Abokin Aikina Hausa Novel Complete
ABOKIN AIKINA
*TAKU NA BIYU.*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*Alhmdulillah! Allah ya ara mana lokaci mun dawo bakin aiki. Barkan mu da sallah! Fatar kowa ya yi sallah lafiya. Allah ya maimaita mana*
*LAMBA TA ƊAYA.*
“Ahirrrrr! Zaituna!!! Kaicon ki da wannan mummunan furucin da ke neman ruguza sauran rayuwarki, da farincikin masu ƙaunar ki gabaɗaya!”
Zancen Ummata kenan, wanda ta ambata cikin ɗaga murya da ƙarajin da ya dinga mini amsa-kuwa, a cikin kunnuwana. Sannan na hango tabbacin karaɗe kunnuwan duk wanda ke cikin ɗakin taron a kan fuskokinsu. Duba da yadda suka tattara na mujiyarsu duka suka sauke a kan fuskarta, bayan hankalinsu da suka miƙa mata, a yayin da take cigaba da bulbulo zazzafan kashedin da take ƙoƙarin yi mini, a cikin faɗa da zallar ɓacin ran da ke shimfiɗe a kan fuskarta.
Mabuqaci Hausa Novel Complete
“Rayuwarki da ta yaran duka ba a hannun junanku take ba! Balle a a ji tsoron raba ku gudun ta salwanta sanadin hakan. Da ke ko babu ke za su rayu a doron duniya, haka ke ma rashin su kusa da ke ba zai hana ki cigaba da gungura rayuwarki ba. Don haka ki so ko kada ki so zaman ‘ya’yan da kike yi a gidan Mukhtar ya zo ƙarshe. Saboda ba kanki farau rabuwa da yara ba balle a ƙare kanki, uwa ta rasu ta bar jaririnta a cikin tsumman goyo kuma ya rayu, balle ke da naki suka tashi hannunki har aka fara cin moriyarsu gaban idonki. Saboda haka ba za ki zauna gidansa a kan wannan dalilin ba, duk inda kike a faɗin duniyar nan sai sun iske ki matuƙar kika saka wa kanki haƙuri da dangana.”
Ni ma kaina ita nake kallo ko ƙyaftawa babu, jikina ya shiga rawa tamkar mazari. Saboda mugun tsoron da zantukanta suka ƙara wa zuciyata ƙaimin gudu, ta shiga harbawa fat! Fat! Fat! Da sauri da sauri tamkar ta ɓalle ƙirjina ta fito.
Babu zato na ji kuka ya fito daga bakina, wanda ni kaina ban shirya zuwan sa ba a daidai lokacin. Saboda hararar da Umma take jefo mini bayan ta gama magana, tamkar idanuwanta su faɗo ƙasa. Bakina yana rawa na furta,
“Don Allah Umma ki yi haƙuri, wallahi ba zan iya rayuwa babu ‘ya’yana ba!”
“Dakata Zaituna!”
Ita ce magana ta biyu da Baba Ali ya yi tun da aka fara taƙaddamar. Sai da ya ɗan muskuta bayan ya gyara zamansa sannan ya ce,
“Da kin san illar da mummunar ɗabi’ar nan ta mijinki za ta janyo miki a nan gaba; da kin nemi garkuwa tun wuri kin kare kanki daga zazzafan farmakin da za ta kawo miki bagatatan.”
Sai da ya tsahirta sannan ya ɗora maganarsa da da cewa,
“Haƙiƙa matsalar Istimna’i ko na ce auren hannu (wato Masturbation) gagarumar matsala ce wacce take shiga zuciyar masu yin ta ta yi kaka-gida. Kuma tana da wahalar fita gabaɗaya a lokaci ɗaya, sai dai albarkacin addu’a da yawaita ibada; sannan ne mutum zai samu wadatuwar tsoron Allah a cikin zuciyarsa, harma ya zamto a samu ya tuba gabaɗaya, ta yadda ba zai sake aikatawa ba.
Mafiya yawan mutane suna yin ɗabi’ar ne da niyyar kauce wa zina. Ba su san cewa shi ma wannan ɗin babbar Kaba’ira ce a cikin addininmu na Musulunci ba!
Matasa da dama tsakanin mata da maza sun afka cikin wannan bala’in. Wasu cikin rashin sanin illolinsa, wasu kuma saboda tsabar Fajirci da rashin tsoron Allah. Yayin da yanayin da wasu za su tsinci kansu a ciki zai haifar musu da wannan gwaggwaɓar matsala. Ba tare da sun gano shi kansa wani nau’in zunubi ne Mai girma ba.
Kuma kamar yadda zina take da mutuƙar illa wurin cutar da lafiyar mutum, haka shi ma wannan yake haifar da tarin matsaloli kamar yadda Alƙali Falgore ya faɗa yanzu.
Ɓangaren cutar da hankalin mutum, da gurɓata tunaninsa, ta cire masa ƙwayar imani da tsoron Allah daga zuciyarsa. Haka shi ma mai aikata ɗabi’ar Istimna’i take lalata rayuwar mutum, mutuncinsa, halayyarsa da lafiyarsa.
Don haka mu a matsayinmu na magabatanki kuma Iyayenki. Ba mu goyi bayan ki sake zama gidansa ba. Alhmdulillah tun da an yi saki a rungumi ƙaddarar kawai a yi tafiya a kanta. ‘Ya’ya kuma ki bar masa kayansa kamar yadda ya nema. Idan ya isa ya saka su gabas ya yanka tsabar ƙiyayyar ki da rashin hankali…”
“Ba ma zai yanka ba don jininsa ne!”
Zancen Yaya Maimuna kenan da muka tsinkayo muryarta cikin gatsali tana zarar ido har da murguɗa baki. Murmushin gefen baki na ga Baba Ali ya yi sannan ya ce,
“Za mu zuba ido mu gani idan fankam-fankam yana kilishi.”
Wani ƙaƙƙarfan kuka ya suɓuce mini mai sauti. Na yage bakina iya ƙarfina na dinga kwararawa, saboda ganin kowa ya yi amanna da a raba ni da yarana. Kuma ni iya gaskiyata kenan zan iya zama gidan Mukhtar a yadda yake so matuƙar zai raba ni da yarana. Ɗakin ya yi tsit babu motsin komai sai na sautin kukan da nake rerawa. Ba tare da na kai kallona kan fuskar kowa ba balle ta Ummata mai mini barazana.
Cikin sautin kukan da nake yi na fara magana ina shessheka tare da sharar fuska da gefen mayafina ina faɗin,
“Don Allah ku bar ni da yarana. Wallahi zan iya mutuwa matuƙar aka ce za a raba ni da su. Saboda matarsa kanta tana buƙatar tarbiyya balle ta yi wa wani. Haka ma shi ba zai tsaya kula da su kamar yadda ake so ba. Da ni suka saba saboda ni ce komai nasu dare ko rana. Ku tausaya mini don Allah matuƙar ana so na cigaba da numfashi…”
Sabon kuka ya sarƙe ni tare da zancen Umma da na jiyo a sama tana faɗin,
“Ko za ki mutu yanzu ba za a fasa miƙa masa yaransa ba! Kuka kuma ki daina yin ruwa, ki yi na jini idan za ki iya. Aure dai ne ke da shi har abadan abade…”
“Tsaya-tsaya Malama Habi! Abin duka bai kai can ba. Duba da yadda ta ɗaga hankalinta, za mu roƙi alfarmarsa a kan ya bar mata yaranta duka idan hakan zai yiyu. Idan kuma za a bi hanyar adalci, za a bar mata yaranta mata shi kuma ya ɗauki ƙaramin yaron namijin. Don haka kai Malam Mukhtar mai shadda, me za ka ce a kan wannan tsarin?”
Harara na wurga wa gefen da Mukhtar ɗin yake zaune, inda na fara jiyo sautin muryarsa cikin sanyin jiki yana magana.
“Ranka ya daɗe na aminta da tsarin duka. Ta ɗauki matan, ni ta bar ni da Haidar. Amma da sharaɗin duk abin da ya biyo daga baya ita ce da alhakin ɗaukar komai…”
“Ɗaukar komai kamar me fa!?”
Alƙalin ya jefo masa wata tambaya. Sai da ya tashi daga zaunen da yake ya ƙara gyara zamansa sannan ya ce,
“Dangane da matsalolin rayuwa na yau da gobe. Kamar yadda ta matsa sai an bar mata yaran; to ta ci gaba da hidimarsu tun da ta nuna ita ce komai nasu tun farko…”
“Ba zai yiwu ba! Saboda ‘ya’yanka suna da haƙƙi a kanka yanzu fiye da wanda kake da shi a kansu. Dalilin suna cikin marhalatiɗ ɗufula, sun fi buƙatar kulawarka yanzu fiye da amfanin da za su yi maka a gaba. Wajibi ne ka sauke dukkan haƙƙin da Allah ya rataya maka a kanka, matsayinka na ubansu kuma wanda yake bango a wurinsu domin su jingina su tashi ko kuma su ji daɗin tsayuwa. Abincinsu, sutura, hidimar magani idan ba su da lafiya, harkar karatun su boko da Arabic duka suna wuyanka. Don suna hannunta wajibi ne a kanka ka sauke nauyin da ke wuyanka. Saɓanin hakan kuma za mu dawo da kai a nan mu yi maka hukunci daidai da laifinka.”
“Ranka ya daɗe a yi haƙuri zan kiyaye!”
Shiru Alƙalin ya yi na ɗan lokaci, sannan ya ƙara ɗaga sautinsa bayan ya ƙare mana kallo ɗaya bayan ɗaya sannan ya ce,
“Alhmdulillah! An zo ƙarshen wannan Sulhu, wanda aka tsayu a kan sakin da kotu ta ƙaddamar wa Zaituna Aliyu. wacce ta fito daga wakilcin tsohon mijinta Mukhtar Mai shadda, sannan an ba ta yaranta biyu mata, shi ma an bar masa ƙaramin yaronsu mai suna Haidar. Idan akwai mai wani ƙorafi zai iya magana tun kafin a tashi daga taron. Ubangiji ya shiga cikin lamarin ya kawar da fitinar da ke ciki.”
“Amin-amin” ce ta dinga fita a bakunan mutanen da ke cikin ɗakin sulhun, amma ni na kasa furta komai illa kukan da nake sharɓa da gefen mayafina. Saboda ko kaɗan tsarin bai yi mini ba, idan son samu ne a bar mini yarana duka ba sai an raba mu ba. Amma hararar da nake gani a cikin idanuwan Umma ya sa na kasa cewa uffan, balle a gano rashin daɗin da hukuncin ya yi mini. Domin na ci alwashin ko da Mukhtar zai zare hannuwansa dukansu a cikin ɗawainiyarsu; zan yi gammo na ɗora wa kaina komai saboda na saba da hidimarsu har ta zame mini jiki.”
“Ranka ya daɗe, dangane da matsalar nan da ake faɗa, ta wace hanya za a bi a shawo kanta?”
Tambayar Mukhtar kenan da na ji a cikin kunnuwana. Sosai na ji daɗin tambayar don abin da ke cizon raina kenan tun lokacin da na ji zancen Baba Ali. Sai da Alƙalin ya yi gyaran murya sannan ya ce,
“Magana ta gaskiya, wajibi ne ga duk mutumin da yake son kansa da arziƙi, kuma yake fatan haɗuwa da Allah lafiya, ya nisanci zina da dangoginta irin su; Luwadi, Madigo, Istimna’i, da sauransu. Sannan ya ƙaurace wa duk wasu dalilan da za su iya kai shi zuwa ga aikata waɗannan laifukan.
Kamar yadda Malamai suka sha fada a ZAUREN FIQHU, Babbar hanyar da za ka bi/za ki bi domin rabuwa da wannan bala’in sun haɗa da:
1. Nisantar duk wani hoto ko video mai nuna tsiraici. (Ka gogevshi daga wayarka)
2. Nisantar shafukan Internet masu nuna tsaraicin da zai janyo maka sha’awa.
3. Dena abota da fitsararrun abokai ko ƙawaye maza ko mata. Saboda sanadinsu komai zai ɗimama ko da an tuba.
4. Nisantar duk wurin da ake cuɗanya tsakanin maza da mata, saboda tsaron lafiya da kauce wa wannan mummunan ɗabi’ar.
5. Ka dena zama kai kaɗai acikin ɗaki in dai ba ibada kake yi ba.
6. Yawaita karatun Alqur’ani da zikirin Allah. da sauran ayyukan alkhairi. Za su natsar da zuciyar mutum ya daina tunanin abin a cikin ƙwaƙwalwarsa.
7. Zama cikin mutanen kirki abin koyi da halayensu, ko kuma karanta labaran waɗanda suka gabata. Domin a ji abin kirkin da suka aikata da ƙoƙarin koyi da su.
8. Tuna Allah a koyaushe, da tuno kusancinsa gare ka aduk inda kake.
9. Tuna kana da cikakken kusancin ajalinka ko kana so ko ba ka so. Saboda za ka rage neman jin daɗin duniya, ka yi ƙoƙarin yi wa lahira tanadi.
Don haka matuƙar aka kiyaye waɗannan; za a rabu da wannan matsalar ba tare da an je wani wuri an fallasa kai ba. Duk da akwai maganin matsalar da ake bayarwa a Islamic center. Amma waɗannan su ne manyan matakan da za a ɗauka, domin a yi wa abin ginshiƙi ko da ana amfani da maganin. Ubangiji ya kawo sauƙi a cikin lamarin.”
“Ni dai ranka ya daɗe! Da da hali da an bar mata yaranta duka!”
Maganar Kawu Sale kenan da na ji kamar ya karanto abin da ke cikin zuciyata. Wani sanyin daɗi ya tsirga mini a zuciya, na yi kasake ina jiran na ji abin da Alƙalin zai ce, domin har na sa raina a kan zai dawo mini da yarona kamar yadda Kawu Sale ya roƙo.
Sai kawai na ji saɓanin abin da zuciyata take muradi, domin kuwa ƙiri-ƙiri ya ce an gama zartar da hukunci babu kwangaba-kwanbaya. Haushi ya sa na miƙe ba tare da an ba ni umurni ba. Ina ƙoƙarin ficewa daga ɗakin sulhun na ji muryar Barira tana faɗin,
“Ranka ya daɗe ƙara na kawo! Saboda sun je ɗaukar kayansu sun haɗa da kujeruna kakaf sun kwashe. Ko da na dawo gidan na tarad da babu su sun yi ɓatan dabo!”
‘Wata sabuwa!’
Zancen da na yi kenan a zuciyata, babu shiri na dawo idona a kanta cike da mamakin da ya hana ni furta ko kalma ɗaya. Sai rawar da bakina yake yi ina nuna ta da hannu, saboda kwata-kwata na manta da Allah ya yi ruwanta a cikin ɗakin. Kuma tun da aka fara zancen ban ji motsinta ba balle sautin da zai tuna mini da ita cikin ɗakin sulhun. Sai dai kafin na yi magana, Umma ta riga ni cike da mamaki ta ce,
“Kujerunki kuma!?”
“E, su nake zancen! Waɗanda kuka kwashe mini lokacin da kuka je ɗebo kayanku! Idan ƙarya nake yi kuma Allah yana ji yana gani!”
To fa😹idan babu rame, me ya kawo zancensa Barcy?😛
08022014771
Ina jiran barka da sallata😕
D. AUTA CE✍🏼
Add Comment