Littafan Hausa Novels

Abu Uku na Oum Aphnan Hausa Novel Complete

Abu Uku Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ABU UKU

 

Na..

Oum Aphnan

 

_Ina ma jama’ar musulmi na duniya barka da sallah,Allah ya maimaita mana na baɗin baɗaɗa_

 

Bismillahir_rahmanir_raheem

Page 1️⃣

 

______________

Sardauna crescent,Kaduna state.

10.23pm

 

“`WOO_GIRLS“`

 

Dare ne mai ɗauke da baƙar hadari ko’ina yayi shiru,sai wucewar ababen hawa jifa² .

Ilahirin mutanen kirki sun soma ɗauke ƙafa zuwa muhallinsu don saukar da hakarƙarinsu akan makwancinsu don huce gajiyar ranar,da tsammatan gocewar ruwan sama mai Albarka.

Sosai Iskar ruwa ke busowa gamida Guguwa gadai dukkan Alamu ana ruwa a kusa da wannan waje kuma daf ruwan yake da gangarowa wajen.

Wa Yafi Sona Hausa Novel Complete

Wawwaigawa nake a nutse don neman wajen da zan fakaice kafin wanann ruwan ya tsuge a kaina ,don bansan lokacin tsayawarsa ba ,bayan shafe tsawon sa’a guda ina jiran ‘yan adaidaita ,amma kwatakwal kamar an sharesu.

 

Can gefen hanya wata Dalleliyar mota na gani ƙirar marcendi GLK baƙa wuluk da ita , a kunne take , danjojinta sun haske ko’ina ,mamaki yasa Hankalina karkata zuwa wajen.

 

Aseem Matashi ɗan kimanin shekaru 37 ne zaune a mazaunin driver ya goya hannuwansa akan kambin motarsa ,yana kallon Budurwar da ta ke tsaye a gaban murfin motarsa ,tayiwa murfin motar rumfa.

Dukda dare ne amma fuskarta kamar madubi saboda makeup da ya dauka zauu! Fuska fa yasha Foundation dasu bronzer leɓe sai sheƙin jan Jambaki yake ido na farfari da gashin idon kanti.

 

Fuskarsa ba walwala irin na wulakantattun matasan masu kudi din nan ,ya dubeta

“Kikace daga nan ina zaki?” “Nop,bani da zaɓi sai inda kayi dani ,Ready to spend the whole night caring of this gorgeous buddy😉”

 

Ɗan caɓe baki yayi kadan wanda hakan ya dade da zame masa jiki ,ba wai yana yinsa don wulakanci bane sababben sa ne.

“Jeki ɗauko jakar ki to”

 

Wani juyi tayi mai jan hankali ta ɗan kada masa boobs ɗin ta kaɗan cikin sigar jan hankali kana tace “Thank You mr man”

 

Ta juya tana karkaɗa masa baya tana wani irin cat walking a tsakanin duhun daren da hasken fitilu ,har ta shige rumfar da ta bar ƙawayenta suna jiranta.

 

A galabaice ya koma yaraf ya kwantar da jikinsa akan kujerar motan damuwa kar ki tona ransa ,so yake kawai ya fashe da ihu ko zai samu sauƙin zugin ransa

 

 

Tasneem Da gudu ta shanyo shataletalen hanyar zata ɗauke hanyar Unguwar su ,har ta gifta ta hango mutum kamar Aseem cikin mota a buɗe. Hakan yasa tayi reverse a nutse ta faka motarta gaba dashi kaɗan ,kana ta fito cikin firi firinta irin na yara marasa natsuwa

 

Da sanɗa ta fara takowa har gaban motarsa ,ya zurfafa sosai cikin tunani yaji an doka ƙafa da ƙarfi ta daka tsalle ta zuro hannu ta cikin glass din motarsa ta kai masa wawiyar runguma

 

Ai baisan sanda ya washe bakinsa gaba-daya ba

 

“Tasneem how are you?😃” ya tambaye ta cikin washe duk haƙoran bakinsa

 

“Wallahi I’m fine…Dan Allah ji zazzafan motar nan” ta ƙare maganar tana dukan motar da hannunta.

 

Dariya ya ɗan yi irin na isassun maza ɗin nan

“Ban taɓa tsammanin ganinki ba ,daga ina haka?”

 

“Nima haka wlh ,nasha mamakin ganinka a daren nan ,kawai naga tsadajjen mota a fake ƙura na bulbuleta ,nace aah🥹ya za’ana wulakanta Sugar mota kamar wanann cikin ƙura,ashe Motar sugar daddy ne,nace No wonder sugar mota belongs to sugar dady….ahnnn sugar😘 You look clean and fresh wlh” ta kare tana kai hannunta kan hannunsa dake lulluɓe da gargasa,tana shafasa a hankali.

 

Waske maganarta yayi ta hanyar wulla mata wani tambayar “Ina zaki haka?”

 

“Wallahi nafito siyan roasted fishhhh🐟ne” ta wani ja sunan kifin irin na ‘yan duniyan University gurls ɗin nan.

 

“Uhmm fish…oh kifi?🤨 Interesting hakan yayi kyau”

 

“Eh wlh kifi😄 and I come fishing😉😅(Ta ɗan saki layi kadan da salon yarensu na en duniya ta hanyar cewa _l come fishing_ tana wani karkaɗa jiki ,sannan ta cigaba da cewa)kawai sai kuma nayi tsuntuwa ,kasan kaifa tsadane gareka😁ganinka sai mai rabo”

 

Ɗan haɗe rai yayi kaɗan kamar wanda yake son tuno wani abu .

 

“This reminds me ,ammm wannan sai ya tunamun ,in kinada lokaci gobe zamu hadu a Joint for lunch🍝🍸”

 

Ji tayi kanta yayi mata gingiringim ,tasan dama tunda ta hadu da aseem yanzu zata farfaɗo daga ƙishin kudin da take ciki.,don haka a take ta soma zabga masa kirari

 

“Oh sugar…sugar dady Allah ya bar Mana Kai ,arziki yayi ta tunbatsa yana kumburi kamar kumfar maliya”

 

“Yes and plz ki samo mun wata chick me kyau haka nan ,kyakyawa ,ƙashar ƙashar da ita kinji”

 

“Ahahaff🤗Bakada matsala ,my sugar😉komai kake so ai an gama kawai”

 

Murmushin saman lebe yayi kana ya buɗe aljihun motarsa ya ɗauko ɗaurin 500₦ mint ɗaya ya miƙa mata

“Oya ga wannan aje aci kifi”

 

Wani suwwa ta ɗauka tana juya ɗaurin dubu hamsin ɗin

“Kai Nagode” ta rungume Dubu hamsin dinta a ƙirji ta ɗauki hanyar inda motarta yake ,har tayi tako uku ana hudu ta juyo ta saƙa hannunta a siririn glasses din murfun motarsa ,Gamida sake Kiran sunansa

 

“Sugar dady?”

Aseem da ya soma danna wayarsa a hankali ya ɗago gamida amsawa da “Na’am”

Ya dauka tayi mantuwa ne zata fada masa wani abu abu

Kawai sai tayi masa blowing kiss ta sake cewa “Nagode sugar Daddy”

 

Murmushi yayi a wannan karon ba tare da yace mata komai ba yana girgiza kai ,halin Tasneem sai ita

 

 

_Ni kuwa nace cashi🤔! Bariki kumfar soso,Wai matashine ɗan shekaru 37 ‘yan mata ke kiransa da sugar daddy kamar wani tsoho….kuɗi kenan ƙumbar susa_

 

Da gudu ta ƙarasa cikin motarta saboda yanda ruwan ya taho da gudu

 

Shima a daidai nan tasa babes din ta dawo ɗauke da handbag dinta yaja Motar suka warwatse a wajen.

 

Wani wawiyar ajiyar numfashi YUMNAH ta saki ,gamida girgiza kai tare da Addu’ar “Allahu ka shirya mu”Kuma daidai nan taji ɗan sahu na faɗin

“Tafiya ne?”

 

Da sauri ta soma daga masa hannu cikin zaƙuwa ,ba space ma a baya ,amma ita wacece da bazata maƙale a gaban ba ,barinma yanda garin yake ƙoƙarin narkewa a tsohon daren nan,Gashi abinda ta fita nema bata samo ba.

 

Tunda suka fara tafiya ta zabga tagumi ba abunda take tunani sai Tsohuwar ta ,dake cikin halin matsanancin ciwo gashi ta gama karade gidajen masu kudin Kaduna ta kasa samo kudin maganin da za’a mata ,wasu ma masu gadi hanata shiga sukeyi .

 

Cikin wani irin ajiyar zuciya mai haɗe da shasheƙar kuka ta lumshe ido ,ta soma addu’a cikin sambatu ,kamar taɓaɓɓiya tama manta a abin hawa take

 

“Ya rab ka bawa inna ta lafiya ,Allah ka jiɓinci lamarin marayunka ya Arhamar_rahimin”

A take ta kife fuskarta akan tafukan hannunta ta goce da kuka.

 

 

 

#Oum Aphnan cares

Littafin Kuɗine dai regular 500₦

VIP 1k

Special 2000₦

Zaku biya ta wannan bank din

7782217014

Mohammad Hassana

Fcmb

Ko katin mtn ma wannan number 09065990265

 

*Garin naji daɗi dai yafi garin na saba…kowa yasan Alkalamina in kin bi babu nadama….Nishadi iya nishadi..Sai littafan Oum Aphnan mai dubban masoya

Add Comment

Click here to post a comment