Akida Ta Hausa Novel Complete

Akida Ta Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

Akida Ta Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

TALLA! TALLA!! TALLA!!!

 

Ina masoya wanda suka bibiye ni a littafina na ABDUL JALAL, da kuma WATA KISSAR yanzu ma na shirya tsaf domin kawo muku wani ƙasaitaccen littafin me ɗauke da sabon salo da kuma sarƙaƙiya,

ga ɗanɗano daga cikin littafin

 

_*AƘIDATA*_

 

 

*PART1*

_Page 1_

 

*written and edited by*

 

_*AYSHERCOOL*

(Daddy’s girl)*_

 

The experience writer of

*ABDUL JALAL*

 

Bismillahir rahmanirrahim, da sunan Allah me Rahama me jin ƙai, Wannan littafi ƙirƙirarren labari ne banyi shi dan cin zarafi ko cin fuska ga wani ko wata ko wata ƙabila ba, idan har wani ko wata yaga wani abu daya yi kaman ceceniya da rayuwar sa ko ƙabilar sa Amin Afuwa banyi dan cin zarafin wani ko wata ba.

Wannan littafin mallaka tane, ban yadda a juyamin labari ta kowane fanni ba ba tare da izinina ba.

Wutarbuntu Hausa Novel Complete

What’s App : 07063065680

Facebook : real Humaira

Watpad : Ayshercool7724

Gmail : Www.ayshertadam@gmail.com

 

Katafaren ɗakin Bacci ne me ɗauke da kayan alatu na more Rayuwa da jin daɗi, idan ka ƙarewa ɗakin kallo zaka tabattar da ma’abocin wannan ɗakin Allah yayi masa Ni’imar Dukiya dan ya ƙawatu da dukkan wasu kayan more rayuwa, kallo ɗaya zakayiwa ɗakin kasan mamalakin ɗakin mace ce, saboda kan madubin dake ɗakin shaƙe yake da kayan kwalliya da gyaran jiki, ga wani show glass ɗauke da takalma da jakunkuna na adon mata kamar wani kantin saida kayan ado, kai da ganin takalma da jakunkunan nan kasan bana talaka bane, Makeken Gadon dake ɗakin ne ɗauke da wata kyakywar matashiyar budurwa ta baje gashin kanta tana bacci cikin nutsuwa.

 

Hasken ranar da ya ratso ta tagar ɗakin ne yake dukan fuskarta wanda hakan yasa ta motsa a hankali, ta buɗe idanuwanta.

Ɗan ya mutsa fuska tayi, ta miƙe zaune ta kalli Agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe tara da rabi na Safiya, a hankali ta zuro ƙafafuwanta ƙasa ta miƙe ta nufi banɗakin dake cikin ɗakin nata.

Aljannar Duniya shi kansa ba ɗaya nata ya isa a tsaya a kalla.

 

Wanka matashiyar tayi ta fito daga ita se towel, abun mamaki har an gyara mata inda ta tashi, ta zauna a gaban mudubi, ta shafa wannan ta goga wancan, gashi komai nata a hankali cikin nutsuwa take aiwatar dashi, riga da skirt na blouse ta ɗakko ta saka da ɗan guntun mayafi, ta ɗora akanta tasaka takalmin ta me matuƙar tsini da jakarsa, seda ta kalli agogon hannun ta ƙarfe goma da rabi dai dai sannaan ta buɗe ɗakin ta fito.

 

Wani irin taku take na ƙasaita, takalmin ta na bada sauti ƙwas, ƙwas, ta fito wani irin ƙaton falo ta zauna, ba ta daɗe da zama ba, me aiki ta kawo fruit gabanta ta ajiye, bata kalli inda fruits ɗin suke ba, se kallon tsintsyar hannun ta da ta ɗaurawa Agogo take yi.

 

“wato Isa rayuwar ƙauye akwai daɗi akwai wahala”

Wanda aka kira Isa yace

 

“Haba ɗan uwa wani irin daɗi a ƙauye? Kai ka taɓa ganin wanda yake birni ya koma ƙauye banda zunzurutun wahala mene ne a ƙauyen?”

 

“to ai Rayuwar ƙauye tafi ta birni kwanciyar hankali, ba tashin hankali ba fargaba, amma kaga birni a nan rashin gaskiya ya ƙare”

 

“tabdijan lallai ma sani, ai tunda Allah ya kawoni birni na samu aikin gadin nan, idan naje ƙauye to ziyara na kai Amma bani babu zaman ƙauye ina daf da dawo da iyalina nan ma”

 

“kai gidan nan zaka dawo da iyalin naka, kaifa kace min zaman fargaba kake a kowane lokaci za’a iya sallamar ka fa”

 

Isa yace “rufamin Asiri in kawo iyalina gidan nan Haya zan kama”

 

Suka ci gaba da hirar su tare da yin taɗi akan rayuwar birni da ta ƙauye

 

 

 

Sake kallon Agogon ta tayi har sha biyu saura minti goma sha biyar, miƙewa tayi cikin takunta na isa ta fito harabar gidan, kai tsaye ta nufi bakin gate, inda me gadi ke zaune yana hira da abokin sa sani suna cin gyaɗa.

 

Isa Yana hangota ya miƙe jiki na rawa yace “Allah ya temake ki, barka da fitowa” bata amsa masa ba tace

 

“har yanzu Sabo driver bezo bane?”

 

Cikin girmamawa yace “Eh ranki ya daɗe be ƙaraso ba”

 

Haɗe rai tayi ta jinjina kai ta koma cikin gidan

 

Sani yace “Isa ita kuma wannan wacece naga jikin ka se rawa yake dan tazo” sani ya tambaye shi

 

Isa yace

“kai bari kawai, itace ‘yar masu gida bata da wa, bata da ƙani shalelen Alhaji kenan, watan ta uku da dawowa daga ƙasashen Turai, yarinyar nan sam bata taɓuwa, gaba ɗaya halin turawa shi take yi, yau kam kashin sabo ya bushe wallahi ”

 

Sani yace “kamar ya kashin Sabo ya bushe meze faru?”

 

Be ƙarasa maganar ba aka fara bubbuga gate ɗin gidan, da sauri Isa yaje ya buɗe, wani mutum ne a ƙalla ze shekara Arba’in ya shigo kaman an koro shi.

 

Isa ya kalle shi yace “Taɓɗijan sabo yau kashin ka ya bushe, yanzu ta fito gurin nan neman ka”

 

Wanda aka kira da Sabo ya shiga rafka salati “na shiga uku yanzu ya zanyi, wallahi yarona ne babu lafiya na kaishi chemist”

 

Isa yace “ai bani za kayi wa bayani ba, seka je ka same ta”

 

Suna cikin maganar ta kuma fitowa, Fuskarta a haɗe babu annuri ta kalli sabo tace

 

“ƙarfe nawa nace maka zan fita?”

 

Jiki na rawa yace “ƙarfe sha ɗaya ranki ya daɗe”

 

“yanzu ƙarfe nawa ne?”

 

“shabiyu da minti goma”

 

“good, bani mukullayen motocina”

 

Sabo yace

“dan girman Allah kiyi hakuri ranki ya daɗe, wallahi yarona ne ba lafiya na kaishi chemist”

 

Cikin tsawa tace “shut up, did I ask you? Kabani keys ɗina”

 

Durƙusawa yake ƙoƙarin yi amma ta dakatar dashi “kai motocin na ubanka ne ko nawa?”

 

“naki ne Hajiya”

 

“idan har nawa ne, ka kawomin makullayena, na sallameka za’a bawa me gadi kuɗinka ya baka, daga yau se ya zama izina a gare ka, Alƙawari yana da mahimmanci cika shi alamace ta amana, lokacin aiki dana ɗauke ka mallakina ne ba mallakin ka ba tunda biyan ka nake, dan haka seda izinina za kayi duk wani abu komai girmansa in ba ibada ba tunda biyan ka nake”

tana gama maganar ta juya ta koma cikin gidan.

guri sabo ya nema ya zauna ya dafe kansa yana salati.

 

Isa yace “Sabo se dai haƙuri, Allah ya baka aikin da yafi wannan”

 

Cike da damuwa Sabo yace “Ameen Isa, Nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, idan ta bada sauran haƙƙin nawa nazo in karɓa”

Sukayi sallama Sabo ya fice daga cikin gidan zuciyar sa a cunkushe babu daɗi.

 

Bayan tafiyar Sabo,

 

Sani cikin damuwa yace “wai Bala in tambaye ka mana, ita bata da mafaɗi bata san dai dai ba, bata san Afuwa da uzuri ba?”

 

Bala yace “Taɓɗijan kai kasan su amma ita kam bata sansu ba, wannan da kake gani tana da wata irin muguwar AƘIDA da ta tashi akai saboda rayuwa da turawa, zuciyar ta kaman Arniya gaba ɗaya Aƙidun turawa ne da ita bana musulunci ba, babu wanda ze iya raɓarta su zauna lafiya, Akwai matar mahaifin ta dake gidan nan ita da ‘ya’yan ta, seta yi sati biyu seta ga dama za su ganta balle maganar fatar baki ta haɗa su, ta maida su tamkar bayin ta, idan kaga dariyar ta to da Mahaifin ta ne, da wani babban Aminin sa, ko wasu ƙalilan daga ƙawayen ta, bata da yadda sam, gani take duk wanda ya fiye raɓarta ba shi da gaskiya, Sabo shine driver na huɗu da tayi bayan dawowar ta Nigeria, ga Albashi me kyau ga mahaifinta da kyauta, amma kowanne ma’aikaci da ƙafarsa yake guduwa saboda izza da bala’in ta, ‘yan aiki kuwa koni na kawo shida daga garin mu amma da ƙafarsu suke guduwa, yanzu kalli duk haƙuri da ƙoƙari irin na Sabo kaga yau yadda ta wulaƙanta shi ta kore shi”

 

Sani ya sauke nannauyar Ajiyar zuciya yace “to ina mahaifiyar ta? Ya aka yi aka bari ta tashi da wannan AƘIDA wadda tayi hannun riga da Akidunmu na musulunci da kuma na Al’adar mu?”

 

Isa yace “Mahaifiyar ta ta rasu, shi kuwa mahaifin ta duk abunda tayi dai dai ne a gurin sa, yace ɓata mata rai tamkar zuba wuta ne a zuciyarsa”

 

Sani ya dinga juya maganganun Isa a ransa yana tunani, Sallama yayi wa Isa ya fito ya tura wheelbarrow ɗin mangwaronsa ya bar arear.

 

************************************

 

Wani matashine da baze gaza shekaru talatin ba zaune akan kujera ya tattara dukkan hankalin sa da tunanin sa akan allon na’ura me ƙwaƙwalwa dake kan teburin gaban sa ko ƙyafta ido ba yayi da alama wani abu ne me mahimmanci yake wa wannan kallon ƙurrilar.

 

Ƙwanƙwasa ƙofar ofishin da’aka yi ne yasa shi dawo wa hankalin sa a hankali yace “yes bismillah”

 

Turo ƙofar ofishin akayi aka shigo, wata matashiyar budurwa ce ta shigo jikin ta sanye da suit baƙaƙe da ɗan ƙaramin veil shima baƙi hatta takalmin ƙafarta baƙine, cikin taku na ɗaukar hankali ta ƙaraso gaban teburin sa tace

 

“barka da hutawa ranka ya daɗe”

 

Fuskarsa babu yabo ba fallasa yace “yawwa sannunki ya aka yi?”

 

Cikin iyayi da yauƙi tace

 

“dama Yallaɓai ne yace yana son ganinka a office dinsa”

Ɗan jinjina kai yayi yace

 

“Alright zanje Insha Allah”

Cikin sigar shagwaba tace

 

“can i offer you something to eat, naga yau kaman ba kaci komai ba?”

Girgiza kai yayi tare da faɗin

 

“No thank you”

 

“Amma Yallabai dan Allah Yusuf fa?”

 

Ba tare da ya ɗago ba yace mata “be shigo ba”

 

Haka ta fita ta bar office ɗin gwiwa a saɓule tana tunani “komai za’ayi ba’a taɓa birge gayen nan daga shi har Yusuf, gara ma wannan akan waccan me kama da saƙagon da magana ma se ya ga dama yake yi” tai maganar a fili da sigar mita

 

Ya tattara system din ya kashe, ya ɗauki wayarsa da mukullin motar sa, ya ɗora top ɗin kayansa a kafaɗa da jakar sa ya fito ya nufi wani ofishin.

 

Yana shiga dayan ofishin ya ƙame cikin girmamawa ya sarawa wanda ke office ɗin da alama shugaban sa ne, be zauna ba seda aka yi masa izini sannan ya zauna suka sake gaisawa.

 

Mutumin ya ɗago ya kalle shi yace

“Abbas kana ganin babu matsala a wannan aikin da’aka baka kasan hatsarin dake cikin aikin zaku iya kuwa? Kana ganin akwai wani cigaba akan case ɗin?”

 

Wanda aka kira da Abbas yai murmushi cikin girmamawa yace “karka ji komai ranka ya daɗe Insha Allah zan iya, zamu yi nasara, kuma ina fatan nasara Insha Allah yanzu idan na bar nan zanje in samu Yusuf

ne kasan shine jigon aikin”

 

“hakane to shikenan Allah ya tabbatar da Alkhairi ya baku sa’a na yadda da ƙwazon ku, Allah ya bada sa’a”

 

“Ameen yallabai muna godiya”.

 

**********************************

 

Zaune yake Ya barbaza takaddu da na’urori masu ƙwaƙwalwa har biyu akan gadon sa ya tattaɓa wannan ya taɓa waccan, kafin daga baya yayi zugum yana kallon hotunan wata tsaleliyar yarinya, yarinyar wadda zata yi kimanin shekaru goma sha takwas sanye take da farin gajeren wando, se wata ‘yar riga a jikin ta itama fara, ta saka farar hula hat ta baza gashin da ya kasa tantance nata ne ko na sawa ne, ga ƙaton baƙin tabarau a idonta ta buɗe fararen haƙoran ta tana dariya, bayan ta wani irin makeken ruwa ne shuɗi sosai, hannun ta na hagu riƙe da igiya da aka saƙalo wuyan wani jibgegen kare, jikinsa fal farin gashi ƙal, ba ƙaramin kyau yarinyar tayi a hoton ba. ko ƙwakwaran motsi ba yayi hotunan kawai yake dubawa kaman yana ƙoƙarin gano wani abu a jikin hotunan.

 

Wayarsa ce ta fara ruri, wanda ya sashi dawowa daga dongon nazarin da yake yi, ya duba wanda yake kiran wayar tasa yaga sunan Abbas akan Allon wayar tasa, yasa hannu ya kai wayar kunnen sa yace “Assalamu Alaikum warahmatullah”

 

Daga ɗaya bangaren aka amsa sallamar sannan wanda ya amsa din ya ɗora da cewa ” ina ƙofar ɗakin ka kana cikine in shigo? akwai labari da nazo maka dashi”

 

“eh ina ciki shigo kawai”

Kafin ya kashe wayar aka turo ƙofar akayi sallama a ɗakin nasa, tashi yayi zaune ya aje wayar yana faɗin

 

“kai tun shekaran jiya daka turomin hotunan wata yarinya bamu kuma haɗuwa ba, kuma ka kashe wayarka, gashi saboda aikin nan ko Office bana zuwa ina ta ƙara bincike, ina ka shiga haka?”

 

Abbas yace “ka bari in zauna se in maka bayani sarkin ƙorafi”

 

“to zauna maza ka koramin bayani, wani labari kake tafe dashi?”

 

Abbas Ya samu guri ya zauna ya ajiye jakarsa ya tattara hankalinsa kan Yusuf sannan yace

 

” Yusuf kaga hotunan yarinyar dana turo maka dasu ta email ɗinka?”

 

“Eh nagani, su nake ta nazari ban san dalilin da yasa ka turo su ba”

 

Abbas ya gyara zama yace ”

hotunan ‘yar gidan Alhaji Nasir Daula ce, kusan aikin mu gaba ɗaya akan ta yake, sati biyu kenan ina zuwa ina gidan su a matsayin me saida mangwaro da yankan farce, na samu karɓuwa a gurin megadin gidan su, hakan yasa idan naje se in zauna muyi ta hira da megadin su sannaan in tafi”

 

Yusuf ya gyara zama yace “to aini banga Alƙar binkicen mu da ita ba”

 

“Injiwa ai ta hanyar ta zamu samu duk abunda muke so, ita kaɗaice ‘yar Alhaji Nasiru, kuma itace target ɗin maƙiyan sa, aikin mu ba’ a akan iya bincike bane hadda bata Kariya”

 

Yusuf yace

“Abbas sanin kanka ne binciken nan na sirri ne, shi kansa Alhaji Nasir be san ana yin shi ba ta yaya zamu bawa ‘yarsa kariya”

 

Abbas yace “Yawwa ɗan gari bazata taɓa sanin Aikin da muke ba, yadda mahaifinta be sani ba itama baza ta sani ba, a hirar da muke dame gadin su yau watan ta uku da dawo wa daga America a can take Rayuwar ta, maman ta ta rasu a hannun step mum ɗin ta take, a tsawon lokacin nan mahaifinta ya sangar tata da kuɗi a taƙaice dai muguwar taɓararriya ce me wata irin AƘIDA ta kafiya da taurin kai ga mugun tsatstauran ra’ayi kamar baturiya, yarinya ce da bata da yadda tafi bawa mage da kare mahimmanci fiye da mutanen dake kusa da ita, bata san zafin talauci ba balle tayi wa wani talaka uzuri ko ɗaga ƙafa hasali ma gani take kaman talakawa bayin sune masu kuɗi bata ɗaga ƙafa ko sassauta wa na ƙasan ta san…..

 

“kaga dakata wannan dogon labari haka, kamin bayani a taƙaice” Yusuf ya katse shi

 

Abbas yace “Dadina da kai ƙosawa, hotunan dana turo maka hotunan tane”

 

Yusuf yace “to me zanyi dasu?”

 

Abbas yace “Yawwa anzo gurin, da dawowar ta a wata ukun nan direbobi biyar aka sallama saboda baza su iya jure halin ta ba, tana da gadara da wulaƙanci, a gabana tayi wa direban ta korara wulakanci jiya, Yanzu haka megadin ya bani labarin mahaifinta yasa shi ya samo mata wani direban daze dinga kaita unguwa, yake gayamin ya gaji da samo mutane tana wulaƙanta su, akwai Albashi me kyau amma halin ta da AƘIDAR TA kesa mutum ya gudu da kansa, dan haka nace ni ya barni zan samo mata direba, kuma kai nake so ka zama direban nata!!”

 

Wani mugun kallo Yusuf yayi wa Abbas

“Ashe baka da hankali, kaime ya hana kaje ka zama direban nata?, ni zanje in dinga tuƙa ƙaramar yarinya tana wulaƙanta ni akan me? Bazan yi ba gaskiya, ai kaine gaba dani a gurin Aikin kai kaje mana”

 

Cikin sigar rarrashi Abbas yace

 

“Calm down brother, nasan zaka iyane kai ƙarshe ne gurin haƙuri, kaga ni bani da haƙuri zan iya lakaɗa mata duka idan tayi min ba daɗi ƙarshe in ƙare a prison in shiga uku, kaikuma kowa ya san ka akan haƙuri da hikima, dan haka zaka iya, ɗazu mukayi magana da Yallaɓai na tabattar masa zamu iya aikin nan, ita kanta yarinyar a cikin gagarumin hatsari take, akwai bukatar a bata kariya da kulawa ”

 

Ɗan tsaki Yusuf yayi yace” gaskiya ni bana son wulakanci ne, yarinya ƙarama ta wulaƙanta ni dan ni talaka ne, gaskiya ni ka gama dani daka haɗani da wannan aikin, daka barni da kayan computers ɗina da damuwar da nake ciki da se yafi min”

 

Abbas ya kuma gyara zama yace “cigaban mu ne idan mukayi nasara dan Allah ka daure, Sannan Yusuf lokaci yayi da zaka cire damuwa ka fuskanci Rayuwa ka manta da ƙalubale ka gina Rayuwar ka”

 

Cikin takaici Yusuf yace

“Abbas kenan kana yiwa matsala ta kallon ƙaramar matsala, amma Allah shi ka ɗai yasan zugi da Raɗaɗin da nake ji a raina idan na tuna ni wane ne, wace Rayuwa zan gina bayan bani da dirakun da zasu riƙe min ginin Rayuwar tawa? Abunda ya faru dani yasa naji komai yafi ta daga raina, yanzu na barwa Allah al’amura na, in riƙe mahallici na, in rungumi ummana da Aikina nasan bani da kamarsu”

 

Abbas ya dafa kafaɗar Yusuf yace “Yusuf nasara bata samuwa ba tare da an jarabci ɗan adam ba, kayi haƙuri da taka ƙaddarar, Allah yana sane da kai”

 

Yusuf yace “Hakane Allah yabani ikon cin jarrabawa”

 

Abbas ya amsa da Ameen, sannan ya ɗora da cewa

“Aiki na gaba se bayan ka zama direban ta sannan zan sanar da kai shiri na gaba, zan gaya maka aikin da’a ke so kayi”

 

Yusuf yace “to Allah ya bani iko ya tabattar da alkhairi ya bamu nasara”

 

“Ameen ya Allah, ɗazu fa mutuniyar ka tazo office ɗina tana ta kwarkwasa, take tambaya ta kana ina?”

 

Yusuf yace “wa kenan?”

 

“kafini sani ai, wacece in ba Sakina ba”

 

Tsaki Yusuf yayi yace “dan Allah Abbas ka dena sa kamin wannan yarinyar cikin lamurana, ni tun abunda ya faru dani duk wata harka da mata gudun ta nake yi, wannan aikin ma da kuka bani kaida yallaɓai dan ba yadda zanyi ne harka ce ta aiki, balle wata Sakina, ni ina tsoron mata nafi ƙaunar tsira da mutunci na da kuma tsayawa matsayin da Allah ya ajiye ni, nayi darasi akan abunda ya faru dani”

 

Abbas yace “hakane kana da gaskiya Yusuf, Amma ka sani idan har mukayi nasara a Aikin nan cigabanka ne, sekafi kowa benefitting gaba kaɗan in aikin ya kankama zan ƙara sanar da kai wasu abubuwan”

Abbas ya ci gaba da kwantarwa da yusuf hankali tare da lallaɓa shi har ya ƙara gamsuwa ya Amince Amince akan zasu je gidan Alhaji Nasiru Daula da weekends domin a tantance shi in ze iya zama direban Wannan yarinya me muguwar AƘIDA sannan a gabatar da Yusuf a matsayin Sabon direban wannan ‘yar Hamshaƙin Attajiri Me murɗaɗiyar AƘIDA!!!.

 

Tun bayan da Abbas ya tafi, Yusuf yake ta tunani akan wannan gagarumin Aiki, yana ƙara duba kyawawan hotunan wannan yarinyar da ko sunan ta be sani ba, she has an innocent face a hoto, gata very young and beautiful amma ya akayi take da halaye marasa kyau haka?

Idan har ya kasance da gaske tana da duk wannan halaye da’aka faɗa masa anya ze iya aikin kuwa?

Amma meyasa Abbas be warware masa yadda aikin yake ba gaba ɗaya yace se ya fara yi wa yarinyar aiki ze gaya masa?

“Allah yasa ba cikin wata cakwakiyar zasu jefa ni ba” yai maganar a fili tare da miƙewa ya tattare kayan da ya baza a kan Katifar sa ya fito daga ɗakin nasa.

Kasancewar Yamma ce bashi da gurin zuwa da yake shi bame yawan shiga sabgar mutane bane, ya shiga ɗakin Umman sa ya ɗakko kayan wankin ta ya wanke tsaf, ya share ko ina, ya ɗora girki se kace mace, cikin nutsuwa yake Al’amuran sa ya kammala dafa shinkafa da miya ya zuba a flask, lokacin ana ta kiraye kirayen sallar magariba yayi Alwala ya fice Masallaci.

 

 

Ayshercool

07063065680

Post a Comment

Previous Post Next Post