Batsa Novels Marubutan Batsa Ku Karanta Wannan
Batsa Novels Marubutan Batsa Ku Karanta Wannan
Assalamu alaikum Jama’a Ina kira wannan Sakon nawa zuwa ga Makaranta da marubuta . I’m Mrs Yareema ni haifaffiyar garin Kano ce ,Kano kuma anan marubuta suka fi yawa . Wannan sakon ba cin mutunci bane kuma Sannan ba Zagi bane kawai nasiha ce kuma shawara , don haka duk Wani mai Son gyarar goben yaran mu yayi share Din wannan Sakon don ya kai inda ake so ya kai don marubutan da suke amfani da Adabin bariki su gyara 🙏🏻 zan fado sunan ko wacce Marubuciya da kuma littafin da ta rubuta na batsa ,don yawa kullum suke yi ,a yanzu marubutan batsa sanannu sun fi 20 a duniyar yanar gizo.
Rafeeq Hausa Novel Complete
Batsa Yayi yawa ga alkalaman marubutan mu , Alhamdulillah Ni ina karatun littafan Hausa Kuma ina karanta kusan duka manyan marubuta . Har akwai Wanda aka basu Aword a 2022 akan cewa littafan su yafi na kowa shahara wato madaukakan marubuta wanda bai cancanta ba , Alkalamin su ya gurbata da batsa amma muna gani makaranta mun kasa Magana . Ga hazikan yara nan marubutan masu tasowa amma babu mai kallon littafan su wanda hakan baiyi ba ,munfi son na batsa .
1)M Shakur Wannan ba sai na fado littafin ki ba ,kowa yasani musamman Littafin Farra da Matan Asokoro . Kuwa darajar Allah ku aje Wannan alkaman naku ku dauki hanyar gyara .
2) OUM Hairan Wannan ke har Zauren malamai an zaunar dake a Kano Amma baki gyara ba , Har yanzu Badalallan Littafin ki yana nan yana yawo kuma yara sun lalace da dama saka makon shi Gidan Uncle , kuma fa kuna da yara zaku so su karanta Abun da kuke rubutawa ku gyara don Allah. Bakya cikin wanda suka samu Aword na 2022 wanda hakan ya kamata dama .
3)Mamugee Tayi littafi Mai suna Deen marshal , a baya littafan ta babu batsa ko romantic amma kuma a yanzu dashi , idan kuma babu Aje a duba . Don haka Wannan Aword da aka bata a 2022 bai dace ba ,bai kuma kamata ba a yanzu itama har alfahari take yi da Kalmar romantic tana rubutawa a littafan ta . Mamu ki koma alkalamin ki tamkar na da Daukaka Allah ya baki to me kuma kike so ,kar ki lalata Alkamin ki mun jin dadin sa .
4)Binta Abale Kowa duk mai bin littafin ta yasan Adabin bariki ne , Kaman babban Yaro , Yar bangar siyasa gasu nan da dama . Don Allah ku gyara Saboda goben yaran mu . Itama kuma ta shigo Aword na 2022 wanda bai dace a bata ba sai idan ta gyara Alkamin ta .
5)Maman teddy tayi littafai da dama na batsa ,a da baya tace ta daina amma kuma a yanzu mun ga ta fara Wani Sabon littafi Mai suna Fyade ,ba zan yanke hukunci ba tun da ban karanta ba ,amma don Allah yanda kika ce kin daina littafan batsa kar ki rubuta a wannan da kika fara . Kin yi littafan batsa yawon su ya kai mizani wai kuma a haka aka baki Aword na 2022 meye mu keyi haka , ga yaran marubuta masu aiki da basira ba’a basu ba ,ana ba marubutan batsa kawai saboda su din sun sanu sun daukaka? Ba adalci a ciki . Kinyi littafin The Sexy Boss,wai Kuma akan shi kika samu Aword a 2022 ga sunan birjik Allah yakyauta .
6)Akwai marubuta masu tasowa suma batsa suke yi ba sai na kama sunan ku ba ,ku daina tun kamin Alkalami na ya hau kan ku ,don idan mun ga gaskiya ba zamu fasa fadi ba .
7)Nimcy luv Tayi littafin Uncle Ne wanda babu komai a cikin littafin sai zallar iskanci da ƙwartanci kuma har yanzu kina sakawa a littafan ki meye haka ? Wai kuma a hakan aka baki Aword a shahararriyar Marubuciya har lamba ta daya 1 a 2022 wannan wani irin Abun haushi ne , sahihan marubutan mu ba’a Basu ba sai ku? Babu adalci ga lalata tarbiya . Allah ya kara rufa mana asiri , Allah ya kubutar da yaran mu masu tasowa daga sharrin rubutun ku .
8)Oum Aphnan wallahi kiji tsoron Allah Littafan ki babu komai ciki sai karya da karairayi Ga koya lesbian da kuma Sex ,ga karyar jarumi kisa trillionerer 7 🤨 haka fa kika sa a littafin ki na sugar Gwauro ga sugar mommies , ki gyara kina da yara Ba zaki so su karanta littafin ki ba .
9)Mrs Sadauki kema ada ba haka alkalamin ki yake ba amma me yasa yanzu kika sauya haba haba wai me kuke nema ne? Wannan rubutun ki da kike yi don manzon Allah ki dakata ku aje Wannan alkamin ku dauki na kwarai ,wanda zai amfane ku duniya da lahira .
10) Aisha Garkuwa tun asali littafan ki batsa ne a ciki me yasa Mutane suke kin fada ne ? Kuma a haka kin fi shekara bakya rubutu amma aka saka sunan ki a masu Aword na 2022 to me kika rubuta a shekarar ne? Ko don kin daukaka kawai aka danne na kasa aka rubuta ki? Kiwa girman Allah kema ki rage ,kinyi littafai da dama NAMIJI BAYA KADAN ,bandirawo gasunan duka sex story ne da abubuwan da yawa wanda bai kamata hannun ki ya rubuta ba ,Don Allah Garkuwa kema ki gyara duk mun ji ki shiru Allah kuma yasa lafiya .
Jinjina ga marubutan da har yanzu suke akan alkalamin su na Gaskiya Daya daga ciki itace BILLYN ABDUL har a yau bata sauya alkalamin ta ba ,mun jinjina Miki sarauniyar marubuta Allah kuma ya tayaki Riko , don Allah kema ki saka baki akan Marubutan nan duka kan ku daya ne ,don haka kin san su sun sanki , kuna top Writers ki tara su suyi ma kansu fada ko ba don kowa ba don yaron mu don Allah. Wani labari naji a yau sai da nayi kuka saboda karanta littafin batsa yarinya yar shekara 15 da cocumber ta biya ma kanta bukata😭 wannan wani irin masifa ne , ku marubuta da aka sani da gyara tarbiya sai ku lalata kuma ? Idan ranku ya baci bisa ganin Wannan sako nawa kuyi hakuri,amma Ni uwa ce ina duba yaran mu ne masu tasowa ,kuma ba kiyayayyar ku yasani rubuta hakan ba gaskiya ce idan tazo dole a fade ta . Mrs Yarima ce.
Share repost don Darajar Annabi kuyi har yakai masu don su gyara .
Add Comment