Zuciyar Mugu Hausa Novel Complete
ZUCIYAR MUGU
*TRUE LIFE STORY*
WRITING BY
*MARYAM ‘YAR MAMA*
*ZAMANI WRITER’S*
&
*BILKISU Z. Ya’U
ZAMAN AMANA WRITER’S*
_Bismillahir rahmanir raheem_
_*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH (S.W.A) DA YA ARA MANA RAYUWA DA LAFIYA, YA UBANGIJI MUNA GODIYA A GAREKA
_*YA UBANGIJINMU KA YI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)*_
*KAMAR YANDA KUKA GANI A SAMA WANNAN LABARIN YA FARU DA GASKE, ZALUNCI, BUTULCI, CIN AMANA, YAUDARA, TSANTSAR TAUSAYI, DUK A CIKIN WANNAN LABARIN, SAI KU BIYO MU DOMIN JIN ABINDA YA K’UNSA.*
Page 1 to 5
Alhaji Balarabe nera shahararren mai kud’i ne, nagartaccen mutum ne, mutum ne mai yi wa mutane hidima, wanda sam dukiyar shi bata rufe mishi ido ba, akwai taimakon na k’asa da shi, baya k’yashin fitar da dukiyar shi ya taimakawa talaka, ga kyauta a tak’aice dai Allah ya had’a mishi duka biyun, ga dukiya me tarin yawa, ga kuma hali na k’warai.
Abokin Mijina Hausa Novel Complete
Alhaji yana da mata d’aya mai suna Hajiya Jameela, suna da yara biyar, akwai Yusuf, sai Alaweeyya, sai Seeyama, sai sadeeq, Sai auta me suna Aisha.
Alhaji da Hajiya wato iyayen su Alaweeya suna matuk’ar k’aunar yaran su, ko kad’an basa yarda wani abu ya tab’a yaran, suna samun kyakkyawar kulawa daga cikin gida yar a waje, idan suna cikin gida babu abinda suke yi na wahala komai se a yi musu, kuma babu abinda suka nema suka rasa komin tsadar sa, a waje kuwa, duk inda zasu saka k’afa to da masu tsaron su, a tak’aice a koda yaushe kuma a ko’ina yaran suke suna k’ark’ashin kulawar mahaifin su.
Wannan tsantsar k’aunar ita ta haifar da shak’uwa mai tsanani a tsakanin yaran da iyayen, dukkanin su yanzu haka suna karatu a fitacciya, kuma shahararriyar makarantar da ta yi fice saboda kyanta da kuma shahararta, masu karatu cikinta kuwa sai ‘ya’yan manya, wato ‘ya’yan attajirai, wannan kenan.
Yau Asabar ranar hutu ce, Dadyn su yana gida ba inda ya je, zaune yake tsakiyar yaran shi, banda zuba mishi shagwab’a ba abinda suke, Alaweeya ce tace ” Dady dan Allah a fita da mu, mu yi shopping,” Seeyama tace ” A’a Dady wajen wasa zaka kai mu,” Yusuf yace ” Dady rabu dasu sarakan son yawo kawai, ” Aisha auta cikin maganarta ta yara tace ” Dady dan Allah muje zansha sweet, wanda ka siya mun sun k’are, suna cikin magana kafin Dady yace komai sai ga Mumy ta shigo falon inda suke zaune ta k’araso itama ta zauna, kallon yaran ta yi, sannan ta kalli Alhaji tai murmushi, tace ” Dadyn mu me ake tattaunawa ne ba’a nemeni ba?” Dady yai dariya, sannan yace ” yaranki ne suka dage a fita dasu yau su yi siyayya,” Mumy tace ” ai kai ka saba mana da hakan, duk lokacin da kake gida kana fita da mu, dan haka yau ma a fita da mu ko muita yi maka kuka ko ba haka ba yarana? ” ta juya tana tambayar yaran, kamar had’in baki a tare suka amsa suka ce ” yes Mum. ”
Dady ya yi dariya yace ” wato kece kika shagwab’a min yara koh? ”
Mumy tace ” wa, ni? ba ruwana kai ne ka shagwab’a mu dukkan mu har da ni,” Dady ya kalli yaran yace ” to yanzu abinda za’ai kowa yaje ya d’auko litattafan shi gaba d’aya ku biya mun d’aya bayan d’aya, duk wanda ya karanta lafiya lau to da shi zamu tafi,” da gudun arzik’i suka tashi gaba d’ayan su, zuwa d’auko litattafan nasu banda Yusuf da Mumy, Dady ya kalli Mum da Yusuf yace ” Ku bazaku bimu ba kenan? ”
Mum tace ” au wai har da ni?”
Dady yace ” ai har da ke na shagwab’a, dan haka kema Allah sai kin yi karatu zamu fita da ke, ya kalli Yusuf yace kaima kaje ka d’auko naka litattafan.”
Da yake Yusuf ya san be iya nashi karatun ba sai yace “Dady kuje kawai ni ba zan je ba,” Dady yace ” d’auko littafan ka karanta in baka iya ba to dole sai mun fita da kai tunda fitar ce yau baka so.”
Sai da kowa ya karanta litattafan shi daga na boko har na islamiyya, Mum kuwa Qur’ani ya sata ta karanta, sannan bayan sun gama karatun dukkan su suka shirya harda Dady suka fita, ba su suka dawo gida ba sai da yamma wajen k’arfe biyar da rabi.
Suna dawowa bayan sun yi sallar magriba da isha’i sannan suka had’u suka ci abinci, suna cikin cin abincin ne sai wayar Dady tai k’ara, yana dubawa yaga Tukur ne ke kira, da saurin shi ya d’aga fuskar shi d’auke da murmushi, bayan sun gaisa Tukur yace ” dama mun kammala karatu ne shine nace bari na kira in fad’a maka a turo min da kud’i zan taho gida nan da sati d’aya.”
Dady yace ” anya, ai shekarun da zasu d’aukeku har ku gama karatun basu cika ba da sauran shekaru Tukur fad’a mun gaskiya dai. ”
Tukur yace ” sun rage shekarun ne, in baka yarda ba ka tambayi abokina, gashi a kusa da ni.”
Alhaji yace ” shikenan Allah ya kaimu, zan turo maka da kud’in, zan yi maka transfer, suna kammala wayar yai mishi transfer a take anan.
Yaran gidan kuwa da ita kanta Mumy jikinsu duk ya yi sanyi jin Tukur zai dawo, da yake wayar Alhaji akwai k’ara, idan yana waya ana jin komai, shiyasa duk hankalin su ya tashi, in suna k’aunar dawowar shi to suna k’aunar mutuwar su haka.
_topha, wai wanene wannan Tukur d’in? Menene matsayin shi cikin wannan dangin? Meyasa kowa baya farin ciki da dawowar tashi? Ku biyo mu domin jin ci gaban._
Mune naku
*’Yar mama
ZUCIYAR MUGU*🖤🖤
*TRUE LIFE STORY*
STORY & WRITING
BY
*MARYAM ‘YAR MAMA*
*ZAMANI WRITER’S*
&
*BILKISU Z. Ya’U
ZAMAN AMANA WRITER’S*
_Bismillahir rahmanir raheem_
Page 5 to 10
WANE NE TUKUR?
Tukur k’ani ne ga Alhaji Balarabe nera uwa d’aya uba d’aya, kuma tun yana k’arami yake zaune a hannun Alhaji Balarabe.
Tun Tukur yana jariri Allah ya d’auki ran iyayen su.
Alhaji Balarabe yana matuk’ar k’aunar d’an uwansa.
Gata kam na duniya babu irin wanda Alhaji bai wa d’an uwan shi tukur ba, tun baida komai har Allah ya azurta shi da dukiya me tarin yawa.
Lokacin da Tukur yai wayau Alhaji Balarabe ya sa shi makarantar boko da ta islamiyya, se dai tun yana yaro tukur baya ji, kuma sam baya maida hankali kan karatun shi, ga neman fitina da tsokana kala-kala.
Alhaji ya kammala karatun shi cikin nasara, domin yana gamawa ya sami aiki me kyau, wanda farawa da iyawa Allah ya sawa dukiyar shi Albarka taita bunk’asa.
Lokacin da ya fara aiki ne Allah ya had’a shi da ‘yarinya ta gari ya yaba da tarbiyarta da natsuwarta, had’i da iliminta, hakan yasa suna dai-daita kansu babu b’ata lokacin aka sa rana.
Bayan an sha biki amarya ta tare.
Tunda amaryar Alhaji ta shigo gidan nan hak’urin zama kawai take yi da tukur ga rashin kunya da nuna gadara a kan komai na cikin gidan.
Amma da yake hak’urarra ce bata tab’a kai k’arar shi wajen Alhaji Balarabe ba, se dai in ya yi a gaban Alhajin ya gani sannan zai kwab’a mishi, duk da bema cika yi mata ba idan Alhaji na gida sai baya nan, tunda yana d’an jin maganar yayan nashi.
Bayan ‘yan kwanaki Alhaji Balarabe ya kai shi wata makarantar kud’i me kyau, se dai sam baya maida hankali a karatun, hakan yasa yai tunanin canza mishi makaranta a tunanin shi ko be gane karatun ne, sai ya zamana kamar ma ‘yanci da dama ya samu na shek’e ayar shi, dan yanzu har shaye-shaye yake yi.
Haka rayuwar su ta ci gaba da kasancewa kwata-kwata Matar Alhaji Balarabe bata jin dad’in zaman Tukur a tare da su, gashi ya saka musu ido, ga kishi duk abinda Alhaji yai musu sai ya nuna kishi da hassadar shi a kanta.
Kuma ya tsani yaga Alhaji na facaka da dukiyar da Allah ya bashi, kuma baya k’aunar yaga yana taimako da ita.
A haka har Allah ya azurta su da yara har biyar, se dai har lokacin halin Tukur be canja ba, sai ya zamana tsangwamar har da yaran Alhajin yake yi mawa, ya tsani shak’uwar da suka yi da Alhajin, sannan makarantun da duk aka sa shi daga k’arshe koro shi ake yi, wad’anda suke da lambar Alhaji Balarabe kuwa sai su kira shi su fad’a mishi zai b’ata musu tarbiyyar yaran makaranta shiyasa suka sallame shi.
Alhaji ya yi fad’an har ya gode Allah, bayan kwana biyu Tukur da kan shi yazo wa da Alhaji magana akan yana so ya tura shi waje karatu, Alhaji yace bazai yiwu ba anan d’in ma ya aka k’are balle ya fita waje, sai Tukur ya nunar mishi da muddin ya kaishi can zai dage yai karatu, Alhaji yace in har yana so ya kaishi waje sai ya maida hankali anan ya gama secondary school d’in shi yaga ya fitar da sakamako mai kyau sannan zai yarda da buk’atar shi, koda Tukur yaji haka yace ya amince, aka saka shi wata makarantar, ikon Allah kuwa ya dage da karatu ba dare ba rana, kuma daga k’arshe kuwa ya fitar da sakamako mai kyau, hakan yasa dole Alhaji ya cika mishi alkawarin shi domin harga Allah a tunanin shi yanzu kuma yana son karatun ne, wannan shine dalilin fitar da shi waje, daga uwar gidan har yaran gidan tsoron shi suke ji sam basa farin ciki da dawowar shi, shi kanshi Alhaji ya ji sak’at da baya nan, amma ya zai yi naka sai naka, wannan kenan.
CI GABAN LABARIN
Muje zuwa
Mune naku
*’YAR MAMA*
&
ZUCIYAR MUGU
*TRUE LIFE STORY*
STORY&WRITTING
by
*MARYAM YARMAMA*
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION*
&
*BILKISU Z.Ya’U
*ZAMAN AMANA WRITER’S*
Page 11-15
Washegari Alhaji yasa driver yaje ya dakko tukur a airport,tukur kyakyawan yarone ajin farko,abinka da fulani farine kuma dogo mai faffadan kirji gashi da sexy eye,yanada tarin suma wanda kullum cikin gyara sumar yake,.yanayin shigarsama ya nuna tantirin yarone..
Yana shigowa cikin gidan ..kowa cikinshi yaduri ruwa banda alaweeya da ko tsoranshi bataji .
Cikin fara’a Alhaji ya rungumeshi don yana matukar son tukur sosai sannan yace”bakin turai har angama karatun kenan”.
Cikin jan aji tukur ya saki alhaji ya zauna akan luntsumemen kujerar yace”eh ai karatunsa ba wuya”.
Cikin karkarwar baki momy da yaranta suka fara gaishe da tukur ,a yangace yake amsawa idonsane ya sauka akan alaweeya dake zaune ba dankwali akanta gashinta yasha gyara sai latse latsen waya take.sanye take da riga gown tasha kyau .
Momy dataga tukur sai kallon Alaweeya yake cikin tsoro ta dan doki cinyar Alaweeya tace”ke bazaki gaishe da karamin dadynki ba”.
Tsaki Alaweeya tayi tadago da idonta tana karewa tukur dake kallonta kallo sannan ta tashi tace”wannan dan iskan bai cancanci yazama ubana ba,Bazan gaisheshiba wallahi”.*
Alhaji ya kalli alaweeya ya daka mata tsawa yana”ke kinsan dawa kike magana,be carefull with me,zaki gaisheshi kosaina saba miki”.
Bude baki Alaweeya tayi tamkar zatayi kuka ta nuna tukur tana”Dad saboda wannan gayen zaka min tsawa,kasan a rayuwata yanda na tsani amin tsawa .shine zakamin tom wallahi ko za’a kasheni bazan gaisheshiba”.
Daukar wayarta tayi ta harari tukur tahau sama tabar falo din,momy dai da yayanta ko motsi basu iyayiba.
Lumshe ido tukur yayi don gaskiya ya yaba da kyawun Alaweeya da surarta “haka alaweeya ta girma”.
Alhajine yasa masu aiki suka gyarawa tukur part dinshi a upstair,suka bashi abinci kala kala.
Washegari an hallara anacin abinci a dinning harda tukur da yaketa satan kallon Alaweeya.
“Daddy dama a makarantane akace mu kawo kudin t.shirt na graduation din mu,kowa ya kawo nice ban kawoba”. Alaweeya ce cikin shagwaba take fadin haka yayin da sukecin abinci a di.
Alhaji ya kalleta ya murmusa yace “ke meya hanaki fada iyeh?bana tura miki dubu dari a account dinkiba”.tukur yanajin Alhaji ya turawa Alaweeya dubu dari a account dinta ,ya murtuke fuska ya buga teburin cin abincin wanda yasa su momy suka tsorata sannan ya aje spoon din dayake cin abinci yatashi yabar wajen cike da bacin rai .
Kowa dake dinning din suka bisa da kallo…yayinda alaweeya ta bi bayansa da harara sannan ta kalli abbanta cikin shagwaba tace “abba nifa dubu dari ba abinda zaimin…please ka daure ka karamin wani,nifa banason taba kudin Account dina don so nake ka cikamin insiya mota”.
Dariya duka suka kaure dashi
Abba yayi murmushi yace “to mama zankara miki shikenan hankalinki ya kwanta,keda sadeek da siyama duk zakuji alert yau”.
Dinning din yadauki murna suna ta “thanks you abba Allah ya bude hanya”.
Momy dake sanye da farin medical gilashi tace “Alhaji kanafa sangarta yaran nan,nidai ka rage basu kudi kaji,saboda ran tukur yana baci duk lokacin da kabasu kudi”.
Ko daya abba bai dauki maganar matarsa ba saima cewa da yayi”na taimakawa yan waje ma,nayiwa mutane hidima balle ya’yana farinciki.yayan nan guda hudu su Allah yabani don haka dole in musu abubuwan da sukeso…banda dangi daga TUKUR sai su.su kawai nake dasu aduniya,kuma inada arziki kar inmusu bazaiyuba,shima tukur din ai inamai sosai acikin yaran wana kai karatu kasar waje iyeh ki gayamin”.
Tashi yayi yayinda suka rufamai baya,suka rakasa har bakin harabar gidan ,driver yabudemai bayan mota yashiga..sannan karamar cikinsu humaira tamikomai briefcase dinsa tamai sunba a kumatu…haka driver yaja motar sunamai daga mai hannu..
Haushine yakama TUKUR dake kallon duk abinda sukeyi ta taga.wani bakinciki ya mamaye mai zuciya,matsawa yayi daga bakin windonsa yazauna akan gadonsa yana neman mafita “dole in hargitsa gidannan,dole in kashe Alhaji in mallaki dukiyarsa sannan inyi facaka dashi”.haka tukur ya ayyana aransa …
Baigama fadin hakaba ,Alaweeya tashigo dakin .tsayawa tayi abakin kofa tana mai aikamai sakon harara domin duk duniya ba wanda ta tsana kamar uncle dinta.
Shiko tukur ko damuwa baiyi da kallon da takemaiba,shidai burinsa yacika burinsa na lalata mata rayuwa,don bazai jureba domin ya kwadaitu da kyakyawar surarta . Ahankali tukur yakalli alaweeya cikin mayaudarin murya wanda yake amfani da ita wajen sace zuciyar mace yace “ala….weeya lafiya kika shigomin daki ina matsayin uncle dinki ko gaisuwa babu”.
Wani yarrr alaweeya taji amma tadake ta murguda baki tana” nazone dama in gaya maka karka kara shiga harkata.in abbana yanamin magana ba ruwanka ehe kaji dai”.
A hankali tukur ya taso daga kan gadon abinka da farin mutum dogo hansome guy mai faffadan kirji ga kuma dogan hanci da sexy eye gashi yamata kwarjini…kafa mata sexy eye dinshi yayi yana mai karasowa,itama Alaweeya takasa dauke idonta daga na uncle amma ta dake ta murgudamai baki tace”lafiya kake kallona kamar wani maye,ko acan turan ka koyo maita”….shiru tayi sakamakon ganin tukur ya nufo inda take.
Mune naku
_yarmama
&
ZUCIYAR MUGU
*TRUE LIFE STORY*
STORY & WRITTING
by
*MARYAM YARMAMA*
ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION*
&
*BILKISU Z.Ya’U
ZAMAN AMANA WRITER’S*
Page 16-20
Yana nufowa wajen,Alaweeya tana ja da baya har tazo bango,shima matsowa yayi har suna iyajin numfashin juna yayi murmushi cikin murya mai sace zuciyar mace yace “Ala..weeya an girma shine na dawo ko sanda zuwa babu iyeh haka akeyi”.
Rau rau Alaweeya tayi da ido don duk rashin kunyanta sai yau tsoran Uncle ya shigeta sannan ta kallesa cikin sanyin murya tace”uncle am sorry is mistake”.
Tukur yayi wani shu’umin murmushi yasa hannu a Aljihunshi ya dakko wata yar tagarda ya bude daka gani kasan hodan ibilis ce,daidai fuskar Alaweeya ya fasa,nan Alaweeya ta lumshe ido tayi luuuuu tamkar zata fadi .tarota tukur yayi ya kaita kan gadonsa,cire rigarsa yayi ya haye kan gadon da niyyar keta mata haddi….haka tukur cikin kankanin lokaci ya lalatawa Alaweeya rayuwa (subhanallah).
Wanka yashiga yana murmushin samun nassara..yafito ya shirya cikin wasu arnayan kaya ,kananun kaya harda sarka ya fesa turare ya dauki daya daga cikin motocin gidan yafice zuwa club dinsu na mashaya.
Bayan wasu dakika Alaweeya ta tashi kanta ya mata nauyi ga wani radadi datakeji,da kyar ta tashi kanta taji ya juyawa duba gadon tayi taga duk bedsheet din kaca-kaca da jini ,kuka msi tsuma zuciya tasa tana tuna abinda yafaru sannan tafara tuna nasihar momy:
_”Alaweeya kece babba,karki kuskura wani abu yashiga tsakaninki da wani namiji,karkiga kinada degree kiyi tunanin akwai namijin dazai aureki bayan kin siyar da mutuncinki,no ko bai ganeba sai Allah yasakamai”_
Kuka Alaweeya ta kara fashewa dashi tashiga toilet d’in uncle ta bude shayan ruwan zafi tahada da ruwan sanyi ta gasa jikinta fitowa tayi ta gyara jikinta,Tana nadamar shigowa d’akin tukur, bata gama rufe bakiba tukur yashigo d’akin ya kalli inda Alaweeya ke zaune akan gado tanata ruzgar kuka yafara waka yana wakar _”my body my money na yo own woo baby”_.
Aguje Alaweeya ta taso ta rik’emai kwalar riga tana “wallahi uncle tunda kai ka lalatamin rayuwa, wallahi saika aureni”.
Tukur da yaji kukanta ko ajikinsa ya kalleta ya tab’e baki yace”Tab’ saidai fa kiyi hak’uri nawuce wajen domin ni bana maimaitawa, kuma bazan aurekiba, ai bama aure a tsakaninmu tunda ke d’iyatace”.
A hankali Alaweeya tasaki tukur taja da baya tana kuka maicin rai tana”uncle kasan ni d’iyarkace kuma ka ketamin haddi, macuci azzalumi sai Allah ya sakamin, ka cuceni ka cuci rayuwata”.
Tukur ya daka mata tsawa yace “get out of my room nonsense banza karuwa”.
Arazane Alaweeya ta tashi tana tafiya da k’yar tafice daga d’akin tukur, lek’awa falon gida tayi taga ba kowa tayi sad’af sad’af ta haye upstair d’inta tawuce d’akinta, danno sakata tayi ta shiga band’aki ta d’ora alwala tayi sallah tana mik’a kukanta wajen Allah yasaka mata.
Washegari duk An hallara a dinning banda Alaweeya.
Alhaji ya kalli siyama yace “jeki kiramin auntynki kice tazo muci abinci.”
Siyama tanufi d’akin Alaweeya, a kwance ta sameta sai kuka take tana rik’e da kanta..
Ihu siyama tayi tanufi dinning d’in tana “dady Alaweeya zata mutu ku taimaka” duka su Alhaji suka haura upstair d’in har gware suke suka nufi d’akin Alaweeya banda tukur daya tashi yayi gaba abinsa.
Cikin gaggawa Alhaji yakira likitoci biyu, nan da nan sukazo suna bincikar Alaweeya sannan suka gano matsalar dayake damunta.
‘Dayan likitan ya kalli Alhaji dayayi tagumi cike da damuwa yace “Alhaji bala, gaskiya rashin lafiyanta yayi tsanani anytime zuciyarta zai buga, kuma munga b.p d’inta yakai 99 _(hawan jini)_ gaskiya abin yaban mamaki, meya damu Alaweeya haka har bugun zuciya harda hawan jini”.
Alhaji yashare gumin daya zubomai ya kalli gadon da Alaweeya take kwance ansa mata drip, yace “Nidai ko k’asar turai zan iya fitar da ita indai ‘yata zata samu lafiya, Amma ya za’ayi ace yarinya ‘yar 21 ta kamu da ciwon hawan jini,me Alaweeya ta nema ta rasa iyeh?”
Likitan yacire glass d’insa yace “Alhaji karka damu in Allah ya yarda zata samu lafiya, amma aguji b’ata mata rai.
Haka likitan suka harhada musu magunguna, suka musu Allah yak’ara sauki suka fice.
Kowa zama yayi yana tunanin meyasa Alaweeya b’acin rai..yarinyar da kullum happy girl ce ga zolaya acikinta.
___________♡♡♡____________
“Dama na kira kane domin in baka wani aiki, dafatan ka iya kisa ko?” Tukur yai tambayar.
Wani basamude ne bak’i k’irin dashi ya kalli tukur dake zaune akan kujerar plastic a wajen shakatawa yace”ai ni Na k’ware awajen iya fashi da kissa shiyasa mutane suke kirana da *sharp bullet*,wa kakeso a kashe maka?”
Murmushin mugunta tukur yayi, ya cire bakin glass d’in dake idonsa kyansa ya k’ara fitowa yace “kasan dai Alhaji balarabe ko?”
Bullet yace “waye baisan Alhaji balarabe ba, kodan taimakon jama’ar da yakeyi dole yayi suna”.
Tukur ya gyada kai yace”good to shi nakeso ka kashemin acikin wannan weeks d’in”.
Zaro ido bullet yayi yana “haba yallab’ai mutumin dake yawo da bodyguard tayaya zan iya kasheshi”.
Tukur yace “indai wannan ne karka damu, nasan yanda zanyi ya rabu da bodyguard d’insa, indai ka kashemin shi kanada million biyar”.
Xaro ido bullet yayi yana “million biyar, ai kawai kasa a ranka Alhaji yazama shekakke.”
Dariya sukayi suka tafa, sannan suka d’auki kwalbar barasa sukaci gaba dasha.