Bashin Zina Hausa Novel Complete
BASHIN ZINA
2023
By Meryermerh
Page1
*Gargaɗi:_* Banyarda a juyamin littafi tako wace irin siga ba, banyi dan cin fuska ko cin zarafi ba, wani ɓangare daga cikin labarin tarihin abinda ya faru ne wani bangaren kuma ƙirƙirarrene. Idan suna ko hali yazo ɗaya amin afuwa ba dagangan nayiba, idan anci karo da kuskure kuma a ciki za’a iya tuntuɓata kai tsaya dan yimin gyara. Allaah yasa mudace
*Matashiya*
Ubangiji Maɗaukakin sarki yana faɗa acikin ayoyinsa bayyanannu kaman haka:
*Bismillahirrahmanir*
Ka ce: “Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwanalfãsha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓõyu, da zunubi da rarraba jama’a, bã da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah.” ( Suratul A’araf: Aya 33)
Iyayenmu Hausa Novel Complete
Kuma Allah Yanã nufin Ya karɓi tũbarku. Kuma waɗanda suke bin sha’awõyi suna nufin ku karkata, karkata mai girma. (Suratu Bisani: Aya 27)
Akwai kuma hadisai da yawa da sukai nuni da illolin zina da muƙarrabanta, Allaah ya shiryemu baki ɗaya.
______Tafiya takeyi bayan tafito daga motar darkly tinted, tana tafiya tana kwalmaɗa sassan jikinta tamkar macijiya. Cikar halittar da Allaah yayimata duk tabaiyana yanda duk wani mai raunin imani da zarar ya kalleta zata tafi da tunaninsa. Gaba ɗaya mazajen dake jiran zuwanta dan su gwada sa’arsu sun ɗau wanka ko wannensu ɗauke da tsadaddun tufafi sun parka motocin su. Abin takaicin ba ga matasanba ba ga manyan Alhazzan da suka amsa sunan girma ba, wasunsu fa sun haifeta wasun su kuma ma sun kusan jika da ita, haka zalika wasunsu ma ƙannenta ne. Ƙa’idarta ce ba a tahowa wurinta se da nutsuwa dan ita a rayuwarta tana son mutane masu nutsuwa, kuma ƙa’idarta ce wanda ya riga zuwa gareta shi zaibita. Yau ɗin wani babban Alhaji ne ke da wannan sa’ar, kaman yanda ta saba haka yabita cikin hotel ɗin zuwa ɗakin da ta saba saukan baƙin nata. (Basma kenan ‘ya ga gawurtaccen Attajiri mutumin kirki Alhaji Ɗahiru Baban Marayu).
___Kaman yanda yasaba tunda ya biyota bai tsayaba har saida tai parking, akan idonsa duk abinda ya faru ya faru idanuwan sa na tsiyayar hawaye har tashige cikin hotel ɗin tare da Alhajin da yayi sa’an Uba a gareshi bama ita datake ƙanwar ƙanwarsaba. Gaba ɗaya yasaki jikinsa ya kwantar jikin kujerar da yake kai ta driver ya rintse idanuwan sa yana tsiyayar hawaye.
Ba ita ta koma gidaba till after 2:30AM, ba sai an faɗa ba kowa ya sani tabbas a wannan lokacin dare ya gama tsalawa. Gaba ɗaya ‘yan gidan kowa yayi bacci banda Ummu da Arfa, duka su biyun sun zuba uban tagumi suna jiran dawowarta.
Sai da ta tsaya a bakin ƙofar da zata sadata da babban falon dake entry na ɗakunan gidan ta share hawayen ta tas, ta ɗakko lip balm ta ƙara gare laɓɓanta ta goge fuskarta, takuma dake ta aro jarumta wadda ke nuna babu damuwa a tare da ita sannan ta sa ɗanyatsarta kan thumbprint ɗin dake jikin ƙofar, take ƙofar ta buɗe ta kutsa kai tashige ciki ta kama hanyar step. Bata ko kalli sites ɗin da su Ummun nata suke zaune ba ta haye upstairs zuwa bedroom ɗin ta. Tana shiga ta watsar da kayanta tashige toilet tana wanka tana tsiyayar hawayen da ta saba zubarwa, wanda ita kanta tasani inda zasu ƙare yaci ace sun ƙare. Saida tayi iya mai isarta sannan tafito ta sa sleeping dress ta kwanta bacci.
Su Ummu da Arfa kuwa tunda sukaga ta dawo lafiya kowaccen su ta tafi ɗakinta ta kwanta dan rintsawa.
Muhammad kuwa Kamar yanda yasaba haka yaita jiranta a cikin motar yana kallon entry ɗin hotel ɗin har qdwsanda tafito ta shiga motarta ta bata wuta babu ko tsoron dare. A take shima ya bawa tashi wuta yabi bayanta, har seda yaga shigar ta gida sannan shima yakama hanyar nasu gidan cike da tarin damuwa. Bathroom yashiga direct ya hau sakarwa da kansa ruwa, saida yaji ɗan dama_dama sannan yaɗauro alwala ya koma bedroom yaita gabatar da nafilfilu, har saida aka kira Assalatu sannan ya fita zuwa Masallaci. 6:30Am dai dai ya koma bedroom ɗin sa ya kwanta dan gabatar da ramuwar baccin da baisamu yayiba kaman yanda ya saba ya zame masa jiki.
Ko da gari ya waye kowa ya koma bacci bayan sallar asuba banda Basma da tashiga kitchen, tunda tai sallar asuba bata komaba sai kawai tagabatar da ‘yan addu’o’inta ta faɗa kitchen dan shirya musu abin kari. Wannan ya zame mata jiki tun asali bata bari kowa ya shiryawa iyalin nasu abin kari sabida muhimmanci sa a wajenta.
Gaba ɗaya cookers ɗin gidansu sun hallara a kitchen ɗin gwanin nishaɗi, suna aiyukansu cike da burgewa da girmama juna, kowanensu da farinciki a tattare dasu har cikin rai kaman yanda itama fuskarta ke ƙayace da murmushi mai nuna rashin girman kai, wasu na yanka wannan, wasu na wanke wancan wasu kuma na miƙa mata wancan. 7:00 dai dai suka jere komi a dining dake palon gidan gwanin sha’awa komi ya tsaru sannan Basma takoma sama zuwa ɗakinta dan rintsawa.
Ƙarfe 9:00 da ‘yan mintina ta sauko cikin shirinta da Maroon Abaya, a dining ta tarar da Ummu da ƙannenta su Arfa, Afra, Farha da Majid suna jiran ƙarasowarta. Tana isowa dukkanin su suka hau rungumeta suna farin cikin ganin farin cikin tasu, saida ta gaishe da Ummu sannan su ka karya a gaggauce sabida taɗan ja lokaci kuma bataso ta makara a aiki.
Kusan a tare suka shiga Companyn yau dan shima zuwansa kenan ya tsaya gaggaisawa da securities da sauran ma’aikata dake harabar Companyn motarta ta kutso kai, ko inda take baiso kallaba yau sabida baƙin cikin yanda abin daren jiya ya tsaya masa a rai amma haka zuciyarsa ta tilasta masa kallon sashin da take. Seda ya sauke ajiyar zuciya sabida yanda kwarjinin ta da cikar kamala da annurin dake fuskarta suka maƙale a idanunsa. Kaman yanda ta saba itama saida ta gaisar da kowa sannan tai wajen da yake dan shiga lifter zuwa ga office ɗin ta. Da Murmushin ta mai tsada shima tagaisheshi ya amsa a daƙile sabida yanda yasaba jin nauyinta in suna gab da gab.
Tofa! Kunji wannan salon kuma ko? Ya kukaji tafiyar? Mainene haka tattare da rayuwar waɗannan mutane? Kudai kucigaba da bina dan samun cigaban labarin.
Comment and share fisabilillaah🤍
_Meryermerh_✍🏻
[07/05, 4:42 pm] +218 92-2035171: *BASHIN ZINA*2023
By Meryermerh
*__Page2__________________________________________________________*
*Jan hankali* A kowane lokaci kaga mutum yana aikata alfahsha kamata yayi kayi masa addu’ar shiriya, zagin masu fama da irin wannan lalurar ƙara yawan ɓarna ne, kuma ɓarnan ba iya su take tsayawa ba har da ku masu zaginnasu dama waɗanda basa zagin. Idan mukai musu addu’a suka shiryu muma abin zai shafi tamu zuriar ne. Allaah yasa mudace.
*Abuja*
______Babban club ne da ya tara manyan ‘yan iska maza da mata. Babu abinda ke tashi aciki se sautin kiɗe_kiɗe da raye_raye. Gaba ɗaya ‘yan matan da mazan sun shawu iya shawuwa sunyi maƙil. Gogayya da cuɗanya a tsakanin su kuwa ba a magana, irin ɗabiar da ko mutumin banza bazaiso ace ga zuriyarsa na aikatawa ba bare mutumin kirki. Samir da ke gefe ‘yan mata sun kewaye shi kowaccensu na burin janye shi ko kuma tasamu ya haɗa da ita idan ya tashi ɗiban na tafiya ɗakinsa dan kwana. Shi kuwa hankalinsa gabaɗaya baya gare su, idanuwansa gaba ɗaya sun karkata kan masoyan nasa guda biyu da yafi jin daɗin mu’amala dasu fiye da kowa, kallo yake musu na ƙurilla kallon karsu yarda su bi kowa in bashiba. Safna duk da sun haɗa ido hakan bai hanata basarwa ba duk da tana shakkar sa amma kuma ai shima gashinan da ‘yan mata tako ina sun kewaye shi, dan haka itama ai dole yabarta ta bi wanda zata ɗan shana ta surkawa dashi.
Itakuwa haikima Samira ko a kolar rigar ta dan ko kallon inda yake batayiba bare ma tasan me yake yi. Maza da mata ne a kewaye da ita tana tiƙar rawarta iya son ranta babu kuma abinda ya dameta.
Misalin ƙarfe ɗaya Samira takama hanyar fita daga Club ɗin wani ƙaƙƙarfan saurayi ya cicciɓeta. Karaf a idon Samir wanda hakan yasa yayi zumbur ya miƙe da nufin bin bayansu amma ‘yan matan dake kewaye dashi suka hanashi hakan tahanyar cigaba da rarumarsa, daƙyar ya fisge yafice amma babu su Samira bare alamarsu. A zafafe ya koma ciki wurin Safna saidai itama babu ko ɗigon alamarta, da ƙarfi ya dunƙule hannu ya buga akan table ɗin dake kusa dashi, kwaleben da ke kan table ɗin ya hau rotsawa abinda yai sanadiyar yankewar hannunsa da glass ɗin kwaleben. Wata daga cikin ‘yan matansa ce ta taso ta rungumeshi tajashi zuwa motarsa inda drivern nasu ke jiran fitowar su suka kama hanyar gidansa.
Ba laifi Laila ta ɗan ɗebe masa kewa, amma hakan baisa buƙatarsa ta biyaba sabida shi sam a rayuwa babu inda yake gamsuwa se wajen Samira da Basma. Har ya bar Laila a wani ɗakin da nufin komawa wani dan ya gaji da jagwalgwala shi da take. Ji yayi kaman ana saka makulli a kofar falon abinda yasa ya leƙa. Safna ce ke ƙoƙarin shigowa gidan abinda yasashi sakin ajiyar zuciya sannan ya ƙara sa ya kamota suka kama hanyar ɗakin ta. Sosai itama ta sauke ajiyar zuciya dan har ga Allaah duk duniya tasani yayanta Samir yafi kowane namiji daɗi da iya kulawa da mace. Haka ya jata sukai cikin ɗaki suka cigaba da morar lokacin a faɗarsu.
___A new York kuwa Alhaji Tasiu Mai Leda ne ke zaune a ƙayataccen falonsa yana tunanin farin cikin idaniyansa uku da suka rage masa a duniya. Tabbas yasani a yanzu burinsa ya kusan cika tunda duka yaransa suna gab da kammala karatuttukan nasu. Se yaji kaman ya kirasu se kuma yayi tunanin dare da banbancin agogon su, kasancewar suna Morocco shikuma yana new York. Da haka dai ya daure da nufin gobe zaikirasu.
Suwane ne ‘ya’yan Alhaji Tasiu Mai Leda?
Samir babban su, da Samira mai binsa sai Safna ƙaramar su. Sun zaɓi yin karatu aƙasa ɗaya a faɗinsu shaƙuwar da sukai da juna barasu iya karatu a mabanbantan ƙasashe ba. Kasancewar bashi da farinciki sama dasu yasa yabi zaɓinsu yakaisu inda suke so. Abinda baisani ba shine yanzu haka da yake tunaninsu su suna ma Nigeria can garin Abuja suna sheƙe ayarsu.
*Kano*
Yau daren juma’a wato Alhamis da dare. Basma bata fita a duk irin wannan daren dan haka yanzu da agogon ɗakinta ke nuna 1:55Am tana durƙushe akan praying mat tana tsiyayar da hawaye, se ta ɗauki lokaci mai tsawo tana addu’a sannan tacigaba da Sallaah. Gwanin birgewa danaga yanda take gabatar da sallolinta dukda surorin da take kawowa basu wuce daga Nasi zuwa Sabbiba, ko a tulawar ƙurani danaga tana yi bata wuce iya nan a karatun nata saidai ta juyo ta sake maimaitawa. Kai idan kaga Basma a yanzu bazaka yarda itace wannan dake parka mota gaban hotel ba maza na raruma. Ko da naga wannan dare tare da Basma saida nayi mata addu’a na roƙa mata shiriya.
Ɓangaren Muhammad ma yau ranar farinciki ce a gareshi, duk irin wannan ranar yana kwanan farinciki dan yasan Basma bata zuwa wajen kowane gardi. Sosai ya raya daren da ibadah bayan sun gama hira da tilon ƙanwarsa abar ƙaunarsa kuma farin cikinsa Inaya.
Comment and share fisabilillaah