Mar’Adams Hausa Novel Complete
MAR’ADAMS
*PAID BOOK*
Free page 1
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert domin tabbatar da an tura ko wannnan 09136918331 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
…….” Katanfarin company ne da tsayawa fadar iyakarsa bata lokacin ne domin mutun bai Isa ya fadi adadin girmansa ba , hatta shi Karan kanshi mamallakin company bazai ce ga iya adadin girmansa ba adalilin kullum sake siyan wasu bangaren yake yana hadewa da company .
Abin Da Ciwo Hausa Novel Complete
“mutane kimanin million biyu da wani abu ne ke aiki a karkashin wannan maikatar daake sarrafa karafuna sanye da kayan aiki .”
mamallakin wannan company ya mallaki companies masu yawa sai dai akwai guda daya wanda ya kasance hadin gwiwa ne tun mahaifinsa na raye suke kula dashi tare da ya’yan ‘yanuwa .”haka ma bayan babu ran mahaifinsa bai wuftar da al’amarin wannan company ba ya cigaba da kula dashi saboda yana matukar qaunar company a cikin zuciyarsa dan ba qaramin wahala mahaifinsa ya sha akansa ba kafin ya samu daukaka da kar’buwa a duniya gabadaya ba .”
A.G.C”wato Abdullahi group’s company,company ne daya amsa sunansa, company né da suke da duk wani nau’in kayan sakawa ajiki ,kama daga na sarakuna ,manya attajirai ,shuwagabanin na duniya , kayanmu na gargajiya har ma dana turawa wato suit da kowani irin design’s na tsarkoki ,daga ko wacce kasa ka bukaci kayansu zaka samu cikin sauki sannan kuma suna zana duk irin design’s din kaya da tsarkokin da kake so har ma da zanen kanfanunnuka ,zanen hotuna kai duk wani nau’in na zane suna da kwararun masu zanawa wuyarta ka zaba desing’s zasu yi maka .”
daya daga cikin maaikatan gurin ya dago yana kallon shugaban da aka d’aurawa halakin kula da ma’aikatar karafuna wanda isowarsa kenan “barka yallabai “barka dai malam mashkur fatan komai dai yana tafiya kamar yadda aka tsara ? dan sam bana son a samu wata matsala sannan bana son a samu sa’banin akan karafen can ka tabbatar an cigaba da samun irin wadan can, sannan wadan can kayan Ina son akawo su da wuri dan mai gida zai …. “bai kai ga karasa maganarsa ba sautin qarar jet din mai gidansa ya katseshi hakan yasa a hankali manager malik ya d’aga idanunshi dake manne da bakin glass zuwa sararin samaniyya cikin sauri yace “shikenan kaje ka cigaba da kula da duk masu aiki ga mai gida nan ya iso .”
ADAM TARIQ ABDULLAH kenan, shugaban kafanunnunka ATA companies …… matashin dan kasuwan da yafi kowani dan kasuwan bahaushe kudi a Duniya kallo daya zaka masa ka fahimci matakin shekarunsa, bazaka kirashi da yaro ba haka zalika bazaka kirashi da dattijo ba shi din matashi ne me kimanin shekaru talatin da bakwai a duniya fuskar shi babu yabo babu fallasa kasancewar haka yanayinsa yake, kullum haka zaka ganshi fuskar nan tashi a hade tamkar hadari sai dai na wannan lokacin ya zarta na sauran lokutan baya wanda hakan ya faru ne akan abinda ke dawainiyya da rayuwarsa.”
.Adam Tariq abdullahi wanda ake kira da (mr ATA) a duk fadin duniya kyakkyawa ne ajin farko mai tsantsar kamala da kamewa tattare da haiba sai dai sam bai da faraa komai cikin zafin rai da zuciya yake aiwatar wa , ” rayuwarsa rayuwa ce dake da bambamci data sauran mutane , shi din mutun ne miskili mara saukin Kai dan idan kayi Kuskuren shiga track dinsa zaka gane baka da wayo dan ya iya duk wani nau’i na tozarci da rashin mutunci tare da disga mutun sabanin mahaifinsa da mahaifiyarsa da sauran yanuwnasa da suka kasance masu tsanani saukin kai tausayin mutane tare da tallafawa bayi mabukata ,fari ne sol dan babu digo tabo ko daya ajikinsa hatta bakin kwayar idanunshi gauraye yake da fari ,dogo ne sosai mai matsakaicin jiki , da kyakkyawar fuska da idanuwa , fatar jikinsa na ya’yan masu kudi sai sheiki yake daga samansa har kasansa babu makusa sannan babu alamun babu a tattare dashi yana da matakin karatu na Phd akan kasuwanci kuma har lokacin yana kan karatu bai ajiye ba ,shine ya tattara gabadaya kyawun mahaifiyarsa hajiya zulaiheart da mahaifinsa marigayi barrister Kuma shararen dan kasuwa Alhaji Tariq Abdullah .”
“duk wani ma’aikacin dake aiki agurin tsayawa yayi cak ya kasa cigaba da aikinsa kamar yadda aka umarcesa saboda kwadayin ganin wannan kyakkyawar fuska har sanda jirginsa mai saukar ungulu ya sauka idanunsu na kanshi , sai da jirgin yayi kamar minti biyu da tsayawa sannan a hankali kofar jirgin ya bude Inda ya matso a hankali shi bai fito daga cikin jirgin ba haka zalika shi bai zauna sosai ba yana kada kafarsa daya cikin nuna Isa da izzar shi din wani ne .a zahirin ake iya ganin gangar jikinsa wanda hakan yasa kayan dake sanye dashi suka bayyana, Suit ne wando da riga ruwan madara yayinda yar cikinsa ya sakance baki kafafunsa sanye da black shoe’s haka idanunshi na manne da farin glass yana qarewa haraban gurin kallo tare da kallon ma’aikatan dake aiki .”
a natse ya fito hannunsa daya na cikin aljihun wandonsa yana taku daya bayan daya cikin Isa da izza yayinda escort dinsa ke gefen hagu da damansa kowannensu sanye da suit iri daya da makaman tsaronsa wato bindigu .”daya daga cikin escort dinsa na rike da wata karamar brief case kalar suit din jikin Mr ATA .” manager malik ya karaso da sauri cike da ladabi ya tsaya a gabansa “ranka shi dade mr ATA barka da zuwa? shiru ne ya biyo baya na kamar second biyar sannan a hankali ya motsa labbansa da kyar “barka m . malik ya kokari ?.” alhamdulillah sir ” m.malik ya fada yana mika masa hannu Mr ATA ya mika masa dayan hannunsa dake waje yayinda har lokacin dayan hannunsa ke cikin aljihun wandonsa ” gaskiya naji dadin yadda na iske kamfani kowa na kan aiki Wanda nasan duk cikin kokarinka ne dan ga dukkanin alamun aiki na tafiya yadda ya kamata ya karasa maganar yana zare hannunsa cikin na malik ya tsotsa bayan keyarsa sannan ya cigaba da magana yana tafiya a natse “kana yin yadda ya dace daman ba daidai bane tsuntsu ya cinye tsaba batare da yayi aiki ba “ai yallabai dole ayi aiki yadda ya kamata dan kai din na dabam ne sannan bakayi abinda tsuntsun zai cinye tsaba batare da yayi mata aiki ba “ka ajiye wannan maganar na gama daita yanzu, ma cigaba daga baya ” m.malik ya gyada masa Kai alamun yaji cike da ladabi yace “sir mu karasa zuwa office mana ? runtse idanunshi yayi kawai batare da yayi kokarin aikata hakan ba .”
bayan kamar mintuna talatin ya numfasa “Petir da sinadarin gas tsawon shekara bakwai kenan nayi Ina nema a wani yakin a cikin apapa ban samu ba sai gashi kwatsam na sameshi bayan na kashe billiyoyin kudade , sai dai ka taki sa’a dan Kai na zaba a matsayin wanda zai kular min da gurin …”
duk wannan maganar da yake har lokacin bai zauna ba tafiya yake ahankali a haraban ma’aikatar “Kai amman gaskiya naji matukar dadi ranka shi dade sai dai da za’a barni anan na cigaba da kula da bangaren karafai zai fi min , dan ba lallai ka samu Wanda zai kular maka da gurin nan yadda ya kamata ba .”
“karka damu m. malik already y ma nazo da wanda zai cigaba da kulawa da nan din ,adaidai karshen wannan maganar tasa ya samu guri ya zauna akan wata hadaddiyar kujera mai runfa zagaye da kujeru na alfarma dama Kuma duk sanda bai ra’ayin shiga office dinsa ba idan yazo anan yake zama ya d’aura hannunsa daya akan table , Shima m. malik ya samu guri ya zauna yana fuskantar me gidansa da sauraronsa “na zabeka ne saboda baka da wasa akan aikinka gashi kana da rikon amana da mazantakan kula da komai fatana ka cigaba a yadda na sanka .”
Ya Kai hannunsa na hagu bangaren hagunsa , nan take escort dinsa me rike da brief case ya daura brief case din hannunsa akan table ya bude ya ciro wasu manyan freme mai dauke da zane day day har guda goma Kuma duk abu daya ne zane acikinsu .
Mr ATA ya dauka ya tsurawa zanen lumtsamtsun Idanunsa masu fitar da zaiban haske tsabar hasken dake cikinsu, second biyar ya dauka yana kallon zanen sannan ya numfasa ya ajiye akan tablet din gabansa yana cigaba da kallo “ko ka samota m. malik ? ko samun labarin wanda ya santa ? “Ina har yanzu dai tukun nan yallabai amman Ina iyakar kokarina kuma zan cigaba wai shin wa….”babu ruwanka da wannan hurumin m.malik dan …..” qarar daya daga cikin wayoyinsa ne ya katse shi yayi shiru batare daya ci gaba da magana ba yana jiran a miko masa wayar escort din dake rike da wayoyinsa ne ya miko masa “my sweetheart ” .ya fada tare da rusunawa mr ATA .
da sauri mr ATA ya amshi wayar a hannunsa ya manna a kunnenshi ya mike tsaye cikin tsananin tashin hankali da girmamawa ya fara tafiya yana magana a natse “inna lillahi dan girman Allah sweetheart ki qara hakuri dani , ki Kara bani lokaci zan yi qokari ,okay I know nasan kin yi hakuri dani amman Ina da tabbacin wata rana zakiyi farinciki sosai, ina kan neman matar da zan aura ni dai ki tayani da addua murmushin gefen baki ne ya bayyana akan fuskarsa adalilin uzurin da tayi masa nan take ya samun natsuwar zuciya ya cigaba da abinda yake .”
*******
LAGOS
Da misalin karfe biyar na yammacin ranar laraba “Yammata ne su hud’u zaune a cikin wata hadaddiyar mota kirar land cruiser prador ,mutun biyu zaune a gidan bayan ,yayinda biyu ke zaune a gaba akan titi masha dake surelere , humaira dake kusa da mubina ta Ciro wayarta iPhone 12 Pro max acikin jakarta ta soma d’aukarsu snap tana ta’ba kafad’ar mubina dake driving dan ta shigo cikinsu ,mubina tayi murmushi ta dan shigar da fuskarta tare da d’aga yatsunta biyu kana ta maida hankalinta kan tuki .”
tafiyar mintuna ce ta kawosu Apapa gra suka tsaya a gaban wani makeken get da aka rubuta ABDULLAHI ESTATE tare da yin hon ,daya daga cikin masu gadin estate din ya leko adaidai lokacin da mubina tayi kasa da glass din motar ganin yaran estate din ne ya koma da sauri ya bude .mubina ta danna hancin motarta ta shiga Katafaren estate din nansu mai d’auke da gidaje fiye da ashirin sama da kasa sai dai acikin gidajen akwai guda daya wanda ya bambamta dana saura wato gidan hjy zulaiheart .”
yanayin gidanta ya bambamta dana saura ne sakamakon marigayin mijinta yafi sauran yanuwansa tarin dukiya kuma ko bayan mutuwarsa yaranta sun cigaba da qawata mata gidanta kullum cikin gyara yake da canza kayan ado na zamani , ‘yan aiki ma sun bambamta dana saura ,yan aiki guda goma sha biyar ne ke zariyar kula da kowoni bangare na gidanta ,sannan kowannensu sanye da fararen kaya masu ratsin baki .
babu mutun ko daya na cikin ahlin estate din dake tsaye akan kafafunsa domin yin aiki sai dai dan aiwatar da ibada , kowa acikin gidan dan gata ne hatta bakin dake zuwa gidan jin kansu suke tamkar ya’yan wasu saboda mutuntaka na mutanen gida, tsarin gidan hjy zulaiheart kuwa kace a gidan turawa ne kowani bangare shirye yaki da kayan alatun na more rayuwar duniya ,haka ma kofar da zata shigar da mutun bangaren hjy zulaiheart tsare yake da securities guda biyu masu duba jikin mutane koda zaa shigo da wani abun cutarwa .
mubina ta dauki hanyar inda aka tanada domin paka motocin bangaren gidan hjy zulai nan take sauran yanuwanta kuma kawayenta suka hada baki gurin cewa “ya haka kuma ?”Sai data dan marairace fuska sannan tace “dan allah mun dan shiga muga su marsi kwana biyu bamuga juna ba daga nan ma sai mu tsaya muyi sallar magrib da ishai sai kowace ta kama gabanta dake duk suna shiri da juna yasa babu wacce tayi mata mutsu har tayi parking tare suka firfito daga cikin motar suka nufi hanyar gidan hjy zulaiheart ,babu wacce ta jira ayi checking din jikinta ko mata iso shiga ciki kasancewar nan din ma gida ne a wurinsu tunda bangaren danuwan mahaifansu ne .
sallamarsu maryam da nana hauwa’u suka ji suka mike cike da farinciki suka rungume juna suna wa juna barka da zuwa sannan suka zube akan royal chair’s suna tambayar hajiya zulaiheart “mami tana ciki tana amsa waya maryam ta basu amsa zamansu ko cikakken minti biyar basu yi ba sai ga mutun uku cikin masu aikin gidan kowacce sanye da farin kaya da ratsin baki hannunsu rike da tire , tiren na farko lemu da ruwa ne ,sauran biyu din kuwa duk kayan motsa baki danginsu snacks da dambu naman rago , suka gaishesu cike da girma mawa ,suna gama ajiyewa baki abin motsa baki suka Kara gaba suka koma bakin aikinsu ..”
“Daga ina haka dan naga alamun kamar fita kukayi ?
“eh ! fita mukai muje birthday din wata abokiyarmu da muka qare karatu tare ne , dawowar mu kenan nace mu shigo kwana biyu bamu ga juna ba inji cewar mubina “ai kuwa mun gode muma kuna ranmu ,wallahi kullum sai nayi maganarku inji cewar maryam , nuzla taí saurin cewa “babu wani maganrmu da Kikeyi ga baki ga hanci amman zuwa ya gagreku kullum kuna gida kunshe kuna faman posting a social media .”
“wannan kuma da sister kike ba dani ba nana hauwa’u ta fada tana murmushi tana kallon maryam , maryam ta kai mata duka ta kauce da sauri tana sake murmushi tana cewa “ai sister daana daura kashi to wallahi data daura nata nifa idan tanayin wani abu har takaici take bani ahankali suke hirar yaushe gamo duk da suna cikin wuri daya amman sukan dauki lokaci basu hadu ba kowa yana nashi wuri .”
Suna cikin hira idanun mubina ya sauka akan tangamemen hoton mr ATA dake manne da bangon falon yana sanye cikin suit bakake fuskar nan tashi kmr Koda yaushe babu faraa amman hakan bai hana kyawunsa fitowa ba .” ta d’auki sama da mintuna talatin tana kallonsa Yayinda sauran yan’uwanta suka cigaba da hirarsu, murmushi ne ya subuce akan fuskar mubina wanda bata san sanda tayisa ba , nana hauwa’u ta Kai hannu ta dafa kafadanta tana cewa “ya’akayi mubina kika tsare mana yaya da Ido ko dai ko dai ? a matukar firgice wacce aka kira da mubina ta waigo ta sauke idanunta akan nana hauwa’u tana sakar mata murmushi tare da sauke ajiyar zuciya “wallahi kamar kin sani yar’uwata tunda na taso babu abinda nake so kamar ya adam “inna lillahi kice dai saboda kiga hotonsa yasa kika matsa lallai sai mun fara shigowa nan?inji cewar diyana “kuyi hakuri wallahi yana cikin dalilin saboda na kwana biyu bangansa ba ko wulgarwasa fa ina jin ma kamar baya kasar ko ….”?
wannan furucin da tayi yasa gbdy yan’uwanta suka maida hankalinsu kanta cike da tausayawa , nana hauwa’u ta dinga kallonta cike da matsanacin mamaki dan tasan mubina da tsatsanin kunya uwa Uba aji dan ta sha ganin yadda takewa samari wulakanci, samari ma yayan masu arziki amman bata da lokacinsu “wallahi nana hauwa’u da gaske Ina son ya adam so Kuma me tsanani da Ina da tabbacin zai aureni da zan ajiye komai na furta masa Ina son shi saboda son da nake masa bana wasa bane, maryam dake zaune kusa da nana hauwa’u tayi murnushi kana tace “zai soki mana amman sai kinyi kmr kina kiyi gsky ,dan wallahi kallon fuskar shi ma abar tsoro ce kullum fuska a hade ga babu mgn mai dadi komai daga nonsense,rubbish, stupid girl ,crazy girl ,Ke ni gbdy tsoro yake bani bana ko iya kallonsa. suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya suna cewa “shegiyar matsoraciya ,shine dan iskanci kike bata kwarin gwaiwa taje yaci ubanta ?
“suka sake kwashe da wata dariyar ”
Nan hirarsu ta koma ta mr ATA wasu na bawa mubina goyon baya ta fada masa zai amince tunda bai tsaida matar aure ba ,yayinda wasu na nuna mata illar hakan amman ita mubina ko uffan bata furta ba illa dai tana ji Kuma tana sauraronsu daya bayan daya, a natse maryam ta tsurawa mubina Ido “mubina idan kin tabbatar kina son shi shawarata ki cire tsoro dan nasan shi kike ji , ki furta masa in sha allahu zai amince Kuma zai soki tunda duk kin hada abubuwan da zaki sace zuciyar kowani nmj “Kai yar’uwata kina gani zai Soni kuwa ?why not ya Adam zai amince da sauri ma a wannan zamanin namiji ya samu macen dake sonsa kmr yadda kike son ya AD ai babu jiran da zai tsaya yi ,kefa sauraniya ce acikinmu karki ji komai na baki goyon baya dari bisa dari ki ……..”
Kiran hjy zulaiheart ne ya katse maryam ta mike da sauri ta nufi d’akin mami ta barsu suna cigaba da tautaunawa byn wasu mintuna hjy zulai ta fito tana sakar musu murnushin jin dadi tana aiyana Ina ma Adam dinta zai daure ya zabi mata a cikinsu kamar yadda sauran yanuwasa sukayi gasu nan masha Allah dan kusan auren zumunci ake yi a family din amman dai zata gwada yi masa magana taga ko za’a yi sa’a ya amince ,suka hada baki suka gaisheta a mutunce ta amsa tana tambayarsu lafiyar iyayensu , anan suka qarasa yini suna Hira daga wannan hirar zuwa wata hira sai dare suka kama gabansu .”
******
Bayan wata daya
aka wayi gari akaga gawar mubina agdan qanwar mahafiyarta zainba an kasheta ta hanyar tsoka mata wuka a daidai saitin zuciyarta Kuma aka bar wukar ajikinta ba’a cire ba hankalin family’s din abdullahi ya tashi matuka mahaifiyarta kuwa kuka da sambatu take tana cewa daga ziyara shikenan an kashe min ‘ya daga ziyara fa ,daga ziyara fa!! haka ta dinga furtawa har abun yaso zame mata kmr ta zautu saboda ita kadai gareta mace sauran ya’yanta duk maza ne ,sauran yanuwanta sunyi kuka kamar zasu bita lahira maryam kamkame da hannun mubina tana wani irin kuka me ban tausayi saboda akwai sabo me tsanani a tsakaninsu “waye yayi mana haka ?waye ya kashe mana yar’uwa ?an kasheta batare da burinta ya cika na auren ya AD ba sai lokacin mutanen gidan suka San da batun soyayyar da mubina ke yiwa AD batare da bata lokaci ba jamian tsoro suka shiga lamarin suka shiga d’aukar gawarta hoto yayinda daya daga cikin police Ke rike da farar takarda yana rubuce rubuce akan gawar byn sun gama sannan aka cire wukar aka soma kokarin shiryata zuwa makwancinta Inda har lokacin jini bai daina tsiyayya ba.”
Mr ATA na gidansa dake banana estate yana kallon zanensa dan wani lokacin idan yana son hutawa can yake zuwa yayi kwana biyu idan ya gaji ya dawo gida wurin mahaifiyarsa dan bazai iya yin nisa daita ba , Kiran sweetheart dinsa ya samesa inda cikin kuka take sheida masa halin daake ciki a zaune yake amman bai san sanda ya mike tsaye rike da zanensa gam yana furta kalmar innalillahi “yaushe kenan ? ya furta cikin tashin hankali ” okay ganin nan zuwa nan da wasu yan mintuna bai tsaya katse Kiran ba ya mike ya leko zuwa falonsa na uku Inda ya bawa masu tsaronsa umarnin fita yana gama fadar haka ya koma ya shirya dan daman yyi wanka cikin kankanin lokaci ya fito ya karasa Inda motarsa yake aka bude masa gidan baya ya shiga ya zauna zuciayrsa na tsinkewa hankalinsa na sake tashe sai dai ba’a iya hango bacin ransa a fili sai dai daga ciki yake iya bayyanashi ai kuwa da yana nunawa da duk ahlinsa sai sun fahimci yadda yaji mutuwar mubina .Kyawawan idanunshi wadan da suka wadatu da gashin idanu ya zubawa gawarta dake kwance a parlour dan har an fito daita domin tafiya daita makwancinta .duk da kasancewarsa mutumin da baya sakewa da ‘yanuwansa amman yaji zafin mutuwar mubina sannan ya tausayawa iyayenta kasa furta komai yayi duk da maganar yake son yi amman maganar taki fitowa hankalinsa sai sake tashi yake yana mamakin yadda aka kashe mubina yana wannan tunanin aka fito da gawar mubina da jini duk ya bata likkafani aka nufi gidanta na gaskiya .”
Bayan an dawo daga kaita duk yan’uwa suka yi tsuru tsuru kowa ka gani yana cikin tsananin tashin hankali me tsananin ,Sosai mr ATA yaji mutuwar yar’uwarsa duk da ba wani sabo ne a tsakaninsu ba, batun tana son shi kuwa sai lokacin yaji abun ya mugun tsaya masa rai duk da yasan babu digon sonta a zuciyarsa kawai dai tausayi ne da jimami , yan’uwa sun jajantawa juna “yarinyar da bata da hayaniya yaushe take fad’a bare a samu abokin gabarta da har zai yi sanadin mutuwarta ,bata shiga harkar mutane kullum cikin faraa take inji cewar hjy zulaiheart kowa mamakin da yake yi kenan a tsakaninsu .muryar mr ATA a sanyaye ya dube police officer din dake tsaye kusa da mahaifiyarta yana mata tambayoyi “kuyi iya bincike da zakuyi Ina son a gano wanda yayiwa mubina kissan gilla dan sam bazan barshi ba koda kuwa danuwana ne ,” ya karasa maganar cikin tsananin fushi “karka damu ranka shi dade tabbas zamuji da komai bai ce komai ba ya k’arasa kusa da mahaifin mubina dake rike da wukar da’a aka kashe masa tilon diyarsa ya dafa kafad’arsa sannan ya karbi wukar daga hannunsa yana kallon wukar mai dauke da kan sarauniyya ya dinga kallon wukar da akayi kisan sabuwa ce fil da alamun ma akan mubina aka fara amfani dashi ya furzar da numfashi kana ya soma mgn “karka damu uncle jay dake haka yake kiransa inshallahu za’a gano ko waye yake da saka hannu gurin kashe mubina ka kwantar da hankalinka muddin Ina raye sai nasa an gano wannan mashekin .”ya karasa maganar jijiyo kansa na mikewa, hawaye ya zubo a idanun mahaifin mubina ya daura hannunsa daya akan hannun Mr ATA dake kafadarsa “na gode ADTA dake shima hk yake kiransa Allah ya jikan mahai ….”kasa karasawa yayi saboda kukan daya ci karfinsa dan sai lokacin ya samu damar zubar da hawaye mr ATA ya rungumeshi ajikinsa tsam yana rarashinsa .”
bincike sosai akayi akan mutuwar mubina sai dai har wannan lokacin da ta cika wata biyar da mutuwa ba’a samu nasarar gano hannun wanda yayi kisan ba a karshe mahaifinta yace abar case din ya barwa Allah komai amman mr ATA yace sam a cigaba da bincike da kyar uncle jay ya shawo Kansa ya hakura , maryam ta dade tana Jin mutuwar mubina a zuciyarta dan ko runtsawa bata yi duk sanda ta tuna maganarsu na karshe kafin akasheta sai ta rushe da kuka Mai tsanani “ki tayani da addua marsi ina Kara Jin qaunar ya ad a cikin zuciyarta gashi bani da yadda zanyi ya fahimceni tsoronsa ya hanani fuskantarshi da maganar amman zanyi qoqarin fad’a masa acikin satin nan Allah yasa idan na furta masa ya amince ya aurenni ,ni ko baya sona zan zauna dashi haka bare ma wuyarta mu kasance miji da mata tuni zan mantar dashi wani kiyyaya Allah sarki rayuwa kenan mubina Allah yayi Miki rahma ..”
*******
Bayan shekara daya
Yana zaune akan gadon hjy Zulaihat sanye cikin kananan kaya wondo da riga ash colour idanunshi sanye da farin glass yana fama tura sakonni ta shigo dakin ta nufi inda beside dinta yake “sweetheart! ya kira sunan da yake kiranta dashi sabani Kowa dake kiranta da mami “Yaakayi my love ta amsa tare da kallonsa “ko zan samu black tea ?yayi mgnr yana cigaba da aiki “me zai hana shalelena bari nasa maryam ta kawo maka nayi baki ne .
“No abarshi kawai sweetheart idan itace zata kawo min yaran da babu abinda suka iya sai shirmen banza da wofi .tayi shiru shima yayi shiru ,shi dai bai san dalili ba amman baya son maryam a kusa dashi Kullum qara jin tsanarta yake wanda da zaa tsaresa da bindiga bazai ce ga dalili ba, shi dai hk kawai yake jin baya sonta a duk cikin family’s dinsa na bangaren uwa da uba .”
ta juya ta bude beside tana duba abinda ya shigo daita “yauwa ko zaki bawa auta ta kawo min idan tana nan “still bai dago ya kalli inda take ba ?dagowa tayi a natse tana sauke numfashi sannan ta d’an matso kusa dashi ta daura hannunta akan sumar kanshi tana lumshe ido kana tace” ai duk abu daya ne da auta da maryam dukkaninsu shirmen banza da wofi suka iya zai fi kyau ka kawo wacce bazata dinga maka shirmen banza da wofi ba ta dinga maka abinda kake so ” . “ta fad’a tana dauke hannunta akan sumar kanshi .”ya dan dago a hankali ya kalleta suka hada ido yaga yadda fuskarta ya canza sosai alamun bata ji dadin abinda ya fada ba, ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yace “am very very sorry ma “shikenan yanzu auta zata kawo maka ta dauki abinda ya shigo daita ta fice daga dakin “.
Byn minti goma auta ta shigo a hankali tmkr kazar da Kwai ya fashewa aciki bakinta dauke da sallama hannunsa kawai ya mika mata tana mika masa cup din tea ta fice da sauri ta bar dakin, yana cikin aiki ya samu kira daga danuwansa hisham ya dauki wayar “hello hisham ! “Okay just give me ten minutes I will meet you there ya fad’a yana kokarin kashe system dinsa byn ya kashe ya dauki system dinsa ya rungume a qirjinsa ya nufi kofar fita .”
yana qoqarin fita maryam na qoqarin shigowa dakin hannunta rike da akwatin sarkokin hjy Zulai da wayarta on exepecting taji tayi karo da gangar jikin mutun nan take system dinsa yayi tsalle daga qirjinsa yayi kasa …,”da wani irin mugun sauri tayi watse da kayan hannunta har ma da wayarta tayi kasa ta tarô system din da hannuwanta duka tun bai kai kasa ba ta shiga uku ,shi kuwa ATA tsaye yayi batare da wata alamun damuwa a tattare dashi ba yana dubanta sai dai kallo daya zaka masa ka fahimci ransa ya baci da abinda tayi ,shi bama system din yafi damunsa ba kamar haduwar da jikinsu yayi .”
jikinta na rawa ta miko masa system tana cewa “am … am very sorry kayi hakuri dan allah ban …..”ai batasan sanda tayi shiru ba sakamakon wani kwallo da yayi daita da system din nasa gbdy kamar ball sai gata a waje bisa gwiwowinta ta dunkule guri daya ,
bata bi ta kanta ba ta maida hankalinta ga system dinsa ,nan ta hango system ya wargaje a kasa kallo daya tayiwa system din ya fahimci ya tashi aiki nan fa hankalinta ya sake tashi “stupid girl kawai .” ya furta da karfi yana qarasa fitowa daga cikin dakin sosai ya daga kafarsa daya zai daki gefen cikinta yaji sautin muryar hjy Zulai “karka soma adam “.
Numfashi ya sauke yana waigowa zuwa inda take tsaye ranta a matukar bace tace “me yayi zafi adam zaka kashe yar mutane ne ?laifin me tayi maka ?tayi masa tmbyr ajere ransa a matukar bace yace “ask this nonsense girl .” ya fad’a yana nuna maryam da dan yatsansa hjy zulai ta qaraso tana kokarin daga maryam “me kikayi masa yake kokarin kasheki “?
ranta a matukar bace ta soma magana, ahankali ta zayyanewa hjy zulai komai tana sheshekan kuka tmkr ranta zai fita ..”naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana dubansa ” shine zaka mata irin wannan hukunci ko da gangan tayi bai dace ba bare babu daya “ya kada kai zai wuce “adam ! ta tsaidashi ta hanyar kira sunansa Ya juyo a matukar fusace yana dubanta ” daga yau kar na kara ganin ka ta’ba lafiyar jikinta bama ita ba kowani yaro a gidan nan ban amince ba ban lamunta ba kaji na fada maka……..”
iska ya shaka ta cikin bakinsa daman kuma duk sanda ransa ya baci baya fesar da iska a fili sai dai acikinsa juyawa yayi ya kama gabansa .”hjy Zulai ta kamo maryam suka shiga cikin dakinta tana bata hakuri “ki dinga kula kinji maryam wannan yayan naki hakurinsa mai yawa ne ta zaunar da maryam akan gado itama ta zauna tare da daura kan maryam akan ciyarta ta daura hannunta akan sumar kanta tana shafawa” ki tayani da yi masa addua allah ya yaye masa wannan nukufurcin da zafin rai da yake fama dashi “.Allah kiyaye na rasa wanda zan wa addua sai mutumin daya tsaneni kamar ya kasheni ta fad’a acikin ranta mami tace ,”zaki tayani yi masa addua maryam ?.”cikin muryar kuka ta gyada mata kai kawai ba dan zatai ba “Yauwa na gode Kwarai diyata allah yayi miki albarka .”
Da daddare ATA na zaune akan makeken gadonsa yana operating din wayarsa hjy zulai ta shigo bakinta dauke da sallama lumshe lumtsatsun idanunsa yayi saboda ganinta duk halin damuwar da yake ciki da zarar ya ga mahaifiyarsa yake jin sanyi aranshi “fatan kina Lfy sweetheart “?ya tambayeta yana riko yatsun hannunta daya cikin nashi “alhamdulillah ta fada fuskata babu yabo babu fallasa .”ga coffe ta mika masa sannan ta zauna kusa dashi ya saki yatsun hannunta ya karbi cup din coffee ya kai bakinsa “me zakayi breakfast dashi da safe ? yayi shiru yana tunani can yace “komai sweetheart dina zata ci nima zanci .”
Adam!!! ta kira sunansa har sau uku ya sake rike hannunta gam cikin nashi yana kurban coffe yana lumshe ido har dimple dinsa na lotsawa ,” ina son nayi wata magana mai mahimanci da kai,nan take ya bar abinda yake ya tattara dukkanin natsuwarsa zuwa gareta “abinda kayi dazu sam banji dadi ba dan allah na roki arziki ba dan ni ba karka sake maimaitawa .”tai shiru tana jiran taji me zai ce “ya lumshe mata idanunshi “naji amman itama ki mata mgn ta daina shiga hanyata “wannan kuskure aka samu domin kuwa maryam na qoqarin gani bata shiga harkarka ba “.
“kai ba ita ba kowa acikin family’s din nan yana takatsntsan ba yara ba ,ba manya ba sai kace wani azara ilu “yayi murmushin ciki wanda ita kadai take iya fahimtar haka ,”wallahi ka canza kai gaka nan kullum cikin bakin rai da miskilanci yanzu kai ko shaawa rayuwar gidan nan bakayi kowa na son kowa kalli su hisham dasu tariq sweetie nah kenan ya dauko mai sunanshi tsab ,kai hatta muhd bello da ba dan gidan nan ba yana jan yaran gidan nan ajiki amman kai kowa tsoronka yake ji Kmr wani dodo wallahi ka dinga son mutane dan mutane rahma ne.”
“to ni nace bana son wani ne acikinsu ?ya fad’a a shagwabe yana daura kanshi saman cinyarta ”
girgiza kai kawai tayi tana daura hannunta a sumar kanshi tana shafawa tana kallon kyakkyawar fuskarsa mai cike da haiba ga kwantaccen gashin fuskarsa dake mugu mugun qara masa kyau sosai ya kwanta luf luf saboda gyaran da yake sha .
“ni sweetheart kin kasa ganewa ne nifa raini ne banason su kuma yan renin sense ne kinga gara na dinga kama kaina “yyi mgnr Kmr bashi yayi mgnr ba ,girgiza kai ta sake yi kana ta cigaba da mgn “sai abu na gaba “ya batun aure ko har yanzu baka samu true love din ba ? .”Yes of course ban samu ba sweetheart ,”yanzu kai baka tausayawa wannan mamartaka da shekarunta yaja ? ”
“Adam at any time zan iya amsa kiran allah ko sai bayan mutuwata zakayi aure ? tayi mgnr tamkar zatai kuka nan fa hankalinsa yayi mugun tashi ya mike zaune tare da riko hannuwanta gabadaya cikin nashi yana kallonta cike da matsanancin soyayyarta gbdy yanayinsa ya sauya kamar zai yi kuka dan baya qaunar abinda zai nisan tashi da mahaifiyarsa bare rabuwa ta har abada ,muryarsa a kasalance ya soma mgn “haba sweetheart me yasa zaki fadi haka ?”
Me yasa bazan fadi haka ba ?ai gaskiya na fad’a kaki kayi aure kai dai kullum aiki kawai kasa gaba baka ma duba lamarina bare ka tausaya min Adam , bana son na koma ga allah banga aurenka da ya’yan ka ba ta qarasa mgnr cikin raunanniyar murya wannan karon kam hawaye ne taf acikin kwayar idanunta “karki min hk sweetheart Kinsan illar zubar da hawayenki akaina, kuma Kinsan babu abinda na tsana kamar na ganki cikin damuwa “idan har da gaske baka son ganina cikin damuwa to ka dan duba ko a cikin yammatan estate din nan ai bazaka rasa masu sonka da aure ba sai ka zabi biyu ko daya acikinsu “.
Ya ware mata lumtsatsun idanuwanshi sosai yana mamakin jin abinda tace “har mata biyu sweetheart ina zan kai su ? “bansani ba ta fad’a tana zabga masa harara sannan ta cigaba da mgn “wallahi shine burina ka auri mata biyu kuma duk arana daya saboda kasancewarka namiji kwaya daya tilo da allah ya mallamin “girgiza kai kawai yayi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa batare da yayi yunkurin sake cewa wani abu ba ya sake jin sautin muryarta “zakayi abinda nace ko nasa araina sai bayan na mutu zakayi aure ?” ya shafa goshinsa yana cewa “okay zanyi kokarin yin haka sweetheart.” Ya fadi hk ne dan ya kawo karshen mgnrsu .”ko kai fa yaron albarka allah ya zaba maka mata na gari , runtse idanuwanshi yayi sosai tare da yin shiru yaki cewa komai dan har kanshi ya fara ciwo .”
Mmn sudais
Add Comment