Yar Senator Hausa Novel Complete
ƳAR SENATOR
_Full of Arrogance, Ego, Jealous And_ _Love_
*CREATED AND WRITTEN*
_BY_
UMMEETA
MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION
*”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’*
بِسم الله الرحمن الرحيم
_”’It doesn’t matter who we are, we all have our successes and failures, we all make mistakes, but what really matter is how we move forward and how much we learned from our mistakes”’_
*PAGE 1-2*
Mota ƙirar Elantra fara tas da baƙin tinted ce tayi parking a bakin gate ɗin wani tangamemen gida, fasalin gidan, da girmansa da kuma tsarinsa kaɗai ya isa ya tabbatar wa mutum cewa gida ne na masu arziki, komai na gidan ya haɗu
Baitul Jinn Hausa Novel Complete
Horn aka danna kusan sau uku, kafin mai gadin da bai gaza shekaru 45 ba, ya zo cikin sauri ya buɗe gate ɗin, duk da cewar ya ji ciwo a ƙafarsa, amma hakan bai hana shi yin sauri ba saboda gudun masifa
Motar na shiga cikin gidan ta tsaya, ganin hakan ne ya sa yana gama rufe gate ɗin ya zo da gudu ya tsaya yana jiran fitowarta
Buɗe ƙofar motar tayi, ta fara fito da kyakkyawar ƙarfarta da ta sha jan lalle, da takalminta flat shoes sky blue, kafin a hankali ta fito gaba ɗaya, tana sanye da doguwar rigar atampa dark blue mai manyan patterns sky blue, sai ɗan ƙaramin gyale sky blue tayi rolling kanta da shi
Kyakkyawar budurwa ce ajin farko, ta haɗu ta ko ina, tun daga fuskarta, tsarin jikinta da komai ma, ƙaton glass ɗin da ya mamaye kusan rabin fuskarta ta cire tana kallonshi
Ya buɗe baki zai yi magana ta ɗauke shi da mari sau biyu, kaɗan ya rage ya faɗi, dafe kumatunshi yayi yana kallonta
Ta ce “Habu! Yaushe ka fara raina ni? Ko kuwa so kake mutane su fara raina ni? A gidanmu a ce sai nayi horn sau uku sannan zan samu damar shiga, bayan tun lokacin da aka ɗauke ka aiki sai da aka gaya maka horn ɗaya nake yi!”
Cikin girmamawa ya ce “dan girman Allah Hajiya kiyi haƙuri, wallahi ɗazu ne na ɗan fita mai mashin ya kaɗe ni, kin ga ma ƙafar ciwo take mun wallahi da ƙyar nake tafiya, ki yafe ni… ”
A tsawace ta katse shi “kai dalla rufe mun baki, ina ruwa na da ciwon ƙafarka, Allah ya sa guntilewa ma tayi me ya shafe ni… To bari in gaya maka wallahi kwananka a gidan nan ya ƙare”
Bata jira jin me zai ce ba, ta shige motar ta bar shi nan yana rafka salati, a ƙaton wurin da aka ƙawata dan ajiye motoci tayi parking, kafin ta jawo handbag ɗinta sky blue ta fito
Kai tsaye babban parlourn su ta wuce, parlour ne da ya ji ababen more rayuwa masu masifar kyau da tsada, aljannar duniya kenan
Mutane biyu ne a parlourn suna fira, kallo ɗaya zaka musu ka gane iyayenta ne, kujerar da mahaifinta yake zaune ta nufa, ta zauna kusa da shi sai turo baki take kamar zata mishi kuka
Cikin kulawa da so ya kalle ta ya ce “Baby ya aka yi? Wa ya taɓa mun ke ne?”
A shagwaɓe ta ce “ba Habu ba ne… ”
“Wane Habun? Ba dai mai gadi ba”
“Shi mana, wai har ni zanyi horn sau uku kafin ya iya buɗe mun gate, dan kawai yana so mutane su raina ni! ” ta ƙarasa kamar zata yi kuka
Da sauri ya ce “a’a a’a Baby, don’t cry(kar kiyi kuka), ai ba girmanki bane kiyi wa gateman kuka… Yanzu me kike so? ”
“Daddy ai kai ma ka sani”
“A kore shi?”
“Umm”ta faɗa tana ɗaga kai
“An gama, tashi mu tafi” a tare suka miƙe tsaye
Mahaifiyarta dake zaune gefe tana kallonsu, ta ce “Alhaji, yanzu ma sake biye wa yarinyar nan zaka yi, ka kori wannan bawan Allahn?! ”
“Ƙwarai kuwa, ke ba kiji abunda ya mata bane?”
Miƙewa tayi cikin fushi ta ce “to me ya mata? Dan kawai be buɗe mata gate da wuri ba shi ne tashin hankalin? Kowa bai da uzuri ne sai naku? Watanmu huɗu da dawowa wannan sabon gidan, cikin watannin nan kuwa masu gadi ɗai-ɗai har goma sha uku ka kora saboda ita, in ka kori wannna sha huɗu fa kenan! ”
“Eh na kore su, kuma zan kori fiye da haka ma in dai akan Baby ne, dan farin cikinta nake so ”
Shiru kawai tayi tana kallon ikon Allah dan ta san duk surutun da zata yi ba zai hana ya kore shi ba dan ba yau aka fara ba, ita kuwa wacce ake yi sabida ita sai juye-juye take tana murmushi, ko a jikinta
Sama ya haura ya ƙirgo sauran kuɗin mai gadin, sannan suka fita harabar gidan shi da Babynshi, sun tarar da Habu kan benci ya zuba tagumi, yana ganinsu ya durƙusa ƙasa da sauri
“Malam Habu, ba na gaya maka sharaɗin Baby ba? Na gaya maka bata horn sau biyu, amma ba ka ji ba ko! ”
“Dan Allah Alhaji kayi haƙuri, wallahi ƙafa ta ke da rauni, a yafe mun hakan ba zai sake faruwa ba nayi alƙawari”
“Dama kuwa ta ya hakan zai sake faruwa Malam Habu tun da yanzu zaka bar gidan nan”
“Alhaji ka tausaya mun, wallahi da aikin nan nake rufawa kai na da iyali na asiri, kar ka kore ni dan Allah ” Habu ya faɗa cikin kuka
“Ai fa sai dai kayi haƙuri, tunda Baby ta furta kalmar kora a kanka, to ka zama korarre… Ga cikon kuɗinka, kar ka bari in fito in same ka a nan” ya ja hannu Babynshi suka koma ciki, Habu kuwa sai share hawaye yake ta yi
Suna shiga ɗakin, mahaifiyarta ta fito, kai tsaye wuein Habu ta nufa, ta kira sunanshi, “Malam Habu”
Da sauri ya ɗago ya ce “na’am Hajiya, dan Allah ki ba Alhaji haƙuri wallahi ba zan sake ba”
“Ka ga Malam Habu, na san ba kayi sati biyu a gidan nan ba, amma dai ka fahimci yanda Alhaji ya ba yarinyar nan muhimmanci, ba zai saurare ni ba tunda har tayi magana, amma kayi haƙuri ka je, in na samu labarin gidan da ke da buƙatar mai gadi, zan kira ka, kafin nan, ga wannan ka ja jari ka ji ko” ta miƙa mishi kuɗi, naira dubu hamsin
Har ƙasa yake yana mata godiya, kafin ta juya ta koma ciki, shi kuma ya shiga ɗaki dan ya tattaro kayanshi kamar yanda aka umarce shi
Bayan fitar Alhaji daga gidan, mahaifiyarta ta shiga ɗakinta, ta tarar da ita ta cire kayanta, daga ita sai towel, da alama dai wanka zata shiga, zama tayi a gefen gado, ta kira sunanta “SUNAIHA”
“Na’am Mummy”
“Zo nan”
Zuwa tayi kusa da ita ta zauna ta ce “gani”
“Yanzu Sunaiha abunda kike yi kina kyautawa kenan? ”
“Me kuma nayi Mummy? “ta faɗa a shagwaɓe
“Da kike sa mahaifinki yana korar mutane ba gaira ba dalili, ba ki san hanyar samun kuɗinsu ba kenan har su samu abunda suka ci?”
“To Mummy raina ni fa suka yi”
“Hakan ba raini bane Sunaiha, kiyi wa mutane uzuri mana, ki daina biyewa Daddynki wata rana fa aure za kiyi, kuma ba ko wane namiji zai ɗauki wannan rashin kunyar ta ki ba”
Wani murmushi tayi da ya ƙara fito da kyaunta, ta ce “tab, ai Mummy duk wanda zai aure ni dole sai ya kasance mai haƙuri da ni ko yayi gaba… Kuma ma ai kin san irin mijin da nake so in aura”
Harara ta zabga mata, ta ce “ai shiyasa har yanzu kike gida a zaune muna auna tsayi ni da ke, kuma idan kika biyewa wannan shirmen na ki zaki tsufa a gidan nan ina gaya miki” ta miƙe kawai ta bar ɗakin a fusace
Ita kuwa dariya tayi ta kwanta kan makeken gadonta tana murmushi, ba komai ke sa ta murmushin ba illa tuna irin mijin da take mafarkin samu a rayuwarta, kusan minti biyar tayi a kwance kafin ta tashi ta faɗa toilet
*SUNAIHA ABUBAKAR NURADDEEN* , Cikakken sunanta kenan, ƴa ce ɗaya tilo a wurin iyayenta, mahaifinta Senator Abubakar Nuraddeen Mai Doki, babban Engineer ne kuma ɗan siyasa wanda ake damawa da shi har yanzu a jahar, mahaifiyarta kuwa Hajiya Binta Muhammad, Sunaiha ta kasance ƴar gata ce a wurin iyayenta, musamman mahaifinta da ya ɗauki son duniya ya ɗora mata tun lokacin da aka tabbatar musu da cewa Hajiya Binta ba zata sake haihuwa ba sakamakon lalacewar da mahaifarta tayi, Alhaji Abubakar kuwa bai kasance mai son auren mata biyu ba, hakan ya sa bai ƙara aure, ya haƙura da Sunaiha da Allah ya ba shi
Tun tana ƴar ƙaramarta ya shagwaɓa ta, duk abunda take so shi yake mata ko da kuwa baya so ko mahaifiyarta ba ta so, in dai zata yi farinciki wannan ba damuwarsa ba ce, sanadiyar yanda mahaifinta ke mata ya sa take jin kamar ta fi kowa, hakan ya sa take da girman kai, ji da kai da kuma wulaƙanta mutane kuma ba ruwanta komai girmanka ko tsufanka ko namiji ko mace, ita kowa ta raina, ga shi kuma Allah yayi ta da farin jini da kuma kyau, kowa na sonta amma ita ba kowa take kulawa ba sai masu kyau da arziki kamarta, wannan halin na ta kuwa tun tana primary school, har ta kai secondary, sai a lokacin Hajiya Binta ta fara jin abun yana damunta sosai, tayi faɗa tayi nasiha amma a banza dan Sunaiha ta riga da ta hau layin da Daddynta ya ɗora ta, sai dai duk wannan ɗabi’un nata, tana ɗauke su ne akan waɗanda jininsu ya haɗu, duk da cewar idan halin ya motsa tana musu, amma bai kai wanda take yi wa sauran mutane ba.
Bayan ta gama secondary school ɗinta, Alhaji Abubakar ya tura ta london wurin wani yayanshi da ke can dan tayi karatu, ƴaƴanshi biyu, babbar mace ce sai namiji wanda tare da Sunaiha suka yi karatu, a can ɗin ma ba’a tsira ba dan ba abunda ya rage a ɗabi’unta. Wani lokacin iyayenta ke zuwa ganinta, wani lokacin kuma ita ce ke zuwa idan suka yi hutu, a haka har ta kammala karatunta ta dawo gida Nigeria
Daga nan Mummy (Hajiya Binta) ta fara takurawa Alhaji Abubakar da maganar aurar da Sunaiha, dan ta fi so ta ga tayi aure ko wannan halin na ta zai rage, amma da aka mata maganar miji sai cewa tayi ita har yanzu bata haɗu da irin mijin da take so ba, a cewarta akwai wanda take mafarkin samu, shi ne irin tsarin mijinta, dan haka idan ba irin wannan mijin ba, ba zata taɓa yin aure ba, wannan maganar ta matuƙar ɓata ran Hajiya Binta, amma sai ta ga shi Alhaji ko kaɗan abun ba damunshi yayi ba, sai cewa ma yayi zai taimaka mata wurin samun wannan mijin, ta kwantar da hankalinta, Hajiya Binta kuwa ta sa musu ido ta ga ikon Allah ta yanda za’a nemo wanda ake gani a mafarki, ta gaji da magana yanzu addu’a kawai take yi, Samari kuwa ƴaƴan manya, masu arziki sun fi a ƙirga waɗanda ke zuwa neman aurenta, amma ko wanensu da irin wulaƙancin da take korarsa da shi.
WANNAN SHI NE TAƘAITACCEN BAYANI AKAN *ƳAR SENATOR*
_CI GABA_ ~~~~~~~~~~~
Senator Abubakar na office ɗin shi yana aiki, wani mutum ya shigo da sallama, sai da suka gaisa kafin ya nuna mishi kujera ya ce “zauna mana Alhaji”
Murmushi yayi sannan ya zauna, sake gaisawa suka yi, kafin mutumin ya ajiye file ɗin dake hannunshi ya ce “ranka ya daɗe ka manta da maganar fitarmu ne? ”
“A’a Alhaji Sani ban manta ba, akwai wanda nake jira ne shiyasa”
“Akwai wanda kake jira kuma? ”
“Eh, Alhaji Makama ne, although personal issue ne ba na aiki ba, amma yana da flight ne by 12 zai tafi China, shiyasa na ce ya zo nan kawai mu haɗu dan ka ga yanzu almost 11:20am”
Agogo ya duba, ya ce “to ba damuwa, Allah dai ya sa lafiya”
“Lafiya ƙalau, kawai magana ne akan Sunaiha”
Da mamaki ya ce “Ah! Ta dawo ne? Ko tana can? ”
Murmushi yayi ya ce “ta dawo ai, ta kusan wata biyar ma da ta dawo, yanzu ma maganar aurenta ne ake yi”
“Allah sarki, ai wallahi ban sani ba, ashe har ta samu miji, ga yaron nan kusan kullum sai ya mun maganar ta”
“Wane yaro kenan? ” Senator ya tambaye shi
“Yaron waje na, Usman, tun ranar da na aike shi gidanka, da ya dawo ya gaya mun ya ga hotonta a parlourn ku, kuma ta kwanta mishi, shi ne fa na ce bata ƙasar amma idan ta dawo sai ya zo su ga juna”
“Ai da tun lokacin ya kamata ka mun magana… Anyway, yanzu ma lokaci ba ƙure ba, dan bata tsayar da mijin ba, zai iya zuwa ya ganta, kasan dama ita mace allura ce cikin ruwa…. ”
Alhaji Sani ya ƙarasa mishi “mai rabo kan ɗauka… Na ji daɗi sosai, in sha Allah zan gaya mishi sai ya shirya gobe ya je ganinta ɗin”
“Hakan ma yayi, zan sanar da ita”
“To na gode… Bari in je sai in jira ka a waje to”
“Ba damuwa”
Miƙewa Alhaji Sani yayi ya fita, a bakin ƙofa suka haɗu da Alhaji Makama, sai da suka gaisa kafin ya wuce shi kuma ya shigo ciki
Duk dai maganar ɗaya ce, shi ma ɗan wajensa ke son Sunaiha, shi ne ya zi nema mishi alfarma dan ya je ya ganta, Alhaji Makama shi ma babba ne a fagen siyasa, Senator Abubakar ya gaya mishi Sagir zai iya zuwa ganinta anjima da yamma, godiya Alhaji Makama yayi kafin ya bar office ɗin, sannan Senator Abubakar shi ma ya fito
Sunaiha na gidansu babbar ƙawarta, IKRAM, suna shirin zuwa wurin bikin wata ƙawarsu, lokacin Daddynta ya kira ta, wayar na fara ƙara ta ɗauka da sauri dan ta san shi ne, ai kuwa da ta tabbatar shi ɗin ne, ba ɓata lokaci ta ɗaga
“Hello Daddy na” ta faɗa
“Baby na, kina ina? ”
“Daddy ina gidansu Ikram, za mu je wurin bikin da na gaya maka ne”
“Mummynki ta san kin fito? Kin san wancan lokacin ma haka ta yi ta faɗa da kika fita tana bacci”
Dariya tayi ta ce “eh ta sani Daddy, tana parlour ma lokacin da na fito”
“To shikenan…. Dama zan gaya miki ne kina da baƙi dan ki koma gida da wuri, ɗayan zai zo yau da yamma, Sagir Abdullahi Makama, ɗayan kuma sai gobe”
Numfashi ta sauke tana girgiza kai, ta ce “shikenan Daddy, i’ll be back on time”
“That’s my girl, take care, ba zan dawo da wuri ba shiyasa na gaya miki yanzu”
“No p Dad, take care too” tana gama faɗr hqka suka kashe wayar
Wani numfashin ta sake saukewa ta ce “oh ni Sunaiha”
Ikram da ke faman shafa jambaki, ta ce “hey, what’s wrong? ”
“Hmm, i have a guest, da yamma”
Dariya Ikram tayi ta ce “to meye? Abunda ma na san za ki sa shi ne sahun waɗancan! ”
“Ke ma kin sani ai, suna ɓata lokacinsu ne kawai, dan ina tunanin ma Prince ɗina ba’a garin nan yake ba, dan har yanzu ba mu haɗu ba”
“Prince dai, Prince dai, Prince dai… Wai a mafarkin naki gidan sarauta kike ganinshi? ”
“Ko ɗaya, ba’a gidan sarauta nake ganinshi ba, but he’s the Prince of my heart”
Dariya Ikram tayi sosai, ta ce “prince of ur heart, ban taɓa ji ba… To idan shi ne prince, who’s the King of ur heart”
Murmushi tayi ta ce “My Dad, He’s the KING, while My dream Boy is the Prince”
Dariya ta sake yi, ta miƙe tsaya ta ɗauki mayafinta da jakarta, ta ce “Allah ya ba ki lafiya Sunaiha ta, tashi mu tafi”
Sai da ta zabga mata harara kafin ta miƙe ta ce “Ameen.. Ki ci gaba da dariya, wata rana sai na gaya miki na haɗu da Prince ɗina”
“Hmm, all the best” daga haka suka fita.
Add Comment