Kwantaccen Ciki (Molar Pregnancy) Abunda Yakamata Ku Sani

Kwantaccen Ciki (Molar Pregnancy) Abunda Yakamata Ku Sani

 

 

 

 

 

 

 

 

KWANTACCEN CIKIWatson (MOLAR PREGNANCY

 

MENENE KWANTACCEN CIKI KUMA YA YAKE A MAHANGAR BINCIKE DA ILIMI NA KIMIYYA TA ZAMANI DA KUMA ILIMIN LIKITANCI A MUSULUNCI DA GARGAJIYA?

 

Zan Kawo Bayanin ne Bangare biyu, Da Bangaren Fahimtar Likitocin Zamani da kuma Fahimtar Likitocin musulunci da gargajiya, Saboda haka bayanin zai yi tsayi, Amma zan fara kawo muku Bayanin Binciken Likitocin Zamani, kafin Daga Bisani a karshen Rubutun kuma zan yi Bayanin Abinda Likitocin Musulunci Suka ce kuma suka Dogara da shi tare da Magani gabadaya InshaaAllahu.

 

بسمالله الرحمن الرحيم

 

KWANTACCEN CIKI A MAHANGAR BINCIKEN ILIMIN KIMIYYAR ZAMANI 👨🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️

Gidan Marayu Hausa Novel Complete

Kwantaccen Ciki ko Cikin Molo🫄🏻 Ko Kwantaccen Ciki wani nau’in alamun juna biyu ne da wasu cikin mata kansamu kansu dashi wanda kuma a zahiri gaskiya ba ciki ne na haihuwa ba kamar yadda suke tsammani duk da abun ya tattara dukkan alamomin samuwar ciki na zahiri.

 

Bisa kididdiga adukkan mata dubu “1000” masu ciki🤰🏻 akan sami guda daya🤰🏻 “1” ya zamto cikin molo ko cikin karya…. wanda 999 sune ke dauke da ciki me kunshe da jariri… Viable Pregancy.

 

SHIN YA CIKIN YAKE,🤰🏻 ME KE JAWOSA KUMA ??

 

Wani ciki🤰🏻 ne dake faruwa sakamakon tangardar kwan haihuwa wanda wata kwayar halitta da ake kira TROPHOBLAST a turance da aikinta samarwa da jariri sinadaran abinci da rayuwa acikin mahaifa kan rikide ta hau girma akaran kanta ya zamto tayi girman da ya mamaye cikin mahaifa ta samar katon tsiro me kunshe da ruwa ko tsauri WATO cysts ko TUMOR sakamakon wadancan kwayayen haihuwa marasa rai ko inganci da suka shigo cikin mahaifar mace daga kututar kwayaye wato OVARY

 

Wanda wannan yasa afarkon samuwar abun duk wani alamu na ciki mace zataji ta fara fuskantarsa kama daga tashin zuciya, zazzabi bame tsanani ba, rashin son warin abu, zubar da miyau, kasala da sauransu. Wani abu ma da zatai gwajin ciki na fitsari ko jini kai tsaye zata ga ya nuna POSITIVE alamun ta samu ciki saboda HcG din is High….

 

Kuma zai cigaba da girma kamar yadda ciki ke girma ahankali har aga tasowar cikin… shiyasa da yawa in akace musu ba ciki bane basa yadda. Wasu sai aita fama dasu suqi, har su rika kiransa da kwantacce a lokacin da sukaga girman ya dakata… ko kuma lokacin watannin haihuwa yazo ya wuce har sun qara shekara… sai kaji ana kwantaccen ciki

 

SHIN DUK IRI GUDA NE KO YA RARRABU ???

 

Ya kasu rukuni biyu ne kacal; akwai COMPLETE wato me gaba daya, da kuma INCOMPLETE me ragayya….

 

RUKUNI NA FARKO (COMPLETE)

 

A irin wannan ainishin shimfidar cikin mahaifa wato (uterus layer) inda jariri ke kwanciya ciki ya zauna ita kanta shimfidar takan rasa ingancinta ma’ana takan tattare ta murmude tai tudu da kwari…. domin daga cikin kwayoyin halittun gado chromosomes 46 da muke saki wato 23 daga mace, 23 wanda ke bada total na 46….

 

Akan samu Chromosome din MATAR ne kurum zai iya zamowa jariri wato viable egg…. Shi MIJIN empty sperm cell ya saki… WANDA tunda kuwa saida kwan namiji ciki zai tabbata amma gashi sai mace ce keda normal egg toh irin wannan kesa zubin shimfidar mahaifar ya jirkice shi kuma wancan tumor din na trophoblast sai yai amfani da wannan viable egg na macen ya girma ya cika cikin mahaifar mace (uterus)…. Arika ganin kanar ciki gareta… kuma ko yaushe in an duba HCG za’a ga high kamar de mai ciki…. yadda de kukaji na fada abaya…..▪

 

RUKUNI NA BIYU (PARTIAL)

 

A partial shi kuma cikin 23 pairs din na chromosome MACE tana sakin normal egg tare da 1 pair na chromosome… shi kuma NAMIJIN sai ya saki 2 pairs na chromosome maimakon 1 wato shi kadai ya samar da 46pairs maimakon 23pairs wanda inka hada da 23pairs din na matar sun tashi 69 pairs maimakon a sami total na 46.

 

Hakan shikesa ga cikin ya shiga akwai ciki na gaske ba tumor ba toh amma fa bazai ta6a rayuwa ya zama cikakken jariri ba…kuma adede wannan lokacin ga growth din trophoblast din da ya kusa cika mahaifar mace…. don haka nan ma za ai ta ganin HCG high amma fa bazai ta6a zama ciki ba.

 

Saide a PARTIAL din akwai kuma Partial me Normal Karyotype wato chromosome din daidai ne kowa ya samar da 23 ana da total 46 amma kuma ga trophoblast ya samar da tumor kusa da jaririn… toh a irin wannan ne yakan girma ya zama ciki a haifi jariri koda kuwa baida cikakkiyar lafiya.

 

A irin wannan ne ake jin hausawa na cewa kwantaccen wance de ya tashi.. duk da cikin kan shafe shekaru. Amma gaskiya ba acika samun irin wannan din sosai ba, saide dama irin wannan tun a ultrasound ake iya bambancesa.

 

ME KE JAWO HAKAN LIKITA👨🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️ ???

 

Abubuwan dakan jawo haka sun kunshi;

 

1. Akwai shekaru musamman macen dake kusa ko kuma ta haura shekaru 35

 

2. Kasancewar mace ta ta6a samun hakan abaya, akwai yiwuwar kara maimaitawa

 

3. Sai rashin daidaiton sinadaran halitta (hormonal imbalance)

 

Wannan matsala musamman a me COMPLETE MOLAR likitoci kan kalleta amatsayin daya daga cikin cuttukan cancer na mahaifa wato choriocarcinoma.

 

Duk abunda ke iya kara girma akaran kansa tabbas kode ya zamo cancer ko kuma benign tumor wato wanda ba cancer ba amma in aka barsa zai iya zama cancer

 

Domin idan har bayan an cire cyst din kuma HCG yaci gaba da tsayawa High akwai zargin ya riga ya zama cancer dole adora mace akan CHEMOTHERAPY… kuma ana warkar da cancer din cikin ikon Allah in anfarga da wuri.

 

Idan kuwa aka barshi toh kasan cancer tana iya yaduwa zuwa wasu sassan kuma hakan ce zata faru wanda akarshe mace zata iya mutuwa a dalilin cancer hanta ko huhu ko hanji alhalin tushen ciwon a mahaifa ne. Wannan tasa zarar likita yace miki cikin MOLO ne toh karki 6ata lokaci kurum aciresa ….

 

ALAMOMIN KWANTACCEN CIKIN🤰🏻 KO CIKIN MOLO

 

Alamomin sun kunshi;

1 Ganin Fitar jini me duhu ta gaba,

2 Ciwon baya ko mara,

3 Ganin jini na fita kamar dunqulen grapes fruits da kuma

4 Matsanancin tashin zuciya da amai……

 

WADANNE GWAJE-GWAJE AKE YI 👨🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️

 

Akanyi Gwajin Jini💉🌡️ domin duba hemoglobin level saboda tunanin karancin jini, sannan akuma duba HCG wato hormone din juna biyu da kuma ultrasound scan

 

MATAKIN DAUKA

 

1. Kai tsaye bayan tabbatar da molar pregnancy ne abunda ake kira Dayilteshin & kyuritaj wato manuwal bakyum Asfireshan SHINE: Abunyi acire tissue din baki daya…. domin barinsa bazai ta6a zama jariri ba, dama ba ciki bane kuma koda partial ne wanda ke kunshe da ciki shima ba girma zai ba.

 

Bayan kuma ancire din ba’a kuma barin mace ta dauki ciki…. akalla sai bayan shekara. Saboda ana so aci gaba da auna HCG level din lokaci lokaci har zuwa shekara bayan cire molar din domin idan yaci gaba da zama HIGH kamar de akwai ciki toh alamace ta PERSISTENT GESTATIONAL TROPHOBLASTIC NEOPLASIA wato ya tabbata cancer. Don haka dole ai maza afara mata chemotherapy akashesa… inba haka ba zata yadu zuwa sauran organs… kunga ko hakan is deadly.

 

2. Ko kuma idan dama bata da sha’awar kara haihuwa tana jin tagama shikenan sai acire mahaifar baki daya kurum. Duk da nan gaba kuma lokacin menopause in estrogen dinta yai low wasu suna samun hot flashes wato premenopausal symptoms wanda ake musu hormone replacement therapy toh ammafa macen da bata da mahaifa ita baza ayi mata wannan ba… domin zai zame mata matsala tunda ya kunshi estrogen alhalin bata da uterus…. Progesterone only method shine therapy din da zata iya amfani dashi.

 

Don haka akeson ko yaushe in likita ya tambayi mace wani abu toh ba boyeboye koda dangane da mu’amalar auratayya ne ta fadamasa gaskiya ba’a yiwa likita karya koda kuwa kinayiwa mijinki shi likita in akai masa karya kanki kika cuta….

 

Wannan shine molar pregnancy a Madogarar Ilimin Kimiyya ta Zamani ko Likitancin👨🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️ Bature atakaice.

 

KWANTACCEN CIKI (MOLAR PREGNANCY)🤰🏻 A MAHANGAR ILIMIN LIKITANCI NA MUSULUNCI👳🏻‍♂️🧕🏻 DA GARGAJIYA

 

Shi Wannan Ciki Ba Komai Bane face Guba Ta shedanun Aljanu wadda suke zubawa mace a Cikin Farjinta zuwa Mahaifa ta Hanyar Ko dalilin Jima’i da ita da Aljanin yake alhali bata sani, hakan na Faruwane a Dalilin Rashin kiyaye Addu’o’i kafin kwanciya, da Kuma Rashin yin Addu’ar da Manzon Allah S.A.W ya Koyar kafin Fara Jima’i,

 

Idan Ma’aurata basa kiyaye Addu’a kafin kwanciya kokuma basa yin Addu’ar Fara Jima’i itace Bismillahi, Allahumma Jannibnashshaitana wa Jannibishshaytana Maa Razaqtana, Ma’ana, Yaa Allah ka Karemu daga Sharrin shedan Kuma ka kare abinda Zaka azurtamu da shi na Jariri ko ciki daga Sharrin shedan, Hakan ne Za a samu Kariya kar Miji yayi Inzali tare da shedan, ta hakane ake samun Kangararren yaro kokuma Cutar da ba san kantaba a Mahaifa Allah ya sawwake,

 

Da Fatan Magidanta Da matan Aure za a dinga iyabakin Kokari wajen kiyaye Wannan Addu’a Domin kare kanmu da Lafiyar iyalanmu daga Afkawar Shedanun Aljanu cikin Lafiyarmu da Zuriyyar da zamu haifa nan gaba, Wannan shine Matsayin kwantaccen Ciki a Mahangar Kimiyya ta Musulunci da Gargajiya Yah Allah ya karemu

 

Me neman Cikakken Hadadden Maganin Kwantacce kaitsaye a Dauki Lambar wayarmu a kiramu ko a Mana magana ta manhajar whatsapp InshaaAllahu muna da hadadde, kuna Muna Bada taimako kan kowacce irin matsala ta Cututtuka ko Matsalolin Rayuwa

_Manufar Mu A Kullum Itace Wayar DA Kan Al’umma, da bada taimako akan ko Wace irin matsla ta raywua Bisa koyarwa ta addinin musulunci

Al Huda Islamic medicine kututubaimu dumin samun magani cutakanku dayardar Allah .

07050855528

Post a Comment

Previous Post Next Post