Littafan Hausa Novels

Rashin Haihuwa Hausa Novel Complete

Rashin Haihuwa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

RASHIN HAIHUWA

 

_(Ƙaddarar wasu matan)_

 

Na

Ouummey

 

Wattpad @ouummey

 

 

 

 

Ouummey 004

*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu’ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

 

 

 

_Free Chapter Four_

 

Ragowar ranar nayi ta ne cikin damuwa da tunani, kwata kwata na rasa meke min dadi a duniya, irin yadda kaddara ke kwallo da rayuwa ta abin ba’a cewa komai.

Mai Jiddah Hausa Novel Complete

Ko da dare yayi kasa barci nayi, so nake na samu wani mu zanta ko naji sanyi cikin rai na sai dai na rasa wa ya kamata na yi maganar da shi, Ummi na kullum cikin son ganin ta kwantar min da hankali take inda ni kuma nake tabbatar mata lafiya nake a kullum ko da ba hakan bane saboda gudun shigar ta damuwa, yaya ta daya mace wato Salima sai dai bana jin zan iya maganar nan da ita saboda gudun sa ta jin kunya, ragowar yayye na biyu maza ne, duk da suna tausaya min suna kuma so na sai dai bana jin zasu gane halin da nake ciki.

 

Ban san yadda aka yi hannu na ya danna number Abban mu ba kamar yadda muke kiran mahaifin mu se jin muryar sa nayi yana min sallama, a lokacin dukkan wani rauni da nake ta boye wa da dannewa ya bayyana kan sa ta yadda ban san ya akayi ba se ji nayi na fashe da matsanancin kuka me tada hankalin duk me saurare, shiru Abba yayi be kuma cewa komai ba tun bayan amsa min sallama da yayi, haka ya bar ni nayi kuka na har na gaji murya ta ta dusashe kafin can kasa yayi gyaran muryar da ya shaida min yana bukatar in saurare shi, ban musa ba na katse ragowar kuka na se yar sheshsheka da ajiyar zuciya.

 

“Uwatah”.

 

Yadda ya kira sunan cike da kwantaccen lafazi da sanyin murya yasa naji sabon kuka na neman kufce min, na amsa masa da murya me rawa

 

“Na’am Abban mu”.

 

“Bani hankalin ki nan ki saurare ni sosai”.

 

A wannan karon itama sheshshekaar dakatar da ita nayi tare da sake shigewa cikin katifar gado na me aminci

 

“Rayuwar duniya gaba ki dayan ta jarrabawa ce, ita kuwa rayuwar aure yar hakuri ce, uzuri a gurin da babu muhallin sa, kau da kai a abinda yake zahiri ko da an cuta maka, danne bukatar kai saboda ta abokin rayuwar ka, ji ka nuna baka ji ba, ka gani ka nuna baka gani ba haka kuma a taba ka ka nuna baka san an yi ba ta hanyar yafiya.

Base kin ce min komai ba ba kuma se kin fada min halin da kike ciki ba, kukan ki ya bayyana min komai, sai dai ina so in tuna miki da abin d kika manta, ni baban ki ne, dan Adam kuma ajizi, da ni dake Allah muke bautawa gaba ki daya haka kuma wajen sa muke neman taimako, kama ta yayi da damuwa tayi miki yawa ki tashi ki dauro alwala ki fuskanci qibla ki kai kukan ki wajen me duka cikin kaskan da kai, yi masa kirari da kuma tsarkake shi, ina me tabbatar miki da wallahi in kika yi hakan zaki sami saukin kome ke damun ki, damuwar ki zata yaye, ruhin ke ze aminta haka kuma zaki sami nutsuwar zuciya.

Ba kamar ni ba da in kika fada min sai dai in miki kalamai wanda bayan haka ba abinda zan miki in Kuma ba so kike in zama uban kawai me shiga sha’anin rayuwar auren yar sa ba.

Yanzu maza ki tashi kiyi kamar yadda na fada miki kinji, insha Allah nima zan taya ki, a kullum cikin addu’a ta kike uwatah ke da sauran yan uwan ki amma zan kara da izinin Ubangijin mu, ina fatan Allah ya yaye miki kome ke damun ki, ya aminta da ruhin ki ya kawo miki sauki da salama a rayuwar ki, zan kira ki da safe, Allah ya bamu alkhairi”.

 

Kit Abba ya kashe wayar sa da ya gama min wannan bayanin, be saurare ni ba, bance masa komai ba game da halin da nake ciki amma ga mamaki na wallahi se na ji kaso fiye da hamsin cikin kuncin da nake ci ya kau, lallai na gaida iyayen mu,  ya Allah  kasa iyayen mu su cika da imani ka saka musu da mafificiyar aljanna, Amin.

 

Batun yanzu ba ina sha’awar rayuwar Abban mu da Ummin mu, so da yawa ina fadar in da ace kowane miji kamar Abban mu yake da ba’a samu gurbacewar rayuwar aure ba, da ba’a sami yawaitar matsalolin aure ba, da ba’a samu yawaitar zawarawa ba haka da mata basu ji tsoron aure ba, in Kuma na dube shi ta fuskar uba se in ga lallai babu ya’yan da suka kai mu yin dacen uba nagari, se in dun ga tausayin wanda Abba be kasance mahaifi gare su ba har in dinga ganin lallai sun yi rashi babba.

 

Alwala nayi na shimfida tsaftatacciyar pray mat dina dake nan kamar sabuwa saboda samun gyara na sa wadataccen hijab dina na kabbarta sallah, a cikin kowace sujjada kuka nake yi gaban Ubangiji ina rokon sa sauƙin rayuwa, farin cikin rayuwa, haka kuma yayewar bakin ciki tare da cikawa da imani, irin kukan da nayi ba zan ce ga sanda nayi shi ba dan tun da na dora goshi na a kasa naji bani da wani sauran karfi ko kwarin zuciya.

 

Cikin ikon Allah na yi raka’a goma wato sallama biyar sannan na daga hannu na cigaba da addu’a, ina shafawa na dau Kur’anin da na aje gaban sallaya ta na budo Suratul mu’umin na soma karatu cikin kyautatacciyar kira’a murya can kasa dan gudun takurawa abokan rayuwa ta a gidan, sai da nayi surori uku bayan ta sannan na rufe tare da sake wasu addu’o’in na kuma shafawa, abin babu karya ba kuma yaudara tun kafin na kai ga idar da sallar naji zuciya ta wasai tamkar ban taba sanin wani abu wai shi damuwa ba, farin ciki da walwala suka cika rai na tamkar wadda akayi wa bushara da kujerar hajji.

 

Agogo na kalla wanda ya nuna karfe biyu da rabi na dare na tashi na cire hijab din da na sa na rataye shi tare da maida daurin dan kwali na na nufi gado na na kwanta hannu na rike da calbi ina ja cikin kirari wa madaukakin sarki, cikin rahmar Allah se gashi na samu salamammen bacci me cike da jin dadi kamar kar na farka dan se da nayi da gaske na iya tashi asuba ba kamar ragowar ranaku da ake kiran farko a kunne na ba saboda damuwar da kan hanani bacci, lallai Allah buwayi ne garara misali haka kuma duk wanda ya bar Allah tabbas yayi hannun riga da nutsuwar fili har ma da ta boye.

 

Ba fa wai na manta da abinda Salees ya min bane, ba kuma na manta da kara ta da ya kai wadda zamu je yau bane kawai dai damuwar hakan Allah ya cire min daga rai na.

 

Ban yi gigin yin breakfast ba dan ban manta layin d ya shata min ba na cewar in har ban kwana dakin sa ba to bani da girki gaba daya, ma’ana har dafa abinci, a can baya da yasa dokar na damu amma a yau se naji ni hakan ma yayi min dan gashi na samu damar bajewa a gado ina baccin safe kasancewar asabar babu aiki.

 

Se after 10 na tashi nayi wanka da shower gels dina da ragowar turarukan wanka masu kamshi da gyaran fata wanda a kullum yanayin yadda nake kula da jikina yake bawa wanda suka san ainihin shekaru na mamaki, dan da yawa mutane basa yarda na kai shekaru na, so da yawa se kiga ana bani shekara Ashirin da biyar da shida koma da hudu, nidai in irin haka ta faru sai dai nayi dariya kawai, amma fa bana mamaki dan ko ke kika kalle ni ba zaki ce nayi talatin har da biyu ba wanda sune shekaru na na gaskiya da gaskiya .

 

Doguwar riga na sa kirar Morocco, kafin kace me na zama wata bakar balarabiya saboda yadda rigar ta min ainihin kyau ta bi dirarren jiki na ta zauna Kamar yar asalin ƙasar, kai har ma nafi dan su ba su da cikakken diri irin nawa.

 

Karamin fridge dina na bude tare da zubawa kayan snacks din ciki ido sannan a hankali na debi samosa uku tare da drink na maida murfin na rufe, a tsanake naci abina na kora lemo na kara da ruwa me dan sanyi, take naji ciki na y dauka masha Allah na koma  tare da zama kan doguwar cushion din dakin ina bibiyar chats din kawaye na cikin group din mu me suna *UWAR GIDA*.

 

Knocking din da aka min yasa na dan saurara daga karanta wani post da nake yi kana na tashi na tafi na bude bayan na kuma jin wani, Sahal ne me bin Ilham, tsakanin su shekara daya ne dan yanzu sha biyu yake yayinda ita take sha uku

 

“Daddy yace ki fito”.

 

Yace tare da barin wajen da sauri, jinjina kai nayi tare da komawa daki ina fadin

 

“Wata matsalar ta dawo” a raina dan zan iya cewa Sahal har yafi Ilham dan shi kan kamar uwar sa ta bashi zuciyar ta ne, bakin hali a cikin yaron abin se addu’a shiyasa tun farko ban sake masa ba bare ya raina ni ko da dai b wai girmama ni yake ba duk tsare gida na, tun hutu ya tafi gidan iyayen Mariya kuma ko da aka koma makaranta be dawo ba ta can yake tafiya se yau da aka dawo dashi.

 

Sai da na koma gaban madubi na sake gyara zaman mayafi na na kara turare kadan me sanyin kanshin da baya tashi sannan na dau waya ta da karamar purse dina na fita, basa falon hakan yasa na fita compound bayan na rufe kofar falon.

 

A tsaye na hango Salees jikin motar sa wadda ina fitowa ya bude ya shiga, takawa na shiga yi zuwa wajen su sedai kafin na karasa ya ja motar sa yana yi wa maigadi horn ya bude gate tsayawa nayi kallon ikon Allah se kuma na bar shi as tun d ta kusa dani zai wuce maybe ze tsaya in shiga,

 

“Motar ya cika, ki biyo bayan mu a naki tun da kina dashi”.

 

Sakatoto nayi ina bin shi da kallo kafin kuma na kau da mamaki da sauri dan wannan kadan ne daga halin shi, shi in har kuna fada to fa ba zaki kuma jin dadin sa ba, duk yadda ze bata wa mace rai to se yayi so tuna haka se kawai na saki murmushi me kyau na gyada kai na alamun toh na juya zuwa wajen mota ta.

 

Farin ciki na daya , kamar yadda yace ina da motar, mota kuma ba karama ba domin suna gogayya da tasa a wajen kudi, bangaren tashe kuwa har ma tawa ta zarta tasa, ina tsananin so da kaunar motar domin kuwa Abban mu da hannun sa ya bani kyautar motar lokacin da Mariya ta haifi Amir wata shida da suka wuce.

 

Cikin tuki na na natsuwa na fitar da motar daga gidan tare da hawa titi na nufi babban gida kamar yadda suke kiran family house din su inda nan ne iyayen Salees suke.

 

Gefe da tasa motar na aje parka tawa sai dai ban fito ba sai da na gama addu’o’i na na samun rinjaye kan makiyi dan kusan zance makiyan nawa ne mutanen da zan hadu dasu.

 

Bakin babban falon Hajiya Iya nayi sallama tare da daga labulen na shiga bayan na sabule takalman kafa ta, a duk cikin mutane takwas dake zaune a falon ba’a sami ko daya da ya iya amsa min sallamar da nayi ba wanda hakan ba bakon abu bane a waje na, gefen one sitter na samu na zauna kana na shiga gaida Hajiya da ta nuna kamar bata san da shigowa ta ba tana yi wa Amir dake hannun ta wasa, seda na maimaita gaisuwar sannan ta amsa min a watse.

 

Daga Lafiya lau din bata kuma cemin komai ba nima kuma naja baki na nayi shiru, sai da ta gama da shalelen ta sannan ta mikawa Hannatu kanwar Salees dake zaune a wajen Amir kana ta fuskanto mu gaba daya.

 

“Uhm, kace mene?”.

 

Dan muskutawa Salees yayi ya fara rattabo zance kamar me karanta labari

 

“Hajiya karar khadeejah na kawo miki, ban san meke yawo a ranta ba, ban san wake zuga ta amma gaba daya ta birkice, gaba daya ta canja halaye da dabi’un ta ta kwaso mugayen akidu da ra’ayi ta ɗorawa kan ta.

Babu damar naman Amir tayi wani abu yanzun nan se ta hayyako ta fara fadin maganganu marasa kan gado, kwata kwata bata neman zaman lafiya kamar yadda ita Mariya ke son su rayu cikin salama, a kullum burin ta ta kuntata min ta bata min rai.

Duk ma kuma ba wannan ne babbar damuwar ba, kin ga yaran nan wallahi khadeejah yadda ta tsane su bana jin ko makiyin ta ta tsana haka, daga ni uban su har ita mahaifiyar su bamu san me mukai mata ba da take neman saukewa kan su.

Shekaranjiya iIlham d zazzaɓi ta kwana me zafi saboda yadda ta fasa mata baki ga kuma kunnen ta da ta murde saboda wai tayi mata rashin kunya wanda zan iya rantsewa baby ba zata yi haka ba sedai yarinta, wai kuma daga uwar ta ce ta dinga sassauta hukunci shikenan ta dau fushi da ita da yaran har tana tafiya wajen aiki ta bar baby bata je makaranta ba saboda tana tutiya da tinkahon baban ta ne ya sai mata mota, Hajiya Iya fa abubuwan da zan iya fada miki kenan kuma akwai wasu bayan su sai dai in zan zauna lissafa miki wallahi zamu wuni ba mu gama ba, shiyasa na kawo ta gaban ki ta fadi meye matsalar ta da ni, Mariya ko yayana”…………..

Add Comment

Click here to post a comment