Littafan Hausa Novels

Cin Amanar Aure Hausa Novel Complete

Cin Amanar Aure Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Cin Amanar Aure

 

 

_Rubuta labari da tsarawa✍🏻Maryam Shu’aibu Sulaiman (Mrs Ibrahim)_

 

 

_Alhamdulillah, godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai bayar da baiwa ga wanda ya so kuma ya ga dama. Ina godiya ga Allah da ya sake bani dama haɗi da basirar sake kawo muku sabon littafina mai taken *CIN AMANAR AURE*. Ina fatan wannan littafi ya ba da darasussuka ga kowanne mutum mace har da ma mazan baki ɗaya. Allah Ka ƙara shiryar da mu baki ɗaya. Allah Ka sa saƙon da nake son isarwa ya je ga inda nake buƙatar zuwansa. Amin _

 

 

 

_Wannan littafi ƙirƙirarren labari ne, ban yi shi don cin zarafin kowa ba, sai don ilimantawa da faɗakarwa haɗi da nishaɗantarwa. Duk wanda labarin nan ya yi daidai da naki/naka ina neman afuwarku_

 

 

_Sannan wannan littafi na kuɗi ne, ki biya 300 ki sha karatu, don ba zan yi free pages da yawa ba.

 

 

 

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallargidana, fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kaɗai ke maganin ƙishi_

 

*Alƙalaminmu ‘Yancinmu *

 

 

Paid Book #300

 

Free Page 1&2

 

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

 

 

 

_Shi dai wannan littafi labari ne kan wani magidanci da matarsa wanda suke rayuwa a wani babba gari da ke arewacin Najeriya_

 

 

……Wanene Ahmad? Ahmad shine mijin Laila. Ya kasance wanda ke gudanar da harkokinsa na kwangila, kuma mutum ne mai tsananin son kuɗi wanda komai zai iya yi don ya samu kuɗi, sai gashi iftila’i ya hau kansa ana binsa wasu kuɗaɗe wanda ya ara a kamfanin da yake aiki, kuma kuɗaɗe ne masu mugun yawa. Ahmad ya shiga damuwa bai san taya zai biya su waɗannan kuɗaɗen ba.

 

Uwar Ta Gari Ce Hausa Novel Complete

 

Matarsa Laila ta kasance mace ce mai biyayyar aure da haƙuri, tun tana ƙaramar take tsananin son Ahmad wanda ɗan ƙanin mahaifinta ne. Ba a samu wata matsala ba wajen ƙulla alƙawarin aure a tsakanin su, har dai zuwa lokacin da aka yi musu auren zumunci, duk da yake ba wata shaƙuwa suka yi ba, don ita Laila ta fi son sa ba kamar shi Ahmad ba. Sai dai tunda suka yi aure ba ta jin daɗin auren ko kaɗan, saboda muzguna mata da yake yi, amma a haka take zaune da shi saboda haƙurinta da kuma biyayyar nasihar da iyayenta suka yi mata. Wannan shi ne labarin waɗannan ma’aurata.

 

 

Bari mu tsundima cikin labarin.

 

 

Zaune take a falo ta yi uban tagumi, kana ganinta ka san cewa damuwa ta yi mata yawa. Ahmad ne ya shigo tare da sallama, amsa mishi ta yi kana ya zauna. Duk da yake ya lura da halin da take ciki amma sam bai kulata ba, ita ma da yake ba sabon abu ba ne a wajen ta hakan ya sa bata damu ba.

 

Sannu da zuwa ta yi masa, ya amsa mata. Wayar Ahmad ce ta yi ringi cikin sauri ya ɗauka, sallama ya yi daga haka bai sake cewa komai ba sai Innalillahi da ya furta. Cikin alamun tashin hankali Laila take tambayarsa, “Lafiya?”

 

Shiru ya yi kana ya ce, “Wallahi masu bina kuɗi ne suka kira ni wai sun bani wata ɗaya, ni kuwa ban san yadda zan samu wannan kuɗaɗen ba. Gashi ina ta neman wata kwangila har yanzu ban samu saka hannun maigidana ba. Sauran kuɗaɗen da nake bi bashi na waccan kwangilar, su ma har yanzu ba su fito ba. Kuma ga shi waɗannan mutanen suna ce min idan ban basu ba za su ƙwace min duk abinda na mallaka. Ni kuma wallahi ban san ya zan yi ba.” Ya faɗa cikin yanayin damuwa.

 

 

Shiru Laila ta yi, sai can kuma ta ce, “A matsayina na matarka wacce ya dace na baka shawara, ina ganin kamata ya yi ka zama mutum mai ɗaukar ƙaddara a duk lokacin da ta zo maka, mai kyau ko marar kyau. Ka yi haƙuri ka yi ta addu’ar samun mafita. In sha Allahu nima zan taya ka da addu’a, amma ka daina irin wannan maganar, please?”

 

“To, sannu malama. Ana miki magana sai ki fara kawo wa mutum ma’azi. Ki riƙe wa’azinki ba na buƙata.” Ya faɗa yayin da yake ƙoƙarin tashi ya shiga ɗaki.

 

 

“Oh! Wai yanzu don Allah kai da mijinka amma babu dama ka bashi shawara mai kyau. Allah Ya kyauta!”

 

 

Ahmad kuwa yana shiga ɗaki Safa da Marwa ya fara yi, domin maganar da aka yi masa ta yi matuƙar damunsa, don shi a tsarin rayuwarsa bai yarda da zama cikin ƙunci da talauci ba. “Shin anya kuwa ba zan ɗauki mataki a kan wannan abin ba? Duk yadda zan yi dai na yi, amma har yanzu ban samu abin da nake nema ba. Shi kuma Alhaji ya ƙi saurarata. Amma na san abinda zan yi.” Ya faɗa yana fita daga ɗakin.

 

Falo ya koma ya tarar da Laila zaune a inda ya bar ta. Murmushi ya yi mata, kana ya bata haƙuri a kan abin da ya yi mata, cikin ƙanƙanin lokaci ta haƙura, saboda ita ba mace ce mai mita da son riƙo ba, Nan da nan suka ɗan fara hirar can kuma ya ce, “Laila, ki shirya za ki raka ni unguwa. Amma please ina son ki yi kwalliya mai kyau ta fita kunya.”

 

Cikin fara’a da sakin fuska ta ce masa. “To, Habibina. Ina za mu je haka?”

 

“Ke dai ki je kawai ki shirya, zan faɗa miki.” ba ta musanta masa ba ta tashi ta je ta shirya ta sha kwalliya tare da fesa turaruka masu ƙamshi.

 

Bayan ta gama ta fito falo ta same shi, kana ya ɗauki makullin mota suka tafi.

 

 

Tafiya suke yi a mota sai Laila ta ce, “Habibina, wai har ina za mu je ne haka? Na ga mun yi hanyar bayan gari.”

 

Ba tare da ya juyo ya kalli gefenta ba ya ce, “Za mu je gidan maigidana ne wanda nake so ya sa min hannu na samu kwangilar nan, ina so mu je mu gaishe shi ne, don na ƙara masa magana ko Allah zai sa a dace.”

 

“OK. To, shi kenan. Allah Ya sa mu dace.”

 

Ba Ta san shi gogan nata akwai abin da ya ƙulle a ransa ba.

 

 

Ba da jimawa ba suka isa gidan, da ke wata unguwar masu hannu da shuni da ake cewa Sabuwar London, domin akasarin tsarin gidajen unguwar irin na ƙasashen Turai ne.

 

A gefen ajiye motocin baƙi Ahmad ya ajiye motarsa, kafin su fito ya sake dubanta yayin da take sake gyara lulluɓinta. “Yawwa, don Allah ina son idan mun shiga ki saki jikin ki, kuma ki gaishe shi cikin ladabi da fara’a. Don na san halin Darakta, murɗaɗɗen mutum ne, kuma yana da saurin tsarguwa da fushi. Mu ma lallaɓa shi muke yi.”

 

Laila ta kaɗa kai ta ce, “Na fahimta kar ka ji komai. Allah zai ba mu nasara a kansa, in sha Allah.”

 

Sai da suka fito daga cikin motar sannan Laila ta ɗaga kai ta kalli gidan. Gidan sama ne mai hawa ɗaya, an ƙawata shi da wasu fulawoyi masu ban sha’awa da ƙamshi, ga shi an yi masa koren fenti, mai haske da mai duhu. Rufin gidan kuwa ya ishi jarin wani babban ɗan kasuwar.

 

Wata rantsattsiyar mota ce baƙa wacce aka rufe da baƙaƙen gilasai, ta lura an ajiye a farfajiyar shiga gidan.

 

Laila ta juyo ta kalli mijinta. “Lallai wannan maigidan naka babban mutum ne. Dubi irin wannan katafaren gida. Kuma matansa nawa ne a ciki?”

 

Ahmad ya yi murmushi. “Ai wannan ƙarami ne daga cikin irin manyan gidajen da Alhaji ke da su a garin nan. Kuma ba a nan yake zaune da matansa ba, yana da wani gidan wanda za a sa biyun wannan a cikinsa, a can GRA, a can suke zaune.”

 

“To, nan kuma na meye?” Laila ta tambaya.

 

Wannan Guest House ɗin sa ne, inda yake saukar baƙi, ko wani taron sirri da manyan ma’aikatansa ko ýan siyasa. Ko kuma wani lokaci idan yana son keɓewa nan yake zuwa ya huta.”

 

A daidai wannan lokacin, maigadin gidan ya ƙaraso inda suke a tsaye. “Salamu Alaikum, sannunku da zuwa.”

 

“Malam Ado, sannu da aiki. Ogan na ciki ne?”

 

“E, yana ciki, bai jima da shigowa ba.”

 

“Shi kaɗai ne a ciki?”

 

“E, shi kaɗai ne. Ku shiga kawai.” Malam Ado ya juya wajen Laila. “Hajiya, sannu da zuwa.”

 

Laila ta ce, “Yawwa, na gode. Sannu da aiki.”

 

Suna shiga suka tarar da shi kaɗai zaune akan wata doguwar kujera ta alfarma, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yana duba wata jarida da ke hannunsa, yayin da daga gefe guda wata ƙatuwar talabijin ce mai kamar majigi an kunna tashar BBC World Service ana labarai. Da ganin fuskarsa zai kai shekaru arba’in da bakwai zuwa hamsin. Kansa da fuskarsa babu gashi ko kaɗan ya aske duk furfurar da ta fito masa.

 

Alhaji Sammani Naboza, babban attajiri ne, kuma basarake, domin shi ne Makaman Boza, kuma shi ne Babban Darakta a Ma’aikatar Kula da Makamashi da Ƙarafa ta Ƙasa. Ma’aikatar da Ahmad yake yi wa ayyukan kwangiloli. Mutum ne marar gaskiya kuma almubazzari, wanda duk girmansa yake zama yaro a gaban mace.

 

Umarni ya yi musu su zauna. Suka zauna a sauran kujerun dake gefe masu zaman mutum ɗai ɗai.

 

Laila ba ta ji daɗin irin kallon da wannan babban mutumin yake mata ba, kamar zai cinye ta, duk yadda ta ke sunkuyar da kai da zarar ta ɗago, sai ta ga yana cigaba da kallonta. Ganin gidan shiru babu kowa, in ban da maigadin da suka gaisa da shi a waje, da wani mutum da ta ga ya shigo ya kawo musu lemon kwalba da ruwan sanyi, tana ganin babu kowa a gidan.

 

Bayan sun gama gaisawa sai Ahmad wanda ya lura da yadda maigidan nasa ke kallon matarsa ya yi ƙoƙarin kawar da hankalinsa daga gare ta ya gabatar da Laila. “Ranka ya daɗe, wannan matata ce, Laila. Na zo da ita ne mu gaishe ka.”

 

“Masha Allah. Ai kuwa na gode sosai. Sannu, yarinya. Ya juya ya kalli Laila, sannan Ahmad. “Malam Ahmad, lallai kana da kyakkyawar mata. Gorgeous!” Ya faɗa yana girgiza kai.

 

Laila ta ji wani ras, gabanta ya faɗi. Ta juya ta kalli mijinta wanda ke ta washe baki, abin ko a jikinsa. Ranta ya ɓaci sosai, amma sai ta kanne saboda kashedin da mijin ya yi mata. Ta sunkuyar da kai, ta wayance da duba wayarta.

 

“Yallaɓai, batun kwangilar nan da nake nema dai har yanzu fayil ɗin bai fito ba.” Ahmad ya faɗa yana sunkuyar da kai.

 

Alhaji Sammani, wanda batun kansa ke sunkuye yana kallon jaridar da ke hannunsa amma kuma hankalinsa ya tafi kan Laila wacce ke zaune a kujerar da ke fuskantarsa yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa. Ya lura tana da duk wani abu da yake so a jikin mace, ga ta fara kyakkyawa. Ta ma fi dukkan matansa kyau, kuma a yadda yake ganinta idan ya samu haɗin kanta ba ƙaramin daɗi zai ji ba.

 

“Ina fatan dai Alhaji zai taimaka a duba fayil din nawa” Ahmad ya katse masa tunanin da yake yi, bayan ya lura tarkon da ya ɗana wa Alhaji ya kama shi har wuya.

 

Alhaji ya gyara zama, ya ajiye jaridar da ke hannunsa a gefen sa, ya ɗauki robar ruwa ya zuba a ƙaramin kofin glass din da ke kan tebur a gabansa, ya tuttula har sau biyu ya sha. Ya dubi Ahmad da murmushin ƙyeta a fuskarsa. “Kar ka samu damuwa, Ahmad. Gobe ka same ni a ofis, sai mu tattauna yadda za a ɓullo wa lamarin.”

 

Ahmad ya ƙara rusunawa yana cewa, “Oga na gode. Allah ya ƙara girma.”

 

“Kar ka damu. Ai kai nawa ne.”

 

Jim kaɗan Ahmad ya sanar da Alhaji za su tafi, suka miƙe tsaye. Shi kuwa ya sa hannu a cikin aljihun rigarsa ya fito da ɗaurin kuɗi ýan sababbin ɗari biyu, ya miƙa wa Laila wacce ta ƙi karɓa, sai dai ta rusuna tana godiya. Hakan ya bai wa Alhaji damar ƙara matsowa kusa da ita yana cewa, “Haba, amarya. Mai zai sa ki min haka, wannan ai ba wani abu ba ne. Bai wuce na sa kati ba. Fiye da haka ma ni mai iya baki fiye da haka ne, in ki ka saki jikin ki.” Ya ƙarasa maganar yana dariya.

 

Shi ma Ahmad sai ya biye masa suka ɓige da dariya a lokaci guda. Ba zato ba tsammani sai kawai Laila ta ji saukar hannun Alhaji bayanta, kamar zai rungumota jikinsa. Sai ta ji kamar wutar lantarki ta ja ta. Nan da nan ta yi sauri ta matsa gefe. Shi kuwa Ahmad ya sa hannu ya karɓi kuɗin yana godiya, ya sa a aljihu.

 

 

Alhaji ya yi umarnin su wuce gaba zai yi musu rakiya. Ga mamakin ta sai ta ga Ahmad ya wuce gaba ya bar ta a baya, don haka sai ta yi sauri ta bishi a baya. Kamar ya san abin da za ta yi, sai shi ma Alhaji ya wuf ya bi bayanta, a dalilin haka sai suka yi karo da juna har ya kai hannu mazaunanta. Laila ta ji zafin abin da ya yi mata, don haka ma suna fita kofar gidan da sauri sauri ta bar wajen, don kar su sake haɗa ido da Alhajin. Da sassarfa ta ƙarasa jikin motar Ahmad ta tsaya don jiran ƙarasowarsa.

 

Bayan sun yi sallama da Alhaji, sai Ahmad ya taho ya tarar da matarsa Laila na jiransa a jikin mota, ya buɗe mata suka tafi.

 

A hanya suna tafiya a mota Laila take sanar da shi, rashin jin daɗin yadda Alhajin ke kallonta kuma har ma sai da ya shafa mata bayanta lokacin da take rusunawa tana yi masa godiya, amma a maimakon ran Ahmad ya ɓaci sai ma dariya da ya yi, yana ƙara nuna mata muhimmacin wannan mutumin a wajensa, kuma a cewarsa lallai ta saki jikinta don idan har ya lura bata son halinsa ko alaƙarsu to, zai iya sawa a hana shi kwangilar da yake nema, kuma kuɗin da yake bi bashi ma ba za a sake masa ba. A dalilin haka a cewarsa karayar arziƙinsa ta zo kenan, don haka ya gargaɗeta lallai ta yi duk abin da ya ce mata, don idan ta cigaba da haka za ta jefa rayuwarsu cikin baƙin talauci.

 

 

Tunda ya yi mata wannan maganar jikinta ya yi sanyi, ba ta ƙara cewa uffan ba, har suka isa gida.

 

*********************

 

Washe gari Ahmad da wuri ya shirya domin zuwa wajen Alhaji Sammani, tunda ya tashi safe yake saƙe saƙe a zuciyarsa. Bai san abin Alhaji yake shirin gaya masa ba. Ya tuna da abubuwan da matarsa Laila ta gaya masa kan abin da ya yi mata, ya kuma san tabbas Alhaji Sammani mayen manemin mata ne. Yana fargabar kada jarabar ta sa ta faɗa kan matarsa, amma bai bari damuwar da yake ciki ta nuna a fuskarsa ba, ta yadda ita kanta Laila za ta gane akwai abin da damunsa. Bayan ya gama komai ta yi masa rakiya har wajen mota kana ta yi masa addu’ar Allah ya sa a dace da abin da yake nema.

 

 

Yana isa Ma’aikatar Makamashi da Ƙarafa kai tsaye ya wuce ofishin Babban Darakta, yana zuwa bayan sun gaisa Alhajin yake gaya masa cewa an kai masa fayil ɗin sa ya duba ya ga adadin abin da yake bi bashi, da kuma buƙatarsa ta neman kwangilar kawo tsofaffin ƙarafunan da ake buƙata, don kai wa babbar Ma’aikatar Sarrafa Ƙarafa ta Ajaokuta inda za a narkasu a dawo da su yadda ake buƙata. Kuma wannan harka ce ta miliyoyin Naira, da za a samu maƙudan kuɗaɗe. Irin wannan kwangila mai tsoka ba haka kawai ake ba da ita ba, sai an yi ciniki kuma an yi yarjejeniya ta abin da za a bayar.

 

Ya ce masa, “Ahmad, ka san wannan kwangila da ka ke nema babba ce, kuma idon mutane da dama na kanta. Zan iya cewa kai ne ma ƙarami cikin masu neman kwangilar, don sauran mutane masu ƙarfi ne sosai. Har ma sun je sun gana da wasu manyan Daraktoci a kan haka. Ba zan yi maka ɓoye ɓoye ba, dole sai ka yi hidima sosai, kuma ka sadaukar da wani abu da ka fi so, don a samu abin da ake nema.” Ya kammala maganar yana murmushin ƙeta.

 

 

Ahmad ya ji gabansa ya faɗi.” An zo wajen!” Ya faɗa a ransa. Ya ɗaga kai ya dubi Alhaji Sammani cikin murya mai sanyi ya ce masa.” Ban fahimci abin da ka ke nufi ba, Alhaji. Sadaukarwa wacce iri?”

 

Alhaji Sammani ya fashe da dariya yana kallon Ahmad, “Kar ka bani kunya mana, Ahmad. Yau ka fara wannan harkar ne? Kai ma ka san akwai alherin da ake yi, kuma wannan babbar kwangila ce, tana buƙatar babban tukwici. Yanzu kai me za ka iya bayarwa, don mu san da gaske ka ke yi?”

 

“Haka ne. Amma Alhaji ka san ba ni da komai da wannan kwangila na dogara. Waɗancan sauran kuɗaɗen aikin da na yi ma ba a sake min ba, ballantana in samu ba da wani abu na tukwici a taimaka min dai Alhaji.” Ahmad ya roƙa.

 

“A’a fa Ahmad ya za a yi ka ce ba ka da komai? Bayan kuwa kai ne ke da abin bayarwa? Ina matarka Laila? Ga ka da kyakkyawar mata son kowa ƙin wanda ya rasa! Ai kai kana da babban jari!!”

 

Wata zufa ce ta feso wa Ahmad, jin ta inda Alhaji Sammani ya ɓullo masa. Ya ma za a yi ya yi masa irin wannan cin fuska, don yana neman kwangila a wajensa. Ai babu wani abu da zai yi kwatankwacin girma da mutuncin matarsa. Matar Sunnah ba karuwa ko budurwar titi ba!

 

Da wannan tunani ya tafi gida da shi a ransa. Ya sake tuno da maganganun da Alhaji Sammani ya gaya masa. ‘Ga ka da mata kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa! Ai kai kana da babban jari!!’ Gabansa ya sake yankewa ya faɗi. Bai san lokacin da hawaye ya zubo daga idanunsa ba. Talauci bai yi ba!!!.

 

 

 

 

Uhmm yanzu aka fara wasan ku dai biyoni don jin yanda za ta kaya tsakanin Alhaji Sammani, Ahmad da Laila.

 

 

Please My Fan’s ina naiman afuwarku akan Book ɗin da nafara amma ban samu damar ci gaba ba, saka makon na samu wacce take irinsa ni kuma ba zanyi ace satar fasaha nayi ba dan haka na aje Book ɗin *BA ZAN BAR SHI BA* na ɗauki *CIN AMANAR AURE* shima insha Allah za kuji daɗinsa kamar waccan, dafatan zaku farantamin wajan suburbuɗomin ruwan comment domin nima zan suburbuɗo muku ruwan Typing

 

Ki biya 300 kisha karatu ba zanyi free Page da yawa ba atoh

 

Domin shiga group dan samun Posting ki min magana ta wannan number (09138585050) Mrs Ibrahim

 

Comment And Share

 

 

Mrs Ibrahim ce

Add Comment

Click here to post a comment