A Mafarkina Hausa Novel Complete
A MAFARKI NA
*_MALLAKIN_*
*_AISHA MIKA’IL_*
*(Ayousherh)*
*_DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION_
*_ALLAH SHINE GATAN MU_*
*YA ALLAH INA ROKON KA YADDA NA FARA LITTAFIN NAN LFY ALLAH KASA NA GAMA LFY KURA-KUREN DAKE CIKIN SA ALLAH KA YAFEMIN ABINDA NA FADA DAI-DAI ALLAH KASA MASU KARATU SU AMFANA DASHI*
*بسم الله الر حمن الر حيم*
*Free*
A firgice ta tashi daga baccin da takeyi wanda ya dauketa batare da ta shirya masa ba tareda addu’ar tashi daga bacci duk bawai ta dade dayin baccin bane baifi minti goma zuwa shabiyar da daukan ta ba,domin daga islamiya take tashiga ne domin ta canza kaya taje taya umman ta aikin abincin dare, daganan bacci ya dauketa.
Hawaye ne yafara zirarowa daga idanunta hannu tasa ta dauke sa tareda addu’ar neman tsari daga shedan domin karo na hudu kenan da take wannan mafarkin da yake firgita mata kwakwalwa domin tasan ba abu me yuwa bane samun sa, kullum tana addu’a akan Allah ya yaye mata abun nan domin duk ranar da tayi wannan mafarkin toh ita da samun natsuwa kuwa se bayan kwana biyu.
Abokin Aikina Hausa Novel Complete
Haka ta tashi tacanza kayan sannan ta ta fito domin magariba ta karato zuwa tayi tasamun umma hartayi talgen tuwo tana shirin yin alwala, kallon diyar tata tayi cike da kulawa tana tambayarta lafiya, domin itama ta lura kwakwata bata da natsuwa kwana biyu nan, sheda mata tayi da lafiya kanta ne yake mata ciwo, fatan samun sauki ta mata sannan tace bari kannen ta su dawo se su kar6o mata maganin ciwon kai a kemis.
Daukan buta tayi sannan tashiga bandaki tafito itama tayi alwala tashiga daki ta dauko hijabi da darduma tazo ta shimfida kan tabarmar dake shimfide a tsakar gidan dayake share tsaf ko datti babu.
Shigowar wasu yara ne su biyu mace dana miji masu tsananin kama da juna daga ganin su basai anfada ba yan biyu saboda kansu daya kamannin su daya, akalla zasu kai shekara goma sha uku,tsugunawa sukayi har kasa suka gaida umma,
“Ah ah kaga yan biyu kyautar ubangiji,masu kama daya ya makaranta ya karatu yakuma kiriniya”
“Lafiya kalau umman mu mufa bama kiriniya Allah ki tambaya malam ma ze fada miki karatu kuma munayi ko afnan”
Yafada yana kallon kanwarsa wanda ya kira da afnan,
“Eh umman mu gaskiya yaya affan yake fada ALLAH ki tambaya malam kiji” tafada kaman zatayi kuka,
“To toh naji ku tashi kuyi alwala kuyi sallah ku siyowa antin ku magani”,
Juyawa sukayi suka gaida antin su da bata tayar da sallan ba tana sauraren su.
Hada baki sukayi wajen fadin!
“Anty ina wuni ya jiki”
Amsa musu tayi sannan suka dauki buta kowa ya kama gabansa.
Bayan sun idar suka zauna kowa ya dauko *QUR’ANi* sukayi karatun haddar da aka basu tareda yin azkar gaba dayan su harda umma sannan ta tashi ta tuka tuwon ta, dan da alama antyn su baza ta iya ba, (bata kiran sunan ta saboda Alkunyan yan fari da iyayen mu suke fama dashi).
Suna zaune aka kira sallan isha’i nan suka tashi sukayi gaba dayan su, sannan umma ta basu kudi domin siyowa antin su magani,
Bayan umma ta gama kwashe tuwo ta zuba mata nata yayi sanyi kafin su dawo, se taci tasha magani, bayan sun dawo ne umma tasa musu suma sukaci kowa yaje yayi alwala yayi addu’a suka kwanta, itama bayan tasha magani ne tayi tata alwalan takwanta cike da tausayin kanta da fatan kada tasake mafarkin da tasan bezai ta6a yuwa akanta ba.