Littafan Hausa Novels

Meenah Ameen Hausa Novel Complete

Meenah Ameen Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

MEENAH AMEEN

 

 

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

 

Gidan karamci, rubutu don ci gaban al’umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.

 

 

*RUBUTAWA*

 

*Khadeejah Yar mutan kaita*

 

 

_In the Name of Allah, the Most Beneficent, the most Merciful. All the praises and thanks be to Allah, the Lord of the ‘Alamin (mankind, jinns and all that exists). The Most Beneficent, the Most Merciful._

 

 

*Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Allah nagodema daka bani dama na rubuta wannan littafi nawa ya Allah yadda kabani ikon rubutashi kasa nagamashi lafiya*

 

 

 

*HAPPY SALLAH*

 

__Inayiwa daukacin musulmai barka da sallah fatan kowa ya yi sallah lafiya Allah ubangiji yakarbi ibadunmu yasa munyi karbabiya Ameen_

 

Jarabta Hausa Novel Complete

 

*Inayiwa daukacin Jama’ar Kungiyar NOBLE WRITERS ASSOCIATION barka da Sallah fatan munyi ibada karbabiya Allah yabamu ikon ci gaba da fadakarwa da ilimantar da mutane Allah yakaramana hazaka da baserah baki dayanmu yakara hada kanmu Amen ya hayyu ya qayyum*

 

 

 

 

Labarin *MEENAH_AMEEN* kirkirarran labari ne dana zauna na tsara abina dakaina, banyi da nufin tozarci akan kowa ba

 

 

 

 

“`Bismillahir Rahmanir Rahim“`

 

 

 

 

*PAGE___1&2*

 

 

 

 

 

A hankali yake kurbar tea din dake hannunsa sosai ya maida hankali kan laptop dinsa, da alama abunda yakeyi yana da muhimmanci sosai.

 

Shigowa ya yi falon nasa wanda yake dauke da kayatattun kujeru ash color ne hakama fantin dakin ash ne sosai falon ya hadu, karasawa ya yi cikin falon fuskarsa dauke da fara’a ya karasa wajan ya yan nasa tare da zama gefansa yana murmushi

 

“Good morning babban Yaya.” Ya fada yana kallon yayan nasa wanda tinda ya shigo be daga ido ya kallesaba.

Be amsa masaba kuma be kallesaba, kwabe fuska ya yi tare da tashi ya koma bakin kofa dan yasan laifinsa

 

“Assalamualaikum,” ya ambata sannan ya shigo.

Ba tare daya kallesaba ya amsa sallamar tasa. Akaro na biyu ya karasa ya zauna kusa da Yayan nasa yace

 

“Babban Yaya nafa yi sallamar kuma bazaka kalle niba” ya fada yana turo baki kamar mace.

A hankali ya dago lumsasun idanuwansa kamar mai jin bacci ya saukesu akan kanan nasa, da sauri Kanan nasa ya sauke idanuwansa a kasa dan yasan kallon tuhuma Yayan nasa yake masa be karashe tunanin saba yaji muryarsa ta ratsa dodon kunnansa.

 

“Jiya da daddare ina kaje baka dawo gida da wuriba” ya tambayesa still idanuwansa na akansa.

 

Sosakai ya farayi alamun beda gaskiya “am…uhm..Daman.. gidansu Al’amin naje” ya karasa Fadi yana inda inda kunnansa yaji ankama kara ya saki

 

“Am so sorry Babban Yaya wallahi bazan karaba” ya fada yana rike hannun yayan nasa

 

“Hisham bakajin magana ko kullum kana so kasaman ciwon kai ko?” Yayan nasa ya fada ransa a bace still hannunsa na rike da kunnan Hisham din.

 

“Please kayi hakuri bazan karaba nama alkawari” Hisham ya fada yana kallon yayan nasa, a hankali ya sauke hannunsa daga kunnansa sannan ya kamo hannunsa ya zaunar dashi saman kujerar da yake akai yace

 

“Oya zokai breakfast” ya fada yana hadamasa tea a cup” cike da so da kauna Hisham yake kallon Yayan nasa amsar tea din ya yi dan dama yunwa yakeji . Ture laptop din dake gabansa ya yi sannan ya tashi ya kalli Hisham yace

 

“Kayi sauri ka gama kaje ka shirya na ajeka a school hope kagane” yana fadin haka ya shige bedroom dinsa. Wanda yake a kawace kai tsaye toilet ya shiga domin ya shirya.

 

Yana fita shaf shaf Hisham ya ida break dinsa dan yasan Yayan nasa bayason jira kai tsaye dakinsa ya nufa shaf shaf ya shirya kanan kaya ya sanya sannan ya dauko jakar laptop dinsa ya rataya ya fito sosai ya yi kyau main falon ya fito karaf idanunsa suka sauka kan Aliya da take tayiwa Talatu Masifa wadda a haife ta haifeta amma bataga wannan girmanba ta dage sai zaginta take.

 

“Ke wace kalar jakace kazama bagidajiya na saki kiyiman abu amma da yake ke sakaraice zakiman kwaba,” Aliya ta ida maganar tana hura hanci. Da sauri ya karaso wajan da suke

 

“Haba Aunty Aliya mi ta yi maki haka kike zaginta ai ko ba komai taci albarkacin tsufan…”

 

“Kai dallah malam dakata waya sakaka a ciki shishshiga ko angayama nanma wurin ya….” Maganar ta makale sakamakon ganinsa da ta yi fuskarnan tasa a hade babu alamar annuri atattare da ita ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallonta. Mukut ta hade wani miyau. Idanuwa ya zuba mata batare da ya yi maganaba da sauri tabar wajan, sosai Hisham abun yai masa dadi. Juyawa ya yi yabar falon da sauri Hisham yabi bayansa cikin azama. A mota ya iskesa shiga ya yi yana shiga yaja motar da gudu ya fice daga gidan.

 

A firgice ta shiga dakinsu kan gado ta fada tana sauke ajiyar zuciya Zainab dake zaune tana chat ta kalleta cike da mamaki tace

 

“Ke lafiyarki kuwa kika wani shigowa mutane daki a gigic”.

 

“Hmmm kika sani ko ta yi gamo da zakin gidan ne ya firgitata” Aisha ta fadi haka tana kallon Aliya

 

“Hmmm kudai ku bari Allah ya taimakeni da yau na daku agidan nan”

 

“Miya farune wai” zainab ta tambaya dan taji karin bayani

 

“Hm kunsan mi yafaru” baki suka hada wajan fadin “Aa.” Su duka

 

“Inama Talatu masifa basai ga wannan munafikin yaron ya fitoba aikuwa na dawo kansa ai kamar ance na juya mukayi ido hudu dashi fuskarnan tasa babu annuri wallahi saura kadan na saki fitsari ai bansan sadda na baro wajanba” ta karashe maganar tana zazzare ido, mi Aisha zatayi banda dariya sosai take dariya harda rike ciki.

 

Hade fuska Aliya ta yi tace

 

“Kinga Aisha banason iskanci ya za’ayi kisani gaba kinaman dariya sai kace kinga sabon kamu.”

 

“Yi hakuri sister dole abun yaban dariya dan ban manta haduwata dashi ba.”

 

“Hmm nikam bakusan wani abuba” Zainab ta fada tana murmushi

 

“Saikin fada” suka hada baki

 

“Wallahi nikam Sosai Yaya *AMIN* ke burgeni wallahi ina bala’in sonsa shiyasa na gayawa Momynah” da sauri suka juyo suna kallonta baki dayansu da mamaki

 

“Tabbas yau na tabbar da bakida hankali Zee ki rasa wanda zakiso sai wannan mutumin mai bakar zuciya” Aliya ta fada tana kallon Zainab da keta smiling. Tsaki Aisha ta yi

 

“Hmm ki kyalleta Aliya bakuwace shiyasa batasan wanene *Babban Yaya* ba wallahi”

 

“Inasonsa a haka kuma insha Allah shima zai soni ku zuba idanu ku gani.” Sakin baki sukayi suna kallonta dan sun lura da gaske take tabe baki sukayi sannan sukaci gaba da harkokinsu.

 

 

Ta fiya suke babu mai magana acikinsu sai sautin suratul Rahman dake tashi cikin motar. Dai dai gate din school dinsu Hisham ya yi parking. Kallon Yayan nasa Hisham ya yi haryanzu dai yanan fuskarnan tasa a dauke, langwabar da kai ya yi

 

“Babban Yaya bana da kudi kudina sun kare,” kallonsa ya yi ba tare da yace komaiba ya zaro kudi masu yawa daga aljihunsa ya damkawa kanan nasa a hannu

 

“Take care your self,” ya fada yana kallon kanan nasa cike da so da kauna

 

“Insha Allah Yaya zankula” yana fadin haka ya fice daga motar saida yaga shigarsa class sannan yabar harabar makarantar kai tsaye katafaren Asibitinsa ya nufa yana isa yai parking a parking space sannan ya fito hannunsa dauke da rigarsa ta doctor da laptop dinsa kai tsaye cikin asibiti ya shiga gaisheshi nurse din suka shigayi hannu kawai yake tagamasu batare da ya yi maganaba direct office dinsa ya nufa wanda aka lika sunansa jiki.

 

“Hmm kawata wallahi wannan mutumin ya cika daukar kai da fadin ran tsiya ko dan yaga yana da kyau” wata nurse ta fada tana yatsina fuska.

 

“Hmm kema kin fada amma duk da haka wallahi gayen ya hadu inama ace yace yana sona ai danaji dadi” kwashewa da dariya ta yi

 

“To wallahi ko a mafarki wannan yafi karfinki”

 

“Mtswww nifa matsalata dake kenan wallahi kikasan abun Allah” ta fada tana harar sister maryam

 

“Allah yabaki hakuri da wasa nake” ” shiknn naji abar maganar.

 

 

 

Hawayen dake kwaranya ga idanunta tasa hannu ta goge kallon mahaifiyarta dake kwance rai hannun Allah ta yi, hawayen dake zubo mata taji ana share mata da sauri ta dago idanunta wa’anda sukai ja saboda kuka

 

” *Meenah* ki daina kuka kiyiman addu’a ahaka kaddararmu tazo mana” kara rushewa da wani sabon kukan ta yi cikin shasshekar kuka tace

 

“Mama ya zanyi idan na rasaki rayuwata tana cikin garari bani da kowa bani da komai sai ke sai Allah”

 

“Meenah kekam kike da kowa tinda kina da ubangiji kizama mai da kakiyar zuciya ko bayan ba raina kizama ja jirtacciyar mace kuma kizama mai kare mutuncinki aduk inda kika tsinci kank…..” Bata karasaba suka jiyo hayaniyar mutane, zunbur Meenah ta mike zata tashi rike hannunta Mama ta yi

 

“Na sani karshen rayuwata yazo ki gudu kinjiko yarta karsu hada dake…” Warin Petri din da sukajine yasa hankali Meenah ya kara tashi cike da tashin hankali

 

“Mama dan Allah kitashi mu gudu kada su konamu bazan iya tafiya na barkiba” cikin kuka take maganar kamar wadda za’a zarewa rai.

 

“Ki gudu nace ko” Mama ta fada tana tura Meenah daga jikinta amma ina taki sakinta dago fuskar yar tata ta yi cikin tsananin tausan kansu ta ce

 

“Meenah kada ki damu dani ki tafi kawai Allah na tare dake”

 

“Waimi kuke jirane ku kona yan banza mana, dallah bani ashanar nan kagani” daya daga cikin mutanen dake kofar gidan atsaye suna hayaniya ke maganar tare da fizge ashanar dake hannun na kusa dashi kunnah ashanar ya yi tare da wurgata cikin gidan kan kace kobo wuta ta kama bal_bal cikin matukar tashin hankali Meenah ta kalli mahaifiyarta ta

 

“Mama bazan iya tafiya na barkiba gara su kashemu mu duka” cikin tsawa

 

“Meenah nace kibar gidan nan yanzu ki gudu nace ki gudu” Mama ke maganar cikin tsawa ga radadin ciwo gashi wutar ta kusa kawowa inda suke. Raba jikinta Meenah ta yi dana mahaifiyarta tana hawaye tafiya takeyi tana wai wayen Mama zuciyarta na mata nauyi saida tazo saitin bangon da zata hau wanda beda wani tsawo sosai ta jiyo muryar Mama

 

“Meenah duk rintsi ki kare mutuncin kanki Allah na tare dake bazaki taba wulakantaba..” bata ida jin mi zata fadaba taji hayaniyar mutanen da sauri ta kama bangon ta dire gashi darene batasan ina zatayi ba gudu ta keyi kamar ranta zaifita ba tare data ankara ta bigi wani Katon icce atake tafadi wajan a sume.

Add Comment

Click here to post a comment