Baa San Maci Tuwo Ba Hausa Novel Complete
A SAN MACI TUWO BA…..* sai miya ta k’are.
Labari ne mai daukar hankali fad’akarwa da nishad’antarwa daga taskar
*MARYAM A SALIS* (Ummu Mashkur)
Marubuciyar *SUHAILAT*
Rudin shed’an
HAK’URI NA YA K’ARE
MANAZARTA
*WRITERS ASSOCIATION
*M. W. A*
Kungiya d’aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoyan ta.
Ina godiya ga Allah daya bani ikon fara rubuta wannan littafin Allah ya bani ikon rubuta alkhairi ameen da ptn zaku biyo ni don jin irin salon labarin……ummu mashkur ce
Beelal Book 2 Hausa Novel Complete
*Bismillahir rahmanir rahim*
Pg1&2
Free page
A tsaye take bakin titi tana jiran abin hawa duk Wanda ta tsayar baya tsaya wa hakan kuma baya rasa nasaba da weather da ake ciki lokaci ne na damuna haka jiya aka kwana ana tafka ruwa yanzu haka ma yayyafi akeyi kad’an-kad’an.
Ta gyara tsaiwar ta tare da duba agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunta, taja d’an k’aramin tsaki lokacin da take bud’e y’ar k’aramar umbrella da take hannun ta.
Wata sullu6e6iyar mota ta danno a matsiyacin gudu, duk iya k’ok’arinta na janye jikinta saida motar ta fallatse ta da ruwan kwatamin da yake kwalabatin Wanda ya had’e da ruwan k’atuwar kwatar dake gefen titi
Cikin tsananin 6acin rai tabi jikinta da kallo taga yanda akayi mata sabon wanka da ruwan kwatamin.
Juyowa tayi tabi motar da kallo sai taga an tsayar da motar gaba kad’an, da sauri ta k’arasa wajen motar, kusan minti 5 ba’a bud’e ko murfin motar ba hannu tasa tayi knocking a hankali glass d’in motar ya zuge, wani had’adden gaye ya bayyana fuskarsa babu alamar fara’a.
Itama ta tsuke kyakkyawar fuskarta kafin tayi magana ya wullo mata bandir d’in kudi ji kake tauu! A fuskar ta.
Kafin tayi wani yunk’uri ya figi motar a million, Wanda hakan ya sanya harda mayafinta aka fincika Wanda ya mak’ale a jikin motar ita kuma ta fad’i can gefe.
Allah ya taimaka bata ji ciwo ba, sai dai ta d’an kurje , ta mik’e da sauri ganin mutanen gurin sun far binta da kallo, bandir d’in kudin ta d’auka ba don tayi amfani dasu ba sai don ta d’auki alkawarin sai ta rama abinda akayi mata, sannan ta warware d’an kwalinta da yake babba ne ta yafa cikin sauri ta koma lungun su.
Tana shiga gida band’aki ta shiga,
umma na magana amma saida ta fito ta fad’a mata kwata ta fad’a umman ta ta6e baki “to ki daiyi sauri ki tafi karki janyo a kore ki a wajen aikin.”
Murmushi tayi bayan tagama shiryawa tayi mata sallama ta fita.
Tana godewa Allah da yasa umma bataga wadannan kudin ba, ta d’auki alk’awari koma waye shi yayi mata wannan wulak’ancin sai ta rama sai ta nuna masa kud’i ba wata tsiya bace face daud’ar duniya kuma kud’insa basa gabanta k’ima da darajar da Allah ya bata a matsayin ta na y’ar adam ya fiye mata komai.
Wayar ta ce tafar ringing ta daukar cikin sauri ganin MD ne cikin girmamawa tace.”barka da safiya yalla6ai.”
Bai amsa gaisuwar ba yace.”Hafsat kina inane lokacin program fa har ya gota gashi bak’on mu yazo kuma kin san d’an babban gida ne ba ya son jira.”
“I’m sorry yalla6ai na samu matsalar abun hawa ne.”
“Ok yanzu kina ina.”
“Ina titin unguwar mu. ”
“Bari na turo a d’aukeki.”
Yana gama fad’in haka ya kashe wayar, cikin minti 10 motar gidan radion su ta iso ga mamakin ta MD yana ciki, ta gaishe shi cikin girmamawa dukda ta fahimci kamar yana cikin damuwa.
Motar tana tsayawa ta fito bayan an gama parking, kai tsaye office d’in su ta nufa don had’a file’s d’in da zatayi program d’in dasu yanzu .
Da sallama ta shiga husnah ta amsa kafin tace.”kun had’u da MD kuwa.”?
Hafst ta kalleta me yasa kika tanbaye ni.”?
“Saboda zuwan sa biyu yana nemanki yau kema zaki sha fad’an sa.”
Murmushi hafsat tayi lokacin da take had’a file’s d’in tace.”kinga kuwa har gida yaje ya d’auko ni tare muke dashi.”
Husna ta zaro ido “ke don Allah? Shi yasa dai su fadila suke cewa sonki yake saboda da wata a cikin mu ce tayi wannan late din da tasha fad’a yau.”
Murmushi hafsat tayi “Ku kuka sani da gulmarku dai.”
Ta fad’a tana kokarin fita daga office d’in.
MD ne ya shigo fuskar sa babu wal-wala ya dubi hafsat yace.”kinga zuwanki late yasa MU’UTSIM SULEMAN SULTAN ya gaji da jira yayi fushi yanzu haka cewa yayi na kira masa ke, ina tsoron abinda zaiyi miki saboda shi bashi da hak’uri.”
Hafsat tace.”karka damu yalla6ai muje na bashi hak’uri babu abinda zai faru insha’allah.”
MD yai gaba hafsat da husnah suka bi bayansa kai tsaye parking space suka nufa tunda ga nesa ta hango motar da aka bigeta don haka ta kara sauri don ta tabbatar, aikuwa motarce don ga mayafinta mak’ale a gefen motar wata k’ila ma ba’a kula dashi ba.
Dukda gani d’aya tayi masa baza ta kasa gane shi ba tunda ga kayan jikinsa nan.
MD ya matsa kusa dashi, ya juya baya da alama ya gaji da jira, cikin girmamawa yace.”ranka yadad’e gata nan nakira ta tabaka hak’uri.”
Baiyi masa magana ba sannan kuma bai jiyo ba, ita kam hafsat tsayawa tayi tana tunanin yanda zata rama cin zarafin da yayi mata.
Shiru yaji yayi yawa ba’a bashi hak’uri ba, zuciyarsa ta fara tafarfasa, ya jiyo a fusace, kallo daya yai mata ya juya dukda yaso ya tuna inda ya ta6a ganinta amma ya manta.
Ganin tana 6ata masa lokaci, cikin dakusashshiyar murya yace.”ba kiranki nayi don ki k’arewa halitta ta kallo ba.”
Haushi ya cika ta me zata kalla a jikinsa? Bata san lokacinda ta saki wani tsaki ba.
Tsananin mamaki da al’ajabi yasa mu’utasim ya juyo a matuk’ar fusace don tunda yake ba’a ta6a yi masa tsaki ba.
Juyawar da zaiyi sai jin saukar bandir d’in kud’i a fuskar sa yayi, kafin yayi wani yunk’uri ya jiyo zazzak’ar muryar ta na fad’in.
“Ni ba irin kazar da zaka watsawa hatsi na tsatstsaga bace, mutunci da darajar da Allah ya bani a matsayi na na y’ar adam ya ishe ni, kaima da kake wulak’anta kud’i banyi mamaki ba don nasan rashin sanin zafin nema ne, wata k’ila na tsoho ne Wanda yasha wahala ya tara ake masa albazazzaranci dasu saboda baka san zafin nema ba don Allah ina baka shawara ka koma gida ka koyi maintaining.”
Ga tsiyar ka nan wata k’ila zasu yi maka amfani.
Tana gama fad’in haka ta fisgo mayafinta dake mak’ale jikin motar ta juya da nufin barin gurin.
Ganin garada tayi sun zagaye ta, masu fushi da fushin wani (bodyguards) suna jiran umarnin oga.
Shi kam mutuwar tsaye yayi lallai yarinyar nan bata san waye shi ba tabbas ta tsokanowa kanta harma da iyayenta abinda yafi k’arfinsu, a hankali yake takawa yana dosar inda take bodyguards d’in suka dare suka bashi hanya.
Ita kam tana tsaye babu d’igon tsoro a fuskar ta, MD da husnah kam har sun fara tausaya mata yayinda su fadila murna suke za’a ci zarafinta.
Ba tare da 6ata lokaci ba ya d’auke ta da wani azababben mari Wanda ya haifar mata da rashin ji da gani na y’an sakanni, gaskiya kam marin ya shige ta, wani Marin ya kawo mata a d’ayan 6arin cikin zafin nama tayi k’asa da kanta hucin hannunsa yai gaba da d’an kwalinta, yalwataccen gashin kanta ya zubo bisa shoulder d’in ta, d’agowar da zatayi itama tasakar masa mari hannu biyu dama da hagu.
Dukda cewa yaji zafinsu amma yafi jin ciwon abinda tayi masa a gaban yaransa da ma’aikatan gidan radion.
Ya dubi mutanen dake gurin kowa yai k’asa da kansa………
Ummu mashkur yanzu aka fara
Labarin na kud’i ne 300
Add Comment