Littafan Hausa Novels

Mijin Malama Hausa Novel Complete

Mijin Malama Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

MIJIN MALAMA

 

 

Nimcyluv Sarauta

*_Arewabooks@Nimcyluv_*

 

*1……*

_Allahamdulillah! All thanks to Allah_ _Subhanahu wata’ala, for the opportunity, and ability to start this book MIJIN MALAMA. Am back_ Bayan kammala littafin *IDAN BA KE* labarin Yaa Sheikh da Halisa. Nasan You have been waiting for so long, Ma sha Allah i really appreciate for the love’s nd care, i wnt to let everyone know, wannan labarin ya fi ƙarfin shekara guda a zuciyar Sarauta, ban sani ba, but I knw one thing duk wanda bai karanta zai yi missing. No complain You guys make me proud Sarautar love’s you.

 

 

A lullume garin yake, sakamakon yanayin sanyin da ake ciki, wanda ya fara tun watan Ogusta zuwa watan da ake ciki na Nuwamba. Hazo ne ya yi wa samaniya ado, ga iska mai ƙarfi dake ta shi tana ƙara haddasa sanyin shiga jika, yanayin hunturun daban yake dana ko wacce shekara. Mafi yawanci lokuta a irin wannan ƙarnin manyan cututtukan da suke gaba da sanyi suka fi ta shi, irin su mura, asthma, sikila, ciwon ido, lamoniya, bushewar fata, haɓo, hatsarurruka a titi da sauransu.

Angon Mata Biyu Hausa Novel Complete

Daidai by pass na First bank motar su ta tsaya akan titi saboda go-slown da hazon ya haɗa, tafiyar 9min (4.8km) ce tsakanin Lodge Road zuwa Aminu Kano teaching hospital. A hankali ta ɗago kanta dake sunkuye tun shigarta cikin motar, fararen Idanunta dake maƙale cikin farin Glasses mai ɗauke da photochromic ta watsa akan titin a nutse. Da ƙyar ta fisgi numfashi saboda a ƙirji yake tsaya mata.

“Jeederh!”

Latifa dake zaune a mazaunin driver hannunta riƙe da string motar ta kira sunanta, tasan ta ji ta sarai don haka bata buƙatar ta amsa, Latifa ta ci gaba da cewa. “We live by our own destiny, kuma Allah na son mu haka, You should not worry about that”

Sai a lokacin Majeederh ta ɗan juya kaɗan jikinta a kame tana curewa waje guda, ji take kamar ita kaɗai ke jin sanyin, duk da cewa Latifa ta rufe Glasses ɗin motar ta kashe a.c.

Baki ta buɗe ta cikin liƙab ɗinta za tayi magana,sai kuma tayi shiru can dai ta ce.

“Worry?” “Kamar haka na ce” cewar Latifa “Kada ki yaudari kan ki dole kina cikin damuwa, duk yadda ki ka kai da zurfin cikin ki, nasanki tsayin shekaru talatin da biyar, komai da komai naki na sani, After that, I am your friend”

 

Malama Majeederh jin ta kawai take bata fahimta, gangar jikinta ce kawai a motar, tunaninta, nutsuwarta gabaɗaya sun yi ƙaura daga gare ta. Kalaman Abbu su ne suke mata amsa kuwwa! A kunnuwanta.

Latifa bata gaji ba domin ko Aku zata shafa mata lafiya. “Ki zo ki aure Mijina Majeederh zamu zauna lafiya,na gaji da ganinki haka ba aure, na kasa jure yanayin ke ake faɗawa magana ni nake jin zafinta a zuciyata”

 

Cikin sauri ta juya ta kalli Lafita a ranta tana ayyanna girman wautar Latifa, corner Lafita tayi da kan motar tare da sulalewa gefen gwalta ta shiga cikin asibitin Aminu Kano kai tsaye!

 

“Yes,Malama Majeederh Abdul’aziz Khan” ta ci gaba da driving tana faɗin “Sweetheart ya amince zai aureki, Kinga amintarmu zata sake ƙarfi, ba zan taɓa ɗaukarki matsayin kishiya ba, ki amince Please Please Jeederh”

 

“Ke da mijinki kuna buƙatar ganin psychiatrist” Malama Majeederh ta furta a nutse cikin sanyin murya. Dariya kawai Latifa tayi tana girgiza kai, a ranta ta saka dole tayi forcing Jeederh ta auri mijinta, parking tayi a inda aka tana da domin ajjiye motoci. Ita ta fara fitowa hannunta riƙe da key ɗin motar sai waya, ganin Majeederh bata fito ba ya sanya ta zagawa just to find what’s happening. Hannu Majeederh ta saka ta buɗe murfin motar, tare da zuro ƙafarta waje.

Sai a lokacin Lafita ta lura da yadda farar ƙafar Majeederh ta kumbura har wani ƙyalli take, yanayinta ya sauya gabaɗaya yadda ta kumbura ta buɗe zai bawa kowa mamaki. Da ƙyar ta yunƙura ta fito daga motar can ƙasan ranta tana kiran sunan ALLAH.

“Kamar mai suger? Wannan kumburin ya yi yawa Majeederh, Mami ta gani? Abbu ya gani?” A duk jerin tambayar da Latifa taiwa Majeederh ba wacce ta amsa ko inda take bata kalla ba ta nufi ɓangaren data zo.

 

Da yake Dr Jamal ya san da zuwan nata domin shi ya bata appointment ya sa kai tsaye ta kira number shi, yana ɗagawa ya ce ta shiga. Latifa ta miƙe zata bita zuwa office a kame ta ce. “I need Privacy”

“Take your time” cewar Latifa tana watsa hannu. Brown ɗin Abaya ce a jikin Majeederh, wacce ta amshi fatarta, sai babban hijabi daya sauka har ƙasa wajan ƙafafuwanta hannunta sanye da safa, fuskarta rufe da liƙab ga Glasses ɗin da ya yiwa idanuwanta murfi. Babu abinda ake gani a jikinta sai ƙwayar Idanunta ƙafarta kuma hijabi ya rufe. Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, budurwa ce bata taɓa aure ba shekarunta Talatin da biyar ciff a duniya, cikakkiyar Malamar addinin Musulunci ce, ɓangaren boko ba ba a barta a baya ba.

Zaune ta samu Dr Jamal suka gaisa cikin fara’a ya ɗakko wani babban file ya ajjiye gabanta tare da zaro x-ray ya ɗaga sama ya ce.

“Finally, bayan tsayin shekaru biyu yau mun samu damar gano abinda ke damunki”

Wahalallan numfashi ta sauke a ɓoye,tana yiwa Ubangiji kabbara.

Ta juya idanunta alamar tana son jin me bincike ya nuna? Dr Jamal ya ce

“Mun sha wahala, ko na ce muna kan shan, sai dai duk wacce zamu sha bayan taki take”

 

Idanunta a ƙasa ta harɗe hannu a ƙirji zuciyarta na bugawa da ƙarfi amma ba zaka taɓa ganewa ba, kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana cikin halin jinya. “Ƙari ne ya fito miki a ciki, shi ya haddasa kumburin cikin, shi ne kuma yake girma kullum a cikinki har wasu suke fassara ki, ya yi girman da sai dai ayi miki operation a cire, mun samu issues na wannan domin wata idan ki ka ganta zaki ɗauka ciki ne da ita wata tara”

 

“When za ayi operation ɗin?” Ta faɗa a taushashe ita kaɗai ta san halin da take ciki, bata iya barci ciwon ya ci ƙarfinta burinta a rabata da shi.

“Wednesday, In sha Allah ki zo gobe da yamma da shirin operation” Shiru tayi domin duniyar ce gabaɗaya tayi mata zafi, kamar ta ɗauki wuƙa ta soka a ƙahon zuciyarta haka take ji, rana zafi inuwa ƙona, gida babu daɗi waje babu, family babu, uban daya kawota duniya shi ne ya jefata cikin wannan halin ba zata taɓa yarda Uba zaiwa ƴar shi asiri bisa ƙudirin zuciyarsa ba sai akanta ta gasgata haka, tana rayuwa da asirin mahaifinta a jikinta tana rayuwa da baƙin tabon daya shafa mata wanda ba kowa ya san da hakan ba. “Malama Majeederh Abdul’aziz Khan!”

Dr Jamal ya kira sunanta. Ta miƙe tare da rungume ƙirjinta kamar yadda ta saba ta jima kafin ta ce.

“Thank you,Dr Jamal”

“Your Wlcm, Allah ya baki lafiya” she just smile and quickly leave the office.

Sai ta daidaita nutsuwarta kafin ta fita, tana zuwa ta samu Latifa na waya kallon juna su kayi tana jin Latifa na cewa.

“Wallahi taurin kai ne da Jeederh banda haka mene abin ƙin amincewa da aurenka Sweetheart?”

Ta cikin wayar Aliyu haydar ya sauke numfashi ya ce.

“Tana da gaskiya”

“Wacce gaskiya Beb? Ni da Majeederh ƙawaye ne mun yi trusting juna don ta auri mijina ai ba wani abu ba ne right?”

Murmushi kawai Aliyu ya sauke mata ta cikin wayar, dake waya biyu yake da su, ɗaya a maƙale a kunnenshi, ɗaya kuma a hannunsa idanunsa zube akan screen ɗin ya kafawa photon Majeederh idanu, gabaɗaya jikinta a rufe yake photon kuma tun tana makarantar Noor-Ul-Iman School.

Latifa jin Mijin nata Aliyu ya yi shiru ya sa ta ce.

“Kayi shiru, ko baka sonta?” A nutse ya ce

“Laɗifa Omar, abar maganar haka ya jikinta?” Ta juya ta kalli Majeederh wacce ta shige tana tafiya a hankali jikinta ya ƙara yin sanyi sosai..

“She’s critical condition, tana cikin mawuyacin hali bata son nunawa kawai don Allah Sweetheart kayi conversing nata ta aureka kaga sai mu zauna mu biyu”

Bai ƙara magana ba ya kashe wayar yana rufe idanu, bai taɓa ganin fuskar Majeederh ba, ko surar jikinta ko da yaushe a suturce take kaifin Idanunta shi ke ruruta masa abinda yake ji. “What kind of love is this? Ina Son ki Malama Majeederh Abdul’aziz Khan”

Kashe wayar Latifa tayi tasan Aliyu haydar baya ƙaunar auren Majeederh baya sonta bakiɗaya, ita ce ta takura masa har ya amince.

Da sauri tabi bayan Jeederh lokacin tana tsaye gaban motar jikinta duk rawa yake ta kifa kanta saman motar.

“An very sorry for keeping you waiting, muje ko?”

Jeederh bata kalli Latifa ba ta buɗe motar ta shiga, abubuwa da yawa suke damunta ga ciwon Limoniyarta dake shirin ta shi. Ganin yanayin Malama ya sanya Latifa jan motar da sauri Allah ya taimaka babu go-slow har suka isa Lodge Road.

Babu kowa a unguwar sai wasu samari guda uku wanda suka damu jama’a, tunda Motar su Majeederh ta tsaya samarin suke kallon motar, a kame ta fito hannunta riƙe da waya domin ko jaka bata ɗauka ba, cikin nutsuwarta da kamilalliyyar muryarta wacce ko Latifa sai tayi da gaske take jin me take cewa saboda sanyin muryar da jan aji irin na Malama Majeederh Abdul’aziz Khan bata fiye maimaita magana ba.

“Jazakallah-bil khair Latifa Omar”

“Ur welcome, bari na shiga gida sweetheart ya dawo tuni” jinjina kai tayi.

Jeederh na ƙoƙarin nufar gate ɗin gidan su ka ji saukar muryar wani yana cewa. “Karuwa an dawo ne” wani irin runtse Idanunta tayi, zuciyarta ta buga ƙirjinta ya riƙe nan take ta shiga kokawa da numfashinta.

Samarin su kayi dariya ɗaya daga ciki ya ce

“Maganar gaskiya Yusuf ya faɗa, ana fakewa da addini ana yawon karuwanci gari gari” cewar Kabiru.

Yusuf ya ƙara cewa “Babu mamaki idan ka cire hijabin jikinta tsirara zaka ganta, abun fa duk gaibu ne shi ya sa ban fiya yadda da mace mai hijabi ba, Allah ya isan Muslunci ke fa namanki ya halarta aci kuma…..,”

Kau! Kau! Kau! Aka ɗauke Yusuf da wasu kyawawan tagwayen maruka, Majeederh kasa motsawa tayi saboda riƙewar da bayanta ya yi ta shiga kiran sunan ALLAH. Latifa ta juya da sauri ganin Mijinta Aliyu Sufyan Alhassan ta ce.

“Ka barshi, shi da Allah tabbas yana ji kuma yana gani zai musu hisabi tsakaninsu”

Aliyu ya ture Latifa idanunsa ya rine jikinsa na kyarma ya ce.

“Zan ga uban daya tsaya maka, zaka maimaita maganganunka a gaban alƙali, how dare you insulate my wife like that?” Da sauri Latifa ta ce “Your wife, Aliyu?”

Sai a lokacin ya fahimci sakin layin da ya yi kamar zai tashi sama ya ƙwace key ɗin hannun Latifa tare da shigewa mota ya bar wajan.

Abun ya bawa Lafita mamaki sai bata damu ba tasan zafin zuciyar Aliyu baya iya saita kansa.

 

Malama Majeederh na shiga bedroom ɗinta toilet ta shige ta sakarwa kanta shower tun daga tsakiyar kanta har ƙasan ƙafafuwanta, bata damu da ciwon Limoniyarta ba hanyar da zata shaƙi iska kawai take nema, zuciyarta a cushe take.

“Allah kana kallo ban taɓa riƙe hannun ko wanne namiji ba, ba a taɓa riƙe hannuna ba, Ubangiji ka shiga cikin lamarin” duk yadda taso tayi kuka amma ta kasa. Latifa ta samu Mami a parlour ta ce “Sannu da gida Mami”

Wani irin kallo tayi mata ta ce “Kici gaba da biyewa yarinyar banza irin Majeederh, wallahi zata ɓata miki tarbiyya kuma zan kira mahaifiyarki na sanar mata” Latifa ta ce

“Haba Mami, a gida ku aibata Majeederh a waje ma haka? Ko tausayin ciwonta bakwa ji, mene laifinta?” Mami ta ce

“Yanzu ke ba a ɗakin mijinki ki ke ba? Shekarar ki goma da aure Ita kuma tana yawan barbaɗa” Ruma dake zaune ta ce

“Ni wallahi kallon mai ciki na kewa Majeederh haihuwa yau ko gobe”

Latifa ta ce “Ko a film da littafan hausa ban taɓa jin Mace ta samu ciki babu ɗa namiji ba, Majeederh ba zata taɓa aikata zina ba,ciwo ne kuma Allah yana iya jarabtar bawansa mumini da haka, i trust with all Majeederh Allah na tare da ita, rashin aure da wuri baya nufin lalacewar tarbiyyar mutum!”

Tana faɗin haka ta fice daga cikin gidan ko wajan Majeederh bata shiga ba.

Tun da Majeederh ta shiga bedroom bata sake fitowa ba, hatta shigowar Abbu ta ji amma bata fito ba, jama’ar gidan ba su damu ba Aaliyyah ce kawai ta shiga damuwa. Wasa wasa har ƙarfe biyu na dare ko abinci bata ci ba, lokacin Aaliyyah na zaune ta kasa barci ta miƙe a hankali ta fita zuwa bedroom ɗin Jeederh taci sa a yana buɗe, a durƙoshe ta samu Majeederh ta haɗa uwar zufa jikinta na rawa da karkarwa daga ita sai rigar barci. “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Anti Jeederh jikin ne?” Ta nufeta ganin kamar zata mutu ya sanya ta fita a gigice ta shiga kiran sunan ƴan gidan.

“Abbu, Mami, Anti Ruma, Raihana mun shiga uku Anti Jeederh zata mutu”

Kafin ka ce me duk sun fito tsakiyar Main parlour, Abbu fuska a ɗaure ya kalli Aaliyyah ya ce.

“Kirata nan”

“Ba zata iya fitowa ba” cikin tsawa ya ce “Ban damu ba, tama mutu mana?” Aaliyyah na ƙoƙarin juyawa sai ga Majeederh ta fito abinda basu taɓa gani ba shi ne hawaye akan fuskarta, ko mahaifin daya haifeta ba zai ce ya taɓa ganin kukan Majeederh tana babba ba sai yanzu.

Malama Majeederh ta zube a tsakiyar parlourn “ki faɗa mana mene yake damunki?” Cikin dauriya muryarta na rawa ta ce

“Abbu ƙari ne, haka Dr Jamal ya ce” ya kalleta yana son jin tausayinta amma ya rasa mene ya hana shi jin hakan..

Ta kasa daure ciwon ta ce “Ka tausaya mini Abbu” “ki tausaya kan ki Majeederh!” Cewar Abbu.

 

Ihu! Ta sanya a karo na biyu, tana ambaton sunan ALLAH. A wannan sa’in rayuwarta na cikin tsauni biyu ne, halin RAI ko MUTUWA. “Ya ALLAH” ta furta jikinta na rawa kamar an jona mata wutar lantarki. “Anti Jeederh mu je asibiti, idan ba a cire miki wannan ƙarin na cikinki ba, tabbas zai iya kai ruhinki zuwa kushewa”

“La’ilaha illallah!” Ta ce. Ba ta taɓa jin azaba da raɗaɗi irin na yanzu ba, kamar ana hura mata wuta a mararta haka take ji. Wani nishi ta yi mai ƙarfi, Idanunta suka kakkafe tana girgiza kai numfashinta na sama, Aaliyyah ta gigice ta kasa yin haƙuri kawai sai ta fashe da kuka “Kada ki mutu don Allah, kada ki barni Anti Jeederh” banda Aaliyyah ba wanda ya damu. Majeederh ta riƙe hannun Aaliyyah ta sake yin wani nishin mai ƙarfi wanda ya fi na baya sai ga kukan jariri ya cika parlourn, zuciyar Abbu ta buga, aka shiga kallon kallo jikin kowa a sanyaye, Mami tayi ta maza ta ɗaga Majeederh sai ga jariri ya ƙara sa faɗowa ƙasa, sai ihu yake.

“Mun shiga uku, MAJEEDERH haihuwa kika yi? Jariri nake gani haka? Babu aure babu miji ina aka samu ciki har nake ganin haihuwa?” Ba ta da amsa domin ita kanta ba ta tsammaci ciki ne a jikinta ba, bata taɓa kawowa ɗa take ɗauke da shi ba, me ya sa Dr Jamal ya ce mata ƙari ne? Yaushe ta samu ciki a ina kuma?. Cikin kuka Jeederh ta ce

“Ban sani ba, ban sani ba, ba ni da masaniyar ciki ne a jikina, ban san ɗan waye ba, ban san yaushe na samu ciki ba, ban taɓa aikata zina ba, wallahi wallahi ban san cikin waye ba, ban taɓa sanin ina ɗauke da ciki ba”.. Cikin fushi damuwa da takaici Abbu ya ce “Allah Ya isa….

Add Comment

Click here to post a comment