Littafan Hausa Novels

A Sanadin Direba Hausa Novel Complete

A Sanadin Direba Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

A SANADIN DIREBA

 

Book 1

 

Free book

 

Shatu wai nikan bazaki fito ba ne sai munrasa kallon yauma. haba ke kullum sai kinsan yadda kikayi muka muka makara. cikin wata sanyayyar murya me dadin sauurare naji wacce ake kira da shatu tace ganinan fitowa yanzu ke wlh saude bakida hakuri. wacce akakira da saude tace eh naji kede fito mutafi Dan nasan yanzu maa mun rasa wani wasan. Tana rufe baki saiga wata kyakykyawar matashi yar budurwa wacce a kallo daya bazamuce mutum bace saboda wani sihir taccen kyau datake dashi maa shaa Allah cewar saude. Shatu tace to ai sai mu han zarta tafiya karkisa na rasa abunda zai kaini wannan gurin.saude tayi murmushi tace aikoda naji Nide nasan wannan kwalliya da badan haladu akayi taba.to Allah yasa kwalliya. Tabiya. Kudin sabolu audu yazoshi karya karya miki. Alkawari. Nanda nan fiskar shatu ta sanja ranta taji ya baci duk dade kamar addu’ah taji sauden ta mata. Saude ko ganin sanjawar qawar tata sai taji babu dadi takarasa kusa da shatu ta kamu hannunta batace komiba suka karasa can cikin gidan kasar wata bishiyar bedi inda suka samu tatu tanata aikin hada fura sukayi sallama cikin nitsuwa suka durkusa har kasa sukace. a tare tatu barka da wannan lokaci sannu da aiki tatu ta dago ta amsa musu sallamar tace sai yanzun kenan aka gama shirin. tafada. Tana me. Kallon yar tata da da aminiyarta Kansu a kasa sukace eh tatu zamu tafi. tace to Allah ya tsare kuma banda wasa a hanya banda yawan kallon mutane. ta juyarda kallonta kan saude tace banda kula samari musamman bakaken bakin RUGAR USMANU. Atare zuciyar su ta buga suka kalli juna suka dauke kai a tare gudun fallasuwar sirrinsu saude tariko hannun shatu tace ma tatu in shaa Allah zamu kiyaye tatu tace to Allah ya kiyaye hanya yadawo daku lfy bada kai dare a hanya atare suka mike sukace to tatu. Aiko dama shatu Allah Allah take su fita gidan dan hankalinta gaba daya baya tare dasu cikin sauri suke tafiya duk da Sauri a ta fiya ba halinsu bane.

 

Abinda Ka Raina Hausa Novel Complete

duk inda suka wuce sai anbisu da kallo saboda kyawawan halayyarsu da kuma kyawun halittarsu duk Dade babu marasa kyau a wannan RUGAR ta BELLOJI saboda ko acikin fulanima sudin daban suke wajan kyau suna cikin tafiya har sunyi nisa sai ji sukayi ana musu sallama ta bayansu jin wannan sallama kawai yasa shatu jin ranta yayi duhu bugun zuciyar ta ya sanja saboda tawa iriyar kiyayya take ma haladu wacce ita kanta basatan yawarta baa. saude taso ace ta tsaya koda gaisawace suyi amma tasan bazama ta fara wannan gan gan cinba itade yazama dole ta tsaya. Ta juya cikin sakin fuska ta amsa masa hade da gaidasa inaa shikan yayi nisa wajan bin sahibar sa kallo wacce tunda tafara tafiya batako juyaba saida tasha kwana sannan haladu ya sauke wata wa halalliyar ajiyar zuciya. Yace saude tundazo ko nake jira kafun natafi duk da nasan na makara nakasa tafiya.yafada cike da rauni acikin muryar tasa saude tace eh kasan halin qawar tawa kafun ta shiryama aiki ne yace hakane to ya zancammu kinsan lokaci yanata kara towa kuma baya jira gashi har yanzu banji daga gare koba saude tace hakane amma ka kara min lokaci kaga yanzu tamin nisa kuma nasan bata son tafiya ita kadai sannan yakamata ace kaima zuwa yanzu kana wajan shadin. Yace hakane bari naje nadau sabdata saumun hadu a can.saude tace fatan Nasara yace kisa a ranki danni akayi shatu. saude tayi murmushi kawai batace komiba ta juya domin ci gaba da tafiya. baiwar Allah shatu fatiya kawai take babu ko waige saboda yadda take jin zuciyar ta ko sauden bata son gani tana shan kwana tasamu waje akan wani dutse ta zauna domin baza ta iya tafiya ita kadaiba da side saude tasan yadda zatayi. Aiko saude ta shawo kwana ta hango sahibar tata fuska a hade tayi murmushi kawai ta karasa can kusa da’ita tace to tawajan audu tashi mutafi ko aiko nan take ta sake fuskarta hade da murmushi me kawata fuskarta da dimple dinta me zurfi da fadi ta kamu hannun saude tace Allah ameen sahiba ta Allah yakarbi Wannan baki naki. Kawai kallonta saude take cike da tausayi amma ta kasa cewa komi. Shatu ta bude baki ga wushir yarta siririya tace taho muyi sauri nasan yanzu yanacan yana baza ido ta inda zai hangoni. Saude tace to muje suka ci gaba da tafiya har suka karasu wani babban fili amma yacika sosai da mutane babu masaka tsinke dakyarde suka samu wajan zama suma domin kallon shadin duk da har anwuce zangon farko anfara na 2 hankalin shatu yatafi can wajan bakin da suke zuwa kallo wajan zamansa da abokana Sa take kallo amma babu shi balle abokanansa take taji hankalinta ya tashi tana shirin kuka idonta a rufe saiji tayi wata sanyayyar iska tana feso mata a saitin zuciyar ta da wani irin sauri ta bude ida nunta aiko karaf sai cikin idanun junansu a take sukaji wani irin sanyi yana kwaranya a cikin da wajan gangar jikinsu yaza mana basa gani da jin komi sai bugun zuciyar su shatu tayi karfin halin janje NATA idanon a kan audu wadda shikuma ya kasa hakan aransa yake rokon Allah yasa shatu rabonsa CE domin rashinta Dade yake da rashinsa a doron kasa. Shatu kuwa anata ran takejin akaf fadin duniya babu me rabata da audu saboda koma miye ita a hakan take son abunta. Sai sakin murmushi takeyi ita kadai kanta a kasa amma tanaji kaifin idanun abun sonta suna yawo a ko wacce gaba da jijiya dake jikin taa. batare da sun San yawan lokacinda suka dauka a hakanba saiji sukayi ana ihu da tafi fir git suka dawo hayya cinsu Ashe wai har angama shadin babu abubda suka kalla acikin wasan kamar kullum daga haduwarsu.

 

Aduk karshen shekara wato a kaka lokacinda da duk wani fulata yake dawo da amfanin gonarsa gida ana shirya wasan shadi wadda samari zasu hadu akan son mace daya za’ayi wasan shadi duk wadda yaci yaci Wannan gasa tofa dashi za’a daura mata aure koda kuwa ba shine abun sontaba tofa saide tayi hakuri domain Wannan al’adar ita akeyi tun iyaye da kakanni. ganin yadda shatu tafada duniyar tunani yasa saude kamu hannunta tace tashi mutafi gida kindeji abunda tatu tace mana. Shatu taja wata duguwar ajiyar zuciya tace yanzun ahaka za’ata tafiya a Wannan gari namu babu wani sanji.uhmm inji saude tace gashinan de kina gani yanzu ma lawandi shine yayi Nasara akan sanini wadda hakan yana nuna mana hanne tazama matar lawandi duk kuwa da yawan tsanarsa da takeyi.shatu ta daga ido da sauri ta kalli wajan zamansu audu idonta zai fara fidda ruwan hawaye yadaga yatsarsa guda daya ya nuna mata sama ma’ana Allah yana tare dasu. ta jinjina kanta ta tashi ta kama hanyar gida aranta tabari tana kumawa zata tambayi tatu akamme ake Wannan shadi sannan miye dalilin da yasa suka tsani yan RUGAR BELLOJI.

 

To saimu bi bayan shatu domin jin wannan amsar sannan waye wannan audun?

 

Comment fisabilillah sisters

 

 

Add Comment

Click here to post a comment