Abin Da Ciwo Hausa Novel Complete
ABIN DA CIWO
Written by:oum zuhriyya
_duk wacce take so ta shiga grp din wannan novel din me suna *ABIN DA CIWO* tayi min magana ta wannan number din 08109202921, iya comments ɗinku iya typing di nah, wannnan lbrn ya kunshe abubuwa da dama kamar su makirci, sharri, dana sani da dai sauran su_
Page 1
“Dan Allah habibi kayi hakuri yarinyar nan har yanzu dae da sauran ta kwata kwata shekarun ta basu wuce sha shida ba kaga kowa har yanzu bata mallaki hankalin kanta ba, amma wannan hukuncin daka dauka din yayi tsanani wlhhh”
k’arashe maganar Abida tayi cikin rawar murya da firgici
“Dakata! Abida kullum ke kike bani hkr akan abubuwan da yarinyar nan take yi wannan karan kam wlhh bazan dauka ba sai ta tafi gida, hakuri na ya ƙare kuma maganar karancin shekaru da kikeyi ae ba’a kanta aka fara aurar da yara ba, dazata ringa tsula min tsiya ina hakuri da ita”
Daulatul Arab Hausa Novel Complete
cikin tsananin bacin rai najib yake maganar domin kuwa amal ta kai k’ololon bata mishi rai, duk da dukan daya yi mata hakan be ishe shi ba ji yake kamar ya shak’e ta ta mutu tsantsar bacin ran daya ke ciki, ita kuwa amal kuka take yi kamar ranta zai fita, mik’ewa tayi daga tsugunne da tayi a gaban shi, tafiya takeyi kamar wacce kwai ya fashe ma a ciki idanun ta sunyi luhu luhu sun kumbura sintin, bata tsaya ko ina ba sai cikin dakin ta gaban mirror ta wuce direct, tsayawa tayi tana qare ma kumburarren bakin ta kallo hade da kumburarren idanun ta, wani irin kunci take ji a cikin ranta idan ta tina wai yau yaya najib ne ya mata irin wannan dukan kuma akan laifin da ba nata ba…
Shi Koh najib Binta yayi da harara yana jin wani abu me kama da tsanar ta yana shiga cikin ranshi..
Amal
Wani ƙaramin trolly ta dauka a cikin set din akwatin auren ta kayan data san zata bukata ta fara jerawa a cikin trolly din tana ci gaba da sheshekar kukan da bata san yaushe zata daina ba da kyar take bude idanun ta sbd irin zugin da suke yi mata ga kuma uban kumburin da sukayi, fitowa tayi daga dakin nata tana jan trolly din kayan ta wucewa tayi ta gaban najib da Abida da suke zaune a palour sunyi jugum kamar masu karban gaisuwan mutuwa Koh wannen su da abin dayake tinani a cikin ranshi, Koh kallan su bata yi ba domin kuwa anzo gaɓar da ta rasa gane wa tafi tsana tsakanin Abida da yaya najib, cikin sheshekar kukan da takeyi take tafiya har ta isa bakin titi bata damu da mutanen da suke ta Binta da kallu ba sheshekar kukan ta takeyi har akan titi kusan awa daya ta shafe tana tsaye a titi tana kukan takaici da bakin cikin auren najib da tayi da kyar ta same me napep domin anguwan nasu shiru yake bayi da hayaniya da tarin jama’a kwatan ta mishi gdn baffa Adamu tayi domin kuwa shi kadae ne mutumin da take yi ma kallon mahaifi a duk fadin duniyar nan, da kyar ta ciro trolly din nata daga napep din ta shiga cikin gidan baffa Adamu da fargaba fal ranta tsoron ta daya zasu yarda da ita Koh kuma suma zasu Aminta da sharin da aka k’ulla mata.
Abida
Matsawa tayi daff da najib har suna jin bugun zuciyar junan su narkewa tayi a jikin shi tare da sake wani kuka me cike da kirsa cikin kissa da kisisina irin nata ta fara cewa.
“Ko kadan banji dadin yadda ka dau hukunci akan yarinyar nan ba habibie, ka duba kaga fuskar ta yadda ya kumbura sintin dan Allah”
Tana maganar ne tare da shafa kasan cibiyan shi zuwa maran shi a sunnu a hnkli domin kuwa tasan wannan salon yana mugun saukar dashi daga fushi kuma yana mugun tayar mishi da sha’awa.
Lumshe ido yayi yana cigaba da karban salon nata sannan ya bude baki dakyar cikin kasalalliyar Muryar shi me cike da sha’awa kamar ba yanzu ya gama zuba bala’i ba yace
“Na gaji da halayyar amal a gdn nan ta canza daga tarbiyyan dana bata, sanin kanki ne cewan amal tarbiyyan mu ce amma yanzu ta zamo wani abu daban, Gara dai taje gidan tasan me zata fada ma Abba qila shi idan yayi mata faɗa zataji ta gyara halayen ta”
Dummmmmmmm Abida taji gaban ta ya buga wani irin kunci taji a cikin ranta data ji yace wai Abba yayi ma amal fada, irin dukan data ga najib din yayi mata ae ta dauka amal tana zuwa gida kuma sai maganar saki, amma daya ke Abida ta kware a makirci sai ta qara marairaicewa a cikin jikin najib tana cewa
“Da gaskiyan Ka Gara su Abba su mata faɗa qila taji nasu tinda mu ta raina mu, amma inaga kamar lamarin nan nata akwae shafan aljanu, lokaci guda fah amal ta sauya har tana ce min wae bani da maraba da dusa a wajen ka”
Fashewa Abida tayi da kuka tana me qara shiga jikin shi, runtse ido yayi domin kuwa baya son jin kukan abidan nashi Koh kadan, sannan baƙin cikin sauyin hali amal ma yana damun shi, Nanata kalaman Abida yayi yana kuma jin mamakin yaushe amal ta riƙa har haka? Koh dan taga yana jin dadin mu’amalar aure da ita ne yasa take tinanin ita kadae ta iya kwanciyar aure ita Abida bata iya ba, kuma dae idan amal yar mutumcice ae har abada Abida ta fi karfin rashin kunya a wajen ta, ƙara janyo Abida yayi cikin jikin shi yana me sunsunsar wuyan ta yana shaqan daddadan kanshi jikin ta tare da tausaya mata domin kuwa yasan ba kowacce mace bace zata iya jure abinda amal takeyi mata .
_(Ni oum zuhriyya na kasa gane waye me takura ma dan uwan shi tsakanin amal da Abida)_
Amal
“Innalillahi wainnailayhirrajiun AMAL miye wannan nake gani a fuskar ki? Kamar shatin hannu? Ga idanun ki sun kumbura kamar zasu fashe, innalillahi wainnailayhirrajiun AMAL ki bude baki kiyi min baya Ni dan Allah najib din ne ya buge ki Koh Abida?”
Rungume Hajiya mama tayi tare da shegewa jikin ta tana sakin wani sabon kukan me cin rai, cikin rawar murya tace
“Yaya najib ne ya buge Ni kuma yace na bar mishi gdn shi”
“Innalillahi wainnailayhirrajiun ”
Hajiya mama ta iya furta wa tana jimamin wani irin laifi ne amal din tayi har haka da zaisa najib ya mata irin wannan dukan sannan ya kure ta, kai kuma menene ai be kamata yayi ma matar shi irin wannan dukan ba..
“Ki shiga dakin ki kiyi wanka ki gyara jikin ki sannan ki fito kici abinci idan kin nutsu sai ki fada min abinda ya haɗa ki da najib din”
Mik’ewa tayi da kyar ta shige cikin dakin nata tana ci gaba da kukan domin kuwa bata san yaushe zata daina ba, bata da burin daya wuce yaya najib ya sake ta amma ita kanta tasan hakan ba karamin abu bane..
Da kyar ta samu tayi wanka da ruwa me dumi sosae ta gasa jikin ta domin duk jikin nata ya mata tsami, doguwar riga ta sanya marar nauyi tare da gyalen shi dan siriri ta yafa a kanta, duk da fuskar ta dake kumbure bai hana kyan ta bayyana ba, amal dae yar tsaka tsaki ce ba tsananin doguwa ba kuma baza kace mata guntuwa ba siririya ce amma akwai ta da uban hips kamar ita tayi ma kanta nonuwan ta kuwa ba’a magana domin kuwa manyan gaske ne hancin ta dogo dashi har baka ga bakin ta dan mitsitsili me dauke da baki da pink din lips bakin ya zagaye pink din kamar wacce tayi linning da bakin gazal eyebrows din ta kowa kamar tayi cabing a takaice dae Amal kyakkyawa ce ta aikin karshi domin kuwa duk yadda mace take jin takai ta kawo toh fa Amal ta wuce nan irin ta cikin mata gaskiya basu da yawa, fitowa tayi ta karba abinci a wajen Hajiya mama ta fara ci, durawa kawai takeyi ba wai don abincin yana yi mata dadi ba kwata kwata jikin ta ba dadi har wani zazzaɓi zazzaɓi take ji, ae kuwa tana kammala cin abinci sai ga muryan baffa Adamu yana sallama wanda haka shi ya tabbatar ma Amal cewan ya dawo, gaban tane yayi mummunar bugawa domin kuwa batasan cewan zai bi bayan ya bane Koh akasin haka .
Tagumi ta zuba tana kallon plate din da taci abinci a ciki amma hankalin ta baya wajen tinani takeyi yadda zata kaya a wannan case din kiran da taji an kwala mata shi ya tabbatar mata da cewan hajiya mama ta gama faɗa ma baffa Adamu (Abba) cewan tazo, amma kiran tayi tare da mik’ewa tayi hanyar palourn shi data ji Muryar Hajiya mama yana fitowa ta wajen, gaban ta yana dukan uku uku domin batasan me zata tarar ba.
Da sallama ta shiga cikin palourn sannan da tsuguna ta duk’ar da kai tana me cewa
“Abba ina wuni”
Kallon ta yayi da kyau sannan yace “Amal d’ago fuskar ki nagani”
Dagowa tayi tana kuma jin bugun zuciyar ta yana qaruwa kamar zai fasa kirjin ya ya fito .
“Subhanallahi ashe dae da gaske dukan nake yayi, ke Amal miye ya haɗa ku har ya miji wannan dukan?”
Cikin in’ina ta fara magana muryan ta yana mugun rawa tace
“Abba dama dama nifa ban mishi laifi ba shine yace wai…….”
Shiru tayi tare da zazzare idanun ta zuciyar ta yana ci gaba da bugawa da mugun karfi.
Hajiya mama me ta katse mata shirin da cewa
“Kin yi shiru muna sauraren ki”
Da kyar ta bude baki ta kuma cewa “hajiyama da Abba ku fahimce Ni WLHHH ban aikata ba WLHHH ALLAH” ta karasa faɗa tana fashewa da kuka me tsuma zuciya.
Hajiya mama da Abba har suna hada baki wajen cewa “miye kika aika tan?”
Shiru tayi sai sheshekar kukan ta dayake ci gaba da fita a sannu a hnkli .
Hajiya mama ne ta katse shirun da cewa “abban najib inaga fah maganar nan babba ne dan haka ka kira najib kaji daga bakin shi”
Shiru yayi kamar bazae ce komai ba sannan yace.
“Allah ya kyauta”
Daga nan be kuma cewa komai ba sai wayan shi daya dauka ….
Najib
Gaba daya abida ta gama ruda shi da salon ta duk da bacin ran daya ke ciki bai hana shi jin dadin abin da take mishi ba, tini yaji bakin cikin Amal ya fara raguwa a ranshi yana nitsawa wata duniyar suna cikin wanann yanayin ne sai wayan shi ta fara ringing guntun tsaki yayi domin kuwa baya son wani abu ya katse mishi nishadin daya ke ciki tare da matar shi abida mace me mugun kawaici da hkr a wajen shi…..
Domin shiga grp din ABIN DA CIWO sai kumin magana ta wannan number 08109202921
ABIN DA CIWO*
Written by:oum zuhriyya
_duk wacce take so ta shiga grp din wannan novel din me suna *ABIN DA CIWO* tayi min magana ta wannan number din 08109202921, iya comments ɗinku iya typing di nah, wannnan lbrn ya kunshe abubuwa da dama kamar su makirci, sharri, dana sani da dai sauran su_
Page 2
Najib
Dag’a ta yayi daga jikin shi tare da duba waye me kiran shi.
“subhanallah” ya furta tare da d’aga call din dayake kara shigowa wayan shi.
“Assalamu alaikum Abba ina wuni”
Ya furta zuciyar shi na bugawa kadan kadan domin kuwa yasan zai sha fada a wajen Abba ba kadan ba, duk da laifin da Amal ta mishi babba ne amma yasan bai kamata ya dake ta ba a matsayin ta na matar shi ta sunna.
“Kasami ni a gida yanzun nan, ka bar duk abin da kakeyi”
Kittt Abba ya kashe wayan.
cikin son jin gulma irin na abida ta matso jikin najib tare da cewa
“Habibie lafiya Dae? Waye ya kira ka?”
Guntun tsaki yaja kamar bazai bata amsa ba sai kuma yace, “Abba ne yake nema na”
Har tana taune harshen ta tsaban gulma tace “Allah Dae yasa ba takardan ta zai ce ka kai mishi ba”
Kafe ta yayi da manyan idanun shi masu cike da kwarjini .
Shan jinin jikin ta tayi ganin irin kallon dayake mata sai ta katse mishi kallon da cewa
“wlhh ina tsoran zuciyar Abba, dan Allah yaya idan kaje ka sakaye laifin Amal, Koh ba aure tsakanin ka da Amal ae nan kam gidansu ne. bani son abin da zai raba zumunci ne shiyasa kaga duk nabi na damu wlhhhh”
Sa kai kawai yayi ya fice daga gidan batare daya ƙara ce mata k’ala ba.
Yana fita ita kuwa ta kai ma fuskar ta mari tana cewa
“na cika baran barama wlhh, zan barar da aeki na da kai na garin shegen son jin gulma irin nawa”
Abba
“Najib matar ka kuma ‘yar uwar ka Amal ta zo gdn nan dazu cikin kuka da fuskar ta duk a kumbure, shin zamu iya jin abin daya kawo ta gida, domin kuwa tace mana kai ne ka ce tazo gida”
“Eh Abba nine nace Amal ta zo gida”
Shiru palourn yayi. Amal in banda zare idanu ba abin da takeyi
Hajiya mama ne tace
“cikekken bayani mukeso muji daga bakin ka najibullah”
“Kamar yadda na fada muku yanzu Abba Ni ne nace tazo ta, Abba daga aure na da Amal zuwa yanzu ta zubar min da ciki a ƙalla sau uku kenan”
Shiru yayi kamar me tinani domin abin yana kara cin zuciyar shi kamar yanzu ne ta mishi laifin.
Juyuwa Abba yayi yana fuskantar Amal tare da cewa “Amal anyi haka?”
Gyada kai tayi sannan ta fara magana cikin rawar murya tana cewa
“Abba Ni wlhhhh ban sani ba kawai dai idan na daina ganin al’ada na na kamar wata biyu sai ya kawo min wani tsinke yace min na saka a cikin fitsari na idan na saka sai yace min wai ina da ciki idan ya kalla jikin tsinke yaga layi biyu, toh Abba idan akayi haka da wata daya kuma idan al’adan nawa ya dawo sai yace min wai na zubar da ciki”
K’arashe maganar tayi tana sakin kuka me cin rai, kukan da kana ji kasan iya gaskiyar ta take fada musu.
Hajiya mama data ke zaune a wajen abin ya mugun daure mata kai har ta rasa ma abin cewa game da case din
“Yanzu dai ke Amal kina nufin bada gangan kike zubar da cikin naki ba?”
Abba ya fada yana tsare ta da idanun shi.
Cikin rawar murya ta kuma cewa “wlhhhh Abba Ni bansan me yake fada ba iya abin dana fada maka shine iya abin dana sani wlhhhh”
Tabbas Abba yaso ya gamsu da bayanan nata amma kuma yaran yanzu abin tsoro ne, kallon shi ya maida kan najib sannan yace “najibullah ya akayi kake sanin cewa ita Amal ce take zubar da cikin nata bawai kawai tsautsayi bane?”
Wani murmushin takaici najibullah yayi sannan yace “Abba kaga da farko Dae ranar wata jummu’a da bazan manta ba ina tare da abida wajen karfe 12 na dare mukaji motsin Amal tana buge buge da kuka kamar ranta zai fita. Muka shiga dakin ta tinda ga bakin kofa muka ci karo da jini a malale a cikin dakin nata ga kuma kwallin hollondia a gefen ta, cikin matukar razana da rudewa muka Kaita asibiti, sai Dae muna zuwa asibitin bayan an duba ta tare da gyara mata jiki muka sami mummunar labari daga bakin Dr cewa wai tayi amfani da wasu pills ne masu ƙarfin gaske na zubar da ciki a cikin drinks, kaga kuwa ita ta zubar da abin ta tinda shigowan mu dakin na ta mun tarar ta gama sha knn ta fara wannan buge bugen data ji azaba.
Sannan na biyu kuma akwai lokacin data ƙara samun cikin Abba tin da na fahimce yarinyar nan tana da ciki na hana ta zuwa makaranta nace ta bari sai za’a fara waec na mata registration sai tayi exams din dalili na nayin haka kuwa shine ina matuƙar tsoran kar kawaye su kara zugata ta kuma zubar min da cikin dana jima shekara da shekaru ina nema, ai kuwa duk wannan kulawan dana ringa batan a banza. Domin kuwa na dawo daga aiki knn na same ta kwance jini yana fita a jikin ta tana kuka kamar Dae yadda tayi a wancan lokacin cikin fargaba na dauke ta na Kaita asibiti ina tsaye akan ta tare da Dr din dayake duba ta, Abba wlhhhh tallahi yana bude gaban yarinyar nan sai ga wasu pills na zubar da ciki da tayi inserting Koh narkewa basu gama yi ba, a wannan lokacin ji nayi kamar na sake ta tsantsan takaici amma haka na jure Koh ma ku ban fada ma ba nayi Dae mata faɗa tare da nasiha ta nuna min ta dauki fadan danayi matan ta kuma bani hkr amma Abba duk a banza domin kuwa a wannan karon ma pills din na kamata dasu a kasan pillow da take bacci kuma ga hollondia din ta zuba a kofi sai Dae ban kai ga sanin tasha maganin ba ko kuma zata sha ne na shigo na kamata ohon mata, Ni kuma shine zuciya ya ɗebe Ni nahau dukan ta domin kuwa duk wa’azin dana mata bata dauka ba knn. Shekara goma ina neman haihuwa amma Allah ya bani ta wajen ta saboda bakin hali irin nata shine take min asaran babies Dina, ga rashin kunya da takeyi ma abida kamar sa’ar ta duk hkr da kawaici irin na abida amma abin ya fara Kaita bango”
Salati Hajiya mama dake zaune a gefen Amal ta narka sannan tace “duk hkr irin na abida da kawaici irin nata kike so ki kure ta, anya lafiyan ki klau kuwa Amal?”
Karshe maganar yayi da wani irin daci a Muryar shi domin kuwa har wani b’ari yake yi tsantsan takaici.
A wannan gabar kam Abba hnklin shi yafi karkarta ga maganar najib yana kuma mamakin yaushe Amal ta falle har haka da zata zubar da ciki har kusan uku . Duban shi ya mayar kan Amal sannan yace
“Amal duk abinda yayan ki ya fada gaskiya ne?”
Gyada kai ta kara yi a wannan karon ma sannan tace “Abba amma wlhhhh bani nake zubar da cikin ba”
Hajiya mama ne tace “toh yanzu ke Amal wani hujja zaki bamu da zamu yarda dake. Idan mun ce k’ila cikin ki na farko abu aka zuba miki a hollondia baki sani ba kika sha Toh cikin ki na biyu fah, da aka sami pills din da kikayi inserting basu gama narkewa ba a jikin ki, shima cewa zamuyi bude ƙafan ki akayi aka zuba miki?”
Abba ne ya cab’e zance da cewa “Nima tunanin dana keyi kenan, miye hujjan ki na bake kika zubar ba?”
Cikin Muryar kuka ta kuma cewa
“Abba bani da hujja iya abinda na fad’a muku tun farko sune iya abinda nasani, kuma wlhhhh Abba daya min duka yanzun ma bansan waye ya ajiye min magani a daki na ba kuma wlhh bansha hollondia daya ke tunanin nasha ba”
“Toh Ni a matsayi na mahaifin ku dukan ku zan muku nasiha da kuji tsoran Ubangiji kusan akwae mutuwa da hisabi, ban yarda ba ban amince ba najib naji ka ƙara dukan Amal domin kuwa yanzu matsayin matar sunna take a wajen ka ba kanwa ba, ke kuma Amal kiji tsoran Allah ki kare mutuncin auren ki idan kinsan ke kike zubar da cikin nan kiyi ma kanki faɗa ki daina yin kafin kiyi dana sani mara amfani, na dawo kan ka najibullah ka ɗauke matar ka ku kuma gida kar naji kar nagani kuyi hkr da junan ku”
Hajiya mama ne tace
“Abban najib Ni kumaa Dae ina nema wani alfarma”
“Name kenan?”
Abba ya fada yana kallon ta.
“Ina so a bar min Amal anan na kwanaki uku zan dan gyara ta tinda kaga bari har uku tayi amma basu fada mana ba kuma jikin ta yana bukatar gyara”
“Ku dai mata ba’a raba ku da qaqaleqaqale, ae yanzu cikin nata bawai zubewa yayi ba tinda tace bata sha hollondia ba kuma babu wani jini a jikin ta, shi Dae najib zuciya ne ya ɗebe shi ya hau dukan ta”
Sai yanzu najib ya tuna fah da cewan tabbas yanzun ba jini a jikin nata.
Hajiya mama ne ta kuma cewa, “duk da haka Dae a bar min ita din dan Allah na kwana ukun”
Abba ne yace to yanzu kam izinin mijin ta zaki nema.
“Murmushi najib yayi yana sosai Keya sannan yace, Hajiya mama an baku sati guda”
Godiya Hajiya mama tayi tare da kuma cewa “rana ita yau sai kazo ka dauki ta ko kuma Allah Dae yayi muku albarka ya baku zuri’a me albarka”
Da Amin suka amsa dukan su sannan najib ya musu sallama ya tafi gida.
Abida
“Na rantse miki da Allah kawata ta kuma shan hollondia din, dan yanzu haka kam tana gida ya Kad’a shegiya ta zama ba ciki ba miji. Har Ni wannan ta tsitsiyar yarinyar zata aura ma miji, AE kadan ta gani alqawari ne sai na sa najib ya tsane ta kuma wlhhhh sai ta rasa yadda zata saka rayuwar ta tinda tace dani zata buga sai na tabbata ta zama abin kwatance a idon duniya”
Horn din mutan shi da abida taji ne yasa tayi saurin katse wayar ba tare da ta gama fadar abin da take faɗa ba.
Add Comment