da wasa kar in ƙara jin ka kirani da wannan sunan dan ni tuni na daɗe da barwa uwarka Fatima kai, dan haka zamu zauna ne a nan a matsayin masu taimakon juna idan ka taimakawa kan ka ka nemo kuɗi, yadda ya kamata to zaka samu abinci idan kuma baka nemo ba to ka kwana da sanin da yunwa za kake zama”

 

Zubar hawayen Beelal sun riga yi buɗewar bakinsa , saboda ganin irin rayuwar da zai gudanar mai cike da uƙuba a birnin Lagos, an rabo shi da wajen mahaifiyarsa mai so da ƙaunarsa wacce duk runtsi duk wuya sai ta nemo masa abin da zai ci ko da a ce ita ɗin ba za ta samu ta ci ba, to ta gwammace ta samo masa idan ya ci sai ta yi farinciki. An kawo shi inda bai san kowa ba sai wanda ya kawo shi, shi kuma wanda ya kawo shin yana ƙyamatarsa ba ya ko ƙaunar ya kira shi da sunan mahaifi saboda nakasar da Allah ya halicce shi da ita.

 

“Za kake nemowar kuwa? Duk da wasu na cewa wai zafin nema baya kawo samu, to ni dai na ƙaryata haka, sai dai in mutum bai dage ba, dan da ya dage dole ya nemo, sannan ka bar zubo min da wannan hawayen munafurcin dan taimakon ka na yi kar kasa wasu su zargi sato ka na yi, to shin ma

in ba barar ba menene ya dace da mutum irinka, mai irin suffarka, mai ɗauke da nakasa kamar kai, ƙafa a lanƙwashe hannu a lanƙwashe, ai babu wani babban abin da ya dace da kai sai bara wato kake yawo kana faɗar SADAKA FISABILILLAHI” Ya faɗa yana hararar Beelal.

 

Hannu ya sanya ya goge hawayen da suka maida fuskarsa tamkar sun samu safa da marwa, hawayen da zubowarsu ya zama al’ada kuma farilla duk da ba wai kukan nasa ya tsaya bane, amma haka ya share hawayen nasa, kai kawai ya sunkuyar yana jin ba daɗi har cikin rai da zuciyarsa, dan baya so ake kiransa da nakasashshe duk da yana ɗauke da nakasa, ba ya son a kira shi da nakasashshe musamman in hakan ya kasance an faɗa masa dan a muzanta shi, a nuna masa shi ba kowan kowa bane saboda nakasar da ke tare da shi, duk da in aka masa hakan sosai yake muzanta, sosai yake jin babu daɗi a cikin ransa dan yana gani kamar mutane na ganin shi ya yi kansa a haka, suna manta cewar Allah ke halittar mutum a yadda ya so a kuma lokacin da ya so.

 

“Wuce mu je ai dai ka ji abin da na ce in kuma ka ƙi to jiki magayi, dan ni idan ma baka kula ka nemo kuɗi da abinci ba ko a jikina wai an tsikari kakkausa, dan kai ne zaka zauna da yunwa wataƙila ma ta yi sanadin barinka duniyar kowa ya huta” Cewar Idrisu yana yin gaba ya nufi shagon, cikin sanyin jiki Beelal ya bi bayansa tunanin mahaifiyarsa cike da zuciyarsa yana tuna irin tsantsar kulawarta garesa da nuna masa halittarsa da Allah ya yi a haka ba komai bane, ba kuma dan ba ya son sa bane sai dan a haka yake son ganinsa, kuma akwai wanda halittarsu ta fi tashi nakasa dan haka ya zama mai godiya ga ubangiji, wannan abubuwan da mahaifiyarsa ke nusar da shi game da nakasarsa shi ke sanya ya ji shi ma kamar kowa ne.

 

 

Dan duk abin da uwa take yiwa yaro yana nan zaune daram a ƙwaƙwalwarsa in ma mai kyau ko akasin haka, Allah ba mu ikon tarbiyantar da ƴaƴanmu kamar yadda ya ɗora mana nauyin hakan amin .Suna zuwa Idrisu ya tura ƙofar da take a kare.

 

“Wane ɗan iskan ne zai turo ƙofa babu neman izini” Aka faɗi hakan daga cikin shagon tare da ɗura wani zagi mai gunna.

 

“Kai dalla can ni ne, ka bi sannu kar ni ma ka harzuƙa ni yanzun nan mu hau sama mu faɗo” Shi ma Idrisun ya faɗa yana lailayo nasa ashar ɗin, tare da bankaɗe labulen shagon ya shige ko sallama babu.

 

“A ah shegen ashe kai ne” Cewar Imran da ke ringishe a kan katifa yana zuƙar sigari.

 

“Dallah can wai har ni kake yiwa wani eya ne” Cewar Idrisu yana miƙa wa Imran hannu ya bashi sigarin da yake zuƙa shi ma ya kai bakinsa sai da ya mata zuƙa biyu ya fesar sannan ya zauna a gefen katifar.

 

“Ai na ɗauka wani ne, da ban, zai kawo min raini”

 

“Kai dai ka sani, to ya ake ciki ne?”

 

“Kai dai bari Baaba wallahi al’amura duk sun caɓe babu wata hanyar samun kuɗi yanzu, ni machine ɗin ma da nake ja na mayarwa mai shi saboda sai in wuni ina yawo amma ba na samun fasinja wai sai a yi ta cewa a buge nake” Cewar Imran yana kallon Idrisu.

 

“Da gaskiyar su ai”

 

“Au haka ma za ka ce”

 

“To ai kai ɗin ne ya za a yi ka shayu ka yi tatul kuma ka ce wai za ka samu fasinja, tsakani da Allah waye zai yarda ya hau bayan bugagge wataƙila ma duk kana warin sholi”

 

“Dalla can rufe mana baki, ai duk kanwar dai ja ce daga ni har kai waye gwara, kai ma warin sholishon ai ko jikinka ba ya bari” Cewar Imran yana kai wa Idrisu wani uban duka a baya.

 

“Kai maida wuƙar Malam na zo mana da hanyar samun kuɗi yanzu cikin sauƙi, duk da dai dama ba wai ba ma sakun kuɗin ba kawai dai suna ƙarewa ne a wajen siyan kayan maye da neman matan banza, amma dai yanzu ga wata haja da nake ganin za mu buɗe…

 

“Kai rufa ni ka saya ni wallahi duk iskancina bai kai nan ba” Imran ya katse Idrisu yana wani harararsa.

 

“Kamar ya? Kai fa matsala gareka, ai ka bari na mutu ma kafin ka binne ni”

 

“Haba Idrisu daga tafiya gida wajen bushashshiyar matarka ko za ka samo mana kuɗaɗen da kake zato Yayarta ta kai mata, kuma kawai sai ka saro mana hodar iblis ka ce mu buɗe haja, son kulawa su yi ram da mu, azo ana A’i ina indo”

 

Wata irin dariya Idrisu ya ƙyalƙyale da ita, yana nuna Imran da yatsa.

 

“Ka fi kowa sanin ba na son rainin hankali” Cewar Imran cikin ɗaure fuska.

 

“Ai Baaba dole na yi dariya daga ambaton haja sai ka ce hodar iblis ce bari ka ga hajar da nake nufi, mai lasisi ce, kuma hajar mai jini ce” Cewar Idrisu yana buɗe murya ya shiga ƙwalawa Beelal kira, da ya daka ta a ƙofar shagon bai shiga ba amma yana jiyo duk surutan su.

 

“Kai gurgun mage, gurgun mage!!” Ya shiga ƙwala masa kira kamar wani makaho.

 

“Na’am” Cewar Beelal ya shiga share hawayen fuskarsa. Sannan ya ja ƙafarsa marar lafiyar ya tunkari cikin shagon gabansa na dukan tara-tara.

 

“Gurgun mage kuma waye ka samu haka ko shi ne ka baiwa ajiyar hajar tamu da kake ta faɗa” Cewar Imran yana son jin amsar sa daga wajen Idrisu.

 

“Assakamu alaikum” Cewar Beelal daga ƙofar shagon amma ko labulen bai ɗaga ba yana jiran sai ana amsa sallamar tasa an bashi izinin shiga sannan ya shiga, kamar yadda Mamarsa ta koya masa.

 

“Kai ba zaka shigo ba” Idrisu ya faɗa yana kwararo wani uban ashariya.

 

Labulen ya buɗe a hankali ya miƙa ƙafarsa cikin shago ransa cike da tsoro fal dan gabaɗaya ma sai ya ji yana matuƙar tsoron su.

 

 

“Kai dalla dakata a nan” Imran ya dakatar da Beelal cikin tsawa.

 

“Kai amma kai dai Allah wadaranka Idrisu, ya za ka kirawo mana almajiri bayan ka san mu kan mu muna da buƙatar abinci” Ya cigaba da faɗa tana yiwa Idrisu kallon tuhuma

 

“Kai dalla sakarai ni ne kake cewa Allah wadaraina, to sai dai Allah wadaranmu baki ɗaya saboda duk kanwar ja ce, to wannan da kake gani tun daga arewa na taho da shi kuma shi ne hajar da nake baka labari yanzu”

 

“Kana da hankali kwa Idrisu wannan abin ne haja? Ko dai ka samu taɓi ne bayan barinka garin nan”

 

 

“Na manta kan ka na kwakwa ne, gabaɗaya ya zama dusa ba ya ja ko kaɗan, kayan maye sun masa ƙawanya, to bari na maka gwari-gwari, wannan ɗan gidan wannan matar ne wacce take zaune da sunan wai tana aurena, shi ne yaron da nake baka labari ta haifa, to yadda ka ganshin nan a haka ta haifeshi shi yasa na sallama mata shi, duk da ma ba wai na san ɗawainiyarsa daga shi har ita bane, sai dai wannan zuwan na yi tunani zai mana mugun amfani a garin nan shi yasa ma na sato shi ba tare da ta sani ba na taho da shi”

 

“Ikon Allah na zaune ya faɗi, kai yanzu wannan in banda dai wahala mai ka ɗakko mana yaro hannu a ƙame ƙafa a shantale to ma uban me wannan zai mana” Imran ya faɗa yana aikawa Beelal da mugun kallo dan shi gabaɗaya ma kallo ɗaya ya yiwa yaron ya ji ya tsane shi, ganinsa ma yake kamar aljani.

 

“Maida wuƙar tukunna in faɗa maka manufata a taƙaice, daɗina da kai baka cin ribar zance, to wannan yaron na ɗakko shi ne dan yake bara yana samo mana abubuwan da muke buƙata, kama daga abinci kuɗi da dai sauransu” Idrisu ya faɗa yana wani murmushi tare da wani karkaɗa kai na jin daɗi.

 

“Shegen ina yinka nawan wallahi ai kai fa kan ka na ja ba kamar nawan ba amma in jika, gaskiya ka mana babban kamun da za mu daɗe muna mora tabbas wannan duk inda ya shiga zai samo sadaka, baka ma ganin yadda tsofaffi wanda ma basu da nakasa suke samo sadaka irin waɗan da ke zuwa neman kuɗi daga arewa da sunan bara, ka ga tsohuwa ta takarkare tana zabga waƙar bara ƴar jagora tana mata amshi kuma fa ita ba gurguwa ba, ba makauniya ba babu wani ɓangare na jikinta da yake a nakashe amma kuma sai ta maida hakan hanyar samun kuɗi, kuma wallahi sosai suke samun kuɗi, ka gansu idan suka tashi tafiya gida arewa sun koma da maƙudan kuɗin da ba lallai ne wanda suka zo nan ɗin da sunan neman kuɗi ba su samu ko da rabin hakan ne”

 

 

Imran ya kai ƙarshen maganar yana kallon Idrisu.

 

” Kai ai sai yanzu nake jin mugun daɗi da na taho da yaron nan, dan na san tsuntsunmu zai kama tarko”

 

“Sosai ma kuwa”

 

“Kai gurgun mage ƙaraso ka zo nan” Idrisu ya faɗa yana kallon Beelal da ya takure daga wajen ƙofa ya ƙi shigowa cikin shagon.

 

Haka ya janyo ƙafarsa ya ƙaraso wurinsu, ga ɗakin ban da warim sigari baka jin komai.

 

“Kai idan za ka saki jikinka ka saki jiki, dan nan fa shi ne garin da za ka cigaba da rayuwa a cikinsa, idan kuma ba haka ba za mu ladabtar da kai ta ƙarfi da yaji” Imran ya faɗa yana yiwa Beelal wani kallo na tsana da tsangwama.

Beelal dai kansa a sunkuye yana durƙushe a gabansu.

 

“Ka ɗago ka bamu amsa mu ba ma son wannan munfurcin sadda kan irin na uwaka” Idrisu ya faɗa cikin ɓacin rai.

 

“Zan yi Bab…

 

“Ba?” Cewar Idrisu yana kallon Beelal da mamaki, dan ya san dai ɗazun nan ya gargaɗesa a kan kiransa da suna Baba .

 

“Gaskiya da sake abokina ya ma za a yi wannan abin yake kiranka da Baba son ya ja ake kallon mu ai wannan abin kunya ne wallahi” Cewar Imran

 

“Ni ban san ya zan ke kiranka ba, ba zan iya faɗar sunanka ba” Cewar Beelal yana hawaye ganin duk sun tsare shi da ido.

 

“To haɗi garemu dan ka kirani da sunana ni fa na faɗa maka na janye dukkan alaƙa d dangantakar tsakani na da kai” Cewar Idrisu.

 

“Kawai yake ce maka Alhaji, ko da wani ya ji ya kiraka da hakan zai ɗauka taimakonsa yake kuma wannan suna ne mai ɗaga daraja kawai yake kiranka da haka” Imran ya faɗa yana kallon Idrisu.

 

“Amma na ji daɗi da ka samo min wannan suna to kuwa ba ni kaɗai zai ke faɗawa ba kai ma haka zai ke kiranka” Cewar Idrisu yana murmushi.

 

“Kai tanƙwashen kifi faɗi mu ji, dan yadda ƙafa da hannun nan naka suka sha kwana sai suka min kama da kifi tanƙwashe” Imran ya ce yana kallon Beelal.

 

“Alhaji” Cewar Beelal ƙwalla na taruwa a cikin idanunsa.

 

Hahahahaha gabaɗaya suka ƙyalƙyale da wata irin dariya kamar mahaukata sabon kamu.

 

 

 

Masu son Beelal buk 1 su min magana

MMN AFRAH 09030283375

Post a Comment

Previous Post Next Post