Littafan Hausa Novels

Ayi Min Adalci Hausa Novel Complete

Ayi Min Adalci Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

AYI MIN ADALCI*

 

*King and Queen writing chamber*

 

 

 

BONUS! BONUS!! BONUS!!!

 

BAYAN WATA SHIDA

 

Abubuwa da dama sun faru ciki har da zamowar mahaifin Barrister Shaheedah sarki, sannan an ɗaura auren Faisal da Barrister Shaheedah. An sha shagali sosai, har sarauta aka yiwa Faisal Sardaunan samarin Muri, arziƙin ya auri ƴar sarki shi yasa aka yi masa sarauta.

Faisal kuwa naira ta zauna masa sosai, idan ka kalle shi ba zaka taɓa cewa shine Faisal ɗin da ka sani a baya ba. Yayi jajur da shi kamar balarabe, ga wani kyau da yake ƙara yi kullum.

Da Ciwo A Zuciya Ta Hausa Novel Complete

A wata unguwar hamshaƙan masu kuɗi waɗanda ake ji da su a Kaduna ya sayi ƙaton gida. Inda suka zauna shi da amaryarsa Barrister Shaheedah ko kuma na ce Gimbiya Shaheedah tunda yanzu ta zama ƴar sarki. A nan kusa da unguwar da suke ya sayawa su Goggo wani danƙareren gida ya zuba musu duk wani kayan more rayuwa, da ƴan aiki da za su rinƙa yin komai…Sannan ya bai wa Habibu aiki a babban kamfaninsa na man fetur, dama yayi karatu aikin ne dai Allah bai kawo ba.

 

Haka a ɓangaren su Oumar da Auwal su ma Faisal bai manta da su ba, ya samar musu aikin yi a manyan ma’aikatun Gwamnati. Kasancewar Faisal ya san manyan mutane ta hannunsu ya bi ya samowa Oumar aiki a NNPC shi kuma Auwal a CBN, Mudassir kuwa tun daga ranar ya zama abokin su Faisal sosai suka zama kamar da can sun san juna lafiya k’alau suke zaune babu wanda yake ƙyashi wani.

 

Su Goggo an samu duniya, ta je Umra ta je Hajji. Ga muhalli mai kyau sutura mai kyau ga lafiyayyen abinci, ko aiki Goggo ta yunƙura za ta yi da sauri ƴan aikinta suke dakatar da ita…Wani lokacin idan Goggo ta zauna tana tunanin rayuwar da suka yi a baya sai ta fashe da kuka ita kaɗai, tunda take a rayuwa ba ta taɓa zaton za ta tsinci kanta a irin wannan daular ba, lallai yanzu ta yarda da karin maganar nan dare ɗaya Allah ya kan yi bature. Hutu da jin daɗi sun zauna a jikin Goggo idan ka kalleta ba za ka taɓa zaton tsohuwa ba ce sai an faɗa maka…

 

Haka a ɓangaren Faisal shi da amaryarsa Gimbiya Shaheedah, soyayya suke zubawa junansu kamar ba gobe. Gimbiya Shaheedah ba ta san tana son Faisal ba har sai da ta aure shi, sannan ta tabbatarwa zuciyarta babu wanda take matuƙar so da kauna kamar shi…Akwai fahimtar juna sosai a tsakaninsu, lafiya kalau suke zaune sai zubawa juna soyayya suke idan ka kalle su dole su burge ka yanda suke matuƙar kulawa da junansu. Duk bayan sati biyu sai Faisal ya ɗauki amaryarsa Shaheedah sun je sun gaida mai Martaba wato mahaifin Barrister Shaheedah. Ƙasashen waje kuwa duk bayan wata biyu sai sun je yawon shakatawa sai sun daɗe a can suna shan love ɗinsu kafin su dawo…..

 

Haka kawai Barrister Shaheedah ta ji tana sha’awar yin kasuwanci. Ba ta yi wani jinkiri ba ta sanar da mijinta wato Faisal, ba tare da shakkar komai ba kuwa ya ba ta 50million ya ce ta fara da wannan.Idan ya ga kasuwancin ya karɓe ta sai ya kara mata wasu kudaɗen. Nan take Barrister Shaheedah ta shiga safarar gold and diamond, daga ƙasar Dubai tana kawowa nan Nigeria ta sayar. Ba iya nan ta tsaya ba har da su rigunan abaya take sayowa ta zo tana sayarwa a nan gida Najeriya. Sosai kasuwancin nata ya karɓu nan da nan kuwa kuɗi suka fara zauna mata, ganin haka yasa Faisal ya ƙara mata wasu 50million din ya ce ta ƙara jari.. Cikin ƙanƙanin lokaci Barrister Shaheedah ta zama matashiyar attajira, domin ta iya kasuwancin sosai…Dama tuni ta daɗe da ajiye aikinta na Lauya..

 

A cikin masarautar Muri kuwa Umma ta zama matar Sarki, komai sai dai ayi mata. Ba ta da kishiya ko ɗaya, shi kansa Sarki Hamza da kansa ya ce, ba zai yiwa Umma kishiya ba saboda ta yi masa halaccin da ba zai taɓa mantawa da shi ba. Duk da jama’a suna damunsa sosai akan ya ƙara aure bai kamata ba yana babban Sarki ya zauna da mace ɗaya ba. Shi kuwa yana ji sai ya share kawai domin gani yake idan ya ƙara aure tamkar ya ruguza duk wani farin ciki da yake tsakaninsa da iyalinsa ne, shi yasa ko kaɗan ba ya sha’awar ƙarin auren. Umma tana da kirki sosai, kowa a cikin gidan sarautar idan ya buɗe baki sai dai ka ji ya yabe ta.

Wani danƙareren gida ta ba wa mahaifinta Aminu da kakanninta Malam Tijjani da Inna Mairo. Anan suka yi zamansu lafiya cikin kwanciyar hankali sun manta ma da sun yi zaman Nijar sai dai idan sun tuno su yi ta labarin abun..

 

 

*INA LABARIN HAJIYA BILKISU?*

 

Barrister Shaheedah ce a zaune ita da Faisal a kayataccen falonsu wanda ya gaji da haɗuwa sai shagwaɓa take zuba masa “Baby ka tashi don Allah mu tafi” kallonta yayi ya saki wani murmushi kafin ya ce,

“Yanzu shopping ɗin lallai sai da ni za ki je?”

“To, ai idan babu kai ba zan ji daɗin tafiyar ba” murmushi kawai yayi tare da miƙewa tsaye ya ce, “Alright tashi mu tafi.”

Da sauri kuwa ta miƙe tare da riƙe hannunsa ta ce, “Baby mu tafi”

Hannayensu sarƙe a cikin na juna suka fito compound ɗin gidan, kai tsaye inda ake ajiyar motoci suka nufa…

Da gudu wani dattijo ya zo gabansu ya ɗan rusuna kafin ya ce, “Alhaji fita za mu yi ne?” Gyaɗa kai Faisal yayi ya ce,

“E! Fita za mu yi amma da kaina zan yi driving na hutar da kai”

“To, Alhaji Allah ya kiyaye hanya” yana faɗin haka ya juya ya bar wajen da sauri..

 

Wata mota mai ƙirar benz suka shiga, suna ƙoƙarin fita daga gidan suka hango Goggo ta shigo hannunta riƙe da Anwar. Dakatawa Faisal yayi tare da fitowa daga cikin motar, da saurinsa ya nufo su Goggo sai faman sakin murmushi yake, Anwar kuwa da ya hango Abbansa ya nufo inda suke shi ma da gudu ya nufe shi. Suna haɗuwa Faisal ya ɗaga Anwar sama tare da rungume shi tsam a ƙirjinsa, ƙaunar yaron yana jin yanda take mamaye masa duk wani lungu da yake cikin zuciyarsa.

 

Kallon Goggo yayi kafin ya saki murmushi ya ce, “Goggonmu mu shiga daga ciki ko?”

“A’a ba zama na zo yi ba, na ga alamun ma fita za ku yi.” Gyaɗa kai Faisal yayi ya ce,

“E fita za mu yi yanzun nan Wallahi sai ga shi kun shigo”

Ya ƙarashe maganar yana sakin wani murmshi.

“Dama ɗanka ne ya taso ni lallai sai na kawo shi wajenka, to ga shi nan na kawo ka ga sai ku fita tare ko?”

Murmushi mai sauti Faisal yayi kafin ya ce,

“Anwar me yasa ka taso Goggo da ranar nan?” Shiru Anwar yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa…..

Barrister Shaheedah ce ta gaishe da Goggo da sauri kuwa Goggo ta juya ta fice daga gidan, tare da Anwar su Faisal suka koma motar tasu suka fita daga gidan.

 

Bayan sun gama siyayyarsu sun fito inda suka ajiye motarsu, suna ƙoƙarin shiga motar “Faisal!” Gaba ɗayansu suka waiwaya inda suka jiyo amon muryar wacce ba za su taɓa mancewa da ita a rayuwarsu ba.

Ganinta suka yi cikin wani mawuyacin hali, sai tafiya take da kyar tana jan jiki kamar wata macijiya….

Kallo d’aya Faisal yayi mata ya kawar da kai tare da jan wani dogon tsaki.

“Mtssss! Taho mu tafi” ya faɗi tare da jan hannun Barrister Shaheedah, ƙin tafiya Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “Faisal Hajiya Bilkisu ce fa ba ka ga a halin da take ciki ba tana buƙatar taimako pls mu taimaka mata…”

“Allah ya kiyaye na taimakawa wannan matar Wallahi da na taimaka mata gara a ce zubar da kuɗin na yi… Ke yanzu har kina da bakin zuwa ki ce na taimaka miki?”

Hawaye ne ya zubo daga idanun Hajiya Bilkisu ta durƙusa har ƙasa tana roƙon Faisal,

“Don Allah Faisal ka taimaki rayuwata ka daure ka biya min kuɗin magani Wallahi idan ba ka biya min ba mutuwa zan yi….”

“Ai Bilkisu mutuwar ita tafi dacewa da ke, gara ki mutu ki je can ki tarar da abinda kika aikata…”

Fashewa da kuka Hajiya Bilkisu ta yi, ta tsugunna har ƙasa tana roƙon Faisal akan ya taimaka amma Faisal yayi kunnen uwar shegu da ita ya ƙi kulata ballantana ya saurareta. Barrister Shaheedah kuwa ranta ne ya soma ɓaci ganin yadda Faisal ya ke wulakanta Hajiya Bilkisu….

Kallon Anwar Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Ɗana Anwar taho gare ni, ni ce Ummanka ka ji ko?”

Maƙe kafaɗa Anwar yayi ya ce, “A’a ni ba ke ce Ummata ba, ni kin ga Ummata” ya faɗi yana nuna Barrister Shaheedah..

 

Fashewa da kuka Hajya Bilkisu ta yi cike da gadara Faisal ya ce, “Alhamdulillah! Ko iya wannan abunda ya faru a nan wajen yanzu, ya isa ya zamo miki darasi Bilkisu, ga shi dai ɗanki na cikinki gudunki yake duk me ya janyo wannan son duniya da amsa kuwwar shaiɗan..Don haka ni yanzu ba ni da lokacinki ki kama gabanki ki san inda dare yayi miki ina gargaɗinki karki kuskura ki ƙara zuwa inda nake idan kuwa kika ƙi ji Wallahi sai na ba ki mamaki, sannan ina son ki jira sakamakon da zai biyo bayan abinda kika aikata ba ki ga komai ba Wallahi wasa farin girki….” Yana fadin haka ya juya da sauri ya shige cikin motarsa, cikin sanyin jiki Barrister Shaheedah ta ɗauko kuɗi a cikin jakarta tana niyyar miƙawa Bilkisu…

“Idan kika ba ta ko naira biyar ce Wallahi ban yafe miki ba” Faisal ne ya fadi daga cikin motar yayin da ya ga Barrister Shaheedah tana shiri miƙawa Hajiya Bilkisu kuɗi…

 

Cike da tsananin ɓacin rai Barrister Shaheedah ta zo ta shiga cikin motar zuciyarta duk babu daɗi, kallon Hajiya Bilkisu take a tsaye cikin rana jikinta ban da wari babu abinda yake yi. Tun tana kallonta har suka ɓacewa ganinta gaba daya, durƙushewa Hajiya Bilkisu ta yi a wajen ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya gami da tsantsar nadamar abinda ta aikata…

A cikin ranta take tunanin yanzu da tuni ita ce a cikin waccan motar, da tuni ita ce cikin kwanciyar hankali da jin daɗi…

“Gaskiya na cuci kaina ni Bilkisu ban san ya zan yi ba Allah na tuba ka yafe mini” ta faɗi tana rushewa da wani sabon kukan, mutane kuwa zagayeta suka yi wasu tausayi ta ba su duk da basu san abinda ta aikata ba, yayin da wasu kuma suke ta faman faɗin Allah ya ƙara dama ita duniya ai haka take idan ka bita a sannu ma da ya ka ƙare balle ka bita da gaggawa….

 

Ko da su Faisal suka koma gida, kwata-kwata ya kasa samun nutsuwa a cikin ransa. Wani irin ɗaci zuciyarsa ta rinƙa yi masa, sakamakon ganin Hajiya Bilkisu ji yayi a ransa inda yana da ikon kasheta da tuni ya kashe ta saboda tsanar da yayi mata….

Yana zaune a falo shi kaɗai yana ta faman tunani, Barrister Shaheedah ce ta kawo masa juice mai sanyi tana lallashinshi da kyar ya ɗan kurɓi juice ɗin sai ya ji zuciyarsa ta ɗan yi sanyi kaɗan, nan take ya shiga ambaton Allah.

A hankali ya ji zuciyarsa ta sanyi sosai, shiru yayi yana ta tunani…

 

Nocking ɗin da ake yi ne a ƙofar falon nasu ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya tafi, a hankali Barrister Shaheedah ta je jikin ƙofar ta leƙa ta jikin ƴar ƙofar nan da take jikin ƙyauren, hankalinta ne ya tashi sakamakon ganin Hajiya Bilkisu jikinta yana ta faman rawa.

Cikin sanyin jiki ta saka hannu ta buɗe ƙyauren.

Faisal da ya ƙurawa ƙofar idanu domin ya ga wanda zai shigo,

Ana gama buɗe ƙyauren ya miƙe tsaye a fusace ya ce,

“Uban waye ya kawo ki gidana? Ki yi saurin fice min daga gida tun kafin ranki ya ɓaci”

Barrister Shaheedah ce ta tako ta zo har inda yake ta kama hannayensa ta riƙe

“Please Habiby ka yi haƙuri don Allah ka saurareta please my horny”

Ɗan rusunawa Faisal yayi ya dubi Bilkisu a wulaƙance ya ce, “Ina sauraronki”

Wani yawun baƙin ciki Hajiya Bilkisu ta hadiye,

yanzu wai ita ce sai wata ta saka baki sannan mijinta zai saurareta? “Gaskiya ni BILKISU na cuci kaina” durƙusawa ta yi a gaban Faisal ta dafa kafafunsa cikin raunin murya irin mai cike da tsantsar nadama ta ce,

“Don Allah Faisal ka yafe min laifin da na yi maka, ka yafe min don Allah ko zan samu sassauci a cikin halin da nake ciki. Na san duk alhakinka ne yake bibiyata, idan ba ka yafe min ba Wallahi ban san yanda zan yi ba…”

Zaunawa Faisal yayi akan kujera ya dafe kansa, yayi shiru…

 

Ganin haka yasa Barrister Shaheedah ta zo kusa da shi ta zauna tare da dafa kafaɗarsa ta ce, “Haba my Habiby ka yafe mata mana, ka san Allah yana son masu afuwa daga cikin bayinsa” wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya dubi Bilkisu ya ce,

“Tunda matata ta saka baki na ji na yafe miki duniya da lahira, amma batun igiyar auren da take tsakanina da ke babu ita na tsinke ta gaba ɗaya ukun kar ki ƙara yin tunanin sake zama inuwa ɗaya da ni…”

Ɗora hannu a kai Bilkisu ta yi, kafin ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya gami da tsantsar nadama..

“Ke Bilkisu ya ishe ki haka, kiyi saurin fitar min daga gida yanzun nan tunda na yafe miki, kuma na daƙile igiyar auren da yake tsakanina da ke…” Faisal ne ya faɗi yana nuna Bilkisu da hannu cikin tsananin ɓacin rai.

Durƙushewa Hajiya Bilkisu ta yi a wurin, ta dubi Faisal cikin muryar ban tausayi ta ce,

“Faisal na sani ka daƙile duk wata alaƙa tsakanina da kai, na san na ɓata maka kuma na cancanci duk wani hukunci daga gare ka amma don Allah ina neman wata alfarma a gare ka..”

A wulaƙace Faisal ya dube ta ya ce, “Ina jin ki Allah yasa zan iya”

“Don Allah ka daure ka siya min magani Wallahi idan ban samu maganin ba nan da kwana uku mutuwa zan yi” ta faɗi hade da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi…

 

A wulaƙance Faisal ya dube ta ya ce, “Bilkisu kenan! Ina tarin dukiyar da kika samu a wajen marigayi Alhaji Hashim? Kar dai ki ce min yanzu duk babu ita?”

Girgiza kai Bilkisu ta yi ta ce,

“Tun lokacin da aka raba gado aka bani nawa, sai na haɗu da wani mutum mai suna Alhaji Kamilu, shine ya ce min na kawo kuɗin nawa shi ma ya kawo na sa mu fara business a Dubai..Na yarda da shi sosai, na ɗauki gaba ɗayan dukiyata har da kadarorina muka haɗa ni da shi muka tafi Dubai domin mu fara kasuwanci tare..

Yayin da muka je can, ni ban san komai ba kuma ban san kowa ba ban da shi, sai ya rinƙa amfani da wannan damar yana cutar da ni. Kullum idan zai fita waje sai ya kulle ni a gida, sai bayan magriba yake dawowa idan na yi masa maganar kasuwancin namu sai yi min masifa yana cewa ba ni da haƙuri ko kuma ya ce ina zarginshi zai cinƴe min kuɗi…A ƙarshe da ya gaji da takurawar da nake yi masa, sai ya fara nuna min ainihin kalarsa. Sai ya shiga nemana tun ba na amincewa ina guduwa har ta kai yana zuwa har ɗakin da nake ko ba na so sai yayi min ta ƙarfi da yaji, sosai ya mayar da ni matarsa duk lokacin da ya so amfani da ni zai zo ya biya buƙatarsa ba tare da tunanin halin da zan kasance a ciki ba…

Tun ina damuwa har na zo na daina na rinƙa ba shi hadin kai yana yin yadda ya ga dama da ni…

Kwatsam! Wata rana ya ce min na shirya zai tura ni can Germany tare da wani abokinsa na fara saro mana kaya domin mu fara kasuwancin namu, da murnata kuwa na shirya ya haɗa ni da abokin nasa wai shi Joseph ƙarfe 11 na safe muka shirya muka hau jirgi, ashe ban sani ba duk shirinsa ne a jirgin Najeriya ya sako ni ba a cikin jirgin Germany ba, ashe yaudarata yayi shi da abokinsa tunda muka sauka a aiport ɗin Malam Aminu Kano ban kara ganin Joseph ba, kuma nan take na fahimci Najeriya aka dawo da ni..Nan take kuwa na shiga cikin rudani domin gaba ɗaya dukiyata tana hannun Alhaji Kamilu, da kyar na samu wani mai taxi ya kai ni unguwa uku na ba shi ƴan sauran canjin da suka rage mini, sauran kuma na kama gida haya anan unguwar..Kullum tunanina shine ya zan yi na koma Dubai domin na haɗu da Alhaji Kamilu haka ne yasa shiga neman kuɗi a lallai sai na tara kuɗin komawa Dubai ɗin na karɓo kuɗina a wajen Alhaji Kamilu. Sana’a na ke yi da kyar wani Alhaji ya ara min bashin dubu ɗari biyar na kama shago na fara sana’ar sayar da abinci kala-kala, sosai kasuwar tawa ta karɓu nan take kuwa na fara tara kuɗin komawa Dubai wajen Alhaji Kamilu…

Kwatsam wata rana na tashi da wani matsanancin ciwon kai, da zazzaɓi mai zafin gaske, da kyar da siɗin goshi na kai kaina asibiti. Anan likita yake shaida min ina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato (H.I.V AIDS) kuma ta fara yin ƙarfi a jikina. Hankalina ya tashi sosai, karo na farko da naji nadama ta shige ni akan abinda na aikata a rayuwata..

Sosai likitan ya kwantar min da hankali tare da ɗora ni akan magani, duk ƴan kudaɗen da na tara domin na koma Dubai sai da suka k’are gaba ɗaya a wajen sayan magani, na dawo kan jarin da nake juyawa su ma ba su daɗe ba suka kaf na dawo abincin da zan ci ma yana bani wahala. Ga Alhajin da ya ara min kuɗin nake juyawa ya saka ni a gaba a lallai sai na biya shi kuɗinsa, ga gidan da nake haya su ma sun saka ni a gaba ban biya kuɗin haya ba. Ga maganina ya kare gaba ɗaya kuma babu kuɗin sayan wani, haka ne yasa na tashi na dawo nan Kaduna na miƙa ƙoƙon barata a wani masallaci ana nema min taimako, da kyar wata mata ta taimaka min da wani dan ƙaramin d’aki a gidanta nake kwana, idan ka kalli ɗakin ba zaka taɓa cewa mutum zai iya kwanciya a cikinsa ba. Ranar da na ganku na zo wucewa ne na hango Shaheedah ta shiga mota shi yasa na ƙaraso wajenku domin na nemi yafiyarku ko zan samu sassauci daga rayuwar da nake fuskanta mai cike da ƙunci da baƙin ciki fiye da wanda na jefa ka a ciki….”

 

Tana kai wa nan a zancenta sai ta sake fashewa da kuka mai har da sheshsheƙa, Barrister Shaheedah ma hawaye sai faman kwaranya yake a kan fuskarta kamar da ita abin ya faru,

A hankali Faisal ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya dubi Hajiya Bilkisu ya ce,

“Haƙiƙa Bilkisu kin ga karshen maci amana tun anan duniya ko? To ina ga an je can Lahira? Ki godewa Allah ma da kika same mu har kika nemi yafiyarmu amma ya zaki yi da alhakin marigayi Alhaji Hashim?”

Sake fashewa da kuka Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Wallahi ban sani ba na yi nadamar abunda na aikata a rayuwata don Allah Faisal ka taimaka min”

 

A nutse Faisal ya dubeta ya ce, “Na ji zan saya miki magani in sha Allah ba zaki sake yin rashinsa ba, zan hada ki da wani Likitana da zai rinƙa duba ki kullum, sannan zan baki gida ki zauna iya tsawon rayuwarki ba zaki rasa ci da sha ba…” Durƙusawa Hajiya Bilkisu ta yi tana ta faman zubawa Faisal godiya domin jita yi kamar kyautar Aljanna ya bata..

Numfasawa Faisal yayi ya ce,

“A dalilin kaza ƙadangare ke shan ruwan kasko saboda haka ina son ki sani duk wannan abinda na yi miki saboda kin ci darajar ɗan da yake tsakaninmu wanda kika gudu kika bar shi a lokacin da yafi kowa buƙatark…”

Shiru yayi sakamakon buga ƙofar da ake yi da karfi kamar za’a karyata,

 

Ba tare da tambayar ko waye ba Faisal ya buɗe ƙofar, ƴan sanda ne wajen su goma a tsaitsaye. Cike mamaki Faisal ya dubi ogansu ya ce,

“Yallaɓai lafiya kuwa?”

Murmushi dan sandan yayi ya ce,

“Kayi haƙuri Faisal mun zo tafiya da Hajiya Bilkisu ne”

Shiru Faisal yayi na dan wani lokaci kafin ya dubi ɗan sandan ya ce,

“Yallaɓai indai don ni za ku kama Bilkisu na riga na yafe mata ku yi haƙuri ku koma”

“Faisal kenan! Idan kai ka yafe mata su ƴan’uwan marigayi Alhaji Hashim sun yafe mata? Kuma hukumar ƴan sanda ma ai ba su yafe mata ba”

“Amma yallaɓai….”

“Ka ga dakata Faisal duk abinda za ka faɗi ka bari aje can station ɗin muma ƴan aike ne”

Ganin haka yasa Faisal ya buɗe musu ƙofar ya ce, su shigo, nan take kuwa suka shiga suka kama Hajiya Bilkisu tare da saka mata ankwa a hannu suka tusa ƙeyarta tana kuka tana komai amma ko tausayinta babu a tare da su kawai ingiza ta suke yi kamar za su cinƴeta ɗanye…..

Gaba ɗaya Faisal sai ya ji jikinsa ya mutu ya rasa mai yake yi masa daɗi, domin har yanzu akwai sauran rububin son Hajiya Bilkisu a cikin ransa duk da tsantsar butulcin da ta yi masa a rayuwa…

 

 

BAYAN KWANA UKU

 

Faisal ne da Barrister Shaheedah a zaune a falonsu suna kallon tv, BBC HAUSA ne suke labarai gaba ɗaya hankalinsu yana kan tv din. Ji suka yi ɗan jaridar yana cewa

“Kotu ta yankewa matar marigayi Alhaji Hashim mai dala hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa zarginta da kashe shi har lah…” Bai kai ga ƙarshen labarin ba Faisal ya kashe tv ɗin yana dafe kansa da ya sara masa ciwo lokaci guda, Barrister Shaheedah kuwa fashewa da kuka ta yi ta tashi ta shige cikin dakinta.Gaba ɗaya yinin ranar su Faisal ba su yi shi a cikin walwala ba, har su Goggo sai da suka jinjina abin tausayin Bilkisu gaba daya ya kama su, ba ta da kowa a Najeriya da ya wuce su Faisal shi yasa suka shiga tsananin damuwa bisa hukuncin da aka zartar mata, haƙiƙa Faisal da yana da halin da zai ceci Hajiya Bilkisu da tuni ya ceceta sai dai babu hali idanu ne kawai nasa….

 

 

BAYAN WATA ƊAYA

 

Barrister Shaheedah ce ta tashi jikinta duk babu daɗi, ga kasala da tashin zuciya da suke damunta. Ganin haka yasa Faisal ya kirawo likitansa domin ya duba ta, gwajin farko ya tabbatarwa da Faisal tana ɗauke da ciki wata biyu…

Sosai Faisal yayi murna tare da yiwa Allah godiya, zai samu zuri’a tare da matar da ya fi so a cikin mata, Anwar ma da aka faɗa masa an kusa haifa masa sabon baby kullum murna yake tare da ɗokin yaushe Ummarsa za ta haifo masa babyn sai dai ta kwantar da hankali amma duk da haka kullum sai ya tambaya.

Sosai Faisal yake tarairayar Barrister Shaheedah tare da bata kulawa ta musamman, har cikin nata ya cika wata tara…

Ranar Juma’a da safe nak’uda ta taso mata, nan da nan kuwa Faisal ya ɗauke ta sai asibiti, ba ta daɗe tana naƙudar ba Allah ya sauke ta lafiya ta haifo kyawawan ƴaƴanta su biyu…

Identical twins kamar su ɗaya sak kamar an tsaga kara, mace da namiji ne.

Murna a wajen Faisal da sauran ƴan uwa da abokan arziƙi ba a cewa komai, da ranar suna ta kewayo aka raɗawa yaran suna…

Namijin aka saka masa sunan mahaifin Faisal wato Muhammad Sani amma ana kiransa da Halim ita kuma macen aka raɗa mata sunan Umma mahaifiyar Barrister Shaheedah SALMA amma ana kiranta ana kiranta Ummi…Mai martaba ma sosai ya ji daɗin samun jikokin da yayi ya rinƙa murna tare da yiwa iyayensu kyaututtuka na musamman…….

 

Haka rayuwar wannan ahali ta cigaba da gudana cikin tsafta da kwanciyar hankali, Faisal ya zama Daddy Barrister Shaheedah ta zama Umma……

 

 

*Tammat bihamdillah*

 

Alhamdulillah anan na kawo karshen wannan littafin nawa mai suna AYI MIN ADALCI BOOK 2 abinda muka karanta dai-dai Allah ya bamu ladan abinda muka yi kuskure Allah ya yafe mana gaba ɗaya…….

 

 

Duk mai bukatar complt BOOK 2 kai tsaye yayi magana ta cikin wannan number 07069475482 ɗari uku ne #300 babu tsada sai na ji daga gare ku…..

 

 

*HUSSAIN YUSUF*

2347069475482

Add Comment

Click here to post a comment