Littafan Hausa Novels

Auren Bauta Hausa Novel Complete

Auren Bauta Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

AUREN BAUTA*

 

(the amazing cook)

 

 

 

 

 

By mmn walid and walida (mrs aliyu)

 

 

 

Marubuciyar

*tawa kaddarar*

*dangin sa*

*uwata*

*rabo na ce* to be continued in shaa Allah

 

 

 

Page 1

 

 

 

 

“Sai yanzu kika dawo ƴar iska tun ɗazu da aka aike ki ɗebo ruwan sai yanzu kika ga daman dawo wa kuma kina ji na nace miki sanwar wake da shinkafa zan ɗaura da ruwan shine kika je kikai zaman ki don kina min baƙin cikin kuɗin da zan samu ko, shegiya da fuskar kamar ta aljan”

 

 

 

Duk wannan faɗan da inna harira bata taimakawa ƴar yarinyar da take ɗauke da ruwa akan ta, duk kuwa da ganin cewar yarinyar ta gaji sosai

 

 

 

sai da tayi ta gama sannan ta sauke,

“kuma kije gonar malam ki wo min in kin ga dama ki daɗe kamar kinje lahira gaida iyayen ki”

 

 

Ɗan ɗankwalin da take ɗauro karar ta ɗauka tayi waje da shi, directly gonar ta nufa wanda bashi da nisa da gidan ta ɗebo karar sannan ta kama hanyar gida tana yi tana nishi daga gani yunwa ce da kuma gajiya a tattare da yarinyar

 

Zuciyar Mugu Hausa Novel Complete

 

Da sallamar ta ta shiga gidan ta ajiye karar sannan ta zundumi ruwa a randa ta ɗan sha kaɗan bata san ta cikawa cikin ta ruwa

 

 

 

“shiga madafi ki ɗauko ragowar ɗumame ki don yadda kike zaro min idandinan nan naki a cikin wannan baƙar fuskar taki ai wannan sai in mummunan mafarki”

 

 

 

 

Abincin ta ɗauko zata fara ci kenan inna harira ta kuma saka ta aikin hura wuta na wake da shinkafar da take saidawa

 

 

 

A bakin murhun ta zauna tana hura iccen tana cin sandararran tuwon dawan da idan aka jefe ka da shi sai kaji ciwo saboda tsabar taurinsa

 

 

 

Sai da ta gama girka wake da shinkafar tsab sannan ta kwashe a ƴar fantekar da ake kwashewa sannan ta gayaws inna harira ta gama

 

 

“lantana lantana”, inna harira ta kira ƴar ta da ke yi mata talla don kuwa asmau bata da kan inna harira tace yadda fuskar ta take baƙa haka ma kwakwalwar take sam babu haske a tattare da ita

 

 

 

Asma’u ce ta ɗau fantekar inda lantana ta shige gaba suka tafi tallan haka suke yi kullum ita lantana itace me kan talla amma ban da asma’u

 

 

 

Sai bayan sallah la’asar sannan suka dawo inda suka tarar da inna harira da baƙuwa a zaune a tsakar gida akan tabarma

 

 

 

Ƙwalawa asmau kira tayi ta ƙarasa inda take sannan ta nuna wa matar asmau

 

“hjy kina ganin zatayi, don ni ƴar nan babu abinda take min anan, kullum sai dai taci tayi kashi kan talla babu shi yanzu in ta tashi aure wazai mata kayan ɗaki, ga shegen baƙi kamar kwalta”

 

 

 

Matar da aka kira da hjy ta dubi asmau sannan tace

 

“to ba wai baza tayi ba kamar yadda na faɗa miki abuja ni fa nake kai yara aikatau, wannan kuma kamar yarinya ce”

 

 

“ahap haka kike gani ai wannan in ta kama aiki kamar jaka haka take, reno shara wanki wanke wanke duk ta iya”

 

 

 

Hjyr ta kuma kai duba asmau wacce kan ta yake a ƙasa sannan ita sam bata fahimci inda zancen su ya dosa ba

 

 

“ni dai da waccen ce” ta faɗa tana nuna lantana ƴar inna harira, inna harira sai tayi dariya irin ta basarwan nan

 

 

“haba bazaki so kiɗau wannan ba ai alanƙosa ake ce miki indai lantana ce ba abunda zata iya, yanzu tallan wake da shinkafar da take kai min ma tace zata dena tunda ɗan me gari yace yana sonta shi yasa nake neman hanyar da kuɗi zasu dinga shigo min, ga bikin lantana ban ajiye ba ban ba wani ajiya ba, kuma auren ɗan me gari kashe kuɗi gare” ta faɗa tana ajiyar zuciya

 

 

“to shike nan indai kince wannan ɗin zatayi ai shike nan, amma idan na tafi da ita kuma aka ƙi ɗaukar ta zan dawo miki da ita”

 

 

“na yadda amma kice su fara gwadata tukunna kafin su yanke hukunci da wannan ɗan ƙaramin jikin nata shine yake sawa mutane suna yi mata kallon yarinya ce”

 

 

 

Sukai sallama kan kashegari da asuba zata zo ɗaukar asmau zuwa garin abuja aikatau

 

 

 

***********************

 

 

 

Asmau sunana na kasance ni kaɗai a wajen iyaye na babana ɗan nan garin ne azore wanda yake a ƙaramar hukumar minjibir ta jihar kano,

 

 

 

Garin fulani ne sosai don gida tsilli tsilli zaku dinga gani in kun shigo sannan sai kuma gonar mutum a jikin gidan sa, irin dai ginin fulani, in kaga gida ɗaya sai kayi tafiyar mill kafin kaga wani

 

 

 

Ban san iyaye na ba kasancewar sun rasu, mahaifiyata ta rasu lkcn haihuwar ƙanina, inda aka rasa aka rasa ɗan,

 

 

 

Shi kuma mahaifina sai da na ɗan tasa kaɗan sannan Allah yayi masa rasuwa, sai kulawata ta koma hannun wan mahaifina

 

 

 

Inda yake min rikon sakainar kashi, don kuwa babu ruwan shi da duk wani daya shafe ni duk abinda matar shi zatai min baya cewa komai wannan shine taƙaitaccen tarihi na

 

 

******************

 

 

 

 

Da sassafe hjy ta zo mukai sallama sannan muka kama hanya inda naci karo da wasu ƴammata waɗanda zamu tafi da su, amma duk sun girme ni don ni sai na zama kamar wata ƴar tsana a ciki su

 

 

 

Sai da muka je gezawa sannan muka samu ƙaramar mota inda zata kaimu abuja, haka aka cunkusa mu a motar nan kamar dabbobi inda ita kuma hjyr ta zauna a gaba ita kaɗai

 

 

 

Tafiya ce kamar ta yada shege ba ƙaƙƙautawa sai da muka je kaduna sannan direban ya tsaya muka fito muka ɗan huta, sannan muka kama hanyar abuja

 

 

 

 

Lfy ƙalau muka isa abuja inda muka sauka a kubuwa, anan gidan hjy yake, ɗaki ta bamu guda, tace duk mu sauke kayan mu

 

 

 

 

Ni dai kamar an min duka haka nake ji don kuwa a gajiye nake, kwanciya nayi sai bacci, inda ƴammatan da muka zo da su kowacce take ta buri tare da fatan irin gidan da za a kaita, ni dai tunda na samu bacci ya kwashe ni sai nace saba’ul khairi

 

 

menu of d day

*wake da shinkafa served with local salad & zobo drink*

 

 

wake da shinkafa

 

 

“`ingredients“`

 

“`wake“`

“`shinkafa“`

“`gishiri“`

“`man gyaɗa“`

“`haɗin salad“`

 

 

“`method“`

 

 

1) bayan kin gyara waken ki saki ki wanke ki ɗaura akan wuta, sannan ki bishi da ruwan kanwa (optional)

 

2)sai waken ya dahu, sannan ki ɗauko wankakkiyar shinkafar ki ki zuba ki juya ki saka ɗan gishiri sannan ki rufe

 

 

3) idan ya dahu sai ki sauke ki yi serving da soyayyan man gyaɗa, ko tankwa, da yaji sai kiyi ganishing da salad aci lfy

 

 

*LOCAL SALAD*

 

“`ingredients“`

 

cabbage

lettuce

carrot

cucumber

green pepper

lemun tsami

man gyaɗa

maggi

 

 

“`method“`

 

1) ki wanke lettuce, cabbage, cucumber, green pepper ɗinki, ki barsu su tsane sannan sai ki yanka su irin yankan da kike so

 

 

 

 

2)ki kankare bayan carrot sannan ki wanke shi daga nan sai ki gurza shi

 

 

3) ki ɗauko kayan haɗin da kika yayyanka ki haɗa da carrot sannan ki haɗe su waje ɗaya, ki ɗauko lemun tsami ki ɗiga kaɗan ba dagawa ba yadda dai zai miki sannan ki zuba mai ki zuba maggi ki juya sai ki juye a salad bowl sai ci

 

 

 

 

*zobo drink*

 

“`ingredients“`

 

Ganyen zobo

Citta

Kanunfari

Abarba

Cucumber

Sugar

Flavour

 

 

“`method“`

 

1) ki ɗauko zobo sai ki wanke shi ki zuba masa ruwa ya sha kansa sannan ki ɗaura a wuta, tare da citta, ɓawon abarba, sai dakakken kanunfari ( “`sirrin daka kanunfari shine ƙamshin shi ya fi fitowa idan an daka shi akan a watsa shi haka“`)

 

 

2) idan zobo ya tafasa ya dahu sai ki sauke shi ki juye a babban mazubi yadda zai sha iska, kafin ya huce kuma bari mu haɗa ragowar

 

3) ki fere yanka abarbar da cucumber ki ƙanana yadda dai zasu miki daɗi wajen blending sai ki markaɗa su kina yi kina tacewa kina ƙara markaɗawa har dai a samu yadda ake so

 

4) sai ki ɗauko wannan zobon naki ki tace ki ɗauraye ganyen ki kuma tace wa har sai maa shaa Allah, sannan ki haɗa da ruwan cucumber & abarbar nan

 

 

5) ki zuba sugar, flavour ki zuba a jug a saka shi a fridge yayi sanyi sai shaa

 

 

 

 

 

*ASMA’UN SABIT*

 

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

 

 

 

 

 

ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)

 

 

 

page 2

 

 

 

 

 

 

Kashegari da sassafe aka tashe mu, koko da ƙosai aka bamu, muka karya sannan hjy ta tasa mu a gaba domin neman wa kowa gidan aiki

 

 

 

Muka dinga zagaya gari zuwa gidajen masu hannu da shuni da kuma masu matsakaita ƙarfi ana ajiye mu da ɗai ɗai,

 

 

 

Sai da ya rage mu biyu sannan muka hau mota muka nufi wuse zone 4 kamar yadda naji hjyr tace wa driver taxi ɗin da muka shiga

 

 

 

A ƙofar wani restuarant muna sauka inda muka shiga ciki,

 

 

 

 

Hjy ce ta nuna mana wani ɗan loko wai mu zauna a can kafin ta dawo, kusan minti biyu ta ɗauka sai gata inda ta kira mu muka bi ta cikin gidan

 

 

 

Wata mata ce muka samu tana zaune a saman wata three sitter daga gani itace me wurin

 

“gasu nan kamar yadda na faɗa miki su biyu ne” matar da ke zaune a ɗakin ta gyara ɗan glass ɗin da ke fuskar ta sannan ta kalle mu kamar ta ga wasu kashi ko abun ƙyanƙyami

 

 

 

“me zanyi da waɗannan jariran” ta faɗa a wulaƙance

 

“na faɗa miki indai zaki kawo min ƴar aiki babba nake so amma me zan yi da waɗan nan, gwara ma waccen amma wannan kamar ba a daɗe da yaye ta ba”

 

 

Ta ƙarashe zancen ta idon ta akaina

 

 

“wallahi hjy munnira ƙaramin jiki gareta amma da shekarun ta”

 

 

 

 

Mahawara suka fara yi inda hjyr da ta kawo mu ta fi hjy munnira baki don haka dole hjy munnira ta yadda ta ɗauke mu bayan an sani shara nayi

 

 

 

Sai da suka gama cinikin abinda za a dinga biyan mu a shekara sannan hjy tai sallama da mu, ita kuma hjy munnira ta kira wata laure wai ta tafi da mu ta nuna mana aikin daya dace mu

 

 

 

Can bayan gidan muka je inda anan ake duk wani hada hada na girki, ƙaton kitchen ne, sai kuma wajen wanke wanke sai kuma wasu ɗakuna guda biyu da ke can gefen daga ƙarshen katangar inda anan akace mu ajiye kayan mu

 

 

 

Kowaccen mu aka haɗa ta da aikin daya dace da ita, ni dai kitchen aka kai ni inda wacce muka zo da ita aka kai ta wajen wanke wanke

 

 

 

 

Ina shiga kitchen, naga girman kitchen ɗin, ban taɓa ganin irin wannan kitchen ɗin ba sai yanzu

 

 

 

Girki ake yi kamar ba gobe, tsayawa kawai nayi ina kallon ikon Allah tare da ƙarewa kitchen ɗin kallo,

 

 

 

“ke ya sunan ki” naji wata ta faɗa

 

“asmau” na faɗa a hankali, kallon banza naga ta bini da shi

 

“ke amina waye yace a kawo mana ƴar jaririyar nan kitchen mu da muke aikin wuta” ta faɗa kamar taga kashi

 

 

“hjy ce tace a kawo ta nan” inji wacce aka ƙira da aminar

 

“to sai sa ta tsabtace jikin ta don nan bama gayyata ƙazanta” sim sim sim na fice inda na nemi hanyar da ɗakunan kwana suke

 

 

 

Ƴar jaka ta na ɗauko, sam babu wasu kayan arziƙi don duk kayan da nawan yawancin su ba wanki, wasu kuma a yayyage

 

 

Zama nayi ina kallon ikon Allah, ban jima da zama ba sai ga wata ta shigo

 

“me kike yi a ɗakin nan bayan kowa yana waje yana aiki, kar dai bincike kike mana a kayan mu”

 

 

“wallahi ba haka bane, wanka akace inzo inyi in canza kaya kuma naga kayan nawan duk babu wanki” na faɗa d ido na duk ya kawo ruwa saboda banji daɗi zargin da tai min ba

 

 

Jakar tawa ta zazzage a ƙasa ta fara duba kayan cikin ta, bakin ta a taɓe

 

“kije wajen wanke wanke ki samu ƙananan sabulai ki haɗa ki zo kiyi wanki”

 

Miƙewa nayi na fita, nai mamakin dana ƙarasa wajen wanke wanke na samu sabulai, kamar ba da kuɗi a ka siye su ba, tsinta na fara yi har na haɗa iya wanda nasan zai ishe ni sannan na tafi ɗakin

 

 

Kaya na na ɗiba sannan na je bayan ɗakin inda banɗakin mu yake na wanke kayana tas sannan na shanya

 

 

 

Wanka na shiga da ragowar sabulun na saɓi jikina kamar ba gobe, don a

 

 

 

Don kuwa a azore ban isa in samu wannan damar ba, sai dana gama wanka na sannan na fito

 

 

 

Sai yamma sannan kayana suka bushe na kwashe, a ranar dai ban koma kitchen ba sai kashe gari

 

 

Cikin hukuncin Allah na fara aiki a kitchen amma ba abinda nake yi sai aike, dauko wannan ɗauko wancen haka dai

 

 

 

Kafin ka ce me wannan har na zama ƴar gidan, na son komai na kitchen, sannan na san inda ake ajiye komai

 

 

Gidan cin abincin hjy munnira gidane da a kullum a ke dafa kusan buhu biyu na shinkafa da ta tuwo

 

 

Babu irin variety na abincin da ba a yi, waina sinasir, alkubus fankaso, ta ɓangaren shinkafa ma

 

 

Jollof rice fried rice, duk dai wasu sunfari na dafa abinci ana yi, ba wai duka a ke ci anan ba, akwai waɗanda ake fita da su,

 

 

Don kuwa akwai certain hotels ɗin da suke zuwa suna yin order abinci anan gidan, ga kuma costomers da suke zuwa suna siya su tafi da shi

 

 

 

Ga waɗanda suke siya su ci anan, akwai wasu mutane ma da ake musu abincin gidajrn su anan, kullum akwai abincin da za a dafa na certain gida akai masa

 

 

 

Nakan yi mamaki amma dana ji cewar yawanci gidanjen ministers ne da house of reps da senators ake kai musu waɗanan abincin saboda mutanen da suke tarawa sai na daina mamaki duk da dai ban san ko su waye ba

 

 

 

don haka aiki a gidan nan in aka tashi tun safe sai mukai ƙarfe 10 :00pm bamu gama ba

 

 

Amma kuma mu girki ne kawai akwai ƴan wanke wanke, akwai kuma ƴan service, akwai masu kaiwa gidaje, group group ne kowa da group ɗin sa kuma kowa ya san aikin sa

 

 

 

******************

 

 

 

*b̫a̫y̫a̫n̫ s̫h̫e̫k̫a̫r̫a̫ b̫i̫y̫u̫*

 

 

 

 

Na zama ƴar gida yanzu don kuwa ba abinda bana shiga ayi da ni ta ɓangaren girki,

 

 

A lokcn ne hjy munnira ta ƙara buɗa restuarant ɗinta inda yanzu babu abinda ba a yi, snacks ne ɗrinks ne, duk daia abinda kake so idan ka zo restuarant ɗin mu,

 

 

Kuma kullum cikin hukuncin Allah ƙara samun costomers muke yi, yanzu ba a shakkar bani girki ko ya yake don kuwa a gaskiya na iya

 

 

 

Kasancewar ni ce ƙarama a kitchen yasa kowa sai kaji yace asmau don Allah juya min kaza, kwashe kaza, wannan ne ya sa ni ko wane ɓangare na kitchen ina shiga

 

 

Ba kamar cooks ɗin kitchen ɗin ba, yadda in a ɓangaren sarrafa shinkafa kake to ana zaka zauna, in a ɓangaren snacks kake to anan zaka zauna, haka ma in a ɓangare drinks kake ko miya ko salad ko wani abu na kitchen

 

 

 

Ma’aikatan a rarrabe suke kowa yasan aikinsa, amma banda ni, ni ina kowane ɓangare kuma duk inda naje sai na tabbatar da cewar na koyi abunda suke

 

 

Wannan ne yasa a kitchen ɗin nai fice tunda komai aka bani zan iya kuma zan yi shi kamar ba ƴar ƙaramar yarinya ce tayi ba

 

 

 

*****************

 

 

Sabit yana zaune a office ɗinsa cikin fararen yadinsa waɗanda kana kallon su kasan ba ƙananan kuɗi aka sa wajen siyan su ba, wayace a hannunsa yana ta danna wa

 

 

Tun ɗazu yake kiran ta amma bata ɗauka ba, tsaki ya ja tare da ajiye wayar

 

“wallahi sam banga amfanin wayar mata ba ace mutum sai yai ta kiran ki a waya amma wai bakya kusa da wayar” be gama mitar sa ba sai wayar tashi ta fara ringing

 

 

Tune ɗin daya saka mata kenan don haka wayar tana fara ringing ya gane ita ce, idon shi ya kai kan screen ɗin wayar inda aka rubutu *only u*

 

 

Ɗan tsaki ya kuma sannan ya ɗauka a yangance kamar wani mace

 

” *SD* don Allah kayi haƙuri wallahi ina sallah ne ka kira” duban shi ya kai kan agogon bangon ɗakin inda ya ƙarfe 03 :15pm

 

 

*only u sallah me kike yanzu kar dai kice min azahar”

 

” wallahi *SD* na shiga meeting ne shiyasa ban samu nayi sallah akan kari ba, ya kake ”

 

 

“amma meeting sai ya hana ki sallah wai sai yaushe zaki san mahimman cin sallah haba only yanzu haka zamu yi aure ki dinga nuna wa yaran mu, yanzu lkcn sallah bazaiyi ba a bar abinda ake yi a tafi ai sallah ba”

 

” *SD* kasan matsalar bank fa su koman su a ka’idance yake kar ka damu in shaa Allah tarbiyya me kyau zan muyi wa ƴaƴan mu, kaji”

 

 

Ta shiga kalailaye shi da kalaman da tasan suna kwantar masa da hankali kafin kace meye wannan har sun koma kamar ba abinda ya faru,

 

 

 

Sai da suka gama shan soyayyar su sannan sukai sallama akan zai zo da daddare, daga nan sukai sallama kowannen su zuciyar su tana alfahari da kuma ƙaunar junan su

 

 

 

 

Menu of d day*

 

Veg cous cous with kidney sauce`

 

 

“`ingredients“`

 

_Cous cous_

_Butter_

_Cabbage_

_Peas_

_Carrot_

_Canned sweet corn_

 

 

“`recipe“`

 

1) ki wanke carrot ki yanka shi size ɗin da kike so, sai ki wanke peas sai ki haɗa su ki tafasa su da ɗan gishiri, tafasa ɗaya sai ki sauke ki wanke su da ruwan pampo wannan wankewar zai sa su suyi shar kuma su rike kalar su sai ki ajiye a gefe

 

 

2) a wanke cabbage a yanka sannan a ajiye shi aside, sweet corn ɗin shima a tsane ruwan shi a ajiye shi gefe

 

 

3) ki ɗaura ruwan zafi, idan ya tafasa, sai ki ɗauko cous cous ɗinki a cikin bowl, sai ki ɗan zuba masa dan ruwan zafin, ba dayawa ba ya ɗan sha, *a zuba yadda bazai yi wa cous cous yawa ba* sai ki ɗan bari ruwan ya tsotse

 

4) ragowar ruwan daya ke tasafa a kan wuta sai ki saka colander “`(in babu colander zaki iya yin na buhu amma a tabbatar da buhun be taɓa ruwan ba)“`a kan sa, sannan ki kawo jiƙaƙƙen cous cous ɗin ki, ki zuba, ki kawo kayan peas da carrot ki zuba ki rufe ya turara

 

 

5) idan ya ɗanyi wani lkc kika buɗe kika ya dahu sai ki sauke, ki juye cous cous ɗin a wata roba, ki zuba melted butter, da sweet corn da kuma cabbage sannan a juya a zuba a food flask

~bon appétit~

 

 

“`kidney sauce“`

 

 

“`ingredients“`

 

_Kidney_

_Attaruhu_

_Albasa_

_Maggi_

_Man gyaɗa_

_Tomato paste_

_Curry_

_thyme_

 

 

“`recipe“`

 

1) a wanke kidney a cire tsakiyar nan don kuwa wataran har tsakuwa ake gani

 

 

2)sannan sai ki tafasa ta da albasa da maggi da thyme, idan ya tafasa sai ki tsame ta a gefe

 

 

3) a grating attaruhu da albasa, ki saka man gyada kaɗan a tukunyar ki sai ki dan bishi da albasa da tafarnuwa, idan man ya ɗau zafi sai ki zuba attaruhun ki da albasa a barshi ya soyu

 

 

4) idan ya ɗauko soyuwa sai ki ɗauko kidney ɗin nan ki saka ki ƙara maggi, tomato paste sannan ki sa curry sai ki rage wuta ki bar shi ya ƙarasa

 

👩🏽‍🍳 “`bon appétit“`👩🏽‍🍳

 

*ASMA’UN SABIT*

 

 

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

 

(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)

 

 

 

 

 

 

ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)

 

 

 

P⃗a⃗g⃗e⃗ 3🌹

 

 

 

 

 

 

Badia ƴa ce a wajen alh hamza da matar sa hjy bilki, dukkan su ma’aikatan banki ne, inda alh hamza yake aiki a *CBN* ita kuma hjy bilki take aiki a zenith bank

 

 

Ƴaƴan su uku mata biyu sai namiji 1 hauwa ita ce babbar ƴar su dr. ce a asibitin general hospital dake abuja tana da aure da ƴaƴa biyu

 

 

Sai badia wacce a yanzu take aiki a zenith bank amma ba branch ɗin su ɗaya da mmn ta ba, sai ɗan autan su nura wanda yake karatu har yanzu a china

 

 

 

Rayuwar gidan su badia irin rayuwa ce ta western style babu ruwan iyaye da matsawa ƴaƴan su duk abinda kayi dai dai don haka rayuwa ake yi ba kwaɓa balle harara

 

 

 

Yo ina ma suka ga iyayen nasun balle su kwaɓe su in suna ba daidai ba, kuma cikin hukuncin Allah sai ya shirya musu ƴaƴan babu me abin ashsha masu zuciyar samun na kansu ne amma batu addini sai a slow

 

 

 

Badia sun haɗu da sabit ne lkcn da ya zo bank ɗin su bayan ya samu matsala da master card ɗinsa sai ya kasance badia ce ta gyara masa matsalar

 

 

 

Badia irin dogwayen matan ne masu ƙirar coca cola, fara ce amma duk da farin ta hakan bai hanata shafa man da zai ƙara mata haske ba, Allah yayi da son gayu, don haka take da manema dayawa, gayun ta da kyan ta da kuma iya ɗaukar wankan ta yasa take taƙama da kanta

 

 

 

Tunda ta ɗaura idon ta akan sabit taga gaskiya wannan yayi mata don haka sai tai tayi masa salo salo daban daban ko zai taya, amma ga mamakin ta sai taga kamar ma tana yi da dutse ne

 

 

 

Don haka sai ta kau da ƴar kunyar nan tamu ta mata tace masa suyi exchanging contact incase ko wani matsalar zai kuma tasowa ba sai ya sha wahalar zuwa bank ba

 

 

 

Sabit be kawo komai ba don haka sai ya yadda da abinda tace, ko bayan da to koma gida ta ɗauka zai kira ta amma sai taji shiru, kwana da kwanaki kullum jiran call ɗin sa take amma shiru

 

 

 

Rannan sai ta kira shi inda ga mamakin ta wai yama manta da ita, sam bata ji daɗin yadda yai mata ba amma kuma sai ta ɗau ƙudurin in shaa Allah daga lkcn ba zai kuma cewa ya manta da ita ba

 

 

 

daga lkcn ta zama me kiran shi, tun yana basarwa har yazo yana ɗan dauka har kuma cikin hukuncin Allah suka fara soyayya har gashi suna shirin gabatar da junan su ga gabatan su don a tabbatar da soyayya su,

 

 

 

******************

 

 

 

Sabit ɗa ne na huɗu kuma ɗan auta a wajen hjy fatima da kuma alh bashir, mahaifiyar shi shuwa ce mace me kyau da kwarjini ga ƙaunar ƴaƴan ta, ita bata damu ba ko zata ɓatawa kowa indai hakan zai farantawa ƴaƴan ta wannan soyayyar da ƙaunar da take wa ƴaƴan natan ne ma har yasa ta sa mijinta ya gina wa kowanne daga cikin ƴaƴan natan ɓangaren shi a cikin tafkeken gidan da suke,

 

 

 

Sannan ƙwararriya ce wajen haɗa sanwa, idan ta shiga kitchen ta haɗa dinner sai mutum ya manta sunan sa saboda tsabar daɗi da kuma tsari, wannan ne ya sa ta sha alwashin duk ɗan ta daya yi aure matar bata iya girki ba sai ya ƙara kuma a hakan ake har yanzu

 

 

 

Alh bashir mutumin adamawa ne fulani ne fari kyakkyawa da shi, wannan kyan na bayin Allahn nan yasa idan kaga ƴaƴan su sai ka saki baki barin ma ace sabit wanda kamar su da hjy fatee har ya ɓaci, don haka duk cikin ƴaƴan su ya fi su fari da kyau

 

 

 

Ƴaƴan su huɗu isma’il shine babba, likita ne matan sa biyu, ta farkon auren soyayya ne, amma matar bata iya girki ba don haka sai ta saka shi ƙara aure inda ita ma ta biyu ya kasance da babu ce hausawa suka ce gwanda ba daɗi

 

 

 

Wannan yasa har yanzu isma’il a ɓangaren iyayen shi yake cin abinci, na biyun su shine sulaiman shi ma matan sa biyu duk babu gwanda wajen girki sai na uku mansur wanda shima matan nasa biyun amma su da ɗan sauki sauƙi

 

 

 

Sai auta sabit wanda ake ta shirye shiyen auren sa tooo shin badia ta girki kuwa bari dai mu bisu mu ji ita kuma ya nata yake

 

 

 

********************

 

 

 

 

Sai ƙarfe 06 :30pm na yanna sanna ya shigo gida duk saurin sa na dawo wa gida da wuri don ya samu ya shirya ya tafi wajen badia amma hakan bai samu ba

 

 

Wanka kawai ya shiga yana cikin wankan ne ma yaji wayar shi na ringing ko be gani ba yasan badia ce don ringing ɗin daya saka mata ne

 

 

 

Hankalin sa akwance ya ƙarasa wankan sa ya fito, yana fitowa wayar tana kuma shigo wa, towel ɗin da ke hannun sa ya ajiye sannan ya ɗau wayar

 

” *SD* sai yaushe zaka zo tun 05:00pm nake jiran ka amma shiru kamar bazaka zo ba”

 

 

“only yi haƙuri wallahi aiki ya tsare ni a office, more over ina son mu haɗu da alh ku don ina son jin yadda za a tsara wannan lamarin don na ƙagu in ganki a gidana”

 

 

Ɗan dariya tayi irin na nuna jin daɗi sannan tace masa

 

“kamar kasan kuwa ya dawo shima, bari in gaya masa kana son ganin sa don kar ya fice”

 

“dats my only shiyasa nake son ki, kuma nake ce miki only don daga ke ba ƙari” ya faɗa hankalin shi a kwance don shi mutum ne da baya son tarkacen mata

 

 

Tayi bala’in jin daɗin wannan maganar tasan wanda har ta kasa ɓoye murnar ta ta fara zuba masa shagwaɓa

 

 

inda shi kuma wannan abun nata na bala’in birge shi yana bala’in son yaga mace ta iya shagwaɓa, haba me zakayi da macen da babu wani sanyi a tattare da ita, shi ya fi son mace faran faran wacce kullum zaka ganta very lively sannan wacce ta iya shagwaɓa

 

 

Ta kasance fara doguwa kyakkyawa duk wannan abun daya ke nema a mace ya same shi a badia shi yasa yake tunanin daga ita babu ƙari, haba gashi fari kyakkyawa ai sai fara me kyau inji sabit

 

 

 

Sauri yai ya ƙarasa shiryawa inda ya shiga masallacin gidan su yayi sallah magariba daga nan ya wuce gidan sahibar tasan

 

 

A ƙofar gidan su ya faka motar sa sannan ya kira ta, tana zaune a gaban dressing mirrow ta gama tsara kwalliyar ta irin yadda sabit yake so taji call ɗinsa

 

 

Ɗauka tayi a yangance sannan cikin shagwaɓa tayi masa magana

 

” *SD* sai yanzu ka zo duk na bushe kwalliyar da nai maka duk ta goge” ta faɗa kamar gaske, wannan maganar tata har cikin ranshi ya ji ta yadda ta kashe muryar ta sannan cike da shagwaɓa

 

“awa nawa kike ki sake min wata zan iya jira a waje”

 

“wasa nake maka bari insa a shigo da kai”

 

“ok ” ya amsa tare da maida wayar aljihun sa sannan ya tsaya gana jiran ai masa iso zuwa cikin gidan, bai daɗe ba sai ga me aikin su ta fito inda ya bita har farfajiyar gidan inda suka saba taɗi ya samu wuri akan ɗaya daga cikin fararen kujerun da suke wajen ya zauna

 

 

 

Ko da ta gama kwalliyar tata da fesa duk wasu turakan da ta san masu ƙamshi ne sai ta ɗauko hijab ta saka, tana ta mita a ranta

 

 

Ita ta rasa irin sabit, duk irin kwalliyar da tayi sai dai yace tabi kwalliyar da hijab, sannan kuma ya hana su taɗi a ckkin sitting room sai dai a waje yacce duk wanda zai shigo ko zai fita sai ya gansu, wallahi daba dan san da take masa ba da tuni sun rabu don wani lkcn abin nashi kamar ɗan ƙauye haka yake yi ba wayewa ta faɗa tana fita wajen sa

 

 

 

 

👩🏽‍🍳 *menu of d day*👩🏽‍🍳

 

 

 

“`Alala“`

 

 

 

 

Ingredients

 

 

_Wake

Kwai

Hanta

Dankali

Alayyahu

Oil

Maggi

curry

Attarugu,

albasa

Leda

 

 

“`method“`

 

 

 

1) surfa waken ki saiki wanke shi sosai kisa attarugu , albasa da ki kaishi inji a Markado miki

 

 

2) ki wanke hantar ki ki dafa ta da albasa,maggi thyme idan ta dahu saiki sauke ki aje gefe

 

 

3)ki fere dankalin turawanki ki yanka shi cubes ƙanana, sai ki yanka dafaffan ƙwan ki shima ƙanana, alayyahu a fara wanke shi sannan shima a yanka shi sannan a ajiye

 

4) sannan sai ki ɗauko markaden ki saiki dauko mai ki zuba aciki kisa maggi da curry ki kara ruwa in ƙullun yayi kauri amma ruwan da kika tafasa hantarki kikara yanka albasa ki buga kullon ki ɗauko hantar ki da ƙwan ki, da dan kalin da alayyahu kixuba ki ƙara bugawa, sai ki ɗan ɗana, idan komai yayi sai ki saka cray fish (niƙaƙƙe amma optional ne)

 

 

 

5) sannan kije ki ɗora tukunyar akan wuta kisa ruwa bayan ki ɗora saiki zo kina ɗiban ƙullun kina sawa aleda kina ƙullawa kina sawa cikin ruwan zafin nan har ki gama ki rufe har ta dahu saiki sauke .

 

 

*Minced meat sauce*

 

 

Niƙaƙƙen nama

Attarugu

Oil

Green papper

Maggi

Albasa

Tafarnuwa

 

 

 

“`method“`

1) ki ɗauko frying pan sai ki zuba ɗan man ki ki saka masa albasa kaɗan idan ya ɗan yi zafi sai ki zuba niƙaƙƙen naman ki sannan ki ƙara zuba albasa, tafarnuwa maggi sai ki ta juyawa har sai ya koma brown, ba a ɗauke masa hannu don sai ya ƙone

 

 

 

2) idan naman ya koma brown sai a ɗan zuba ruwa a rufe ya dahu, ruwan kadan ba dayawa

 

 

3) idan naman ya tsotse ruwan sai a zuba niƙaƙƙen attaruhu, da albasa curry sannan sai a rage masa wuta har ya soyu, shima a dinga juyawa don kar ya kone

 

Sai aci da alalan

 

 

 

 

*Pineapple drink*

 

madara

sugar

abarba

flavour

 

1)ki fere abarbar ki ki markaɗa a blender sai ki tace saboda ba duka bane suke markaɗuwa ba

 

 

Sannan sai ki ƙara mayar da wadanda basu markaɗu ba ki ƙara markaɗawa suma ki tace ki ci gaba da markaɗawa har dai ki samu yadda kike so

 

2) ki juye a cikin roba mai kyau sai ki ɗauko wannan madarah ki juye a cikin wannan ruwan abarbar ki zuba sugar (amma nafi gane in dan tasafa sugar da ɗan ruwa idan ya narke sai ki sauke ki barshi ya huce) kisa flavour

 

3) a juye a jug a saka a fridge don ya yi sanyi sai sha

Add Comment

Click here to post a comment