Abinda Ka Raina Hausa Novel Complete
ABINDA KA RAINA
*PAGE1*
Bismillahir Rahmanir Raheem****
…………
Kyakkyawan surayi ne na hango kwance akan Sofa, dag ashi sai fara k’al din singlet da wando 3 quarter ,sumar Kannan nashi tasha gyara kamar wata mace. Irin yadda ya ke baiwa sumarshi tsananin kulawa da tattali, sumar sai kyalli takeyi saboda kyawun da tayi har daukar Ido take kasancewar sa fulanin asali.
Kunan Zuciyata Hausa Novel Complete
Santala santala kafafunshi ya É—aura asaman karamin table glass d’in da yake a kusa dashi yayinda hannuwansa rike suke da system ya dukufa yana dubawa wanda zai tabbatar maka da cewar yana tsananin Jin dadin abunda yakeyi din, Kuma mai matukar mahinmancine a wurin shi, agefe kuma wayoyinsa ne zube akan sofar wad’anda akalla sun kai guda 4 duka manya manyan gaske.
Murmushi yaketa dokawa shi kad’ai a ranshi kamar Wanda yake tareda wani ko Kuma Wanda aka fadawa wani abu da yake matukar son ji. {Dr AHMAD} Kenan !!!
Kyakkyawan surayi ai tashen kyau ,kudi, ilimi, natsuwa ,da wani irin kwarjini da haiba. Shi mutum ne {classy and classic} na tabbata duk Wanda ya kalle sa sau 1 sai yayi marmarin Kara kallonsa saboda ba irin su ne a kewa kallo daya ba a dauke Kai, duk macen da ta kallesa sai tayi fata da burin mallakarsa ,sai dai kashhh! Ahmad yace shi mijin nace d’aya ne rakkkkk……..!
Yayin da dubban yan mata suke ta kawo mashi hari ko yaya zai kare dasu kuwa??????
Dr AHMAD abokinsa d’aya ne rak tun na zamanin kuruciya saboda mugun miskilancin sa ma bazai bar shi yayi yawan abokai ba sannan ba kowane zai iya jure halin nasaba inba kamar MUKTAR ba da yasaba dashi ciki da Bai saboda atare suka taso avtare Kuma sukaje kasar CHICAGO karatu!!!! Muktar likitan fata ne yayinda DR AHMAD yake likitan zuciya!!!
Wayar shi ce ta katse mashi hanzarin abinda yakeyi, kamar bazai daga wayar ba dan yayi tunanin yan matan da suke yawan damunsa ne kullun rana ta lillahi , yana jin wayar tana ta burari bai daga ba har 5miscall sai a 6 dinne ya jawo wayar, sunan My man ya gani ya na yawo a saman screen na wayar tashi yasaka shi amsa wayar ba dan ya shirya ba, dan yasan muktar ba kyaleshi zai yiba har sai ya daga zai samu salama awajen shi.
“I am sorry my man” ya furta cikin melodious voice dinshi. Tin kafin muktar din ya samu abun fada Ahmad yace “dady is calling me ” dipp ya yanke wayar batareda yajira jin abunda muktar din zai fadaba …!
Wayar dadyn ya daga tareda yin sallama. Cikin tsananin fusata dadyn ke fadar” yanzun Ahmad ni zaka mayar mutumin banza??? Karasa Wanda zaka yiwa wulakanci da rashin mutunci Sai ni??? Saboda Banda daraja da kima a idanunka??? To kome kakeyi kazo yanxu part dina ina jiranka” difff dadyn ya yanke wayar yayinda yabar Ahmad cikin tsananin tsoron yadda yaji muryar baban nasa kamar ta zaki da tsananin hargowa da Fada. “Ohhhhh dady why????? Mekuma nayi yanxu fisabillahi???? meyasaya a ke son takura mini? Wai dole sae nayi wani aure yanxu bayan I’m just 30yrs now Kuma ni har yanxu ban ga macen da ta kwanta min a rai ba. in dan ma auren zan yi nafi son larabawa!!!”
Cikin tsananin hanzari ya jawo jallabiyarsa yasaka yasanya takalmi yafito tareda daukar phone guda 1 ya fice a matukar hanxarce kamar xai kife saboda Bai manta yadda yaji muryar mahaifin nashiba.
Zazzaune ya sa mesu afalon dadyn. Ummy, dady sae autar su Rukky.
Da sallama dauke a bakin shi ya shiga dakin yayinda daga Ummy har dady ba Wanda ya amsa saima uwar harara dasuke binshi da ita kamar idanuwansu xasuyi aman wuta, rukky ce kawae ta amsa sallar tashi .Kara Shan jinin jikinashi yayi ya Kara rusunar da kanshi yana gaidasu Amman har yanxu Babu Wanda ya tanka mishi acikin su, tabbas yau al.amarin nasu Mai girmane inji Ahmad.
Saida suka kwashe kusan 20mins falon ba motsin komae saina saukar numfashinsu sai kuwa na fanka da air condition din da ke adakin …. Dadyne yayi gyaran murya yana Mai cewar ,
“Hakurina ya kare akanka Ahmad nagaji da raina mana hankalinda kakeyi Dan haka yau dole ka pada mana wace yarinya kakeso? Mu nema maka aurenta?? Tabbas na gaji aure xanyi maka, arazane sosoae Ahmad ya dago kanshi yana duban dadyn da idanuwanshi dasukayi matukar jaa kamar xai fashe masu da kuka acikin xuciyarshi yake Kara maimaita Kalmar aure da dadyn ya Fada kamar shi??? Ace wae dole sai anyi mashi aure kamar na dole???{God for bid}ya Fada acen kasan xuciyarshi.
Dadyn ya cigaba” ka kalleni da kyau abnda na Fada maka imean it…..! Dan na kura Kai bakasan idona idan kyaleka xa ae saika tsofe sannn xakayi auren ba abnda kakeba mahinmanci sae aikin ka, maxa ka padamin ina sauraranka”
Ahmad inba innalillahi ba abinda yaketa ja axuciyarshi shidae wallahi ko kashesa za.ae baida wacce yakeso balle akaiga maganar wani aure .dadyne ya katse mashi dogon tunaninda ya dauko “Kai fa muke saurare Dan inada abinyi ”
Cikin shagwaba ya fara magana “please dady akaramin lokaci nayi alkhawarin xan kawo maku matar aure da kaina nidae banada ra.ayin ko wace mace ayanxu dady asalima ninafison auren balarabiya.
Wlh karya kakeyi ahmad karka Rena mana hankali mugaji da wann jiran gawon shanun kajiko aure yanxu lokacin yinsane yayi insha Allah. dady yace “fine munfita hakkinka amatsayinmu na iyayenka mun zaba maka matar da ta dace da Kai sann ba shawara bace *UMURNINE* .
afirgice yake kallon dadyn saboda duk yayan abokan dadyn bawani Yi masa sukayi ba gsky he don’t like them any more!!!!.
Bakowa bace wacce muka zaba maka sae face YAR UWAR KACE, JININ KACE,KANWAR KACE JIDDACE diyar uncle Dinka SULAUMAN na bagaggadi ryt?????????,wata iriyar muguwar kidima Dr AHMAD yayi ina baxai taba yuwuwaba wallahi kamarshi??? Duk kyanshi?? Duk kudinshi??? Duk iliminsa?? Arasa wacce za.a hadasa da ita sae wata jakar yar kauye. Kayau???kauyenma irin na bagaggadi??? Tabbas ya shiga ukkunshi kuwa .
Ummy tace dubu dae ka shiga ba ukku ba ,wann ya tabbatar mashi da cewar maganar ba.a xuciya yayi ta ba abayyane ne, dady ne ya cigaba” Kuma ahakan da take zaka aureta ka xauna da ita Kai harma ta Haifa mka yara,sannn karka manta idan ka xagina bagaggadi nida uwarka ka xagina don cenne tushenmu kaima cenne naka.
Add Comment