Gidan Marayu Hausa Novel Complete
GIDAN MARAYU
Story And writing by Amina ma,aji (maman Khairat)
True life story
“`Albishirin Ku dan Allah kucemun Goro fari tas,ni maman Khairat nasake kawo muku wani labari mai rikitarwa, da kuma fad’akarwa, dakuma ilmantarwa duk ku bud’e kunnen Ku ajikina nakeji labarin (gidan marayu) gaskiya Solon daban ne nikaina na jinjinawa labarin nima nabude kunnena, dan in sha Labari“`
JANKUNNE
*Ban yadda wani ko wata sujuyamun labarin tawani fuskaba labarine da yafaru da gaske ba k’irk’irarren labari bane .in labarin yayi dai dai darayuwar wani Ku tuntub’eni ta number wayata zanyi muku cikekken bayani .*
Ido Hudu Hausa Novel Complete
*Drug Abuse*
*Muguji aikata fyade da cin zarafin marayu wannan na,d’aya daga Cikin rashin cigaba, da nutsuwa a zuciya .muguji, ta,amali da miyagun kwayoyi ya na barnatarwa fiye da ilmantarwa wannan sak’one daga Had’akar marubutan Hausa Nigeria*
“Inna yunwa mukeji cikina har ciwo yakeyi ko ruwa kibani zan mutu” yi hakuri sulaiman ga sadiq bayanan baran tana yaje gidan wancen matar ko garin kwakine ya karb’a muku koda babu sugar.
Inna kibamu koda ruwane zamusha ba,jiya akwai sauran garin da kikarage ba dakike tuk’a tuwo kibamu kisaka ruwa”haba sadiq ,daga shigowarka,taya zakace mujik’a garin tuwo?inna kenan kedai kibamu akwai tsamiya kisaka mana guda d’aya tayi tsami “toh sadiq shiga d’aki inna tayi taduba garin ko Cikin tàfin hannu bazaiyi ba yazatayi tunda yaranne suka kawo shawaran kwanan silver tad’auko tawanke take ta tankade garin taga yazama kad’an saboda jiya nik’an batayi laushi ba .
Juye garin tayi tasaka tsamiya ta murza d’and’anawa tayi taji yayi dad’i Kuwa nufan k’ofar d’akin tayi duk sun rik’e Cikin” kutashi kusha gashi duba abun sadiq yayi yagani koshi d’aya zai shenye mik’ewa yayi “ina kuma zakaje?inna zan k’ara ruwa ne dan, ya,ishemu har su Ibrahim sudawo da sayyada ,bude randan yayi ruwan tayi k’asa kalan k’asàn randan yayi yasamu ruwan bari yayi ta kwanta yajuye ruwàn kowa yasha k’annen su,sukaragewa in sundawo daga makaranta susha.
Sulaiman tashi yayi daga kwancen da yayi ” harka tashi E inna natashi kema kisha mana koda kad’an ne.kusha kawai badamuwa,har k’àrfe sha biyu da rabi tayi “sauran yaran suka dawo daga makaranta ” inna barka da gida yauwa kundawo? E mundawo “yunwa inna ” gacen faraufarau kud’auko kusha “inna wannan bazai,isheniba kuyi hak’uri kusha ”
“Inna bari in d’auki roba in tafi bara kozamu samu abunda zamuci ” Allah yabada sa,a sulaiman Amin,haka yata yawo kowani gida yaje shiru yaje gida yafi biyar kafun yasamu guntuwar shin kafa shima Wanda yara sukaci ne suka rage ya k’ara shiga wani gidan yasamu taliya wani gidan tuwoce miyar kuka, duk yahad’a yana fitohwa, suka had’u da sadiq “kasamu kuwa?” alalene itama nakeganin tab’aci sai nera ashirin da biyar wani mutum ne yabamu.
“kagani sadiq mutafi gida ninasamu abinci kuma zai ishemu tunda roban tacika har ,a leda nasaka ” sulaiman muje kawai muk’ara kozamu samu abinda gobe zamuci Allah yasa musamu tuwo ,kagani sai inna tayi mana d’umame”shikenan muje kawai ,bari muyi dabara musaka abincin aleda sai muje kozamu samu wani toh muje .
Sayyada tatafi debo ruwa haka tacika ko,ina tayi shara ibrahim yana zaune ,har su,sulaiman ,sukadawo shida sadiq “inna yaukam munsamo dayawa hakane ” sayyada kid’auko tire mujuye ,haka sukaci abincin dukansu har inna Sauran sukabari sai da safe zasuci .
Sun k’wana ,acikin walwala kowa sai fara,a yakeyi in yatina da sunada abunda zasuci .
***********************
Washe gari
*********************
da sassafe inna tahad’a karare tayi musu d’umame kafun suka wuce makaranta dan har sun, sunsamu ,ana zane wasu,sakamakon basuzo ,a kan lokaci ba,sayyada ko komawa tara basayi saboda babu ,abunda zasuci koda sun koma gida, ne,ga kullum basa zuwa akan lokaci dan sai tawuce wani gida tayi wanke,wanke kafun a bata dubu d’aya da d’ari biyar ga wajen da nisa tundaga sumsumma, har waziri Ibrahim ga cenciki ne, matar gidan sai masifa da duka .
Wani rana kan sayyada naciwo bataje da wuriba”uban meyahanaki,zuwa da wuri Anty ?”kiyi hak’uri kaina keyimun ciwo” toh acikin kud’in ki “naji Anty
Kizuwu,sai wani kallona kikeyi kinzubamun ,ido kaman mayya…
Maman Khairat ce
Add Comment